Sashe 3
Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gabansa ne ya yanke ya fadi a karo na biyu Nan da Nan hankalinsa idam yayi dubu to ya tashi dik wata natsuwa dayake ciki ya nemeta ya rasa Jin abinda Mai martaba yace bakaramin dimaucewa yayiba Amma be nuna Masa hakan ba sai kawai ya Kara durkusawa sosai "ranka ya dade dik wani Wanda zaice ayiwa zainul abideen maganin gargajiya zaicene kawai a fadarsa Domin su kansu masu maganin yanzun baa yadda dasu musamman yanzun da macuta sukai yawa,so dayawa masu magani sukan hada surkullensu su mikawa mutum a matsayin magani karshenta idan yayi amfani dashi jikin mutum ya Kara rikicewa wasu har mutuwa ma sukeyi sanadiyyar masu magani ranka ya dade,ni a ganina a cigaba dayi Masa na asibitin kawai shine maslaha Domin yanzun Ana cewa zaakaisa gun magani to fa idan labarin hakan ya kaiwa wasu tsaf zaa cutar maka da danka kwaya daya tilo magajin ka Kuma ni a tawa shawarar idan ma rashin ci gaba ne a canja mishi wani asibitin a gwada basirarsu a gani ranka ya dade"
Numfashi ya sauke Mai martaba saboda bayanin da sarkin dawaki yayi Masa ya gamsu dashi matuka Dan kaf masarautar hatta su waziri be yarda dasuba kamar yadda ya yarda ya amince da sarkin dawaki dalilin hakan ne Yasa ake kiransa amintaccen sarki....
Da shawarar sarkin dawaki Mai martaba ya aminta na take ya watsar da sauran shawarwarin da sauran mutane ke bashi.....
********
Tallabo fuskarsa tayi tana Kare Masa kallo yadda kullum kamanninsu suke Nan sai Kara canjawa da yakeyi dikda rashin lafiyarsa da canjawar halittar bakinsa be hana kyawun fuskarsa bayyana ba,
Idanuwanta ne suka cika da hawaye "zainul nakosa ka warke hankalina ya kwanta insamu sassauci a zuciyata na ciwon d'ana, zainul Ina fatan batare da na mutu ba kasamu lafiya kaji?kaima ka canja ka koma ainihin mutum kamar kowa..."hawaye suka Shiga gangarowa a idanuwanta,...kansa ya Shiga girgiza Mata alamar ta daina kuka,dakyar ya motsa labbansa ya furta "ki...shi ru"murmushi gimbiya rumana tayi ta juyo ta dubi ummaty dake tsaye a gefe Tana dubansu cike da tausayawa lallai soyayyar da gimbiya rumana take nunawa zainul abideen soyayyace ta gaskiya Dan kullum batada wajen zuwa sama da wurinsa tana duba lafiyarsa minti minti ta shigo ta duba jikin nasa,
"Allah ya saka Miki da alheri ummaty yadda kike kulawa da zainul Allah ubangiji ya saka Miki da gidan aljannah yadda kika dauki dawainiyar zainul abideen muna matukar Jin Dadi da alfahari dake"
Kwalla ce ta cika idanuwan ummaty ta sunkuyar da kanta "babukomi ranki ya Dade koba komi zainul abideen yayana ne Dole in kula dashi"
Murmushi gimbiya rumana tana karewa yarinyar kallo cike da so da kauna,yarinyace karama Amma komi nata irin na manya ne ga natsuwa ga hankali dikda kananan shekarunta tasan yadda ya kamata tasan kyautatawa da tausayi,
Kuriiii yayi da idanuwansa akanta ko kiftawa bagayi ga miyau dake sauka daga bakinsa Yana diga a jikin rigarta Bata damu da hakan ba sai kuka takeyi Tana Kara tausayinsa
Nan da Nan jikinsa ya Shiga jijjiga kafafuwansa suna lankwashewa ko Ina jikinsa rawa yakeyi hankalinta ba karamin tashi yayi ba ganin yadda jikin nasa yakeyi, ta rikesa sosai dikda nauyin da taji yayi Mata be hanata rikesa da karfinta ba Tana ambatar sunansa a bakinta,
Ta dubi ummaty wadda dik ta rikice itama Tai saurin zuwa ta Kama matashi suka rikesa sosai,kuka kawai gimbiya rumana keyi Tana ambatar sunansa, Tana Kara rikesa,
*********
"Ni Kam narasa dalilin dayasa kika Shiga rayuwata kikai Kane Kane Babu Wanda kike takurawa saini,menayi miki haka ne kika gayyatoni kika tsundumani cikin halaka?"
