← Book details Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 49

Sashe 18

Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kikace wanan maganin da aka Aiko dashi Mai muhimmanci ne daga gobir aka Aiko dashi?...Kai hajiya rakiya kinyimun kokari a wanan tafiyar na Kuma ki Dadi na yaba Allah ubangiji yabarmu tare ya Kara hada kanmu... Babban burina be wuce insamu yadda nakeso a masarautar Nan ba,hajiya bakin cikina be wuce yadda aka tabbatarmun da na Gama haihuwaba,da dik yadda Zanyi inshiga infita insamu da namiji da nasamu Amma banida yadda na iya Dan haka Wanda ake takama dashi Shima a nakashe yake Matan su zauna da lafiyar"Tai maganar fuskarta cike da takaici,shiru tayi Tana sauraren dayan bangaren sanan ta kyalkyale da wata muguwar dariya da alama maganar da aka fada Mata Tai Mata Dadi sanan tace,
"Kai hajiya nagode ki gaida oga sai kinjini insha allahu Zanyi yadda kikace zan sanarwa da yarinyar insha allahu komi yazo karshe da izinin Allah "...sun Dade suna magana sanan ta kashe wayar fuskarta dauke da murmushi....

*********
Saida ta gamawa ummaty bayani tsaf ummaty ta bita da wani irin kallo sanan ta cije lebenta cikin kunar zuciya ta Mike ta fice....Koda ta fita ba sashen cikin gida ta nufa ba hanyar kofar yamma ta nufa Bata zame ko Inaba sai wajen famfo ta juya gabas da yamma kudu da arewa ta tabbatar da babu Mai ganinta sanan ta Ciro wata roba empty daga cikin Jakarta ta juye maganin Tai musaya dikda robobin iri daya ne Amma akwai shedar da tayi Wanda zata gane haka ta canja maganin Nan ta Kara wawwaigawa taga Babu Mai kallonta sanan Tai hanyar cikin gidan,Koda ta juya tana hangen hansa'u ta fito sashin rumana da alamar ita ta turo ta duba taga ko zata bashi maganin Dan haka fuskarta cike da walwala ta nufi sashen gimbiya bilkisu inda ta taddasu duka zazzaune a parlor har su fiyya matafiya sundawo Dasu zahira inda suka yada zango a Nan sukwana biyu,ta tsugunna har kasa ta gaida ammiey ta amsa Mata cikin sakin fuska tare da tambayarta ya innarta ta amsa da lafiya Lau tayi hanyar shigewa dukkansu sukabita da kallo da jakar dake hannunta....

Jingine yake a jikin gadonsa idanuwansa a lumshe daidai Nan tayi sallama cikin zazzakar muryarta Mai dadin saurare...ta tsaya tsaye a kofar tana kallonsa tana murmushi,a hankali ya bude idanuwansa wadanda suka kasance farare Tass ya saukesu akan fuskarta,murmushi kawai takeyi Shima ya maida Mata da martanin murmushi zuciyarsa na bugawa sauri da sauri wani Abu keyi Masa yawo cikin jinin jikinsa tamkar mashi Wanda be tsaya ko Inaba sai a kirjinsa.....ita kanta wani yanayi takejin kanta Mara misaltuwa Wanda Bata tanajin irinsa ba wani irin farin ciki ke ratsa ilahirin jikinta Wanda yasata takowa a hankali tana tafiyarta Mai daukan hankali har tazo gabansa besaniba idanuwansa na kanta ta janyo kujera ta zauna ta dire Jakarta a gefe..."yadai ranka ya Dade wanan kallonfa?"Tai maganar cikin sigar daukar hankali..besan lokacinda ya sauke nannauyar ajiyar zuciya ba a fili hade da lumshe idanuwansa ya budesu Wanda ya zame Masa dabiarsa ce hakan...

"Kyakkyawa nagani shine nake kallo"...waige waige ta shigayi kamar me duban wani Abu tace"Ina take"....

"Gata Nan a gabana tana tambayata?bayan tasan da ita nake...hmmm kanwata kinyi kyau sosai"yayi murmushi,da sauri tasa hannu ta rufe fuskarta tana dariya kasa kasa Shima dariyar yayi...

