Sashe 36
Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mai martaba Iya tashin hankali ya tsinci kansa ciki shiya haifar masa da kasa cewa komi saidai sauke ajiyar zuciya kawai da yakeyi minti minti yakan kada Kashi saboda tsananin mamaki da kunar Rai.... Dakyar ya daidaita Kansa yayi gyaran murya Wanda yasa fadar yin tsittt tamkar Babu wata halitta Mai Rai dake cikinta kowa yayi shiru Yana sauraren me Mai martaba zaice dangane da wanan lamarin Mai cike da ban mamaki... "Farko dai Babu abinda zance saidai ince "innalillahi wa Inna ilaihi rajiun dangane da wanan lamari daya faru Mai cike da dumbin ban mamaki da al'ajabi ko a mafarkina ban taba zato ko tunanin haka zata faru ta fannin Wanda nafi yarda dashi ba a duniya wato sarkin dawaki...ummaty dai Bata Kai shekarun da zata aikata wanan taasar ba ita kadai Saida saka hannun wani a ciki tunda bincike ya Nuna cewar ta Dade tana bashi maganin Nan nuni da wanan video dake cikin wayar yusha'u"...
Take yusha'u yayi playing video din daidai inda ummaty ke fadin zainul inbaka maganin naka kasha ne Koko sai anjima....Nan take muryar zainul ta cika fada inda yake cewar ummaty Akan me zanki Shan maganin da kindade kina bani shi ?aibanida wani zabi daya wuce Shan wanan maganin ummaty... Nan fada ta kacame da surutu kala kala da kyar sarkin fada yayi tsawa kowa yayi shiru Yana jiran hukuncin Mai martaba...
"Banida wani hukunci Wanda zan zatar Akan hakan face na yanke alakata da ahalin sarkin dawaki da dik wata zuria tasa na barranta Dasu ko a lahira bana fatan Allah ya hada fuskokin mu Dasu domin dik Wanda zaiyi Mana wanan cin amanar Yana daidai da yasa a halakamu"
Kuka ummaty ta rushe dashi harda shassheka ta Shiga waige waige tamkar zararriya wayarta take nema Amma Bata ganta ba zabura tayi zata ruga aguje innah ta rukota Tana kuka "ranka ya Dade wallahi bani bace bani bace banida hannu a wanan lamarin"
Wani zabura hajiya Kaka tayi jikinta har rawa yakeyi cike da tsana da takaici tace "bake bace to uban waye munafuka?ga sheda kuru kuru kice bake bace mudai kawai anci amanar mu Kuma Allah yayi Mana sakayya insha allahu zainul abideen da kaina zan cigaba dayi Masa magani zai warke Sarai Kuma zai taka da kafarsa babban abinda zan sanar muku shine wallahi idan yaron Nan be farfado ba ya taka da kafafuwansa ba to dagake har uwarki da ubanki sai kun bakunci lahira sai nasa an tsireku munafukan Allah marasa kaunar Allah asirinku ya tonu"...tunda hajiya Kaka ta soma magana ummaty ta kafeta da idanuwa hawaye na gudu a fuskarta dakyar ta juyar da kanta suka hada Ido da gimbiya rumana wadda keta sharar kwallar makirci ita an cuceta takasa magana.. kada Kai kawai ummaty tayi ta danyi murmushi cike da takaici....Mai martaba ya cigaba da magana "inaso ku tattara komi naku ku koma bayan garin Nan kuje can da Zama domin ko ganinku bana sonyi na tsaneku na tsani dik wani Abu daya dangance ku har zuwa lokacin da zan nemeku Dan kaina"...
Waziri da sarkin aska ji sukeyi tamkar su zuba ruwa a kasa su Sha saboda farin ciki...Dama irin wanan ranan suke jira...
