Sashe 42
Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Kujerar Roba ya janyo ya zauna sanan ya kalli ummaty wadda ke tsaye kamar an dasata ta kasa dago idanunta saboda kunya tayi Dan murmushi ke kin amshi soja ne da kika tsaya tsaye kusan awa guda?ki zauna Mana?ko Baki gaji da tsayuwar bane Captain ummu Salma"yayi maganar cike da zolaya Yana sane yayi hakan Dan ya fahinci kunya ce ta lullubeta,
Turo Baki gaba tayi ta Dan hararesa sanan ta dubi innah "innah kinji me ya haris ke cemin ko?wai Captain ummu Salma"...maimakon innah tai magana yunkurawa tayi ta Mike tai hanyar sashin sarkin dawaki "kunfi kusa Kinga tafiyata ni"Tai shigewarta ta barsu nan..
Taku uku tayi zatayi gaba ya ruko hannunta ta tsaya cakkkk "Ina zakije bakiyimun bayayanin waye yazo wajen ki kika fita batare da izinina ba?waye wanan yake Shirin yin karambanin kawo kansa wajen matar wani?hmmmm ummaty kenan to ki sanar dashi tun wuri ya Kama gabansa Dan bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane kina ji Koh"...kici kici. Kwace hannunsa daga garesa ya rike ta kammm Yana Yi Mata wani irin kallo hade da aika Mata sakwanni kala kala....
*WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619*
********
jijiyoyin kansa gabaki daya sun mimmike idanuwansa sunyi jajir ya Mike tsaye jikinsa har rawa yakeyi Yana sauraron wanan audios din da wanan ya Shiga ya gama wanan ya fita...dafe kansa yayi saboda yadda dakin yake juya Masa a guje tamkar Yana gudu cikin mota ...I can't believe....ummahhhhh ya kwalla Kara Yana juye juye cikin dakin....
********
Ummaty ce kwance Kan cinyar innarta bayan tafiyar haris innar nayi Mata Susa cikin kanta tana sauraron redio "innah nikam inaso inji tarihin mu da tarihin muamalar mu da gidan sarki"...kada Kai innah tayi tana mamakin yadda ummaty ke bibiyarta akan wanan lamarin Amma ya zama dole yau ta sanar da ita Koda ba duka bane......
*HASKE WRITERS ASSO...💡*
💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞
*SLIMZY😍*
[1/23, 11:44 AM] 😍SLIMZY😍: 38
Shekarun baya da suka wuce.....
Sarki Muhammad shine mahaifi ga zainul abideen kamar yadda kika sani yanada Yara shida sakamakon matansa biyu ne,gimbiya rumana itace ta farko cikin matansa tanada Yara biyu da sarki Muhammad Zahra itace ta farko sai halima wadda ke bi Mata....gimbiya rumana ta kasance komenene sarki ita yake sawa a gaba saboda yadda yake balain Sonta Yan uwansa Suma suke Sonta kamar yadda kika sani kannen sarki biyu Mata da hajiya kubra mahaifiyar haris da warisah sai hajiya shaawah itace mahaifiyar zahira musaddik da hafsat....sun tun bayan haihuwar halima Allah be sake bawa gimbiya rumana haihuwa ba sunyi yawo asibiti asibiti wajen masu magunguna amsar dai daya CE lafiyarta kalau Allah ne be kawo ba Dan halima ta kusan zama budurwa kafin kwatsam sarki ya bukaci Kara aure,wanan Abu ba karamin tadawa gimbiya rumana hankali yayi ba lokacin da taji cewar sarki zaiyi aure Babu Wanda besan wanan tashin hankali na uwar gidan sarki ba dik fadin garin nan da masarautar nan saboda yadda ta tada hankulan jamaa....sarki da ahalinsa da mahaifiyarsa suka cigaba da shirye shiryen biki dikda sarki Yana kwantarwa da gimbiya rumana hankali Akan wanan aure da yake so yayi...