Zahira ce ta turo kofa tana duban zainul sanan ta dubi ummaty takai Mata wata muguwar harara ummaty kuwa ta daga Mata gira daya alamar lafiya...ta kafeta da manyan idanuwanta,sai kawai zahira ta tabe Baki ta fice fuuuuuu kamar kububuwa ta bugo musu kofa shidai zainul abideen bece komiba sai kauda Kansa da yayi kawai...

Bayan ta Ciro gorar maganin da ta canja ta juye Masa maganin a Kofi sanan ta Dan tofa addua a ciki ta Mika Masa,ganin hakan ba musu ya karba Dan yadda yaga gorar tamkar ruwa bayan yasha ya dubeta "wanan ruwa ne?"tambayar da ya jefeta dashi kenan sai kawai ta gyada Masa Kai "ehh ruwan zam zam ne zan rinkayi maka addua ciki kana Sha"

Murmushi ya Yi Mata Yana kallonta batare da yace komiba....sun dauki lokaci suna Hira sanan bacci Mai nauyi ya daukesa tana zaune gefensa tana kallonsa zuciyarta nayi Mata Dadi wani farin ciki Yana ratsa ko Ina a jikinta hansa'u ta turo kofa...

"Gimbiya nada bukatar ganinki"...gabanta ne ya Fadi Nan da Nan jikinta ya soma rawa ta ko Ina hankalinta a tashe ta Mike da sauri tana fadin "meya faru Kuma"a ranta addua takeyi Allah dai yasa ba matakan tsaro tasa sukaga lokacin da ta canja ruwan maganin ba a zuciyarta Babu abinda take ambata sai innalillahi wa Inna ilaihi rajiun dik ta firgice hansa'u na lura da yadda ta firgice sai. Kawai ta tabe Baki "meye na furgicewa sai kace kin aikata wani mummunan aiki?dik kin bi kin hargitse daga cewa gimbiya na kiranki?cikin seconds da Basu wuce ashirinba kin fita hayyacinki?ummmm kedai kika sani muje ko meye kyaji"...dakyar ummaty ta hadiye miyau ta bi bayan hansa'u gabanta na tsananin faduwa..

*WANAN LITTAFIN NA KUDI' NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS* *DIN 08166177830 KO 07084161619 DAN KARIN BAYANI*
********
"Hauwa wanan shawarar da kika bada me kyau ce Akan ummaty nikaina yanzun bason zuwanta gidan sarki nakeyiba Amma gudun in hanata ya janyo mun magana yasa na kyaleta Amma yanzun tunda kika kawo wanan shawarar shikenan Kinga Babu me cewa hanata akayi"

"Gaskiya bazamu zubawa zabgegiyar budurwar Ido a hakaba sarkin dawaki yadda kaji na fadan Nan shine mafita itama tasamu inda zata tsugunna yafi kawai"...

Dik hirar da sukeyi innah dake tsakar gida tana tsunce wake tana saurarensu hakika hankalinta ya matukar tashi da Jin sarkin dawaki ya amince da shawarar kanwar tasa tashi daya batare da ita ya nemi shawararta ba a matsayinta na mahaifiyarta Amma Babu komi tasan abunyi bazai Sabu ba wankan kuturu da sabulu...

*********
Kafafuwan ummaty tamkar ansa Mata shocking hk ta Shiga da sallama can kasan makoshi saboda yadda ta tsorata ta nemi gefen carpet ta tsugunna da kyar ta hada harrufan bakinta tace "gani ranki ya Dade"

"Ummaty"ta Kira sunanta cikin wata irin siga da gabanta ya Kara faduwa kamar zata saki fitsari...

"Naam ranki ya Dade"

"Ba wani Abu yasa nakiraki ba shine in jadadda Miki muhimmancin bawa zainul abideen magungunan Dana karbo saboda ummaty nakosa yaron Nan yasamu lafiya,gashi bashi maganin akeyi kamar baa bashi kullum jikin jiya iyau ummaty"wasu hawaye suka zubowa gimbiya rumana tasa gefen lafayarta ta share.."shiyasa nakiraki inkara rokonki in jadadda Miki kibashi maganin Nan nasa Akan lokaci musamman na yau Wanda na Baki Dan ba karamin kudi na bada ba Mai maganin ya hadashi saboda bakaken aljanun dake bibiyarsa kinji"ta Kare maganar cikin sigar lallashi...

