Sashe 13
Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*KADA KU MANTA WANAN LITTAFIN NA KUDI NE KUMA YAU SHINE LAST DA* *ZANYI POSTIN FREE PAGE, GA MAI BUKATA* *GA NUMBERS NAN ASAMA YA NEMI KARIN BAYANI NAIRA* *DARI BIYU CE KACAL INA MAI TABBATAR MUKU* *BAZAKUYI* *DANASANIN SIYA* *BA,*
2073065733
*Shaawa ibrahim*
*UBA bank*
*Tura shaidar biyanka ta* *wanan number* 08161306299
601911117 *keystone* **bank Amina jibril* *
*Shaidar biyanka ga wanan* *number** 08166177830
*Ga masu tura Katin waya MTN ake bukata zuwaga wanan number 08039424298 shaidar tura Kati ga wanan* *number 07084161619....*
*SLIMZY😍*
[1/23, 10:40 AM] 😍SLIMZY😍: *HASKE WRITERS* *ASSO...*💡
💞 *ZAINUL ABIDEEN💞*
*SLIMZY✍🏼*
*Wattpad@slimzy33*
*Assalamualaikum zuwa ga masoyana Ina muku fatan alheri,wanan book din na zainul abideen na* *kudi ne Wanda ke bukata dari biyu ne kacal ka nemi* *wanan numbers* 08166177830 *ko* 07084161619 *....SLIMZY* ✍🏼
*12*
"Ya zainul inaso kabani hadin Kai sosai wajen Shan maganin Nan domin inada yakinin zakasamu lafiya cikin kankanin lokaci"ta kafesa da Ido Babu alamar Wasa a fuskarta yadda Tai maganar kadai zaka fahimci maganin nada tsananin muhimmanci,...kallo kawai yake bin ta dashi yadda Tai maganar Yana Kuma bin gorar maganin da kallo zuciyarsa na ayyana Masa Anya zaisamu lafiya kuwa?wanan magani ummaty ta dauki lokaci tana bashi irinsa tunda yasan maganin gorar kanta da ake basa maganin da ita itace dai baa canjawa shin yaushene zaisamu wanan lafiyar da ake Kira Masa zai samu zai samu?...Sarai ta fahimci tunani yakeyi sai ta hura Masa Isa a idanuwansa "lafiya dai Naga kana kallon gorar maganin kodai bakaso ka Sha ne ka gaji?"
Girgiza Mata Kai kawai yayi Yana sauke ajiyar zuciya "gani nayi ummaty mundauki tsawon lokaci kina wahala akaina batare Dana warke ba,sanan Baki taba gajiyawa ba kullum cikin yimun hidima kikeyi,shine nake tunanin Niko da wani irin Abu zan saka Miki dashi wanan dawainiya da kikeyi tawa Koda yaushe babu dare Babu Rana?"
Wani kyataccen murmushi tayi Wanda ita kanta batasan tayishi ba,ba karamin kyau tayi Masa ba Wanda yasa Masa Jin wani Abu ya tsarga Masa daga kwakwalwarsa zuwa zuciyarsa take abinda ke aika sakwanni na jikinsa ya Shiga aikawa dik wata hanya da jinin jikinsa ke yawo ya gawraya gabaki daya...zuciyarsa ta Shiga bugawa sauri da sauri Wanda besan dalilinsa na hakan ba...ya shagala da kallonta ya manta a wace duniyar ya tsinci Kansa sai muryarta ya tsinkayo tana fadin "haba ya zainul,bantaba tunanin Nan gaba idan ka warke zanji inaso ka sakamun da wani Abu ba dangane da taimakon da nayi maka nayishi ne kawai Dan Allah "yadda take motsa bakinta ba karamin burgesa tayi ba siraran lips dinta bakake wadanda suka Dace da doguwar fuskarta Mai dauke da manyan idanuwa shanyayyu masu Kama da me jin bacci...shagwabe fuska ta karayi "yaayah Wai lafiya nake ganin wasu canje canje a tattare dakai meyafaru ne"
Murmushin karfin Hali yayi yanajin wani Abu na taso Masa tun bayan daya shanye maganin data kawo Masa "me kika gani ummaty?"ya tsareta da idanuwansa..."nifa sai Inga Kanata kallo na kamar zaka hadiye ni"ta turo Baki. "Da inada damar hadiyeki Dana hadiyeki ummaty a yadda nakejin bakon lamari tattare Dani a Yan kwanakin Nan banida wani aikinyi Banda tunaninki ummaty da zarar kika tafi kika barni,wasu lokutan har gizo fuskarki takeyi sai Inga kamar kina kusa Dani"ya karasa maganar hade da cije lebensa Yana lumshe idanuwansa... Kallonsa sosai tayi "yaayah kodai wani Abu Yana damunka ne?"Tai maganar dauke da damuwa a fuskarta tamkar me Shirin yin kuka
"Babukomi ummaty mekika gani?"