Cikin kankanin lokaci kuwa aka fara shagulgulan auren sarki da bilkisu diyar sarkin agadaz a wanan lokacin shiyasa zakiga bilkisu tana da tata sarautar da izza saboda itama daga gidan sarauta ta fito....lokacin da aka kawo gimbiya bilkisu gidan sarki basa Shiri da gimbiya rumana ko kadan basa zama inuwa daya cikin kankanin lokaci ta mallake dangin mijin kaf basayi da amarya sai ita hatta mahaifiyar sarki hajiya Kaka sai abinda gimbiya rumana tace takeyi saboda yadda take zuba mulki a cikin gidan,dik wanan baya damun gimbiya bilkisu harkar gabanta takeyi kawai batare da tasan Allah yayi gimbiya rumana a wajen ba....cikin wata uku da auren gimbiya bilkisu kwatsam labari ya karade masarautar cewar ai amaryar sarki na dauke da juna biyu..fadan farin cikin da sarki yayi a wanan lokacin baaa magana haka yayita kyauta Yana rabawa talakawansa hatta mu dake zaune a gidan a da shine sanariyyar da ya bamu kyautar wanan gidan muke zaune ciki Wanda muka baro....gimbiya rumana Koda taji labari sai batayi hauka yadda ake tunani ba Dan kawai gani akai ta Kama farin ciki kuma tabi gimbiya bilkisu suka shirya kamar basu ba dik wata kula da akewa me ciki gimbiya rumana keyiwa kishiyarta tun Bata saki jiki da itaba har ta saki komi ya wuce lokacin ciki nata girma Masha allahu...sosai sarki ya dukufa wajen adduar samun magaji bashi da wani buri daya wuce gimbiya bilkisu ta haifi namiji Dan haka akaita azumi Ana sadaka da rokon Allah na Allah ya sauketa lafiya yasa ta haifi da namiji....wata Tara ciff alkawarin Allah ya cika inda gimbiya bilkisu ta haifo da namiji Kato Mai cike da koshin lafiya da hakora biyu na kasa aka haifesa wanan yasa jamaa akai ta tururuwar zuwa kallon wanan baiwa da Allah yayiwa wanan yaro.....soyayyar duniya sarki ya dorawa wanan yaro Ana haihuwarsa ya Sanya Masa suna Muhammadul zainul abideen akaita shagalin suna inda rukonsa da komi nasa yake hannun gimbiya rumana komi ita takeyi Masa yadda take sonsa bazaki taba cewar ba ita ta haifesa ba komi ita keyi Masa tsakaninsa da gimbiya bilkisu tabashi no-no haka rayuwa taci gaba inda gimbiya bilkisu ta Kara samun wani ciki a nan ta haifo safiyya wadda suke Kira fiyya lokacin zainul nada shekara hudu a duniya nan ma akaita shagali bayan ita ta Kara haihuwar ayshah lokacin zainul nada shekara takwas bayan haihuwar Aysha ne na haifeki kema inda tin bayan haihuwarki Ina zuwa gidan aikace aikace zainul ke makalemun yayita Wasa dake har yakam cemin Allah yasa ammiey idan zata sake haihuwa ta haifo kyakkyawa me kamar ummaty innah saidai inyi Masa dariya kawai shike renonki komi shi yake Miki har ta Kai dik in banje gidansu ba zaizo har nan gidan da kansa da haka har ya koya Miki tafiya da karfin tsiya Dan mikar dake yakeyi yayita tafiya dake kema kuma lokacin inhar zainul zai karbeki to ko nice na Mika hannu bakya yadda tare kuke Wasa a sashin gimbiya rumana wataran har wanka can kikeyi ita ke kula daku a tare sakamakon haka yasa gimbiya rumana ke Shiri da mahaifinki komi na yau dakullum shi take Kira idan zaayi yayi a gidan sarki....
Shiru innah tayi tana kallon ummaty wadda Tai kasake tana sauraron yadda Inna ke kwararo Mata labari dikda labarin da take Bata sama sama ne bawai cikakke take Bata ba a dunkule take Bata labarin...
"Innah kinyi shiru kici gaba Mana"cikin sigar shagwaba Tai maganar....Jan numfashi innah tayi ta sauke sanan ta Dora da "kwatsam wata Rana da bazamu mance ba aka wayi gari da zainul ya kamu da wanan ciwon Wanda kikai wayau kika sanshi da shi an Shiga cikin tsananin tashin hankali a wanan nahiyyar dik wani Wanda ya kwana ya tashi a cikin garin nan ranan Saida ya tausayawa wanan yaro saboda zainul na mutanene yaro ne me farin jini ga tarbiyya uwa uba ga son mutane dikda yanada miskilanci sosai be cika son magana ba Amma baya wulakanta Dan Adam shiyasa ciwon nasa ya girgiza alummar Babu Wanda zai Baki tausayi kamar ammiey mahaifiyarsa wadda take dauke da tsohon cikin afnan lokacin haihuwa yau ko gobe wanan balai da kaddara ta sauko Masa baya iya ko mikewa yadda dai kika girma kika gansa to hakan ne Yana wanan ciwon kikesa rigima zai ankaiki wajen yaayah kamar yadda kike kiransa a wanan lokacin haka rayuwa ta kasance iyayensa basuda kwanciyar hankali kullum suna hanyar asibiti musamman gimbiya rumana wadda dik ta fita hayyacinta saboda ciwon zainul Amma kullum abin gaba yakeyi memakon baya Ana haka gimbiya bilkisu ta haifi ummul khairi wadda suke Kira da afnan sakamakon sunan kakarta ta wajen uba akasa Mata....haka rayuwa ta kasance kulllum gimbiya rumana ke kula da zainul da masu hidimarsa kina manne dashi baya cin abinci komi sai kina tare dashi a hakan har kika girma kika tsincu kanki kece me kula dashi abinda nasani kenan a takaice....
Dakyar ummaty ta hadiyi wani kakkauran miyau Wanda ya tarun Mata "Amma innah kuma Babu Wanda ya taba tunanin cewar gimbiya rumana itace tayiwa ya zainul asiri?"
"Babu Wanda ya taba tunani Dan har yanzun banajin idan Zaki hadiyi kurani wajen cewar itace silar ciwonsa a yarda a yarda Babu Wanda zai yarda saboda yadda ta shiga ran me martaba yadda take mutuwar son zainul abideen banaji akwai abinda zaisa su yarda Dan haka kiyi shiru da bakinki har Allah ya kawo karshenta a gidan"
Ajiyar zuciya ummaty tayi cike da zullumi da tunani inama ace zaasamu recording din da ta dauka na gimbiya rumana?wadda muryarta ce Babu Wanda zai karyata hakan?inama ace Allah zai tona asirinta cikin kankanin lokaci ta daina cutar mutanen cikin gidan tanayi musu kisan mummuke?tonuwar asirin gimbiya rumana shine kawai zai zama cikar burinsu ita da zainul abideen na kasancewa a karkashin inuwa daya wato maaurata,to ya zatayi da haris?...lumshe idanuwanta tayi abubuwa da dama sunayi Mata yawo akai....