Murmushin Nan nata ta sauke a fuskarta takai hannunta Kan glass cup na ruwa ta dauka ta kurba ta ajiye kofin sanan ta Soma magana,
"Bana bukatar jin wadanan tambayoyin daga gareka,ka Adana kalamanka kila zasuyi maka amfani Nan gaba,...inaso ka saurareni sosai da kunnen basira inaso kasani idan har kace xaka bijirewa umarnina to tabbas kashinka ya bushe,...bawani Abu bane yasa na kiraka nakiraka ne in Kara jadadda maka maganar da mukayi jiya Akan yarka ummaty inaso ka datse alakarta da zainul idan ba hakaba zanyi maka alkawarin nadama"
A fusace ya juyo Yana kallonta idanuwansa sunyi jajir ransa a bace "nagaji da wadanan dokokin da kike gindayamun akan me? menayi miki?me yarinyata tai Miki?yadda kika jefaki cikin halaka itama kika dauko hanyar jefata cikin halaka kina tunanin Allah zai barki ne?koko kina tunanin Babu lahira ne?dik abubuwan da kikesani nake aikatawa nake kullawa be isheki ba kenan?saikin hada da Yar Dana haifa?to nagaji wallahi banki asirinmu ya tonu ba Koda hakan na nufin karshen numfashi na a duniya"
Dariya sosai takeyi Tana dubansa yadda yake kumfar baki ta nunasa da yatsa "dubesa saikace wani mutumin airziki Kai a tunaninka idan kwai ya fashe har Dani zata shafa?hmmm bakasan koni wacece ba har yanzun wallahi,shawara daya ce zan baka shine ka kwantar da hankalinka ka saki jikinka yadda muka dauko tafiyar Nan tare mu cigaba tare kabi umarnina sabawa umarnina tamkar barazana da rayuwarka ne Dana iyalinka...."
Zufa ce kawai take tsattsafowa ko Ina a jikinsa ta Yaya zai Soma tunkarar ummaty da wanan maganar?shin Yaya zata dauka?me hakan ke nufi?.....
*SLIMZY😍*
[1/23, 10:31 AM] 😍SLIMZY😍: *HASKE WRITERS ASSO...💡*
💞 *ZAINUL ABIDEEN💞*
*SLIMZY✍🏼*
*Wattpad@slimzy33*
*3*
Nisawa yayi ya sauke ajiyar zuciya ya dubeta a karaye, "kina ganin raba ummaty da zainul shi zaisa kisamu cikar burinki na ganin cewa zainul abideen bashida sauran amfani a masarautar Nan da doron kasa?idan har kikace sai na raba ummaty da zainul abideen zanyi hakan Domin cika umarninki Amma kisani boyayyen kudirinki da nufinki bazai cika yadda kikeso ba Domin ita yarinyar itace jigon tafiyar Nan da mukeyi,rabata da zainul abideen zai kawo cikas a wanan tafiyar da muka dauko muna gab da samun nasara"
Kallonsa tayi na dan wani lokaci Sanan da kauda idonta kamar bazatace wani abuba sai ya tsinkayi muryarta "ta Yaya kake ganin tafiyar bazata yuwuba sarkin dawaki?"