Ta shagwabe fuska "nidai nidai Naga kamar bakada lafiya kuma kaki fadamin yaayah haba?"...dariyar karfin Hali ya karayi batare da yace komiba yanajin wani Abu nayi Masa yawo a sassan jikinsa tamkar Wanda shocking ke shigarsa musamman kafafuwansa da sukai Masa nauyi lokaci daya kamar an Dora Masa bulo sosai yakejin abun na karuwa cikin jikinsa Amma ya dake ya kasa cewa komi da zuciyarsa dake harbawa sauri da sauri tamkar zata fasa kirjinsa ta fito,take ya soma jujjuyawa yana ganin dakin nayi Masa yawo....tana Nan zaune jikinta na karkarwa tana lura da yanayin nasa da yafi na Koda yaushe,batai aune ba ya saki wata irin gigitacciyar Kara wadda Saida ta razana ta toshe kunnuwanta lokaci daya ta runtse idanuwanta tanajin karar har cikin kwakwalwar kanta ga wani irin faduwar gaba,lokaci daya network din kanta ya dauke gabaki daya,ta dauki kimanin seconds talatin a hakan sanan ta fara bude idanuwanta Wanda yayi daidai da shigowar jamaar cikin gidan a rude manya da Yara ciki ko harda Mai martaba Wanda a lokacin Yana cikin sashen gimbiya bilkisu,..
"Subhanalillahi zainul abideen meke faruwa Kuma?innalillahi wa Inna ilaihi rajiu wanan wace iriyar Kara ce wadda ta gigita kowa dake cikin gidan tamkar Mai shigar aljanu?ta karasa maganar tana fashewa da kuka a rude gimbiya bilkisu ke magana yau karar da takeyi takasa nuna damuwarta ta kasa boyewa Tai Kansa tana girgiza sa,idanuwansa sun shige bakin sai fararen sai wani irin Abu yakeyi hade da gurnani kasa kasa kimfaffaki na fitowa ta cikin bakinsa tamkar Mai aljanu...sosai Mai martaba ya rude ganin Dan lelensa a halin da bai taba ganinsa cikba shi Kansa baisan lokacin da yace "asamu malam ya'u ya tofa Masa addua yanzun yanzun"
"Wani malam ya'u ranka ya Dade bayan baya cikin gidan Nan Yana kauye anyi Masa rasuwa?ai a gaggauta Kiran likitansa yazo kawai shi kadai yasan me yakeyi Masa idan hakan ta faru"sosai gimbiya rumana kw zubda hawaye Tana Kara tallabo zainul jikinta sosai wani irin rawa jikinta yakeyi tana Kara rungumesa tamkar zata maidasa cikinta saboda tsananin so...hawaye fiyya ta share ta dubi gimbiya rumana "ummah inaga Bari in ruga asibitin da kaina in dakko likitan Nan tunda Kinga tsayawa ma lalubar nimbersa Bata lokaci be Kinga kowa a rude yake"
"Yi sauri fiyya karki tsaya jiran driver ki driving da Kanki Dan allah".... Bata rufe bakiba likita yayi sallama cikin dakin ganin halin da zainul ke ciki yasa shi saurin ajiye jakarsa a gefe ya bude ya Ciro allura da syringe da sauri ya zuko allurar batare da Bata lokaci ba yayiwa zainul abideen ita Nan da Nan ya Shiga jijjiga suna rirrikesa sosai bakajin sautin komi cikin dakin Nan sai koke koke yau har zahira Saida ta zubdawa zainul hawaye saboda tsananin tausayin halin da yake ciki,ikon Allah cikin minti arbain da tashin ciwon da shigowar likitan bacci Mai nauyin gaske ya daukesa jikinsa ya jike sharkaf da gumi..
Tana Nan rungume dashi kowa ya watse cikin dakin daga ita saishi sai ummaty wadda saboda tsabar kuka idanuwanta sunyi jajir dik sun tasa sai faman ajiyar zuciya takeyi tana tsugunne kanta a kasa zuciyarta cike da tsananin tsoro da fargaba....wani irin kallo gimbiya rumana ta bita dashi Mai dauke da maana kala kala sanan ta dauke kanta gefe daya Jim kadan ta kwantar da zainul abideen ta Mike tsaye ta gyara zaman lafayarta sanan ta kwashi wayoyinta ta dubi ummaty "ummaty idan zakije gida kibiyo sashina" Bata jira cewarta ba Tai gaba baiwarta ta take Mata baya ...
