Sashe 2
Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Murmushi ta sauke a fuskarta "sai yanzun sakon ya ishe maka kenan?Koko yanzun ka gadamar zuwa Kiran nawa?hmmm sarkin dawaki ka Shiga hankalinka Domin wasa Dani da kake Shirinyi tamkar kana wasa da rayuwarka ne"
"Ina sauraronki"shine abinda yace Mata a takaice,
Sosai ta tsaye sanan ta nuna wani farin gorar swan water dake gefe tace "lokaci yayi da zaabada magani Kuma kasan aikinka shiyasa na kiraka Domin ka aiwatar da umarnina,rashin aiwatar da umarnina Yana barazana da rayuwarka data Yar daka Haifa kanta,idan ban aiwatar maka da komiba to hukuncinka zai sauka akan yarka wadda kake tsanin kauna...ka dauka ka Bata takai Domin waadin Shan maganin nasa yau ne,idan besha yau ba komi zai iya lalacewa,sanan Ina Mai sanar maka idan har baka Bata ba ta bashi zan sani kuma zaka fuskanci hukuncina"....Tana karasa maganar Bata jira cewarsa ba ta juya cike da takama fuskarta dauke da murmushin mugunta....
A sandare yake a zaune ya kasa kwakkwaran motsi a wajen ya rasa dalilin dayasa wanan matar ta rasa Wanda zatayi amfani dashi wajen cutar da yaron Nan sai shi?sanan abun takaici tasa yarsa fadawa soyayya da nakasasshe Wanda Babu tabbacin aurensa da ita?me take nufi dashi ne?babban tashin hankalinsa be wuce yadda yanzun ta canja Masa sanin cewar shakuwar yarsa da yaron Yana nuna cewar akwai wata alaka ta zuciya a tsakaninsu,tabbas ta sakashi a tsaka me wuya besan yadda zaiyi da fitinanniyar matar Nan hatsabibiyaba,
Juyawa yayi ya dubi gorar dake ajiye a gefe wadda itace zai dauka ya Kai...gabansa ya fadi wani irin gumi ne kawai ke tsattsafowa a fuskarsa..ajiyar zuciya ya sauke ya Mike jiki a sanyaye ya dauki gorar yana Mai dagata sama yana bin ta da kallo bashi da wani zabin daya wuce aiwatar da umarminta haka ya juya ya fice.....
*SLIMZY 😍*
[1/23, 10:31 AM] 😍SLIMZY😍: *HASKE WRITERS ASSO...💡*
💞 *ZAINUL ABIDEEN💞*
*SLIMZY✍🏼*
*Wattpad@slimzy33*
*2*
********
Shirinta tayi tsaf kamar yadda ta Saba yau ma tayi latti sauri sauri take shiryawa,sanye take da doguwar Rigar jallabiya baka budaddiya da gyalenta Baki ta yane kanta fuskar Nan fayau babu abinda ta shafa tayo hanyar tsakar gida daga dakinta,
A tsakar gida taci karo da mahaifinta Nan da Nan ta zube a gabansa ta Soma gaishesa,"barka da tashi baba fatan antashi lafiya?"
Cike da kulawa ya dubeta "ummaty an fito zaa tafi?"
"Ehh baba"
Gorar hannunsa ya kalla ya Mika Mata "ga wanan ummaty lokacin Shan maganin zainul abideen yayi kinsan dai yadda kike bashi sanan wannan abun da kikeyi taimako ne Allah zai baki Lada Allah Kuma zai bashi lafiya"
Ta Kara sunkuyar da kanta ta Mika hannu cike da ladabi ta amshi gorar ruwan "wallahi baba narasa Gane Kan wanan rashin lafiyar na ya zainul jiya ma fa bakaga yadda jikin ya rikice ba wallahi,gashi Mai martaba yaki amincewa da akaisa ai Masa magani"
Ajiyar zuciya ya sauke Yana Kara duban Yar tasa sanan ya nisa yace "kada ki damu ummaty zai warke insha allahu shiyasa Nima nabaki goyon baya wajen taimakonsa wajen bashi magani a boye batare da sanin kowa ba har Allah yasa yasamu lafiya kinji?tashi kije Rana tanayi"
Ta Mike jiki babu kwari dakyar take taka kafarta ta Shiga dakin mahaifiyarta Tana zaune Kan dadduma Tana sauraren radiyo ,direct wajen drawer ta nufa ta bude ta Ciro babbar Jakarta ta zura gorar ciki Sanan taiwa mahaifiyarta sallama ta fice....
