Sashe 31
Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da karfin jiki sosai zainul ya tashi shi Kansa Yana mamakin Kansa farin cikin da yake tsintar Kansa cikin wadanan kwanakin baya misaltuwa zaune yake Akan wheel chair dinsa shi Kansa mamakin yadda akayi yake rike da cup a hannunsa batare da ya Fadi ba yakeyi da Kansa yakai bakinsa dikda hannun nasa Yana Dan rawa yasha ruwa a hankali ya dawo da hannun ya rike kallon jikinsa yakeyi fuskarsa dauke da murmushi... kafafuwansa yake Dan motsawa da yatsunsa a bakinsa ya ambaci kalmar "alhamdulillahi "...lallai bashi da bakin da zai godewa ummaty dashi saidai yayi Mata addua Dan Babu musu magungunan da take basa a kwanakin Nan suke warkar dashi da kudurar Allah...kada Kansa kawai yakeyi zuciyarsa na ayyana Masa abubuwa da dama waigawa yayi gefensa kadan ya hangi MP3 din da ta kawo Masa yake kwana saurare ya lumshe idonsa ya bude take taji Yana Jin kwadayin dakko mp din Amma Babu Wanda zai dauko Masa zuciyarsa ke ayyana Masa ka gwada mikewa tsaye mana?zaka iya daukowa da kanka ka gwada... gabansa na faduwa ya Dora hannuwansa biyu Akan hannun wheel chair din ya dafa sosai hannuwansa na rawa a hankali yake kokarin yunkurawa Yana numfarfashi Sama sama dai dai Nan ta turo kofar sai kawai ya karasa mikewa kafarsa na tsananin rawa... daskarewa ummaty tayi s tsaye dafe da kirjinta idanuwanta tamkar zasu Fado kasa tana binsa da kallo Yana sanye da purple din shadda da hula yayi masifar kyau ta dauki seconds talatin kafin ta furta "ya zainul Kaine s tsaye?I can't believe alhamdulillahi ya ilahi"murna sosai takeyi kafin ta Ankara yayi baya ya zauna a kujerar saboda kafarsa dake rawa...da gudu tayi Kansa zata rukosa taga ya fada kan kujerar sai ta sauke sassanyar ajiyar zuciya murmushi ya hau yi Mata ita kuwa tsananin farin ciki ya hanata magana...
Kashe mata Ido daya yayi "yadai ummaty"
Sai kawai ta janyo kujera ta zauna nesa dashi kadan ta kafesa da Ido...cikin mintuna hawayen farin ciki suka Shiga sauka a kumatunta...Wanda batasan tansyinsu ba lokaci daya Kuma murmushi yaki gushewa daga fuskarta "ummaty kuka Kuma?menene?umm?ai ban Fadi ba ko?Kinga na fara tsayawa Amma kafafuwana rawa sukeyi ummaty"...yadda yayi maganar ya Kara Bata tausayi ga wani kyau dake fita daga fuskarsa da kwarjini na daban fiye da ko yaushe uwa uba shaddar jikinsa da Tai matukar karbarsa....
"Kukan farin ciki nakeyi ya zainul...nayi matukar Jin dadin ganinka a tsaye da kafafuwanka gani nakeyi tamkar a mafarki ne ya zainul Kaine a tsaye? alhamdulillahi....Allah ya Kara maka lafiya ya zainul...naji Dadi sosai"
"Ummaty ke Zanyi wa godiya keda kika jajirce wajen nema mun magani da kula Dani,abinda iyayena suka kasa fahimta ke kika fahimta,tabbas nadade da tunanin ciwo na bana asibiti bane Amma baba ya kasa ganewa...banida bakin da zan gode Miki saidai incee Allah ya Saka Miki da alheri ummaty...Kuma Ina ganin maganin da kike bani yanzun shi ya sa naji sauki haka sosai cikin kankanin lokaci"
Wani murmushin Jin Dadi tayi zuciyarta Tana godewa Allah da ya hadata da baabah kande cikin kankanin lokaci suka samu wanan ci gaban "alhamdulillahi ya zainul Allah ya Kara lafiya"..
Murmushi ya sauke mata Wanda ya Kara narkar Mata da zuciya yace "ameen ummaty"...
