← Book details Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 49

Sashe 16

Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A can fada suka tarar da zuwan ya musaddik da zahira wadanda zaayi tafiyar tare dasu wanan Karon Banda warisah ,sai wani rawan Kai zahira takeyi Tasha ado ta Sanya wani tsadadden lece ja me flowers golden ba karamin kyau tayi ba cikin Dinkin Riga da sket da yayi matukar karbar fatar jikinta ta yafa gyale red da Jakarta golden takalmi golden shi Kansa musaddik yayi matukar kyau gida ya cika sosai da tawagar Yan rakiyarsu da motoci da bayi da fadawa da aka hadasu dashi tamkar da shi Kansa sarkin zaayi tafiya Yana tsaye yasha rawani sai jinjina Kai yakeyi duka yaran suke zuwa daya bayan daya sunayi Masa sallama fuskarsa dauke da faraa da kulawa yake amsa musu ganin musaddik Saida yaji wani Abu cikin ransa ji yakeyi inama ace da zainul abideen zaayi tafiyar Nan ba Mata ba shida ya kasance magajinsa Kuma babban da'nsa na miji Wanda inda lafiyarsa kalau da dik wani Abu shine zai rinka wakiltar Mai martaba Amma ga yadda Allah yayi dashi....ganin canjawar fuskar Mai martaba yasa gimbiya rumana fahimtar wani Abu a cikin ranta tasani Sarai da zainul abideen lafiyarsa kalau ba karamin banbanci zai Nuna ba Dan tundaga haihuwarsa kowa ya fahimci sarki na mugun sonsa sanan ya zamana shine kadai da namiji Wanda ya Haifa Dan hakan bazata taba Barinsa ya Zama Yana cikin lafiya ba saidai in mutuwa tayi Dan tsatson bilkisu bazai taba gadar sarauta tana raye ba,hakan zai Kare rayuwarsa a kwance sarauta shi da ita sai a lahira...

*********
Zaune take gabansa Yana zaune a wheel chair dinsa yau dik Wanda ya gansa yasan akwai alamar sauki a tattare da shi kasantuwar kwana biyu ciwon nasa be tashiba Dan har wata Yar kiba yayi sosai ga Kumari jikinsa yayi sanan wuyansa dake karyewa wani lokaci be tsayawa yanzun Yana tsayawa ga maganarsa dake fitowa sosai yanzun Babu laifi

"Ya zainul kaganka kuwa yadda kayi "ta kashe Masa Ido daya cikin sigar zolaya

"Menayi kanwar ya zainul"ya kwaikwayi maganarta Yana murmushi...sai kawai ta turo Baki cike da shagwaba "shine kake kwaikwayon maganata?"

"Yi hakuri nadaina tunda bakyaso kinji kanwata"yayi maganar cikin sigar lallashi "oya yanzun gayamun menayi"

"Kayi kyau kayi kiba sosai gashi kwana biyu ciwonka alhamdulillahi baya tashi"...jinjina Mata Kai kawai yayi batare da yace komiba...

Hakan suka wuni tare suna hirarsu cike da nishadi Wanda akasari inhar zata tafi gida dakyar take tafiya,ita kanta yanzun ko a gida cikin tunaninsa takeyi batada wani aiki Wanda ya wuce zancensa Koda da innarta ne wani lokaci sai ta ji inama ta zauna tare dashi su dawwama a hakan,yau ma hakan ta kasance Dan ta manta da zancen wani magani da gimbiya rumana ta Bata,Dan yanzun ta fara Jin ciwo idan ta gansa Yana wahala ta dalilin maganin shiyasa ita kanta ta yanke shawarar tsayawa da basa maganin ta dalilin wani tunani da shiri nata nadaban....akwai abinda takeso ta gasgata game da hakan,tanaso ta fahimci hanyar da gimbiya rumana ta bulla Amma zuciyarta nayi Mata kokwanto Akan yuwuwar hakan....inhar haka ne abinda takeji zuciyarta na fada Mata to tabbas zasu fara Wasa ita da ita saidai idan ta tuna wani Abu zuciyarta na tsananin bugawa,takan tsinci kanta cikin mummunan tashin hankali tsoro da furgici ke lullube Mata zuciya....

