← Book details Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 49

Sashe 10

Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ummah Amma dai ya kamata a canjawa zainul wajen magani ko?ko wani asibitin ne akaishi kila magungunan wancen asibitin ne Basu karbesa ba suke Kara da jikinsa rikicewa tunda ammiey tacemun kwana biyun Nan baa bashi maganin asibitin ba"shiru gimbiya rumana tayi batare da tace komi ba kusan minti biyar "ummah magana nakeyi"a hankali ta maida kanta ga Yar Tata "wallahi tausayin yaron Nan nakeji zahrau ace shekara da shekaru yaro be huta ba yau ciwo gobe lafiya?wanan wace irin jarabawa ce?astagfirullahi Kar nayi sabo Allah ya bashi lafiya "

"Ameen ummah"

*********
Kamar yadda sarki dawaki ya fadawa ummaty bada magani ya dawo dik kwana bakwai yau hakan ta kasance "ummaty ga maganin Dan uwan naki"
Cike da zumudi ta dubi mahaifinta "yauwa baba dama yau zan tuna maka maganar maganin nasa gara a rinka bashi akai akai ko Allah zaisa mu dace"tausayin gaske ta bashi firucinta sai ya dauke Kansa,.
"Insha allahu zaa dace ummaty kiyi ta kokarin Yi Masa"

"Insha allahu baba"

*********
Kamar ko da yaushe a kwanakin Nan biyu da yake samu ya xauna Akan wheel chair yau ma zaune yake Yana sanye da bakaken kaya kaftani masu tsadar gaske anyi musu aiki irin na sarauta yayi kyau sosai yadda yake zaune zaka dauka idan kace ya tashi zai tashi,kunnensa makale da karatun alkurani cikin sabuwar mp3 din da ummaty ta kawo Masa Yana saurare Yana lumshe idanuwa ta shigo, besan ta shigo ba ta Dade tsaye tana jifansa da murmushi sanan ta karaso cikin dakin Shima ya bi ta da nasa murmushi

"Barkanki da zuwa ummaty maanociyar murmushi"yace Yana kallon gefenta tamkar me tsokanarta,

"Umm ya zainul kenan irin kirari din Nan kakemun sai kace wata sarauniya ko matar sarki?ka manta ni din ba kowa bace?"

"Ke din wani Abu ce Mana ummaty tunda ko ba komi babu Wanda yasan tsakaninki da mahaliccinki,idan ya kasance kinada kyakkyawar maamala wajen ibadah da bautar Allah Kinga kinada babban matsayin da shi basarake bashi dashi,saidai shi matsayinsa a duniya ne kadai ke kuwa harda lahira"murmushi tayi batare da tace komiba tana jinjina kanta cike da gamsuwa da maganar tasa,Batare da wani Bata lokaci ba ta Ciro gorar ruwan maganinsa ta bashi ya shanye Tass hade da Yar gyatsarsa ,kallonta yayi Ido cikin Ido "yau karatun da kikemun na boko Zaki cigaba da yimun ya kamata a karamin sabon darasi "

"Angama ranka ya Dade"

"To ki ciremun wanan karatun na kunnena Kinga zai rinka daukarmun hankali idan muna karatun ko?idan mungama sai ki maidamun kunnuwana".

"Toh"tace tare da mikewa tana kokarin cire Masa karatun ta ajiye mp din akan gado ,ta janyo kujerar da take zaune daf dashi suna soma karatun,

Sun dauki lokaci sunayi tana koya Masa Yana dauka,ta sunkuyar da kanta tana karanto mishi yayi shiru Yana saurare,har ta Gama batace komiba "ya zainul a Kara ko a tsaya a Nan?" Nan ma shiru taji ta sake maimata tambayar shiru be amsaba,da sauri ta dago kanta Dan a tunaninta bacci ya daukehi,sai kawai taga Kansa ya karkace gefe Yana wani irin Abu dik gumi ya jikasa sharkaf tamkar ana kwara Masa ruwa "innalillahi wa Inna ilaihi rajiu ya zainul lafiya?menene?" Nan ma shiru babu amsa ba karamin tsorata tayi ba ta firgice sosai ta Shiga jijjigasa sai kawai taga Yana kokarin fadowa daga wheel chair din,...daga murya tayi Tana Kiran fasawansa,shiru Saida Tai Kira sau biyu sanan mutum uku suka shigo dakin ,ganin yanayinsa yasasu saurin rukosa sukai kan gadonsa dashi,sai sassarfa jikinsa keyi tamkar mejin sanyi ga hannuwansa dake lankwashewa kamar ana juyasu,

