Sashe 37
Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tsaye tsaye suke akansa lokacinda malamin da aka Kira yayi Masa adduoi aka shafa masa me hade da ganyen magarya da ayatushifa aka bashi dakyar aka samu ya farfado bakinsa dauke da salati da Kiran sunayen Allah....lokaci daya yake bin kowa da kallo a dakin daya bayan daya da sauri gimbiya rumana ta rungumesa cikin tsananin farin ciki "alhamdulillahi Dan ummah ya farfado na godewa Allah Ashe kanada sauran Shan ruwa a duniya yarona,watakila warakar ka ce tazo kanada sauran numfashinda zaka haifamun jikoki"cikin tsananin farin ciki take maganar tana Kara rungumesa sosai...runtse idanuwansa yayi saboda yadda jikinsa yayi Masa nauyi babu karfi tamkar an cire Masa lakka...cikin karfin Hali ya kalli gimbiya bilkisu wadda take hawayen farin ciki yayi murmushin sanan yace "ammiey Ina ummaty?,ta tafi Bata jirani na tashi ba koh?"ya marairaice Yana tambayarta.....
*HASKE WRITERS ASSO💡*
💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞
*SLIMZY😍*
[1/23, 11:41 AM] 😍SLIMZY😍: 33
Shiru kowa yayi a dakin suna kallonsa batare da sunce mishi wani Abu ba sai ya lumshe idanuwansa ya Kara budesu a kan sister dinshi halima "maman samir Ina ummaty ta tafi gida ko?Dan Allah idan ta tafi a je a kiramun ita inason ganinta sosai"cikin sigar shagwaba yake maganar,
Anty Zahra dake gefe rungume da Muhammad ta share hawayen da ya gangaro mata daga idanuwanta tausayin Dan uwanta ya cika Mata zuciya itadai ta kasa cewa komi tun bayan faduwar hakan domin zuciyarta Bata aminta da zancen ba Allah kadai ya baiwa Kansa sani,a tare suka tako zuwa gaban makeken gadon da yake kwance suka tsaya itada halima,karfin Hali anty Zahra tayi ta ruko hannunsa tana murzawa cikin sigar lallashi "lil brooo"ta Kira sunansa cikin sanyin murya da sauri ya dubeta Yana murmushi "naam anty Zahra"...cigaba tayi da murza hannuwansa "kaga ka daina Kiran sunan ummaty kaji baxaka sake ganin ummaty ba kaji broo kayi hakuri"...cikin rashin fahimta yake dubanta zuciyarsa cike da tsoro me kalamanta suke nufi?ya ma zaayi ace bazai sake ganinta ba yarinyar da ta Zame kasa jigon rayuwarsa jinin jikinsa?...kodai mutuwa tayi gabansa ya yanke ya Fadi ya Shiga girgiza Kansa inaaa hakan ma bazai yuwu ba da kyar ya motsa harshensa dakeyi Masa nauyi cikin sarkewar murya yace "Akan me zaace hakan?wani Abu ya faru ne?"ya Watso wata tambayar a Karo na biyu....kowa a dakin kallon kallo yakeyi sai gimbiya rumana wadda Tai karfin halin kwashe dik abinda ya faru ta sanar dashi ...da hukuncin da Mai martaba ya dauka sanan ta Dora da "Kar insake Jin zancen wanan azzakumar yarinyar a bakinka kaji na fada maka macuciya ce kaji?ka cireta a zuciyarka ka manta da ita tunda Allah yayi Mana arzikin Bata kashe ka ba"Tai maganar Tana shafa Kansa....
Dummmm yaji Kansa yayi Masa gabaki daya network din Kansa ya dauke dakin ya Shiga jujjuya Masa tamkar ana wurgasa sama ana jehosa kasa yakeji ga mummunan faduwar gaba daya darsu a kirjinsa cikin seconds da Basu wuce talatin ba wasu siraran hawaye suka Shiga gudu daga idanuwansa Wanda ya kafesu Akan fankar Sama ko kiftawa bayayi....
Ganin hakan yasa halima tabe Baki batare da kowa ya lura ba ta Dora da cewar "Dole kayi kuka lil broo Amma hakanan zakayi hakuri domin ummaty ta cutar dakai shekara da shekaru saidai Allah ya saka maka ka kwantar da hankalinka ka daina kuka ciwonka yazo karshe insha allahu Allah zai baka lafiya"....