*******
"Idan har ya kasance abinda kika fadamun gaskiya ne hansa'u to tabbas daga ita har ubanta sun Gama yawo a cikin garin Nan"...

"Ranki ya Dade bana taba Baki labarin karya sai na tabbatar dashi abinda na fada Miki gaskiya ne ranki ya Dade"....

Mikewa gimbiya rumana tayi ta Shiga kaiwa da komowa a cikin patlorn tana jinjina Kai cike da tashin hankali.....

*WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN 08166177830 KO 07084161619*

*HASKE WRITERS* *ASSO💡*

*ZAINUL ABIDEEN💞*

*SLIMZY😍*
[1/23, 10:43 AM] 😍SLIMZY😍: 15

*******
"Meyasa kikeso kiyi mun Wasa da dukiya da lafiyar yarona ummaty?"gimbiya rumana ta jefa Mata wanan tambayar Wanda take kirjin ummaty yayi wani irin bugu Wanda Bata taba Jin irinsa ba...ta tsorata matuka da tambayar Amma sai tayi shiru batace komiba kirjinta na cigaba da bugawa...

Cikin sigar lallashi gimbiya rumana ta matso daf da ummaty tana fadin "haba ummaty meyasa zakiyi haka umm?yanzun maganin da nake kashe kudi Ina amsowa yaron Nan ya warke Ashe bakya bashi?"da sauri ummaty ta dago Kai cike da fargaba da mamaki?ta Yaya tasan Bata bashi magani ba kwana biyu?yadda take kallon gimbiya yasa ta gyada Mata Kai tana furzar da iska a bakinta "ehh ummaty Baki bashi ba Mana,nakosa insamu gagarumar kyautar girma daga Mai martaba dik ranan da zainul ya warke na bayyana Masa cewar nice silar warkewarsa da ke to na tabbatar da ke Kanki Zaki samu kyauta da girmamawa na ban mamaki saboda Babu abinda Mai martaba yafi bukata a yanzun haka sama da lafiyar zainul abideen,ba wani Abu yake kwadayi ba kamar da'nsa ya gaji sarautarsa,Kinga Babu yadda zaayi a dauki sarauta a bashi a cikin wanan halin,ki tausayawa Mana ummaty"...dik maganar da gimbiya ke Yi ummaty nada ko kwanto akan maganar,sosai ta Shiga rudani fiye da Wanda take ciki a kwanakin Nan Amma akwai abinda zatayi ta warware kokwanton da zuciyarta keyi Mata,sai kawai ta sauke ajiyar zuciya ta dubi gimbiya..."ranki ya Dade ni kaina Ina tayaku alhinin wanan kaddarar da kuke tattare da ita ta ciwon danku daya tilo,insha allahu Zanyi bakin kokarina wajen ganin min cimma nasarar sama mishi lafiya"

Murmushi gimbiya rumana tayi "alhamdulillahi nagode ummaty nagode sosai da wanan goyon baya Allah Kuma ya bamu saa"

"Ameeen"ummaty tace cikin tsananin rudani take Wanda kana kallon yadda take hada gumi kasan akwai wani Abu can kasan zuciyarta,"karbi wanan na Shan yau ne da shafawa kibashi ki shafa Masa"

"Toh"tace ta karba cikin ladabi sanan ta Mike ta fita....tana tafe hansa'u na biye da ita a bayanta,take zuciyar ummaty ke sanar da ita akwai wani Abu a kasa Amma ko menene zatayi amfani da shawarar da zuciyarta ta Bata idan hakan ne zata fahimci ko menene Kuma karshen rashin lafiyar tasa tazo a hakan ta karasa sashin zainul abideen...

