Sashe 4
Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Fuskarta Babu walwala ta dago idanuwanta ta dubesa a raunane sanan ta maida kanta kasa ta dukar "Haka kawai na rasa samun sukuni cikin Daren Nan,tunanin yaron Nan zainul ya hanani sukuni inaso ingansa Inga halin da yake ciki yanzun"....murmushi yayi irin na manya ya rungumota jikinsa Yana shafa kanta a hankali "haba rumana zuwa yanzun ya kamata kisaba da rashin lafiyarsa tunda ya dauki shekaru Yana wanan ciwon kusan tun bayan haihuwarsa,nikam Banga sabon abuba a wajen ciwon Dan naki"
Kwantar da kanta ta karayi a kirjinsa Tana sauke numfashi "muje ki ga Dan naki kinaso?"...da sauri ta daga Masa Kai alamar ehh ,girgiza kansa yayi yana murmushi rumana Bata girma dikda ta girma ta haifi yara Amma kullum jinta take kamar karamar yarinya,Haka ya tasata a gaba suka nufi sashin yarima zainul,
Rike suke su biyu da zainul dukkansu bacci ne a idanuwansu Amma Babu damar yi saboda yadda zainul abideen ya Bata jikinsa gabaki daya da amai da yayi Wanda sukansu basusan dalilin Aman NASA ba,su kansu sun gaji dashi,suna Shiga dakin fadawan suka zube a kasa suna kwasar gaisuwa,
Ganin halin da zainul ke ciki yasata saurin karasawa ta rukosa jikinta ta Shiga share Masa jiki da kanta da Dan karamin towel din dake wajen ,Mai martaba Yana tsaye Yana kallon yadda take rungume da zainul abideen ko kazantar jikinsa bataji batadamuba ta tsaftace Masa jiki kawai takeyi ita,Saida ta kammala gyara Masa jikinsa ta juyo ta dubi inda Mai martaba ke tsaye hannunsa rungume a kirjinsa ta dubesa a raunane ya sakar Mata murmushi kawai ta sadda kanta kasa hawayen da take boyewa suna sauka a kuncinta,
Kallonta sosai zainul abideen yakeyi Yana girgiza kansa alamar tayi shiru ta Kara rungumesa sosai tanajin soyayyarsa na ratsa sassan jikinta.....
********
Yau ta kasance jumaa yaune mahaifiyar me martaba da ahalin gidan sarki suke zuwa fadar sarki kawo gaisuwa Dan Haka dik ranan jumaa zakaga cikin gidan tamkar Ana wani shaani,
Zazzaune suke a babban parlorn gidan kowa ya hallara anata ciye ciye,
Yatsina fuska tayi kadan "nikam banajin zan Shiga duba zainul yau ko zakuje ni boyewa zanyi Dan banjin zan iya Kai kaina ganin wanan kazantar dake cikin wanan dakin"ta karasa maganar hade da yatsina fuska,
"Kai warisat kada ki manta ya zainul fa Dan uwanki ne be kamata ki kyamace sa ba kiduba halin da yake ciki"
Dan tsaki tayi tana dubanta cike da tsiwa"banson iyayi zahira Zaki fara Koh?kinji nace dama ba Dan uwana bane?kawaidai banida raayin zuwa dubasa ne"ta kauda kanta gefe,
Tabe bakinta zahira tayi "kedai kikasani mu zamuje mu dubashi idanke bazakije ba Kuma ya zainul a tsaftace yake masu kula dashi suna iya bakin kokarinsu sanan ummaty ma Tana tare dashi ai Yar sarkin dawaki"
"Kwadayi ne kawai yasa take makale a gidan sarauta da son asani"
Wani dogon tsaki fiyya tayi daga gefe dik hirar da cousins din nata sukeyi a kunnenta tsananin takaicin kalaman warisah ne yasa ta tabar parlorn Dan ji take tamkar ta shaketa,
*********
Karatun alkurani takeyi da muryarta Mai dadin saurare ya kafeta da idanuwa da alamar yanajin dadin yadda take karatun,....shigowarsu tawagarsu yasata zumbur ta Mike tsaye jikinta na rawa ta zube a kasa Tana kwasar gaisuwa wajen dattijuwar matar da aka shigo da ita wadda ta kasance kakar zainul abideen ta wajen uba.....wani irin kallon kyama da wulakanci warisat da zahira suke bin ummaty dashi Wanda yasata kasa tsayuwa a wajen tayi hanyar fita.....