*******
Shasshekar kukanta ce yasata saurin juyowa bangaren da take zaune ta jingina da kilisa gefenta wayarta ce ajiye,da kyau mahaifiyarta ta kalleta Tana karantar yanayin nata Wanda ya nuna tsantsar damuwa a fuskarta,
"Yanzun safiyya bazaki daina kuka Akan rashin lafiyar zainul ba kiyi Masa addua?Babu abinda yake bukata sama da adduarmu kiyi Masa addua a matsayinki na kanwarsa jininsa inaga zaifi bukatar hakan sama da kukan da kikeyi"
Juyowa tayi fuskarta jike da hawaye cikin tsananin tashin hankali ta Soma magana "Ammy lokuta da dama idan abubuwa suka taru sukai maka yawa babu abinda zakayi kasamu sassauci a zuciyarka inba ka zubar da hawayen ba,Babu abinda narasa a rayuwata ban rasa ci ba ban rasa Sha ba ban rasa komi ba Amma akwai gib'i a cikin rayuwarmu bakuma wani bane face ya zainul Ammy ki duba kiga halin da yake ciki shine kada'i namiji kaf zuri'ar mahaifinmu Amma shine Allah yayiwa wanan mummunar jarabar shine mummunar kaddara ta fadawa Wanda mahaifinmu ke matukar so yake alfahari da samunsa a d'a namiji magajin sarki Amma ya tashi cikin tsananin rashin lafiyarda har yanzun aka rasa maganinta, Dole inyi kuka ammy,sanan babban abinda ke damuna be wuce yadda yake cikin wanan halin Amma Kun kasa yin wani Abu Akan ciwon nasa Ammy daga ke kuwa har Mai martaba kullum saidai kice ciwon ya zainul na asibiti ne ni Kam a ganina bana asibiti bane wanan ciwon nasa ya kamata a binciki masana addini da masu maganin gargajiya ko zaa Dace"ko kafin ta Gama maganar hawaye ya Gama wanke fuskarta tasa hannunta ta share Tana Mai duban mahaifiyar Tata wadda kalaman na Yar Tata suka fama Mata wani ciwo dake cikin zuciyarta,
"Fiyya dik wani mutum Wanda zai kaunaci zainul abideen ya nuna Masa soyayya bayana ne mahaifiyarsa nikadai nasan ciwon da nakeji ganin nakassar da zainul abideen ya tashi cikinta, Amma bani da yadda zanyi sama da inyi yadda ya Dace,ciwonsa na asibiti ne fiyya bana gargajiya bane Babu abinda maganin gargajiya zai Masa face ya Kara rikitar da jikinsa gobe insha allahu munada ganin likita idan munje zanyi Masa bayanin komi dangane da jikin nasa ,Dan Haka ki kwantar da hankalinki insha allahu Dan uwanki zai samu lafiya yanzun Haka zan tura tabawa taje ta sanar wa da masu kula dashi zuwana dubashi"
Girgiza Kai kawai fiyya tayi batare da tace komiba ta sauke sassanyar ajiyar zuciya....
*********
"Ku gyara gimbiya bilkisu zata shigo duba jikin yarima"
Da sauri fadawan dake cikin dakin suka shiga taitayinsu Jin wadda akace zata shigo duba jikin zainul abideen Nan da Nan kowa ya zube a kasa ta shigo dakin da takunta na kasaita da girma Wanda kowa yasan gimbiya bilkisu da sarauta kaf masarautar....
"Barka da zuwa gimbiya bilkisu uwar yarima magajin sarki"shine abinda fadawan suka hada baki sukace a tare,...hannu kawai ta daga musu batare da tace musu komiba ta karasa har gaban gadon,
Ummaty na tsugunne kanta a kasa dakyar ta iya motsa bakinta ta hada harrufa tace "barka da zuwa ranki ya dade"
Juyowa tayi gefen ummaty tayi murmushi Wanda shine amsa gaisuwarta,....kallo daya Tai Masa jikinta yayi tsananin sanyi tausayi da soyayyar Dan nata na ratsa sassan jikinta da jijiyoyin dake cikin jikinta,gefen gadon ta zauna sanan ta juyo ta dubi inda fadawan ke kame ko kwakkwaran motsi basayi Tai magana a takaice "kubamu waje"tun kafin ta karasa maganar suka Shiga fita daya bayan daya,
Ummaty ma juyawa tayi jiki a sanyaye ta koma can kofar dakin ta tsugunna kanta a kasa kirjinta sai bugawa yakeyi,Wanda ita kanta batasan dalilin dayasa dik lokacin da gimbiya bilkisu zasu hadu saita tsunci kanta cikin tsananin faduwar gaba hakan nada nasaba da mulki da Kuma kwarjini da Allah ya bawa matar...
