← Book details Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 49

Sashe 34

Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Cikin kwanakin Nan na rasa abinda yake damunki ummaty Kuma dik Wanda ya ganki yasan akwai damuwa tattare dake kina boyemun hakan ne saboda ban cancanta kifadamun ba ko"ya kafeta da isanuwansa da wani irin kallo me dauke da sakwanni kala kala,

Muryarta na rawa zuciyarta na bugawa sauri da sauri tace"ka cancanta kasani sanan matsayinka ya wuce dik wani Abu daya dangani ummaty"ta kifta Masa idanuwa Tana murmushi,Shima murmushin ya maida mata "idan har hakan ne Ina bukatar sani"

"Akwai lokaci da zaiyi Wanda zan sanar maka Dan haka ka kwantar da hankalinka"

"Shikenan Allah ya kawo wanan lokacin"...ameen tace hade da sauke sassanyar ajiyar zuciya,kallo ya bita dashi Yana matukar tausayinta dikda besan dalilin hakan ba"....

**********
Wani kallo takeyiwa musaddik ji takeyi tamkar ta shakesa saboda tsananin kiyayya,da yasan yadda take kiyayyarsa da be ko kusanto inda take ba ita dik abinda ya dameta ya dameta Dan haka kauda kanta tayi gefe guda ya cigaba da magana "warisah zuwa yanzun ya kamata kibani dama domin bayyanawa zuriar gidan Nan abinda yake tsakanina dake Dan idan banyi wasaba soyayyarki tana iya kaini kabari"...yadda ta kafesa da Ido Shima haka yake kallonta ita kuwa tunda ya soma magana fuskarsa ta rikide mata ta koma ta zainul abideen har ya Gama tayi nisa cikin tunani hade da kallonsa shiko zuciyarsa ce ke wani irin bugawa jira kawai yakeyi ta amince masa Dan yagama yarda da cewar Tana sonsa kenan tunda take binsa da kallo Mai dauke da soyayya "kiyi magana masoyiyata"

Sai lokacin ta dawo daga duniyar tunanin da take ta saki wani mugun tsaki ta Mike daga palon tayi hanyar dakinta tana tafe Yana bin maxaunanta da kallo kirar jikinta kadai ya Isa dik namijin daya kalleta ya Kara kallonta...iska Mai zafin gaske ya furzar daga bakin sa zuciyarsa nayi Masa tsananin Kuna...

Kan gadonta ta fada ta fashe da kukan takaici kullum abinda takeji dangane dashi karuwa yakeyi Kuma kullum sai yazo Mata cikin mafarkin ta Wanda tarasa dalilin wanan bakon al'amarin....hannu tasa ta share hawayenta ko giyar wake Tasha bazata tunkari zainul abideen ta fada Masa tana sonsa ba Dan ita kanta tasan yadda ya tsaneta bazai saurarenta ba zuciyarsa da ruhinsa na wajen ummaty ....hannu Tasa ta dafe gefen zuciyarta dake yi mata azabar ciwo...ga Dan uwanta na tsananin son ummaty wanan wace irin iftilai ke Shirin fada musu....ga mahaifiyarsu Bata son ummaty mafita daya ce tafadawa mahaifiyarta tana son zainul Dan tabar haris ya Suri ummaty da wuri tabar mata shi...to tayaya ita da ta daukarwa zuciyarta alkawarin boye sirrin dake cikinta tayi nisa cikin tunani batasan mahaifiyartata ta shigo dakin ta zauna gefen gado Tana fuskantar ta ba sai ji tayi an ruko hannunta ta matukar tsorata hakan yasa da sauri ta juyo da fuskarta sharbe da hawaye sukai Ido hudu da mahaifiyarta ta fada jikinta hade da sakin marayan kuka Mai ban tausayi...ta rungumota jikinta Tana shafa kanta...

******
Shirin tafiya gida takeyi yau da wuri tun karfe uku na Rana "meyasa kike tunanin akwai abinda zai raba zumuncina dake ummaty ?"

