← Book details Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 49

Sashe 49

Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Har inda aka bizneta zainul da haris Saida sukaje dasu akayi komi sukai Mata addua sosai,zainul yasha kuka tamkar wani mace tsoron duniya da tsoron Allah ya Kara lullube zuciyarsa haka suka biyo ayarin mutane suka dawo,..."mu Shiga cikin gidan"suka Shiga a tare bakinsu dauke da sallama zahar na gefe tana shayar da yaronta tana kuka su zainul suka shigo dukkansu a tare suka Mike tsaye da halima da Zahra suka taho a guje suka rungume kanin nasu suna kuka Mai ban tausayi haris gefe ya koma Yana sharar hawaye saboda tausayinsu dik halima tayi Baki ta fita hayyacinta ga Babu miji da samir da sumayya da sabreen yaranta suna wajen mahaifinsu inda yaran suna hannunta zata danji sanyi a ranta....

Gefe suka koma da zainul da haris da halima da Zahra suka Shiga tattaunawa da maida yadda akayi da yadda gimbiya rumana ke amayo tsutsotsi da kana na kana nan tsokokin cikinta da suka zagwanye abun Babu Dadi haris ne ya Basu shawara akan idan anyi uku su dawo gida tunda Basu sukaiwa Mai martaba laifi ba kuma Zahra tanada aure halima ce zata zo su Roki sarki tare ya yafe Mata ta dawo gidan ubanta da zama da wanan shawarar suka gamsu suka rabu cikin kaunar Dan uwan nasu,har wajen mota suka rakasu suna daga musu hannu tare da ce musu gobe ma zasu zo....haka suka bar wajen cike da alhini.

*******
Dawowarsu zainul gida da fadin rasuwar gimbiya rumana ba karamin girgiza masarautar yayi ba kowa da kowa ya Shiga taitayinsa musamman maaikatan gidan Wanda sukasan yadda gimbiya rumana ke zuba mulki da Isa,...

*Tsokaci* lallai duniya baa bakin komi take ba Kuma abinda ka shuka shi kake girbewa ko wani Dan adam besan yadda karshensa zatayi ba kasan farkonka bakasan karshenka ba shiyasa ake tunasar damu kullum mutuwa ta kanzo maka a lokacin da bakayi tunani ba baka San yadda zata riskeka ba Kayi kokari ka aikata Mai kyau kodan kwanciyar kabari da tashin alkiyama Wanda ranan yauma tubulassara'ir ranan tonon asiri ga ko wani Dan adam inma ka shuka Mai kyau ko akasin haka a fili Kayi ko a boye baka saniba ranan agaban kowa zaayi hisabi kowa nafsi nafsi kowa kokari yakeyi ya karbi littafinsa da hannun dama Allah ubangiji yasa mu karbi littafinmu da hannun Dana muna faraa cikin yantattun bayi daga wuta zuwa aljannah Allah karya bamu ikon cutarda Dan uwanmu musulmi ameen

Hatta gimbiya bilkisu Saida ta zubar da hawaye Jin labarin mutuwar gimbiya rumana Wanda ya tariyo Mata rayuwar da sukayi a baya yau Ina take?

Mai martaba kansa ya Tara jamaar gidan akayi saukar alkurani akayi Mata addua jiki Babu kwari ciki hardasu ummaty wadda Tai kuka kamar zata mutu tare da yafewa gimbiya rumana dik abinda tayi mata fatan itama Allah ya yafe Mata.....

*********
Ana gobe biki halima da Zahra sukazo wajen mahaifinsu suka rokawa mahaifiyarsu gafara halima ta Roki mahaifinta Akan ya yafe Mata batasha wahala ba ya yafe Mata hatta ammiey taji dadin dawowarsu cikin family dama halima muruniyarta ce Dan haka sashinta tabata dakinsu fiyya aka Shiga gyarawa tunda dukkansu aure zasuyi Afnan ce kawai zata rage....