Miyau ne kawai yake gudu a bakinsa sai harshensa da rabinsa yake waje Wanda shike zulalo da miyaun hannunsa daya a lankwashe yake shi kadai sai kada kansa yakeyi Yana murza kafafuwansa,
Kara rungume Dan nata tayi batasan lokacinda hawayen bakin ciki ke gudu daga idanuwanta ba saboda takaici,dubi dik yadda rashin lafiya tasa yake kullum tamkar karamin yaro,janyosa tayi Rabin jikinsa a jikinta ta rungume Dan nata Tana sharar hawaye,
"Allah ya baka lafiya kamar kowa zainul Allah ya nunamin ranan da zan ganka ka koma mutum sak kamar kowa"
Dago kansa yayi Yana kallonta miyau na gudu a bakinsa dakyar ya iya motsa harshensa dake karye ya furta kalmar "ame..en"shafa kansa tayi tana cigaba da zubda hawaye yayinda ya kwantar da kansa a jikin mahaifiyar tasa
Fiyya dake gefensu tsaye sai shasshekar kuka kawai takeyi Tana duban halin da Dan uwan nata yake ciki,sun dauki kinti ashirin kafin ta share hawayenta ta gyara Masa kwanciyarsa ta dubi fiyya tace" muje"
Haka suka juya suka fice jiki Babu kwari a bakin kofa sukai karo da ummaty Tai saurin durkusawa "ummaty kiyiwa fadawan yarima magana su canja Masa kayan jikinsa dik ya Gama jika rigar da miyau"
"To ranki ya dade"
Tana Shiga ta dubesa ta sauke Masa lallausan murmushi hade da sauke ajiyar zuciya,ta janyo jakar datazo dashi ta Ciro gorar ruwan maganin ta ajiye a gefe ta gyara zamanta da kyau ta dago kansa taga ita yake kallo murmushi Tai Masa ta furta a Fili "Allah ya baka lafiya ya zainul kaji inaso ka warke cikin kankanin lokaci kaji?"
Gyada Mata Kai yayi Yana Dan murmushi ta gefe,dago kansa tayi a hankali ta daga gorar ta Shiga bashi wanan ruwa,yasha sosai dikda rabi sun zube a jikinsa Amma Saida ya shanye tas ta gyara Masa kwanciyarsa sanan ta maida gorar cikin Jakarta tadawo gefensa ta zauna....
Dan littafin data Saba zuwa dashi ta Ciro cikin Jakarta ta bude yana ganin Haka ya Soma murmushi itama murmushin tayi Masa tace"ya zainul karatunmu zamuyi kaji"
Ya gyada Mata Kai....
*********
"Sarkin dawaki"Mai martaba ya Kira sunansa,
Kara durkusawa yayi sosai cike da girmamawa "Allah ya taimaki adalin sarki ya Kara maka girma da daukaka da nisan kwana da lafiya da arziki ranka shi Dade"
Jinjina Kai Mai martaba yayi hade da murmushi na nuna Jin dadin kirarin da sarkin dawaki yayi Masa,
Gyaran murya kadan Mai martaba yayi ya nisa "jamaan gari da Yan uwa da dik wani a Hali na wanan na wanan masarautar suna cikin alhini na rashin lafiyar zainul abideen"
Kara durkusawa yayi sosai zuciyarsa na harbawa "Hakane ranka ya dade"
"Shawarwari sunata zuwamin daga wurare daban daban da wadanda sukeda kusanci Dani game da rashin lafiyar zainul abideen cewar Mai zai Hana mu Mika lamarin Nasa ga malaman addini da masu maganin gargajiya cewar ciwon nasa bana asibiti bane ko zaa Dace"