Dik wanan hukuncin da Mai martaba ya yanke ba haka gimbiya bilkisu tasoba so tayi kawai Mai martaba ya yanke musu hukuncin kisaa....shi kuwa sarkin dawaki tunda ya sunkuyar da Kansa ya kasa cewa komi sai zufa da take keto Masa ta ko Ina idanuwansa sunyi jajir haka ya dago Kai ya dubi ummaty suna hada Ido ta runtse idanuwa saboda wani irin bakin ciki da ya taso Mata mahaifinta ne Amma bakinkirin take ganinsa ....innah kuwa yadda take sharbar kuka ne kadai zai baka tausayi idanuwanta sun kumbura sunyi jajir ga wani irin tukukin zafi da take ji cikin kirjinta ...Mai martaba ne ya bada umarni da a fidda Mai su daga cikin fada Yana Gama fadin haka ya Mike yayi hanyar dakinsa inda aka kwantar da zainul abideen aka kunna Masa karatun alkurani bacci ya daukesa....
Warisah da zahira da safiyya harda afnan suna zagaye da Dan uwan nasu ko wanne cikin tsananin tashin hankali yake sai fifita sukeyi masa lokacinda Mai martaba ya Shiga ya Basu umarni da su fita Babu musu ko wacce ta fita jiki Babu kwari....tsaye yayi Akan Dan nasa Yana Kare Masa kallo soyayyarsa na yawo cikin jinin jikinsa wani irin tausayinsa ke ratsa sa ta ko Ina...shi Kansa Mai martaba baisan lokacinda kwalla ta cika a Ramin idanuwansa ba ya cigaba da kallon zainul Yana shafa Masa Kai.....
********
*WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619*
Isowarsu gida keda wuya suka zube Akan tabarma daga innah har ummaty dik sun fita hayyacinsu cikin kankanin lokaci,sarkin dawaki jikin katamga ya tsaya ya kifa Kansa batare da yace komiba,...ganin hakan yasa innah cikin kuka take fadin "malam tunda wanan bala'i ya fada Mana cikin dakikun da suka wuce bakace komiba har a gaban Mai martaba ka kasa magana,Dan Allah malam kace wani Abu Mana kasan ummaty bazata aikata hakan ba"tasa hijjabinta tana goge fuskarta wasu hawayen na gudu,
Mikewa ummaty tayi a zabure cike da takaici ta Zame Dan kwalin kanta sumar kanta dake kwance ta bayyana ta cije lebenta tana fuskantar inda mahaifinta ke tsaye "innah Babu abinda baba zaice domin dik abinda ya samemu shine sanadi"..
Cikin kuka innah ke duban ummaty "kina hauka ne ummaty kinsan me kike fada kuwa?kinaso kice min abinda ake zargi hakan ne Kuma malam yasani?"
Murmushin takaici ummaty tayi tasa hannu ta share hawayen fuskarta ta sauke numfashi "ya sani innah domin shine silar komi shi ya jefani cikin wanan halin na tsinuwar mutane da laana"
"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun"shine abinda Inna ke furtawa tana kallon ummaty cike da son Karin bayani....take ummaty ta kwashe komi dangane da abinda ya faru Wanda ta sani da maganganun da gimbiya rumana ta fada Mata a yau ta kwashe ta fadawa mahaifiyarta... Sosai innah ta girgiza da lamarin dakyar take kada kanta saboda tsananin takaici "malam ka cucemu ka haincemu malam ka cutar da yarka kasata cikin mummunan Hali,kayi Mata pentin da me wanketa sai Allah ka shafa Mata bakin jini... innalillahi wa Inna ilaihi rajiun,Dole zaman cikin garin Nan ya gagaremu Koda sarki ya bamu umarnin Zama bamu Isa mu zauna ba saboda abubuwan da zamu fuskanta,....sanan ko menene ummaty Bata Isa ta fallasa asirin gimbiya rumana ba wadda falladuwar asirinta sai Allah shi kadai ne zai Tona Mata asiri da izinin Allah"...
