← Book details Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 49

Sashe 29

Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani bakin ciki ne ya rufe Masa idanuwa ya Mike a haukace "saboda y'ata ce ko yarki ce?kece kika haifamun ita da zan bada umarni kizo kina tambayata kina Shirin gindaya mun sharadi?saboda son Rai da son zuciya irin naki?saboda rashin Imani da tsoron Allah ,kin isheni kin zamewa rayuwata bala'i gabaki daya kinsani a rudani to Bari kiji wanan karon baki isaba wallahi zan fito fili insanarwa da ummaty ko kedin wacece"...wata uwar tsawa ta daka mishi hade da mikewa tsaye a haukace "sarkin dawaki!!!ya isheka da yimun tsawa,ko ka manta a gaban wadda kakene?in tuna maka?ka manta a gaban gimbiya rumana kake har kake daga murya sama Akan tata?to ka Shiga taitayinka tun kafin insaka fadawa su fitar dakai can bayan gari su dauremun Kai a jikin dutse su farfasa maka jiki da bulala,su shafa maka gishiri su gana maka azaba Mai radadi"ta karashe maganar tana huci hade da nunasa da yatsa tana huci kirjinta Yana hawa Yana sauka....shiru sarkin dawaki yayi batare da yace komiba sai bugawa da zuciyarsa keyi sauri da sauri ta cigaba da magana "maganar kaje ka fadawa ummaty koni wacece ka Dade baka fada mataba sarkin dawaki ni zanfi so kasanar da ita hakan Amma idan katashi ka hada da kanka yadda zatayi danasanin zamowa daga cikin tsatsonka yadda zataji tsanarka fiye da kowa a rayuwa...Ina rokonka kada ka fasa yin wanan mugun gangancin Wanda guguwar ajali ke dibarka,a kashe abinda zan sanar dakai shine umarni ne wanan baka Isa ka ketare ba Dan haka zan siyawa ummaty waya karka kuskura kayi yunkurin karbar wayar Nan a hannunta kaji na fada maka,shashasha tashi ka fice kabani waje"...

Babah kande dake makale Tana sauraron hirarsu duka Jin sarkin dawaki zai fito tayi wuff ta fada wani daki dake gefe Wanda Babu komi ciki sai abincin doki....makalewa tayi jikin bango har ya wuce besan da mutum a wajenba...sosai baabah kande ta furgita kwarai da Jin hirarsu tabbas tasan da saka hannun gimbiya wajen rashin lafiyar zainul Amma Bata taba tunanin akwai sarkin dawaki ciki ba mahaifin ummaty... baabah kande ta tsorata matuka da wanan hirar da taji wato kenan da mahaifinta ake amfani da ita wajen jefata cikin halaka ba tare da tasani ba "innalillahi wa Inna ilaihi rajiun tabdijan"tasa hannu ta goge zufar da takeyi ta gyara daurin Dan kwalinta dake Shirin faduwa...tabdijan akwai gwarama, Yaya ummaty zataji idan tasan da saka hannun mahaifinta a ciwon zainul?ya Mai martaba zaiji ranan da dik wanan kwai me wari ya fashe cewar babban me bashi shawara a fada ya dauka shine babban makiyinsa...tabbas wanan shi ake cewa makashinka Yana tare da Kai...dik na sarkin dawaki me sauki ne Akan gimbiya rumana da Mai martaba keji da ita saboda yadda take kaunar gudan jininsa zainul abideen...girgiza Kai kawai baabah kande tayi jiki Babu kwari ta fito tana Jan kafa a hankali har ta fice ta kofar baya....

*WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS* *DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619*

*********
tun bayan da ta shafa Masa ruwan adduar da baabah kande ta Bata yasha Kuma ta shasshafa Masa a jikinsa yayi bacci tana zaune s gefenta tana kissima abubuwa da dama a cikin zuciyarsa tana kallon yadda yakeyin bacci Yana fuzge fizge tamkar wani Abu na fita a jikinsa minti minti yakan sauke atishawa da karfin gaske mikewa tayi ta tsaya akansa tana tofa Masa adduoi fuskarta dauke da damuwa dik tayi bakim Kirin saboda damuwar da ta tsinci kanta ciki....

