← Book details Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 49

Sashe 19

Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tabe Baki warisah tayi "well dama bawani abubane ya zainul zaakai fadar sarki inda Yan uwansa ke sada zumunci Shima yasada zumunci Koda da bakinsa ne,sanan baa bukatar bare a wajen"

"Ke warisah wanan wani irin magana kikeyi kamar wata jahila?dik maganganun Nan da kikeyi da wa kike?"...da sauri warisah ta juyo a Karo na biyu sukai Ido hudu da zainul Wanda ya tamke fuskarsa ya kafeta da idanuwa,take yayi Mata wani irin kwarjini Wanda wani be taba Yi Mata Shiba har ta kasa jurewa ta kauda idonta daga cikin nasa gabanta na tsananin faduwa,Amma hakan be hanata turo Baki gaba ba batare da tace komiba ta tsaya...

"Ya zainul Bari in kaika koh?"

Girgiza Mata Kai yayi "gyaramun zamana dai kawai a wheel chair din zan iya turawa ai hannuna sunfara aiki inajin dadin jikina".. gaban ummaty ne ya Fadi data tuna wani Abu sai kawai ta fitittike "haba ya zainul ya zakace zaka tura kanka da kanka?ni Banga wani warkewa da kayiba sodai kawai kakeyi ka Fadi Bari kagani muje inkaika sai indawo"...badan yaso ba haka ya amince da bukatar ummaty ta gyara Masa zama ta tsaya a bayansa warisah kuwa gaba tayi cike da takaicin ummaty kamar ta shaketa takeji shegiyar yarinya Yar shisshigi mtswww Tai tsaki Tai gaba da sauri....

Da faraar hajiya Kaka ta tarbi jikan nata "lale marhabin da Mai gidana jiki yayi kyau"yadda Tai maganar kowa sai ya juya ga zainul abideen Wanda ke zaune kan wheel chair bayansa ummaty ce da ke gungure dashi,idanuwan zahira suka sauka Akan fuskarsa Mai annuri da kwarjini Wanda dik Wanda ya kallesa baya iya Kara hada Ido dashi saboda kwarjinin haibarsa uwa uba kyau da Allah ya bashi ,wani abune taji ya tsarga Mata tun daga kafafuwanta har zuwa kwakwalwar kanta Wanda ita kanta ta rasa gane menene kawaidai ta tsinci kanta da son Kara kallonsa a Karo na biyu,hakan Nan zuciyarta na harbawa ta Kara dago idanuwanta ta saukesu akansa ta tsura Masa idanuwa hannunta rike da spoon tana jujjuyawa shiko samm hankalinsa baya wajen Yana wajen iyayensa da sukai Masa caaaa kowa na kokarin Nuna Masa kulawa da kauna da soyayya...

Warisah ce ta zunguri zahira wadda ta lula wata duniyar "malama meye hakan saikace Kinga wani abun kallo?"

Ajiyar zuciya zahira ta sauke "abun kallo ne Mana"tace hade da murmushi

"Ina abun kallo ga wanan nakasassan"tace kasa kasa hade da sauke tsaki

"Tab wlhy yau ya zainul yayi mugun kyau musamman marrooon din kayan Nan dake jikinsa sun masifar karbar jikin nasa ga Yar kiba da yayi,Kuma kingani yafara samun sauki wlhy kamar ba Shiba,babu miyaum Nan Babu hardewar harshe a maganarsa,yadda yake maganar ma tamkar basarake... gaskiya ya zainul ya hadu yanzun Abu daya ya rage Masa shine kafarsa Amma tabbas shidin namiji ne hadadde"

Waigawa zahira tayi ta dubesa da sauri ta kauda kanta hade da tabe bakinta batare da tace wani abuba....

*********
*WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS* *DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619*

tun bayan barowarta fada take cikin tsananin tashin hankali tunda idanuwanta sukai tozali da zainul abideen gimbiya rumana ta Shiga rudani Wanda Bata taba Shiga ba a rayuwata.. zaune take cikin taron yaranta zagaye da ita da yaransu Amma hankalinta gabaki daya baya jikinta

Ya Zahra babbar yarta ce tace"Wai ummah yau lafiya kuwa dik na ganki haka?meke faruwa ne?"ta jefa Mata tambaya tana jijjiga d'anta yanaso yayi bacci...