Hawaye kawai ke gudu a idanuwanta tana tsaye akansa ta kasayin komi,ga zuciyarta dake tsananin harbawa sauri da sauri tamkar zata fasa kirjinta ta fito,Nan ta Shiga tofa Masa adduoi Amma inaaa abun Kara gaba yakeyi sai kuka takeyi ganin yadda jikinsa yakeyi a wahale,idanuwanta ta Kai kan mp3 dinsa Tai saurin dauka ta kunna ta makala Masa a kunne da kyar,ta rukosa da kyau tana faman zubda hawaye....sun dauki minti arbain a haka sanan jikinsa ya fara daidaita yabar wanan abun da tamkar ana lankwasashi,...numfashinsa ke sauka a hankali ga wata zufa dake zuba a fuskarsa,
"Alhamdulillahi"shine abinda ta furta ganin ya samu bacci sanan ta xauna gefen gadon ta tsura Masa Ido...

********
Karfe shida da wani abu ana Shirin Kiran sallahr magriba ta fito dik jikinta babu kwari tana so taje gida Amma zuciyarta cike da tunanin yadda zata barshi takeyi,hakanan ta fito fuskarta babu walwala da nufin tafiya gida,...sashen gimbiya rumana ta nufa Dan ta gaisheta dik yau bataga ta leko wajen zainul ba batasaniba ko lafiya tunda A Rana takan shigo wajensa sau uku ko sau hudu Dan taga jikin nasa,

A parlor ta taddata baiwarta na gefenta tana matsa Mata kafa tanayi Mata kirari,idanuwanta a lumshe,sallamar ummaty yasa ta bude idanuwanta a hankali ta saukesu akanta,take ta sakar Mata lallausan murmushi,
"Ummaty kece?"

"Nice ummah"ta xauna gefen ta nesa kadan "barka da yammaci ranki ya Dade"

"Barkanki dai ummaty ya dawainiya?Kai Allah dai ya biyaki da alheri kinji?"

"Ameen Ummah"Tai jimm kadan a zaune,tana yunkurin mikewa ta tsinkayi muryarta "yau kinyi yamma sosai ummaty,Hala Dan rikicin ya hanaki tafiya ne'

Fuska babu walwala ummaty tace "ehh ummah,Kuma madai yau ciwonsa ya motsa sosai,mundade tare kafin nasamu bacci ya daukesa abun babu Dadi ummah...Kansa kawai Naga ya karye gefe daya"

"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiu,yanzun ya jikin nasa?"

"Toh da sauki ummah,nasa mishi mp3 a kunne na kunna Masa karatun alkurani shine nasamu bacci ya daukesa"

"Mekikace ummaty?ubanwa ya Baki izinin sa Masa wani Abu a cikin kunnensa?tunda kike kintaba ganin ansa Masa Abu a kunnensa na karatu ko wani Abu?waya Baki izini?wani irin karambani ne wanan?wata masifar kike Shirin janyo Mana kenan tunda kike sa Masa Abu a kunne"a firgice ummaty ta girgiza kanta cikin tsananin tsoro tana Shirin yin kuka,
"Inba masifa ba meye hakan?so kike yasamu matsala a kunne kenan Kinga sai ya Zama kurma maganar ma ya daina nakastar ta tabbata kenan mu ki kaimu ki baro"

"Ah ah ranki ya Dade Dan Allah kiyi hakuri bansanibane,da gani nayi tamkar ciwon nasa bana asibiti kadai bane shine nace in rinka sa Masa ko zaa dace"

