Sashe 14
Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*********
Tunda ta fara bashi magani ta daina kunna Masa karatun alkurani kamar yadda aka umarceta akan ta daina saboda a cewar gimbiya aljanu ke basa wahala idan ansa Masa karatun alkurani,yau ce Rana ta farko tun vayan fara basa magani taga jikin nasa babu Dadi ciwon nasa naso ya tasar Masa ta Ciro MP3 din daga Jakarta ta rike a hannunta tana kallonsa...
"Ya zainul Naga kamar kanajin wani Abu a jikinka,tamkar bakajin Dadi ciwonka zai tashi ko?"
Gyada Mata Kai yayi zufa na karyo Masa "hakan nakeji a jikina ummaty yanzun haka Babu abinda nakeyi kamar faduwar gaba Dan nasan irin wahalar da nakesha idan ciwon Nan ya tasar mun ga kafafuwana da suka sirance kamar ba nawa ba ummaty halittata gabaki daya ta canja kamar ba jinsin Dan Adam ba"...tausayinsa ne ya lullube ilahirin jikinta batai aune ba taji saukar hawaye daga idanuwanta ,tasa hannu ta share sanan wata zuciyar ta umarceta da ta kunna Masa alkurani tagani ko zai kori aljanun yanzun Koda zasu dawo daga baya dai ta koresu dikda gimbiya tayi Mata gargadi da hakan gabanta na tsananin faduwar makomar abinda zai faru kawai ta Saida Rai ta kunna karatun alkuranin ta makala Masa a kunne kirjinta na dukam uku uku...
Minti minti takan kallesa taga yanayin nasa sai taga idanuwansa a lumshe zufa na karyowa ta ko Ina a jikinsa,muguwar zaune tayi Tana Kiran makomarta.. shiru shiru kusan minti goma Sha biyar Babu wani abun da ya faru sai ma gani da tayi tamkar yasamu sauki Akan shudewar mintuna dazun ta sauke ajiyar zuciya ta cire Masa daga kunnensa ta dubesa fuskarta dauke da damuwa "ya kakeji yanzun ya zainul?"
"Alhamdulillahi ummaty banajin komi,jikina ya dainamun abinda yakemun dazun saidai rashin karfi kawai da bani dashi Kuma inaji tamkar Zanyi bacci"...murmushi ya subuce Mata a fuska "alhamdulillahi"tace a fili Koda aljanun zasu dawo zata cigaba da bashi magungunan ta gani sanan ta rinka gwadawa da karatun alkuranin Koda a boye ne....irin kallon da yakeyi Mata idanuwansa na rufewa yasa ta rufe fuskarta da tafin hannuwanta "ya zainul kayi bacci sai kallona kakeyi"
"Baki so Ina kallonki ne ummaty?idan kallon naki yanasamun farin ciki fa?"
"Toh shikenan ka cigaba"...sai kawai ya lumshe idanuwansa Yana ayyanowa Kansa abubuwa da dama...Babu abinda ke tada Masa da hankali irin idam ya tuna yadda zai rayu Nan gaba idan ummaty tayi aure tasamu miji,ya rabu da farin cikina harabada Dan gabaki daya ya Gama yanke hukuncin bashida sauran farin ciki a rayuwarsa sai ummaty,yasani ya saka Kansa a cikin tsaka Mai wuya Dan ta Gama kamuwa da soyayyar yarinyar wadda yanada tabbacin harabada bazai sameta a matsayin Mata ba a matsayinsa na nakasasshe Wanda ke kwance saidai a kwantar saidai a tayar...wasu hawayene masu zafi sukebin gefen fuskarsa Yana kwance kan gadon idanuwansa a rufe tamkar Mai bacci....
********
Bayan ta idar da sallar magriba tana zaune ta janyo Jakarta tana Shirin Ciro littafin adduointa gorar ruwan magani ta Fado daidai Nan sarkin dawaki ya shigo cikin dakin nata,bai lura da abinda takeyi ba hankalinsa na kan radiyon innarta daya shigo dauka ita Kam tsare gorar maganin tayi da idanuwa tamkar Mai nazarin wani Abu...hannunta tasa gefen kunnenta ta sama alamar tanason tunoda wani Abu dangane da wanan gorar magani....tamkar ta taba ganinta a wajen babanta?Basu da banbanci da wadda ta taba gani ta bude gorar ta sunsuna ta har kamshin maganin irin wancen nne?to ya haka Anya Kai gaskiya ba iri daya bane...ta kafe akan kallon gorar akan lallai tanason gano wani Abu a hakan mahaifinta ya juyo ya Kira sunanta "ummaty"shiru Bata amsa ba ya sake kiranta Bata amsaba hankalinta ya tafi yayi saurin juyowa Dan ganin me takeyi haka Bata amsa kiransa ba kawai sai yaga idonta kirrr akan gorar magani....