**********
"Ranki ya Dade Zanyi iya bakin kokarina wajen sawa yarinyar idanuwa gaba da baya kamar yadda kikace ranki ya Dade"
"Hansa'u banaso asamu matsala akan wanan aikin Dana saki bawani Aiki bane face kisawa shige da ficenta Ido sosai ki gano mun dik wani Abu da takeyi itada wanan yaron saboda Ina kallon akwai boyayyar soyayya a tsakaninsu Kuma ni zainul bazai auri Yar sarkiin dawaki ba da Raina"
"Insha allahu ranki ya Dade Zanyi dik abinda kikasani harda Wanda Baki saniba ranki ya Dade Zanyi kokari wajen samo Miki labarai kala kala daga wanan sashen"....jinjina Kai gimbiya tayi cike da gamsuwa sanan tace "Zaki iya tafiya daga yanzun aikinki ya fara har illa Masha allahu"
"Angama ranki ya Dade,Allah yaja zamaninki yaja da ranki da lafiya da arziki Mai amfani"...murmushi ta sauke tana jinjina kanta...
********
Gimbiya bilkisu na zaune a bakin gadon zainul ya bude idanuwansa a hankali Yana bin ko Ina da kallo tamkar Wanda ya tsinci Kansa a cikin wata sabuwar duniya...kalle kalle ya shigayi a cikin dakin na Dan wani lokaci sanan ya juyo da idanuwansa kan mahaifiyarsa da sukai jajir ...dakyar ya bude bakinsa ya motsa harshensa da yayi Masa nauyi sosai yace "Ammiey..jiki..na ciwo"Yana maganar harshensa na sarkewa tamkar me koyon magana dukkansu Basu fahimci me yake fada ba Saida ya sake maimaitawa sanan mahaifiyarsa ta ruko hannuwansa idanuwanta na kawo ruwa "zainul Dole jikinka yayi ciwo saboda bakada lafiya kagani yau ciwonka ya tashi sosai har yafi Koda yaushe d'an ammiey"hawaye ya gangaro a fuskarta wani irin bakin ciki da tausayin d'anta ke dankare cikin zuciyarta ,yadda takejin son zainul zata iya sadaukar da komi Dan farin cikin da'nta Anya kuwa tayiwa d'anta adalci?ya kamata ta saki jiki wajen kulawa da d'an nata da soyayyar da dik wata uwa take bawa d'anta, tana kawaici da Kara be bawai Dan Bata sonsa ba Amma lokaci yayi da zata rinka shigowa wajen Dan nata akai akai tare da ziyarar ba zata Dan ganin lafiyar tasa. Dakyar ta sauke numfashi ta dubesa ta share hawayenta ta Shiga shafa Masa sumar Kansa ta Dade tare dashi sanan Tai sallama ta fice dakin....
"Ya zainul ya jikin?"a sanyaye Tai maganar tana kallonsa..Shima kallon nata kawai yayi zuciyarsa ta harba ya lumshe idanuwansa ya budesu sanan yayi Mata murmushi batare da yace komiba kallo daya zakayi Masa ka fahimci Yana matukar Jin jiki sosai...
*******
Bayan sati biyu cikin sati biyun Nan abubuwa da yawa sun faru ciki kuwa harda yawan tashin ciwon zainul abideen abun kullum Kara gaba yakeyi ummaty dik ta kade ta rame ta Kara fari saboda damuwar da take ciki ta dage da bashi maganin da gimbiya rumana ke Bata sanan ta Dade da daina sa Masa karatun alkurani....
Shakuwa da soyayya Mai tsanani ta kullu a tsakanin zainul abideen da ummaty tun be fahimci abinda ke cikin zuciyarsa game da itaba har ya fara ayyanawa zuciyarsa yadda zai rayu batare da itaba Dan ya Gama fidda Rai da samun lafiya tunda shi Kansa yanzun zuciyarsa ta fara Raya Masa ciwon Nan nasa ba na asibiti bane ko na ruwan addua na gargajiya ne saboda yadda dik lokacin da ciwonsa zai tashi yakeji tamkar wasu abubuwa ke Shiga cikin jikinsa suna juya Masa duniyarsa....