"Idan muka Raba yaran Nan babu hanyar da zamuyi amfani da ita wajen bashi magungunan da muke bashi,ko kin manta cewa ummaty ce take bashi magani idan ankarbo?ko kece Zaki bashi idan anrabasu?kisani idan na rabasu to wallahi baki isa ni kisani kice nine zan cigaba da wanan aikin na hatsari ba don itanma dabara nayi Mata yasa kikaga komi Yana tafiya daidai yadda mukeso"
Juyowa tayi wanan karon Tana fuskantarsa fuskarta Babu annuri tamkar Bata taba dariya ba a duniya cikin kakkausar murya wanan karon ta Soma magana,"naji na amince da dik bayaninka na fahimceka Amma kasani wallahi tallahi bazan taba amincewa soyayya ta kullu tsakanin yaran Nan ba,idan har hakan ta kasance to har Yar taka zan batar da ita a doron kasa"
Wani irin faduwar gaba ya tsinci kansa Nan da Nan jikinsa yayi sanyi Jin abinda tace"Babu soyayya a tsakanin me lafiya da nakasasshe,sanan babu soyayya ko aure tsakanin me hankali da Wanda bashida hankali Wanda bashida sauran amfani a wanan duniyar,bazan taba lamunta diyar Dana Haifa a cikina me cikakken koshin lafiya ta auri wanan nakasasshen kotayi soyayya dashi ba,Dana fahimci hakan nidakaina zanyi amfani da almakashi in datse alakarsu Dan Haka ki kwantar da hankalinki ummaty batakai shekarun da zata kulla soyayya yanzun ba dududu kwaya nawa take?inaji yanzun ne zatayi shekara goma Sha bakwai shi kansa zainul din Ina ashirin da biyu yake?Babu Hadi"
Ajiyar zuciya ta sauke Ta tsugunna ta dauke hand bag dinta dake gefenta ta zuge zip din Jakarta ta ciri wrappers din kudi Yan dubu dubu guda biyu dubu dari biyu kenan ta Mika Masa "ga sadakin ka Nan buri na be wuce in bude Ido Inga gawar zainul abideen ba dikda boka ya sanarmun da cewa mutuwarsa tanada wahala,to tunda bazai mutuba ya dawwama a kwance har karshen rayuwarsa"....Tana Gama magana ta juya Tai hanyar fita abinta,
Kudin da ta Mika Masa yake bi da kallo zuciyarsa cike da fargaba
**********
"Ya zainul kagafa yamma tayi Kuma munyi karatu gobe Insha Allahu zan Kara maka a inda na tsaya yanzun zanyi Shirin tafiya gida sai idan Allah ya kaimu gobe ko?"
Canja fuskarsa yayi Nan da Nan ganin tanata Shirin tafiya gida ta barshi kusan dik lokacin da ummaty zata tafi gida to Nan da Nan fuskarsa takan nuna damuwa a kwayar idonsa,Tana Shirin daukar Jakarta ta waigo ta dubi inda yake kwance miyau na gudu a bakinsa suka hada Ido taga kamar hawaye a makale a Ramin idanuwansa,...tausayinsa ne ya lullubeta taji jikinta yayi sanyi ta janyo kujerar gaban gadonsa ta zauna dafdashi Tana Kara kallonsa cikin tausayawa, "ya zainul kardai kacemin abinda nake gani a kwayar idonka hawaye ne na tafiya da zanyi inbarka?Koda na tafi akwai masu kula dakai ya zainul Kuma gobe zanzo kaji?"ta karashe maganar idanuwanta cike da kwalla saboda tausayinsa,...ga mamakinta sai ya Shiga girgiza kansa alamar be yarda ba,
Numfashi ta sauke tasan zaayi haka musamman yau da suka wuni ita dashi batare da ciwonsa ya motsaba tasan inhar zata tafi sai sunyi drama gashi kuwa,ganin ya kafeta da Ido yasa ta boye kwallar dake makale a idanuwanta,"kaga kayi hakuri ya zainul bazai yuwu in kwana a wajenka ba kaji?Amma Ina Mai tabbatar maka da insha allahu da kaina zan tasheka a bacci gobe saidai ka tashi ka ganni nayi maka alkawari kaji ya zainul?umm?ka yarda?
Gyada Mata Kai yayi Yana murmushi,itama murmushin ta maida Masa ta Mike ta dauki Jakarta tabi hanyar kofa ya bita da kallo harta bace sanan ya rufe idanuwansa shikadai a daki Dan fadawan dake kula dashi wani lokaci sukan fice su barshi dagashi sai ummaty
*******
"Meya hanaki bacci har wanan lokacin rumana?"Mai martaba ya jefo Mata wanan tambayar Yana karasa shigowa cikin dakin Yana sanye da Yar shara irinta sarakai ya nemi gefen gadonta ya zauna,
",Ki duba kigani yanzun kusan karfe goma Sha biyu da rabi na dare har yanzun Baki bacci ba ko akwai wani Abu ne?"..