"Kinfi Mai martaba sanin abinda ya dace ne?ko mu kikafi sani muda muke iyayensa?karki kuskura kice Zaki Kara wanan gangancin idan ba hakan ba zan hadaki da Mai martaba"a firgice ummaty ke girgiza Kai tana hawaye tunda take da gimbiya Bata taba canja Mata irin na yau ba Tai Mata masifa,....ita kuwa gimbiya rumana Nan da Nan Tai sanyi da murya ganin yadda yarinyar ta firgice tana hawaye,
"Kiyi shiru ummaty kinji?banji dadin yadda kikayi bane kinsan yanayin jikin nasa sai ki janyo Masa wani abun Kuma shiyasa nai fada Kuma Mai martaba bazaiji dadiba idan yaji labari kinji?da kinsani kitambaya tukunna kafin kiyi haka?daga yau kome zakiyi Masa kizo kitambayeni nice uwarsa kinji?"ummaty ta gyada Mata Kai tana share hawaye,

"Tashi kije gida zan tuntubi Mai martaba akan hakan,ai babbar shawara kika kawo ummaty,kawai dai mahaifinsa bayaso ayi Masa komi na gargajiya shiyasa sai na asibiti Nima nafara ko kwanto akan ciwon nasa kibari inyi magana dashi tukunna"

"Toh ummah"

"Tashi kije kinji ana Kiran magriba ki gaida innar Taki kinji?"

"Toh"

*********
Kaiwa da komowa kawai takeyi cikin dakinta wajen karfe daya na dare abubuwa sun taru sun cunkushe Mata zuciya,mafita kawai take nema ga wanan al'amarin daya bullo...shin tayaya zata bullowa lamarin yarinyar?...Zama Tai gefen gadonta ta kafe gefe daya da Ido ta fada duniyar tunani....kusan minti ashirin ta sauke ajiyar zuciya hade da murmushi ..."tabbas hakan shine mafita cikin sauki ma"....ta furta a fili tana Dan murmushin nasara.

**KADA KU MANTA LITTAFIN NAN NA KUDI NE GA MAI BUKATA GA DETAILS* *NAN A SAMA KUMA DAGA PAGE NA GABA NAGAMA BADA FREE* *PAGES ....INA MARABA DA MASOYA A DIK INDA KUKE*

*SLIMZY😍*
[1/23, 10:39 AM] 😍SLIMZY😍: *HASKE WRITERS ASSO...💡*

💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞

*SLIMZY✍🏼*
*Wattpad@slimzy33*

*Assalamu Alaikum.... Fan's a duk inda kuke ina muku fatan alheri. Wannan book na zainul Abiddeen na kud'ine, wanda yake sha'awar siya ze iya tura kud'insa ta wannan number akan naira dari biyu kacal.*

*2073065733
Sha'awa Ibrahim
UBA bank*
Tura shaidar biyan kudinka ga wanan number
08161306299

6019111117 keystone
Amina jibril
Shaidar biyanka ga wanan number 08166177830

Kokuma ya tura katin waya na mtn na 200 ta wannan number

08039424298 kokuma 07084161619

Kud'in littafin d'ari biyuce kacal game buqatar ci gaban zainul Abiddeen seya tuntub'emu.

*10*

********
"Ya zainul Wai menayi maka ne yau tunda Nazo kake shareni bakason kulanu?ta tunzuro Baki gaba idanuwanta cike da Yar kwalla tana kallonsa,...Shima idanuwansa akanta suke ko kiftawa bayayi yafi minti biyar a haka sanan ya kauda Kansa gefe batare da yace komiba,
Hawayen dake makale cikin idanuwanta ne suka sulalo a fuskarta zuciyarta na harbawa sauri da sauri tsoro falll zuciyarta,batasan laifin da tayi Masa ba tunda tazo yau yaki sakar Mata fuska suyi hira yadda suka saba,Kuma a iya saninta lafiya kalau suka rabu jiya hasalima bacci yakeyi batasan tafiyarsa ba,shin kodai Mai martaba yayi fada akan abinda tasa mishi a kunne ne na karatun kur'ani?har Shima bayaso yasa yake Sha Mata kamshi yau,dikda cewar tasan halinsa Sarai be cika son magana ba miskili ne ajin farko sanan dikda ciwon da yakeyi baya hanasa sarautarsa ta motsa ya rinka magana sama sama kamar bayasonyi,...idan har laifin da tayi jiya ne to tabbas zata daina kunna Masa Kuma insha allahu zata dauke mp3 din ma ta wuce gida da ita.
Chapter 10 · 0% Book details