. *SLIMZY😍*
[1/23, 10:41 AM] 😍SLIMZY😍: *13*
Wani irin faduwar gaba ya tsinci Kansa ciki lokacin da yayi tozali da gorar ruwan maganin da ummaty ta kafe da Ido lokaci daya yayi saurin dago Kansa daidai Nan idanuwansa da nata suka hadu ganin fuskarta da alamun magana ya sanyasa mummunan faduwar gaba da saurin kauda idonsa kirjinsa na tsananta faduwa..."baba barka da dawowa"
"Barkanki dai ummaty,karatun aketatayi ne?injidai kinci abinci?Kuma ba tuwo innarki tayiba"dik a rude yayi maganar Dan ya kauda zatonsa na wurgo Masa tambaya da yake ganin kamar tanada niyyar yi dikda besan irin tambayar ba sanan baisan daga inda tasamu gorar ruwan maganin ba a iya saninsa tunda ya Bata maganin na karshe har yau gimbiya Bata Kara nemansa Dan ya Bata magani tabawa zainul abideen ba...zuciyarsa ta Dade tana zarginta da abubuwa da dama sai yau ya tabbatar da zargin da yakeyi akan gimbiya rumana,wato taje ta bayan gida ta hada Kai da yarinyar Tai Mata wayau tana bashi maganin nakasa Bata sani ba?Kai gimbiya rumana shedaniyar gaske ce tabbas ta saka yarsa a tsaka me wuya dakyar ya iya gyara zamansa akan daddumar ya zurfafa cikin tunani ummaty nata zuba Masa Hira be ma San me take cewa ba sai tsinkayar muryarta yayi da karfi tana fadin "baba meke damunka ne Wai?inata maka magana kayi shiru"Tai maganar kamar zatayi kuka
"Yi hakuri Yar baba kada kiyi kuka dik banji me kike cewa ba hankalina ya na kan wanan labaran na radiyo da nake saurare me kikeso ne Yar baba"ta tunzuro Baki gaba cike da shagwaba ya Shiga lallashinta Yana dauke Mata hankali da labari har ta soma Jin barci....
********
Kwance yake kan gadonsa yayi shiru Yana tunani ya rasa yadda akayi hankalinsa gabaki daya ya koma kan yarinyar da bashi da tabbacin samunta,shin Yaya zaayi yayi aure Yana cikin wanan halin da bashida wani amfani ga ya mace,dik nacinsa dik soyayyarsa da ummaty bazai taba aurenta ba Dan ba Abu bane me yuwuwa yanajin matukar ciwon kasancewarsa cikin wanan nakasar a rayuwa Amma ya gode Allah wani ma ya fishi Jin jiki...runtse idanuwansa yayi ya bude su itace take Masa yawo a kwayar idanuwanta murmushinta,shagwabarta da kukanta komi nata burgesa yakeyi ya Gama yadda da cewa son yarinyar yakeyi dikda besan meneneso ba tun bayan tashinsa har zuwa yanzun yake kwance a nakashe.....babban abinda yake Masa yawo a Rai be wuce yadda yarinyar ke wahala dashi ba harta magani ita ke Nemo Masa Wanda iyayensa suka kasa nema Masa magani a cewarsu ciwonsa na asibiti ne bakin ciki ne ya lullubesa ya Shiga kada kansa,...daidai Nan aka turo kofar dakin hade da sallama Koda cikin duhu yake wanan kamshin na mahaifiyarsa ne Wanda ya banbanta Dana kowa a cikin wanan masarautar
"Zainul bakayi bacciba" Tai maganar tana neman wajen Zama a gefen gadon ta zauna ta kamo hannnunsa..