*********

Bacci sosai ta sameshi yanayi da alamar tun bayan da akayi Masa wanka ya koma baccin Dan hakan batayi yunkurin tashinsa ba saita ajiye Jakarta kasa gorar maganin Mai Kama da rubutu na ciki,

Yusha'u dake gefe sai leken jakar ummaty yakeyi cike da gulma ya taba dayan bafaden dake gefensa ya Nuna Masa a tare suka kalla sanan yusha'u yayi Masa alama da menene wanan din a Jakarta ,dayan ya girgiza Kansa alamar be saniba shidai yusha'u girgiza Kansa kawai yayi Amma zuciyarsa cike take da son sanin menene a ciki Amma sai ya share kawai...sun Dade zaune ganin ta dauko littafin adduointa tana karantawa sai kawai suka Mike dukkansu har zasu fita yusha'u ya dubi ummaty "idan akwai abinda yake bukata Wanda bazaki iyaba ki nememu a kofar gabas ta wajen sashin gidan waziri"...gyada masa Kai kawai tayi alamar to,yadan dubeta ya dubi jakar ya fice....

Ajiye littafin adduointa tayi gefen drawer saboda yadda zuciyarta ke azalzalarta akan abubuwa da dama,shin menene yasa gimbiya ta damu da zainul yasha magani ya samu lafiya?dik soyayyarce ko menene?sanan ta tabbatar Mata da tanason yasha magani batare da kowa yasan Yana Sha ba batare da kowa yasan suna bashi ba har Allah ya bashi lafiya,to ya akai tasan cewar Bata bashi maganin ba kwana biyu?meyasa ta damu har tasa akesa Mata Ido Akan tabashi ko Bata bashi ba?wani tasa ya da Ido ko kuwa zainul abideen din ta tambaya ya fada Mata?,kaiiii bazata tambayeshi bama tunda besaniba.....wadanan tambayoyin da batada amsarsu sune ke damunta cikin kwakwalwarta jiya zuwa yau da gimbiya ta tareta Akan hakan,ya dace tayi bincike sosai Akan hakan,to wa zata tambaya?.....take idanuwan ummaty sukai jajir saboda damuwa da tashin hankali,tagumi tayi ta zuba Masa Ido yadda yake bacci cikin kwanciyar hankali,kwana biyu da besha maganinba har yayi wata Yar kiba yasamu lafiya tamkar ba me ciwo ba....yanzun mafita shine kawai ki gwada bashi maganin Nan kigani idan ciwonsa zai tashi ko bazai tashi ba?idan zaisamu lafiya ko bazai samuba...bashi maganin shine zaisama Miki amsa guda daya cikin tambayoyin dake kunshe cikin zuciyarki...tambayar maganin na lafiya ne koba ba lafiya bane?"...zuciyarta ke karanta Mata wanan shawarar Wanda take ta amince da hakan ta sa gefen hijjabinta ta share fuskarta dake gumi kamar ana watsa Mata ruwa....Bata lura da tashinsa ba tayi nisa cikin tsananin tunani sai bayan ta share fuskarta ta dago idanuwanta da niyyar kallonsa suka hada Ido sai kawai ta sakar mishi lallausan murmushi "barka da tashi ranka ya Dade magajin sarki"tace tana murmushi,shi kuwa gabaki daya ita yake kallo Yana karantar fuskarta tun bayan tashinsa minti goma Sha biyar da suka wuce batasan idonsa biyu ba....kasa ce Mata komi yayi sai kallonta kawai da yakeyi kirrr kifta idonsa bayayi,ganin hakan yasata tunzuro bakinta gaba "ya zainul kayimun magana Mana inji Dadi,kasan tun yaushe nazo kana barci Kuma ka tashi baka kulani ba"Tai maganar cike da shagwaba,kamar daga sama taji Yana fadin
Chapter 16 · 0% Book details