Kuka sarkin dawaki yakeyi cike da nadamar abinda ya aikata a baya take ya zube Akan gwiwoyinsa a gaban iyalin nasa Yana rokar gafararsu Akan abinda yayi Sharrin shaidan ne Yana kuka da hawayensa....dukkansu kuka sukeyi cike da takaici,ummaty tausayin mahaifinta ne ya lullubeta tasan cewar gimbiya rumana tayi amfani da makirci ne wajen samun galaba akansa dikda batasan ainihin tarihi da labarin komiba....
Haka tasa dankalinta tana sharewa mahaifinta idanuwa Tana girgiza Kai "baxan taba yafewa kaina ba,bazan taba iya jure ganin mahaifina Yana zubar da hawaye a gabana ba harabada komi girman laifin da zaimun Koda yakai dutsen uhudu girma Zan yafe Masa kayi shiru mahaifina na yafe maka harabada"....ta fashe da kuka ta fada jikin mahaifinta tana shasshekar kuka ya rungumeta tsamm innah ta taso daga inda take ta karaso wajensu suka rungume juna suna kuka... Turo kofar gidan yasasu juyawa a tare suna kallon hanyar kofar gidan cike da faduwar gaba.. haris ne ya shigo gidan cikin kananun kaya masu shegen kyau wadanda sukai matukar amsar jikin nasa fuskarsa Babu yabo Babu fallasa,kallo daya zakayi Masa kasan cewar Yana cikin tsananin damuwa.....Bata dauke idanuwanta ba daga Kansa har ya karaso inda suke ya tsugunna a gabansu,....hannunsa ya zura aljihunsa ya Ciro farin karamin towel Mai shegen kamshi ya Kai fuskarta ya Shiga goge Mata hawayen da Yana gogewa wasu na sauka ko kifta ido batayi wajen kallonsa "banaso insake ganin hawaye a wanan kyakkyawar fuskar Taki ummu Salma Dan Basu kamaceki ba,inaji a jikina cewar wanan abun daya sameki kaddara ce hade da makirci aka kulla Miki Dan ban yarda ba innocent ummaty zata aikata hakan"...kuka ta fashe dashi "ya haris wallahi summa tallahi bani bace na aikata hakan bazan taba aikatawa zainul wanan mummunan aikin ba banida hannu cikin wanan aikin Babu Wanda zai yarda Dani Amma nasan zainul shikadai zai fiddani cikin lamarin Nan sai Allah "...kada Kansa kawai yakeyi idanuwansa sunyi jajir dakyar ya furzar da iska Mai zafi daga bakinsa ya juyo ya dubi sarkin dawaki cike da jimami da tausayawa "baba ka kwantar da hankalinka,insha allahu gaskiya zatayi halinta da izinin Allah kaji"
Kada Masa Kai sarkin dawaki yayi zuciyarsa cunkushe da tsananin bakin ciki....shiruu sukayi kusan minti talatin bakajin sautin komi sai shasshekar kukan ummaty wadda har muryarta ta disashe kamanninta gabaki daya ya canja ta fita hayyacinta...
Gyaran murya haris yayi "baba idan bazaku damu ba Zan kwasheku a gidan Nan in kaiku wani gidana da na siya can wajen gari Babu Wanda yasan dashi in ajiyeku a wajen ku zauna har muddin Rai sanan inaso in maida ummaty ta koma karatu Koda karatun Nan na bangaren lafiya tayi inaganin hakan zaifi kafin komi ya daidaita Kuma ku kwantar da hankalinku dik runtsi dik wahala Ina tare daku baba Dan girman Allah kada kuce ah ah nabaku kwana uku kuyi shawara abinda kuka zartar saiku sanar Dani"....tunda ya soma magana sarkin dawaki ke kallonsa batare da yace komiba har ya Gama itama inner batace komiba shiru tayi ...ya Dade zaune basuce komiba har yayi musu sallama da nufin zai dawo washe gari....