*******
Kasantuwar yau jumaa yasa dukkansu sukazo gida da iyalansu kamar yadda al'adar gidan take da halima da Zahra ne yaran ummah rumana zaune gefen mahaifiyarsu Alan katuwar dadduma suna taba Hira sama sama gimbiya rumana sai wani Shan kamshi takeyi tana magana da kyar tamkar Dole da alamu yau sarautar ta Mata ta motsa....
Cikin zumudi anty Zahra ta dubi halima tace "albishirinki halima jiya saiga haris a gidana daddare"
"Kai Dan Allah kice yazo Miki ziyara,ai haris akwai mutunci idan ya gadama"
"Shegen ba gidana yayi niyyar zuwaba budurwa ya samu Wai be fada Mata Yana sonta ba da gidansu zaije Amma ya kasa zuwa sai kawai yayo gidana kiji shirme"dukkansu sukasa dariya sai lokacin gimbiya rumana tasa musu Baki "haris kenan iyayen girman Kai dama zaiyi budurwa wanan yaron"
"Ai ummah budurwar ma Yar cikin gidace Amma ya kasa gaya Mata ba wata bace ummaty ce"
"Ummaty!"gimbiya rumana da halima har rige rigen fada sukeyi...take hankalin gimbiya rumana ya tashi ta gyara Zama Tana sauraron Zahra "itafa ummah Amma indai dagaske yake sonta yayi Mata Dan tanada hankali sosai gata kyakkyawa zanso ya aurentan"
Tabe Baki halims tayi ta dubi mahaifiyarta suka hada Ido sai Kuma halima ta hau dariyar yak'e "wallahi kuwa ni kaina zanso ta auri haris kodan ta bar zainul itama ta huta da jinyar Dan ko warkewa zainul yayi bazai aureta ba"
"Saboda menee?
"Tana matsayin Yar sarkin dawaki?bama Yar waziri ba ko galadima sauki sauki tabdijan"...
Bataji dadin yadda halima tayi maganar ba sai kawai ta dauki nuaiym ta fita Dan ta shimfidesu kamar jira takeyi su fita gimbiya rumana a fusace tace 'kinji wani bala'i ko"
Dariya halima tayi "shine daidai ummah ai kawai ko wani bekai maganar Nan gaban Mai martaba ba kiyi kokarin kaiwa dan shine cigabanmu da samun nasararmu da zarar ummaty ta auri haris karasa zainul ba wani Abu bane"
Cikin rashin fahimta gimbiya rumana tace "meye dalilinki na hakan"
"Zamu tattauna ummah xaki fahimci inda na dosa Amma ko labarin auren ummaty da haris zainul yaji to tabbas bakin ciki zai ksrasasa Dan ko ba komi nasan ya kamu da sonsa Koda yarinyar Bata sonsa Dan hakan kija haris a jiki kikai maganar wajen sarki akwai nasara",
",To idan ummaty batason haris dinfa?"
"Bazataki shi ba,saboda haris hadadde sanan ummaty bazata iya Musa maganarki Kota Mai martaba ba"..jinjina Kai gimbiya rumana tayi zuciyarta cike da tunani barkadai...
*******
Sauri sauri suketa aiki tun safe saboda yau jumaa abinci kala kala ya kamata ayi saboda Baki Dan haka baabah kande batasan wainar da ake toyawa ba a sashen gimbiya tana wajen masu aiki Tana duddubawa dikda jikinta Yana Bata anyi magana Mai muhimmanci da ya kamata ta saurara...
A Nan ummaty ta sameta take shaida mata ci gaban da aka samu dangane da maganin da take karbo Masa sosai baabah kande tayi farin ciki da Jin hakan Amma zuciyarta nayi mata rauni da zarar zainul ya warke to tsugunu Bata Kare ba ummaty ce zata Shiga uku...
"Baabah ya naga fuskarki ta canja kamar bakya farin ciki"ummaty ta tambayeta cike da damuwa...
Gudun kada yarinyar ta fahimci wani Abu yasa ta sakin fuska tana fadin "ai Dole inyi farin ciki diyar albarka kawai dai kaina ke ciwo ga aiki tun safe mukeyi"
"Haka ne Bari inje in duba ya zainul ko ya tashi Dan ni zan kaishi fadar sarki idan an sakko masallaci"tana gama Fadin haka ta wuce baabah kande ta bita da kallo cike da tausayi....