Murmushi ya sauke Wanda iya Kansa fuskarsa yace "ammiey banyi bacci ba banajin bacci tunani kawai nakeyi"...shiru tayi Tana Kare Masa kallo "zainul tunani Kuma?tunanin me kakeyi da har zai hanaka bacci kana kallon yadda kake"Tai maganar cike da damuwa tare da maida hankalinta sosai ga Dan nata tana murza hannnunsa tana jiran Karin bayani,...dakyar ya iya motsa labbansa ya soma magana a hankali "ammiey tunanin ummaty nakeyi"shi Kansa besan lokacin da wanan maganar ta fito bakinsa ba Wanda take yayi shiru kamar an dauke wuta,da sauri ta dubesa cike da mamaki da al'ajabi "ummaty Kuma zainul kake tunaninta?Akan me kake tunanin nata"Ta jeho Masa tambaya a Karo na biyu,Mai makon ya Bata amsa sai kawai ya lumshe idanuwansa fuskarsa dauke da murmushi yayi shiru..."kayi shiru zainul"...Nan ma bai tanka Mata ba shirun dai yayi idanuwansa Kuma a bude suke ba bacci yakeyi ba,mamakine da al'ajabi suka lullube gimbiya bilkisu tabbas tasan watan watarana sai hakan tafaru idan hakan ne kuwa to Dan nata ya fada tsaka Mai wuya Dan Babu yadda zaayi ummaty ta auresa Yana cikin wanan halin ko ba ma hakan ba Mai martaba bazai taba yarda ya aura Masa yarda ba jinin sarauta ba....biri yayi Kama da mutum,wato shiyasa yake tada hankalinsa idan har batazo ba,ko Kuma idan tazo ta tafi yayita kunci Babu walwala saidai yayi shiru?Koda Yan uwansa ne sukazo Masa Hira baya kula su?...lallai zainul ya daukowa Kansa abinda bazai taba yuwuwa ba Dan soyayyarsa da ummaty ba zata taba yuwuwa ba gara ma ya cireta a ransa ya duba halin da yake ciki...tunani sosai ta fada hade da tausayin Dan nata tana Nan zaune batasan bacci yayi gaba dashi ba sai da ta juyo da niyyar Masa magana taga idanuwansa a rufe yana sauke numfashi a hankali...hannu tasa ta shafa Kansa zuwa fuskarsa ta Dade tana kallonsa sanan ta tofesa da adduoi ta lullubesa ta rufesa ta fice dakin..
********
"Ummaty Naga kamar ana samun ci gaba Akan magungunan Nan da muke amsowa koh?"Tai maganar tana murmushi
Gaban ummaty ya tsananta faduwa lokaci daya ta tuna da irin wahalar da yakesha da zarar ta bashi maganin Nan sanan ta lura dik lokacin da zaisha maganin ciwonsa yafi tashi Mai tsanani shin me hakan ke nufi?Koda yake ance idan mutum yasamu maganin waraka sai ciwo gabaki daya ya tashi sanan lokaci daya Kuma sai Allah ya kawo warakarsa saita sauki numfashi murya na rawa tace"ehh to anasamun sauki ranki ya Dade Amma idan yasha maganin ciwonsa yafi tashi sosai"
"Dagani har ke sai munyi hakuri zamu samu nasara Akan abinda Mukasa gaba domin Mai maganin ya sanarmun da irin aljanun dake tare dashi wuyar magani ne Dasu da zarar anyi magani sai sufara tashi suna wahal da mutum Amma idan aka daure aka cigaba da maganin da kansu zasu gudu,Dan haka ki kwantar da hankalinki Allah dai ya bamu nasara ga wanan"ta dauko gorar ruwan maganin kamar ko yaushe yau kamar ma rubutu ne da tsaki tsaki ciki ta Dade tana karewa gorar kallo zuciyarta na bugawa lokaci lokaci tanason tuno inda tasan gorar ruwan maganin Nan Wanda Basu da banbanci Amma hakan ya faskara hakanan ta amshi gorar Tai sallama da ita ta fice
Murmushin nasara gimbiya tayi tace a fili "ta yaro kyau take Bata karko,da sannu zan cimma bukatata Akan ko wani shege a cikin wanan masarautar"....ta janyo wayarta tana Mai dialing wata number tana murmushi...
*WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN 08166177830 KO 07084161619*