*SLIMZY😍*
[1/23, 10:32 AM] 😍SLIMZY😍: *HASKE WRITERS ASSO....💡*
💞 *ZAINUL ABIDEEN💞*
*SLIMZY✍🏼*
*Wattpad@slimzy33*
*4*
Gefe ta nema ta raku'be zuciyarta Babu Dadi,kwata kwata batajin dadin yadda warisat takeyi Mata dik lokacin da zasu hadu sai ta bi ta da wanan kallon na wulakanci da kyama Amma hakanan take jurewa,
Hajiya ce ke kallon zainul abideen Wanda shima idon Nasa akanta yake kallo daya zakayi mishi tausayinsa ya kamaka duba da yanayin nasa Amma hakan be hanashi murmushi ba dikda murmushin ba fita sosai yakeyi,ba itama murmushin ta maida Masa takai hannu ta shafa sumar kansa "ikon Allah sai kallo sannnu zainul Allah ya kawo karshen wanan rashin lafiyar taka ya baka lafiya magajin baba"
Jinjina Mata Kai yayi "ameeen hajiya... Kaka"yadda yayi maganar bakinsa na furzar da miyau sai ya baka tausayi,...jin dadin maganar tasa yasa kakarsa sakin kayataccen murmushi Tana shafa sumar kansa,
Daya bayan daya suke karasawa kusa dashi suna duba jikin nasa yayyinsa manya Mata guda uku sai kannin mahaifinsa Mata da iyalansu Suma suna dubashi cike da tausayawa,
Hajiya ce ta dubi warisat da zahira dake gefe suna yatsina fuska tamkar sunji wari ta daure fuskarta "ku kunfi karfin kuzo ku duba jikin yayan naku ne kuna raku'be gefe daya?"
Tura Baki zahira tayi sanin halin kakar su Bata daukar raini yasa ita takaraso gaban gadon Tana magana Tana yatsina fuska ta gaisheshi Banda warisat da ko kallon gefen da suke batayiba ta maida kanta gefe,
A fusace mahaifiyarta ta dubeta "me kike nufi ne warisat?ke kinfi karfin ace kiyi Abu kiyi ko?hajiya Bata isa tace kiyi Abu kiyi ba kenan to karyarki yarinya kafin in bude idanuwana kinzo kin cika umarninta kafin in tattakaki"
Murmushin takaici gimbiya rumana tayi tana karewa warisat kallo Sanan ta dubi mahaifiyarta tace"hajiya kubra kibita a hankali yarinya ce"...
Dakyar warisat ta Tako gaban gadon Tana Harare Harare ta tsaya ta wani bishi da mugun kallo ta kauda kai Tai Masa ya jiki sama sama ta juya Tana wani irin taku,kallo zainul ya bita dashi ya rufe idanuwansa gammn....
Sun dauki lokaci a sashin na zainul sanan suka fito a waje sukai Karo da ummaty tsugunne,
"Allah sarki yarinyar kirki Allah yayi Miki albarka yasa ki Gama da duniya lafiya yadda kike kokari da zainul kinji?"cewar hajiya kakar zainul,
Murmushi ummaty tayi ta sadda kanta kasa,
.
Tabe baki warisat tayi "kwadayi ne kawai irin na yaran talakawa shiyasa ta manne"...kowa yaji abinda tace Amma suka basar sukai gaba ummaty tabi bayansu da kallo,ta Dade tsugunne sanan ta Mike jiki a sanyaye tayi hanyar Shiga wajen zainul
*********
"Banji dadin abinda kikayi ba warisa,wanan abun da kikayi kika nuna kyamar dan uwanki a cikin mutane kin Saida mutuncinki ne a idon kowa kina tunanin iyayensa zasuji dadin abinda kikayi?koko Mai martaba idan yaji labari zaiji dadin abinda kikayi warisah?"