********
Haris zaune gefen musaddik Yana daddana wayarsa yasha kwalliya cikin farar shadda da bakar hula yayi matukar kyau sosai hannunsa rike da farar wayarsa iPhone 11 hankalinsa na kan wayar kowa na zazzaune Yan Matan ma sunsha ado suna Yar hirarsu a gefe can gefe iysyensu ne kannen me martaba suna tasu hirar bangaren hagu Kuma su Zahra ne ke tsokanar hajiya Kaka....sarkin fada ne yayi yekuwa tare da neman izinin zaa shigo cikin fadar... sarki ya amince aikuwa ya bude musu kofa tana ture dashi a wheel chair da sallama bakinta suka shigo kowa ya bisu da kallo musamman zainul abideen da yayi masifar kyau ga Yar kiba yayi Yana sanye da farar shadda da bakar hula irinta jikin haris sai walkiya yakeyi tamkar ya Mike ya taka da kafafuwansa...sumar zaune warisah tayi tunda ta shaki kamshin turarensa zuciyarta ta buga take taji wani Abu ya caketa s kirji ya rufe idanuwanta kawai fuskarsa take gani a mafarkinta yanayi Mata tsadadden murmushin Nan nasa...Jan numfashinta tayi ta sauke ta dauki mintuna a hakan kafin ta bude idanuwanta wadanda suka canja launi suka kankance....
Haris kuwa irin kallon da yake bin ummaty dashi yasa hafsat zungurin zahira ta Nuna Mata suna kada Kai suna murmushi ita kanta anty Zahra radawa halima tayi a kunne "dubi mutuminki"ta juyo ta Ganshi kusan kowa yaga yadda yake bin ta da kallo ... hajiya kubrah kuwa tayi kicin kicin da fuska har ummaty ta fice dakyar ya dawo hankalinsa karaf suka hada Ido da mahaifiyarsa ta watsa Mai harara....
Abinci aka Shiga zuzzubawa ummah rumana da kanta ta Mike cike da iyayi "Bari in bawa yarona abinci Dan nasan Babu me yimun Kara"murmushi Mai martaba yayi "to ai kema Baki jira ayi Miki karar ai da kin tsaya kingani nasan kubrah zatayi Miki"...dukkansu sukasa dariya.
Gefensa tai masauki rike da plate din jelof da nama da cokali sai murmushi zainul keyi sai kawai ya Mika Mata hannu "ummah zan iyaci da kaina"ta zaro Ido tana kallonsa "ah ah zaka Bata jikinka zainul"
"Allah ummah xan iya kawo kigani"Mai martaba kuwa sai faraa yakeyi Yana kallonsu itama gimbiya bilkisu hankalinta na kan Dan nata
"Kawo ummah kigani Allah zan iya"cike da shagwaba yayi maganar Yana Bata fuska tamkar yaro karami...
Haris yayi murmushi "ummah kibashi Mana kuna maidamun brothet yaro bayan ya girma kuma alhamdulillahi Yana samun lafiya"
Sai kawai gimbiya rumana ta mika Masa da bismillah a bakinsa ya karba batare da plate din ya Fadi ba kowa zaro Ido yakeyi cike da mamaki Babu Wanda yayi magana Amma hankalin kowa na Kansa a hankali ya dibo abincin dikda jikinsa na Dan rawa yakai bakinsa tsananin farin ciki yasa Mai martaba tafi Yana fadin "alhamdulillahi"kowa sai murna da sowa ciki kuwa harda warisah wadda takeji tamkar taje ta rungumesa a guje zahira ta karasa ta rungumesa ta baya "yaayah yafara samun sauki alhamdulillahi"...wani kallo warisah ke bin zahira dashi tamkar ta shaketa...ita kuwa zahira kasa sakinsa tayi saboda yadda kamshin jikinsa ke fusgarta tanajin wani irin nishadi cikin zuciyarta....gimbiya bilkisu har kwallar farin ciki Saida tayi....haka ya rinka cin abincun Yana faraa saboda yadda kowa ke murna...
Kuka sosai gimbiya rumana keyi tana godewa Allah yaronta ya samu lafiya har hajiya Kaka Saida ta lallasheta tace farin ciki zatayi tayi dariya haka ta rungume zainul Tana shafa Kansa....
A haka aka karasa cin abincin kowa cike da farin ciki shiko haris Allah Allah yakeyi a gama saboda ya Kai zainul sashensa Dan yaga ummaty ko zai samu saidah cikin zuciyarsa....