Murmushi kawai tayi batare da tace komiba sai kawai ta dauki Jakarta ta Mike tsaye "zan wuce"ta sauke Masa murmushi kallo kawai yake bin ta dashi cike da al'ajabi Dan haka be ja da itaba yace "to Allah ya tsare sai gobe kenan",ta kada Masa Kai idanuwanta cike da kwalla batare da ya gani ba ta sa Kai ta fice....sauri takeyi har tazo daidai sashin gimbiya rumana ta tsaya ta Dan kalla Tana son ganin baabah kande Amma batajin zata iya ganinta yau Dan haka saita sa kanta ta fice....

*******
Sosai boka yakeyi mata bayanin komi da abinda ke Shirin faruwa cike da tashin hankali take sauraronsa har ya Gama....dakyar ta hadiyi miyau a bakinta Wanda yayi Mata dacin gaske saboda tsananin takaici da tashin hankali...kullin magani ya dauko ya kwance ya dubashi cikin ruwa Tana binsa da kallo har maganin ya jika ya tashesa ya zuba a gora sanan ya dauko wani ruwan magani ya zuba ciki ya jijjiga yasa murfi ya rufe sanan ya dubeta "wanan maganin matukar ta bashi shi ya Sha to ya tashi aiki ki matsa mata kiyi mata barazana sanan ki Nuna mata kinsan shirinta dikda inaji a jikina da wuya ku kwashe lafiya nayi iya bimcikena da bugun kasa wajen gane waye dayan da ke taimakonta nakasa ganewa da alama shima da shirinsa"

"Bazai wuce mahaifinta ba tunda dama ya fara yimun gaddama Akan hakan shine ya bullo da haka to wallahi sai na shayar Dasu mamaki dukkansu sainayi sanadiyyar su gabaki dayansu tunda ka tabbatar mun cewar da wuya ya Kara kwanciya to zan Basu mamaki"cike da bacin Rai take maganar da kunar Rai....

Haka ta amshi maganin cike da tashin hankali ta baro wajen boka tamkar mahaukaciya dik komi ya tsaya Mata tunanin yadda zatayi kawai takeyi da yadda zata dauki fansa Akan sarkin dawaki Wanda take zargin shike taimakon ummaty...😂😂😂

******
Baabah kande hankalinta a tashe yake tunda ta saurari tattaunawar gimbiya rumana da yarta a waya take tunanin yadda zataga ummaty kafin su hadu da gimbiya rumana tun safiyar yau take dakonta Amma inaaa Bata ganta ba sai kawai hangen gilmawarta tayi cikin sashen gimbiya rumana Tana biye da hansa'u wadda akasa Tai kiranta....

*WANAN LITTAFIN NA KUDINE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI ,08166177830 KO 07084161619*

💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞

*HASKE WRITERS ASSO💡*

*Dan Allah kuyi hakuri wayata ke hauka kwana biyu da kukaji shiru yanzun komi normal insha allahu zakujini akai akai*

*SLIMZY😍*
[1/23, 11:38 AM] 😍SLIMZY😍: 31

Cakk ta tsaya ganin yanayin fuskar gimbiya rumana Babu annuri Nan da Nan jikinta ya dauki Bari da rawa tamkar mazari a hankali ta jingina da jikin bangon dakin Tana sauke numfashi a hankali,yadda zuciyarta ke bugawa ita kanta tabawa kanta tsoro Dan iyakacin tsorata ta gama tsorata,...ita kuwa ogar takowa tayi a hankali ta karaso har inda take ta tsaya Tana bin ta da kallo Mai cike da tuhuma da zargin...hannu takai jikin kofar Tasa makulli aikuwa take hantar cikin ummaty ta Kara kadawa ji takeyi tamkar ta saki fitsari a inda take,

Hannunta tasa ta dago habar ummaty idonta cikin nata "kunyi gangancin cin amanata keda ubanki ummaty,saurin me kukeyi haka ganin kunga bayana?meyasa kika Bari mahaifinki yayi galaba akanki kuka hada Kai kuke ganin zakuci amanata ku zauna lafiya?"

Cikin rashin fahimta inda ta dosa ummaty ke kallonta dikda tsoro daya cika mata zuciya be hanata yin karfin halin wurga mata tambaya ba "ranki ya Dade ban fahimci maganarki ba da kike cewa nida mahaifina munci amanarki kibani haske akan maganar Allah ya Baki yawan Rai"...ta karashe maganar muryarta na tsananin rawa...