Gyada Mata Kai ummaty tayi "insha allahu ranki ya Dade Allah dai ya bashi lafiya Kuma yanzun haka na bashi wanan maganin na yau ma"...murmushi ne ya kubucewa gimbiya rumana saboda farin ciki Wanda sukai Ido hudu da ummaty daidai lokacin itama ta sakar Mata nata murmushin Wanda ita kadai tasan dalilinta....

*WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS 08166177830 KO 07084161619 DAN* *KARIN BAYANI*

💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞

*HASKE WRITERS* *ASSO💡*

*SLIMZY😍*
[1/23, 10:43 AM] 😍SLIMZY😍: 17

Ajiyar zuciya gimbiya rumana tayi,tadan samu sassauci Akan azalzalarta da zuciyarta keyi gabaki daya batada natsuwa a cikin kwanakin Nan haka kawai take tsintar kanta cikin wani yanayi na rashin yarda....zuciyarta nayi Mata waswasi kala kala Dan haka sai kawai ta dubi ummaty ta gefe kadan "Zaki iya tafiya ummaty sai kinjini"

"To ranki ya Dade,Allah ya Kara Miki lafiya da nisan kwana Allah ya bawa zainul lafiya ya takaita Masa wanan wahalar ya kawo karshen ta albarkacin annabi da alkurani"ta karasa adduar tana Mai dagowa ta saci kallon gimbiya rumana ,sai kawai taga yanayin fuskarta ya canja ta yatsina fuska tace a ciki "ameeen"

Murmushi ummaty ta sauke,ta gano wani Abu a Nan ma sai kawai ta Mike batare da tace komiba tai hanyar fita,wani mugun kallo Mai tattare da tsantsar tsana da wulakanci gimbiya rumana tabi ummaty dashi wadda ita batamasan tanayi ba hankalinta yayi gaba abinta...

*********
Zazzaune suke a fadar Mai martaba kasantuwar yau jumaa kowa na gidan na ciki Dana waje suna zuwa gaisuwar jumaa da sada zumunci a gidan Mai martaba kwansu da kwarkwatarsu hatta da hajiya Kaka mahaifiyar Mai martaba baa barinta a baya itama tana zuwa.

Abinci aketa zuzzubawa kowa a plate ana Mika Masa burabusco da miyar alayyaho Wanda yaji kayan Hadi tayi kyau Tai Kore sharr dik inda ka hautsuna cikin abincin nama ne haka ake zubawa kowa gefe daya Kuma gasasshen naman rago ne Wanda aka badeshi da yaji da mangyada a babban matankadi irin Wanda ake amfani dashi a gidan masu sarauta da gidajen gargajiya bakajin sautin komi a parlor sai karar cokula da plates shiru Babu Mai magana....

Hajiya kubrah ce ta dubi warisah wadda Kecin abinci tana famar yatsine yatsine tace "ke warisah jeki sashen zainul abideen kice a fito dashi cin abinci Shima yaci a cikin Yan uwansa"...dibbbb warisah tayi ta kasa tauna abincin dake bakinta saboda takaici ita ta tsani zuwa sashen wanan kazamin haka ta Mike badan ranta yasoba tana faman zumbure zumbure ta fice hajiya Kaka ta wurga Mata harara tace a fili "ja'irar yarinya Mara mutunci"...kowa yaji abinda tace Sarai sunsan da warisah take Dan dama ba shiri suke sosaiba Dan hajiya Kaka batason raini itako warisah uban kowa ta rainasa ga kyamar talakawa da takedashi...

Girgiza Kai kawai hajiya kubrah tayi Ta cigaba da cin abincinta batare da tace komiba....

Firarsu sukeyi sosai suna dariya shida ummaty lokacinda warisah ta turo kofar ko sallama Babu,ta shigo daidai fuskarsa dauke da tsadadden murmushin Nan nasa me fitowa da ainihin kyawunsa Wanda Allah ya basa sukai Ido hudu da warisah wadda gabanta ya Fadi lokaci daya ,ta kauda kanta gefe shiko daure fuskarsa yayi tamkar be taba dariya ba,...shiru ne ya ratsa na Dan wani lokaci sanan warisah ta dubi ummaty a wulakance tace "ke malama Baki iya tambayar abinda ya kawoni ne?kinyi shiru kina kallona kamar wata mayya"

Murmushi ummaty ta sauke "ya zaayi insan meya kawoki bayan ko sallama wadda adinin musulunci ya tanada bakiyi manaba Kinga Dan ban kulakiba bawani abubane koh?"
Chapter 18 · 0% Book details