*******
Kurrrr da Ido yayi mata Yana aika Mata sakkonin soyayya ta cikin kwayar idanuwanta yayinda itama ta kafesa da Ido ta kasa kauda idanuwanta cikin nasa fuskarta dauke da murmushi Mai kayatarwa...kashe Mata Ido daya yayi Wanda da sauri tasa hannu ta rufe idanuwanta tana dariya...."yayadai my princess kika rufemin fuskarki wadda ita kadai nake kallo injini cikin wata Duniya wadda ban taba tsintar kaina cikinta ba"

Mikewa tayi hannunta har yanzun rufe a fuskarta tana kokarin barin wajen yasa hannu ya riko hannunta ta Shiga kici kicin kwacewa "Kai ya zainul dik ka bani kunya wallahi"Tai maganar cike da shagwaba...

"Haba wareeh idan kintafi ya kikeso inyi kawo hannunki kiji yadda zuciyata ke bugawa "yakai hannunta kirjinsa daidai zuciyarsa...Jin yadda kirjinsa ke harbawa yasata saurin bude idanuwants aikuwa take idanuwansu suka hadu wani Abu taji ya soketa a kirji tamkar kibiya tayi baya zata Fadi ya fizgota ta fada kirjinsa...

Zumbur ta Mike daga kan gadonta rike da gefen kirjinta Wanda taji Yana sokawa kamar yadda taji a mafarkinta ga zufa da ta jike dashin tamkar an kwara mata ruwa,...lumshe idanuwanta tayi zuciyarta na ci gaba da bugawa ta budesu Akan agogon bangon dake manne a dakinta karfe hudu saura minti biyar na laasar...a hankali ta bude bakinta tana dafe da kirjinta "mafarki nayi?da sallar laasar da tsakiyar ranan Nan ba dare ba?"...daidai Nan hajiya kubrah ta turo kofar dakin bakinta dauke da sallama, hango Yar tata da tayi zaune yasa tun kafin ta karaso take fadin "Ashe kintashi ma,na turo a tasheki akace kinata bacci sai nace a kyaleki"shiru warisah batace komiba idonta na tsaye waje daya ta lula duniyar tunani,

Tabata uwar tayi "ke lafiyanki kuwa?"

"Momy mafarki nayi"Tai maganar a sanyaye...

"To kindaiyi addua da kika tashi koh?sai Kuma ki Mike kiyi sallah"

"Momy mafarkin ya zainul nayi"...cakkk hajiya kubura ta tsaya tana kokarin fita da , takai seconds ashirin sanan tayi murmushi ta kada Kai ta fice dakin ba tare da tacewa warisah komiba...

A sanyaye tayi alwala tazo ta tada kabbarar sallah tanayi Amma hankalinta baya waje daya a daddafe ta idar da sallar ta zauna kan dadduma dik jikinta ya mutu da ta rufe idanuwanta sai zainul take gani yanayi mata irin murmushin da yakeyi mata a mafarki ga zuciyarta dake hautsunawa tamkar zata fito kirjinta..."Allah yasadai ba ciwon zuciya bane yake Shirin kamata na Yan mintuna...

Turo kofar akayi da sauri ta dago Kai dikda taji kamshin turaren nasa tasan ko waye ,kyakkyawan saurayi ne ajin farko ya shigo dakin fuskarsa Babu yabo Babu fallasa ya dubeta "ke warisah dazun na tambayeki Baki bani amsa ba"
Turo Baki tadanyi "ya haris bansan mezance makaba dikda idan na fahimceka wadda kake tambayar wacece din ummaty ce me jinyar ya zainul Yar sarkin dawaki, shikenan"..murmushin gefen fuska yayi yasa hannu ya shafa gashin kasa "well kince yau zamu koma ingaida Mai martaba ya kamata muje koh?Kuma Inga jikin na zainul abideen,Allah sarki aminina tun muna yara Allah ya bashi lafiya"

Ameen tace kirjinta Yana bugawa "Bari in shirya ya haris sai mu dauki zahira muje koh?"..ya gyada mata Kai ya juya Yana takunsa na takama da Isa,har ya Kai kofa ya juyo "idan munje zan ganta?"