Wata uwar tsawa gimbiya rumana ta daka mata ",ke dakata muna fuka zakice mahaifinki be sanar dake cewar maganin da kike bawa zainul abideen tun farko ba maganin da yake sashi ciwo bane?dikda a wancan lokacin ke Kanki bakisan maganin menene kike bashi ba Amma na tabbatar a kwanakin baya da yayi mun tawaye ya sanar dake Kona menene shiyasa yanzun kuka hada Kai wajen ganin kun warkar da zainul abideen ni Kuma nawa asirin ya tonu ko?to karya kukeyi dukkanku wallahi nafiku tsafi malamina yafi naku Kuma sarkin dawaki na sanar dashi tun a kwanakin baya yayi kuskuren da betaba yinsa ba ya jefa Kansa cikin danasani Mara amfani Dan nasha sanar dashi asirina bazai taba tonuwa ba saidai nashi wallahi"....idanuwan ummaty gabaki daya sun ciko da kwalla sunyi jajir Jin furucin da gimbiya rumana keyi tabbas tunaninta da zarginta yau ya tabbata na cewa da mahaifinta ake hada Baki wajen ganin bayan zainul abideen.... innalillahi wa Inna ilaihi rajiun shine abinda ta furta a zuciyarta ta runtse idanuwanta da karfi wasu zafafan hawaye suna gudu daga idanuwanta zuwa kuncinta...wani irin bala'i ne wanan yake Shirin tunkaro su? mahaifinta beyi mata adalci ba yayi sanadiyyar jefata cikin masifar da fitar da ita Sai Allah daya halicceta....wayyooo Allah inama mafarki takeyi da idan ta tashi daga mafarkin Nan bazata Kara kwanciya ba harabada...wayyooo Allah kaiconta...ta cije lebenta da karfin gaske har Saida yayi jini sanan ta bude idanuwanta ta saukesu akan fuskar gimbiya rumana wadda ta hada Rai tamkar tunda Allah ya halicceta Bata taba murmushi ba....sai kawai ta zube a gaban gimbiya rumana ta fashe da wani irin kuka Mai ciwo hade da ban tausayi ta ruko kafafuwan gimbiya "ranki ya Dade ban taba danasanin zuwana duniya ba kamar yau inama ace wanan abun daya faru a mafarkine ba gaske ba?menayi muku haka kuka jefani cikin halaka kuka zabi tsomani cikin wanan balain"...ta rushe da kuka Mai karfin gaske Tana rike da kafar gimbiya rumana wadda ko gezau batayi ba dikda kuka Mai ban tausayi da ummaty keyi tana gurfane rike da kafafuwanta...sun dauki minti goma a haka bakajin sautin komi sai shesshekar kukan ummaty dakyar gimbiya rumana ta sauke numfashi ta soma magana wadda har ummaty ta cire Rai da zatace wani Abu "karki kuka da kowa ki kuka da ubanki sarkin dawaki Dan shikadai ne babban aminina tun kafin a haifeki,tun kafin kisan zakizo duniya dik wani kulli dashi muke kullawa Kuma shi ya kawo shawarar amfani dake wajen bawa zainul magani saboda zuciyata Bata aminta da insaka wani yayimun ba gudun kada asamu matsala,sanan kece kawai Zaki bawa zainul Abu ya ci dubada yadda kuka taso kuke kaunar juna dubada yadda ya yarda dake kuka shaku da juna shiyasa kika zamo cikin wanan abun sai gashi ke kina tunanin kedin me wayauce bayan bakida wayaun komi kwaya nawa kike?dududu shekararki goma Sha bakwai a duniya har kike tunani yiwa Yar shekara hamsin wayau?hmmm kinyi gangancin Dan hakan yanzun haka kinada dama ta karshe a wurina wadda idan Kinga Zaki iya to idan bazaki iyaba banki kowa ya kwana a ciki ba"ta makale kafadarta fuskarta dauke da murmushi.....

Mikewa tsaye ummaty tayi fuskarta jike da hawaye Tana kallon gimbiya rumana cike da takaici "Fadi damar data rage a gareni indai bazata jefani cikin wata masifar ba ko ta haddasamun damuwa da ciwon da bazai warkeba a zuciyata zan iya yinsa..."
Chapter 34 · 0% Book details