Wani kululun bakin ciki ne ya tokare wuyan gimbiya bilkisu wadda takeji tamkar ta Dora hannu akai ta fashe da ihu saboda takaici ko sunan ummaty gimbiya bilkisu Bata bukatar ji Dan dik duniya da zaa Bata wuka ta kashe wani to mutum na farko da zata kashe shine ummaty da zuriarta gabaki daya taci amanarsu Kuma insha Allahu sai sunga sakayya da wuri sanan ta Gama yadda da kowa a fadin duniyar Nan...tayi zurfi cikin tunani lokacin da aka turo kofar dakin hade da yin sallama...haris ne ya shigo da hajiya Kaka wadda gabaki daya jikinta babu kwari tun bayan faduwar hakan,....kallon zainul takeyi yadda hawaye ke gudu a fuskarsa take itama idanuwanta suka cicciko da kwalla Dan kallo daya zakayi Masa ya baka tausayi....haris ya xauna gefen gadon ya ruko hannun zainul yaji hannunsa zafi Rau ya dubesa kadan ya kauda Kansa "zainul ka kwantar da hankalinka ka duba halin da kake ciki kaji?wanan Abu saidai mubarwa Allah kawai Amma tariga tafaru ta kuma Kare"...sai lokacin zainul ya kifta idanuwansa ya juyo da kallonsa ga haris...."wallahi haris na rantse da Girman Allah banaji ummaty zata aikata abinda ake zarginta dashi,yarinyar Nan tayi iya bakin kokarinta wajen kulawa Dani Bata taba guduna ba,kashina,fitsarina,dik wata kazanta tawa itace shekara kusan nawa tana wanan dawainiyar?tun lokacin Bata kasheni ba sai yanzun?....Yan uwana inace wasu har guduna sukeyi saboda kazantata Amma ita Bata gujemin ba idan har nayi mata hakan tabbas nayi mata butulci Kuma Allah zai saka mata"...
A fusace gimbiya bilkisu ta soma magana cikin kumfar Baki "ko Kuma Kai Allah ya saka makaba sakaran banza,sakaran wofi"
Gimbiya rumana ta karbe zancen "haba bilkisu meye hakan kikeyi?kibishi a hankali Mana tunda kinsan halin da yake ciki sanan kada kiga laifinsa Dan yayi wanan sambatun Sam baa hayyacinsa yake ba bakisan iya rubutun da aka bashi yasha ba ta shanyesa Dole mu cigaba dayi Masa addua mubisa a hankali"
Kuka sosai zainul yakeyi tamkar karamin yaro cikin kukan ne yake fadin"inhar maganar da kuke fada gaskiya ne na bazan sake ganin ummatyba to tabbas ku shirya dan nan bada jimawa ba abinda kuke gudun zai sameni Dan zan iya rasa Raina a kowani irin lokaci yarinyar Nan itace rayuwata itace jinin jikina itace komi nawa"tari ya sarkesa ya dafe gefen kirjinsa tamkar Wanda zai sheka lahira,
Bakinciki ne yasa gimbiya bilkisu mikewa tabar dakin Dan ji takeyi tamkar ta shake zainul saboda takaicin maganganunsa,...
Rukosa haris yayi Yana lallashinsa dikda can kasan zucuyarsa wani irin kishi ketaso Masa akan ummaty ji yakeyi tamkar ya shake zainul yakeji saboda kishi bayajin xai iya hakuri da ummaty shi Kansa Koda duniyar gabaki daya xata juya Masa baya Yana Nan tare da abarsa as far as iyayenta zasu aura mishi ita zaiyi rayuwa dagashi sai ita Dan haka dakyar ya busar da wata Isaka Mai zafin gaske daga bakinsa Nan da Nan jijiyoyin Kansa suka fito a saman goshinsa badan yaso ba haka yayita lallashinsa saboda wani bangare na zucuyarsa na matukar ji da zainul abideen Dan Yana kaunarsa Shima...