Tadan zaro idanuwa"ita wacee?"

Sai ya basar "share kawai"yace ya fice ta bishi da kallo tana tabe Baki...

*******
Sabuwar waya galleliya gimbiya rumana ta Kira ummaty ta bata Tai Mata godiya sosai ta fito cike da farin ciki tayi wajen aminiyar tata babah kande "babah kande Kinga wayar Nan kafin inje gida zanje wajen likitan waya na unguwar mu ya koyamin ita ya saitamun recording cikinta sanan ya nunamin abubuwa sosai"

Gyada Mata Kai babah kande tayi Tana murmushi "hakan nada kyau ummaty yanzun ayi haramar tafiya gida dare zai Miki a hanya gashi kince Zaki biya wani waje"

"Sainaje wajen ya zainul munyi sallama,yanzun zantafi baabah kada ki manta kince idan nazo gobe Zaki sanar Dani tarihin gidan Nan da mu kanmu yadda muka taso"

"Insha allahu ummaty Allah dai ya kaimu goben da Rai da lafiya"

"Ameen tace"ta Mike ta tafi...

********
Jin alamar da mutane dakin yasata faduwar gaba dikda batasan kosu waye ciki ba,ta Dade a kofar dakin sanan ta tura kofar hade da sallama a bakinta...binsu takeyi daya bayan daya sanan ta sadda kanta kasa ta gaida ya haris Wanda besan tanayi ba ya shagala wajen kallonta...Shima Kuma zainul idonsa kirrr Akan su duka Yana binsu da wani irin kallo.....

Warisah kuwa tabe Baki tayi ta kauda kanta gefe saboda bakin ciki......

*WANAN LITTAFIN NA KUDINE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619*

💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞

*HASKE WRITERS ASSO💡*

*SLIMZY😍*
[1/23, 11:12 AM] 😍SLIMZY😍: 27

Kallon da haris ke bin ta dashi yasa dik ta tsargu sanan babban abinda yake Bata mamaki be wuce warisah da ta gani zaune kusa da ya zainul ba hannunta rike da cup din da yake Shan ruwa dashi da alama Shan ruwan tayi,dago idanuwanta tayi a Karo na farko ta saci kallon gefen da warisah ke zaune taga yadda take Yi tamkar ba itaba sanan ta juyar da dubanta ga gefenta kararff suka hada dashi a Karo na uku dakyar tayi karfi da jikinta ta Mike tsaye cikin sassanyar muryarta ta dubi zainul abideen sukai Ido hudu ta sakar Masa wani lallausan murmushi sai kawai ya cije lebensa Yana kallonta "ya zainul zan tafi sai Allah ya kaimu goben"ta tsaresa da Ido...

Wani irin Abu ne yaji yanayi masa yawo a cikin jikinsa da wata irin kasala da ta saukar Masa dakyar ya sauke ajiyar zuciya yace "to ummaty sai Allah ya kaimu kifa zo da wuri kinji"

Gyada Masa Kai tayi Tana murmushi "angama ranka ya Dade insha allahu"..Shima gyada mata Kai yayi Yana murmushi sai kawai ta dauki Jakarta tayi hanyar fita,har ta Kai kofa ya haris yayi saurin fadin "mu baxaayi Mana sallama ba "cakk ta tsaya gabanta na tsananin faduwa Wanda batasan dalilin hakan ba,sai kawai ta juyo a hankali ta sakar Masa murmushi "to sai anjimanku a gaida momy"...lumshe idanuwansa yayi batare da yace komiba tasa Kai ta fita...

Wani tsaki warisah ta sauke ta kauda kanta gefe zuciyarta nayi Mata tsananin zafi na takaicin ummaty da wutar tsanarta dake Kara ruruwa cikin zuciyarta..

"Abokina Amma jikin Nan naka yayi kyau gaskiya nayi matukar farin cikin ganinka a wanan yanayin Allah ya Nuna mana ks taka da kafafuwanka"yasa hannu ya dauki banana tana barewa
Chapter 29 · 0% Book details