Turo baki tayi batare da tace komiba yadda uwar ke zazzaga Mata masifa tamkar zata daketa,
"Haba momy nifa ba kyamarsa nakeyi ba"
"Ubanki kikeyi ba kyamarsa ba?Ina ganin take taken ki kema bakifi karfin Allah ya maidake haka yadda kika ganshiba, wanan yaron da kike gani yafiki gata a wajen kowa a dangi Dan dai Allah yayoshi Haka ne Dan Haka kibi a hankali shashasha kawai"
Tana gama fadin haka ta wuce tabarta Nan zaune Tana ture turen Baki,
Wata baiwace hannunta dauke da tray tazo wucewa ta karamin parlorn ta Dan durkusa ta gaida warisa wadda ke zaune kafarta daya Kan daya harta wuce ta Kira sunanta a wulakance "ke sadiya zo Nan"da sauri ta zube a gabanta
"Ina zakije da wanan tray din?"
"Ummaty ce tace a dafowa yarima zainul hanta ruwa ruwa ko zai iyaci shine na dafo mashi"
"Jeki"...shine amsar data Bata a takaice ta Mike jiki na rawa,
Lallai yarinyar Nan wato har mukaminta yakai tasa bayi Abu suyi?ita wacece?waye ubanta inba sarkin dawaki ba?samun gurin nata har yayi yawa ace tanabawa maaikatan gidan sarki izinin suyi Abu suyi wadda ita kanta Bata wuce a aiketa tajeba tunda ubanta shi kansa be wuce a aikeshi ba "mtseww"tayi Tsaki a Fili ta janyo Jakarta ta rataya ta dauki gyalenta Tai waje.....
*********
"Umma..ty Ina matukar jin dadin karatun Nan da kikemun sosai waya koya Miki?"yayi maganar a hankali dikda maganar ba fita takeyi sosai ba Amma ta fahimci abinda yake nufi hakan ne yasata sakin lallausan murmushi Wanda wushiryar bakinta ta bayyana,
"A makaranta aka koyamun Yaya zainul shine nikuma nake koya maka saboda inaso ka iya karatu da rubutu"
Dan murmushi yayi kadan miyau ya zubo daga bakinsa tasa Dan towel din da take goge Masa ta share Masa,"ta Yaya zanyi karatu da rubutu bayan ga halin da na tsinci kaina ciki?"
Ta bude baki zatayi magana aka turo kofar aka shigo hade da sallama,
Ganin wadda ta shigo yasata sauri zubewa a kasa, gimbiya bilkisu ce mahaifiyar zainul abideen sanye da tsadadden leshi ja da Baki ta yane jikinta da lafaya hannunta sanye da kambu na ruwan gold dazobba na zinari zagaye da yatsunta fuskar Nan Tata ma dauke da kyau da kwarjini irin na sarauta kamar kullum haka ta karaso gaban tankamemen gadon da zainul abideen ke kwance ita kadai ta shigo Babu Yan rakiya masu take Mata baya....
"Barka da yamma ranki ya dade"shine gaisuwar da ummaty Tai Mata,
Dafa kanta tayi tana shafawa batare da tace komiba ta juya ga d'an nata da tunda ta shigo hankalinsa ya koma ga mahaifiyarsa,yau shigowarta hudu kenan wajensa dikda suna Zama sashi daya Tana iya juyo motsinsa Amma hakan be hanata zagayowa lokaci lokaci,
"Yarima na ya jikin naka?da sauki Koh?mekedamunka yanzun?"lokaci daya ta watso Masa wadanan tambayoyin,
Girgiza kansa yayi "Babu abinda ke damuna ammiey"ya Bata amsa a hankali harshensa na hardewa,
Yadda yake maganar kadai Saida yasa kwalla ta ciko a idon gimbiya bilkisu Amma gudun kada ya fahimci wani Abu yasata dannewa tai murmushi ta juyo ga littafin da ke gefe takai hannunta ta dauka Tana dubawa,murmushi kawai takeyi Tana dubba littafin ta Dan juyo kadan ta dubi ummaty dake tsugunne a gefe "ummaty karatu kike koyawa yayan naki ne?"
"Ehh ranki ya ammiey"
"Masha Allahu hakan nada kyau"bata sake cewa komiba ta Dade zaune tare dasu kafin kanwar zainul afnan ta shigo da gudunta ta fada jikin mahaifiyarsu Tana zuba Mata surutu suka fice tare....
********
Tunda ummaty tazo gida yau takejin jikinta wani iri a Haka Tai sallar magriba tazo ta zauna gefen mahaifiyarta,
Ganin yanayin da ummaty ke ciki yasa Inna ta fahimci akwai wani Abu "ummaty lafiyanki kuwa?tunda kika dawo yau naganki sukuku kamar wani Abu ya faru"