Tana isowa sashinta ta Kira malamin da Mai martaba yasa aka kawo Dan yayiwa zainul magani ta Kira sa a wayar cewar tanason ganinsa akwai maganar da takeso su tattauna...cikin kankanin lokaci baiwarta lubabatu ta sanar da ita zuwan na malamin inda akai Masa masauki a babban patlornta...
Sanye take da alkyabbar ta baka Mai tsadar gaske Tana rike da wayar ta pito patlorn tana taku dai dai,...malam zubair Yana ganinta ya zube kasa Yana kawo gaisuwa 'barka da yamma ranki ya Dade Allah yaja zamaninki sai Kuma naji Kiran gaggawa daga gareki Ina fatan ba jikin nasa bane ya tashi"
Girgiza Kai tayi fuska dauke da damuwa "allah ya gafarta malam ba jikin bane wata damuwa ce nakeson fada maka ko Allah zai sa kanada maganinta Allah yayi Mana maganin damuwar mu"
"To Allah yasa dai lafiya"
"Wasu maganganu ne yaron Nan ya farka Dasu dangane da makirar yarinyar can wadda Sam banji dadinsu ba sun matukar batamun Rai "...Nan ta kwashe dik yadda sukai da zainul bayan farfadowarsa sanan ta Dora da "malam inaso a rinka bashi rubutu Wanda zai mantar dashi yarinyar Nan gabaki daya koma yaji ya tsaneta Dan samm Babu abinda na tsana a rayuwata sama da ko Jin sunan yarinyar Nan malam ka taimakeni"Tai maganar cike da damuwa...
Shiru malam yayi Yana nazarin maganganun gimbiya bilkisu ya dauki minti goma sanan ya sauke ajiyar zuciya cike da alhini yace "ranki ya Dade wanan lamari na yaron Nan abin dubawa ne gaskiya sanan maganar rabasa da yarinyar Nan farar daya daga faruwar lamari bazai taba yuwuwa ba sai a hankali saboda kunsan yadda sabo yake da shakuwa musamman da kukace sun taso tare komi tare sukeyi Dole sai a hankali sanan Zanyi istihara Akan lamarin domin annabi SAW shi Kansa yanayin istihara na neman zabin Allah da rinjaye Dan hakan ki kwantar da hankalinki bazai gagaraba"....
Ajiyar zuciya gimbiya bilkisu tayi fuska dauke da damuwa "to malam a duba lamarin sanan nagode sosai Allah ya saka da alheri"...sukai sallama da malam ta bashi kyautar kudi sanan ya tafi....
******
2pm
Na dare zaune take Akan sallayar sallarta tana adduoi Tana kuka hade da yiwa Allah kirari akan Allah ya bayyana gaskiya cikin gaggawa rokon Allah kawai takeyi tana Kiran sunayen Allah....
Tana zaune kan dadduma zazzabi Mai zafi ya rufeta ga ciwon Kai Mai tsananin gaske Wanda takeji tun bayan faruwar lamarin....
Hawaye kawai ke gudu a fuskarta hade da shasshekar kuka ga wata iriyar yunwa da takeji gabaki daya rabinta da abinci tun safiyar jiya, shasshekar kukanta ne ya tada innah ta Mike da sauri ta nufi dakin ummaty tana mutsike Ido dikda ita kanta bacci barawo ne ya saceta saboda tsananin damuwa..."haba ummaty saiki tashi cikin dare kina koke koke?umm kiyi tawakalli ga Allah kinji ki roki Allah ya bayyana gaskiya sanan ya sanyaya Miki zuciyarki kinji?banaso damuwar hakan ta haifar Miki da wata lalura kinji ummu Salma?"cikin sigar lallashi take maganar,
Dago Kai ummaty tayi fuskarta sharkaf da hawaye da gumi hade da majina tsabar kuka idanuwanta sun kankance ga zugi da sukeyi mata shasshekar kuka takeyi tana kallon innah "yanzun innah shikenan rabuwata da ya zainul tazo kenan?shikenan ta hakan zamu rabu idan ma zamu rabu?ya zainul yaji abinda ya faru yanzun nasani...Amma nasan shi yasan koni wacece bazai aminta da Zan cutar dashi ba...Allah sarki banida sauran wani Dan uwa a duniya"...