Hajiya kubra da mamansu zahira hajiya hadiza dik tattarowa sukayi suka dawo gidan Mai martaba inda aketa gudanar da Shirin biki gida ya cika makil da Baki na nesa Dana kusa ga Kuma nadin sarautar zainul abideen wadda zaayi bayan angama daurin aure sarki zaiyi murabus ya huta ya Dora dansa daya tilo a karagar mulki,

Bangaren su ummaty kuwa Yan kauyensu sun bayyana su gwaggo kuluwa dik sunzo ita kanta ummatyn batada lokaci kullum cikin zuwa gyaran jiki sukeyi gidan hajiya jummai Mai gyaran amare inda gimbiya bilkisu ta biya makudan kudade wajen gyaran amare,a nan ne Ashma da warisah da zahira da fiyya suke sanar Mata ai ashmah ce zata auri haris itace zata auri zainul Wasa da hankali kawai akeyi Mata,....ummaty jinta takeyi a wata sabuwar duniya Mai cike da Jin Dadi da nishadi Bata taba tunanin ko a mafarki zata auri Dan sarki Wanda ke Shirin zama sarki ba uwa uba ta koma matar sarkin kansa alhamdulillahi da wanan baiwa da niimah da Allah yayi Mata.....

Bangaren angwaye baa barsu a baya ba Komi tare sukeyi dik inda zasuje tare suke zuwa kamar wasu Yan biyar kowa sai Sam barka yakeyi.....

"*******
Karfe goma Sha daya aka Soma daura aure inda aka daura auren haris da Aysha (ashmah)fsrko tunda shine babba sai "musaddik da warisah, sai zainul abideen da ummaty ,nurudeen da safiyya...sai a karshe aka daura na yazeed da zahira....bayan angama daura aure ne kuma aka Shiga cikin nadin sarautar zainul abideen inda dubban jamaa da sarakunan masarautu dayawa suka halarta...a nan zainul ke shaidawa jamaa cewar ya bawa baba kande mukamin zama jakadiyyarsa muddin Rai....

********
Bayan magriba Kuma aka tafi zuwa dinner inda Zahra da halima suka hadawa amaren suka Kuma gayyaci kowa da kowa zuwa wajen,...naira Kam tayi kuka sosai a wajen nan abinci kala kala Babu Wanda Babu kowa farin ciki yakeyi hajiya kubra da gimbiya bilkisu da hajiya hadiza da Zahra da halima akwansu kala daya ne leshi sky blue da head dinsu silver amare dukkansu lace dinsu golden ne sai head dinsu silver dukkansu Komi nasu iri daya ne an cashe a wajen an rabashe afnan ta rasa inda zatasa rayuwarta saboda Murna dik inda ka waiga zaka hangeta suna kashe hoto itada anty nafisah kanwar ammiey ....

********
Estate guda kowa da gidansa Mai martaba ya bada cikin gidajensa da estate estate Wanda yake dashi cikin gari kowa da sashensa sanan ko wace amarya ankaita sashenta....motarsu zainul ce ta kunno Kai motoci uku ne suka shigo dik angwaye ne a ciki driver's suka jawosu ...

Ko wanne fuskarsa dauke da faraa haris yace "dare nayi nasan amaryata tsoro gareta Bari in garzaya Kar inbar abuna ita kadai"dariya sukasa dukkansu sukai sallama da juna kowa ya nufi sashensa...

Zainul yasha Nadi fadawa na biye dashi har kofar Shiga ya bude kofa kenan ya juyo ya kallesu "ba a nan zaku kwanaba kuje gidan Mai martaba kafin a gyara naku sashen Saida safe"ya rufe kofar ya barsu tsaye suna kallon juna.....

Sanye take da alkyabbarta Mai ruwan Zuma kanta durkushe tana Wasa da yatsunta da suka Sha lalle ya tsaya Yana Kare Mata kallo...kamshin turarensa ya daki hancinta ta dago Kai a hankali ta sauke idonta cikin nasa suka hada Ido Yana cikin Nadi da farar malum malum yayi masifar kyau ta kasa dauke idonta daga garesa har ya karaso gabanta Bata saniba ya Hura Mata iska ta lumshe idanuwa zata boye fuskarta ya dauketa cakkkk ya Shiga juyi da ita cikin dakin ya sabata a kafadarsa Yana juwa da ita dukkansu dariya sukeyi sosai a take ya direta kasa ya rungumeta tsammmmm suna dariya .....

**Tammat bihamdullah nan nakawo karshen labarina naso inraba page din sai nayi kawai guda* *daya Dan Allah Ina rokonku gafara na rashin posting akaikai wallahi ba haka nakeyi ba wanan* **karon akasi akasamu Dan haka nake rokon gafara daga gareku nagode* **kwarai da kauna Allah ya saka muku da* *mafificin alheri......*
***

**HANKALINA BAYA KWANCE SHIYASA BAKUJINI BA INADA* *MARALAFIYA DAN ALLAH KUSATA A ADDUA ALLAH YA BATA LAFIYA YA* *SAUKETA LAFIYA*

*SLIMZY✍🏼*

*
Chapter 49 · 0% Book details