Girgiza Kai kawai tayi fuskarta na dauke da damuwa Amma saita kakalo murmushi "babu komi zahrau kawaidai yau banajin dadin jikin Nan nawa ne tun jiya daddare ma"

"Ummah Aida kin Kira likita ya dubaki ko"

Gyadawa Yar tata Kai tayi alamar to batare da tace komiba ta maida kanta gefe....Nan yaran suka sauya akalar hirarsu suka koma hirar dangi gabaki daya harda yadda kowa ke Nuna farin cikinsa na ganin jikin zainul yafara kyau...

********
Gimbiya bilkisu ce zaune kusa da Dan nata a patlornta an jingina sa Yana kallon tv hannunta na Kansa tana shafashi cike da kaunar Dan nata,haka kawai yau takejin kanta cikin tsananin farin ciki Wanda ita kanta tasan yanada nasaba da yadda jikin yaron nata yayi kyau su kansu kannen nasa farin ciki ya kasa boyuwa a fuskokinsu sai surutu afnan take zubawa zainul abideen saidai ya dago Kai kawai yayi murmushi Dan shi bame son surutu bane....

Dik wanan budurin da akeyi ummaty na bayan sashen zainul hankalinta a tashe,tun da suka hada Ido da gimbiya rumana a fadar sarki zuciyarta keyi Mata lugude Dan Babu tantama ta fahimci wani Abu dangane da samun lafiyar zainul abideen... Gaban ummaty sai faduwa yakeyi tunanin mafita kawai takeyi ta rasa inda zata tsoma ranta taji Dadi babban tashin hankalinta be wuce tasani tunda gimbiya rumana ta lura to tabbas zata Aiko da magani ita Kuma tayi alkawarin harabada daina basa wanan maganin Mai cutarwa Wanda take kawowa a matsayin nema Masa lafiya Nan kuwa cutar dashi takeyi,tasani cewa akwai babban aiki a gabanta Dan tonuwar asirin Nan ba karamin tashin hankali bane a garesu Baki daya...bama a garesu ba a gareta...ya zaayi ta fahimtar da zainul abideen?Babu hanyar fahimtar da shi,sanan Bata Isa ta Nuna Masa ya rinka pretending Akan ciwonba Dole sai ya tambayeta dalilin nata na hakan...wace amsa zata bashi?"ta rafka uban tagumi idanuwanta sunyi jajir tamkar ta fashe da kuka...

*******
"Ya musaddik baka lura da ya zainul ya fara samun lafiya ba"

"Sai akai Yaya"yace fuskarsa a daure Yana daddana waya,...zahira ta turo Baki "kawaidai naji dadin hakan ne"

"Ina kallonki kina satar kallonsa ai a fadar sarki ko meye dalilin hakan oho"

Dariya ta fashe dashi "wallahi ya musaddik bani kadai bace harda warisah ma ta kalleshi kawai dai ita haushinsa takeji bansan daliliba,Amma hakan be hanata kallonsa ba"....wani Abu ne ya tasowa musaddik ya tokare Masa kirji ya dubi zahira ransa a bace "ke yimun shiru da wanan zancen ya isheni dik kinbi Kim cikani da shegen surutu"

Mahaifiyarsu dake gefe me aiki na yanke Mata kumba ta dubi musaddik Tai murmushi sai sanan ta ce "to Kai meye abun haushi daga baka labari?zaka fara hantarar mun yarinya?ya isheka musaddik,Kinga zahira zonan kibani labari kinji me akayi ya akayi da shi zainul din"Tai maganar fuskarta a sake...cike da shagwaba zahira ta Mike tana murmushi tana waigen musaddik dake watsa Mata harara kamar ya shaketa kishin warisah dik ya cika shi...

Zama tayi dafff da mahaifiyar tata suka cigaba da hirarsu,kasa kasa zahira ke magana kawai sai ta soma dariya tana rufe fuskarta...itama mahaifiyartata dariya tayi ta girgiza Kai...

*******
"Warisah ya Dace ki cirewa Kanki tsanar Dan uwanki haka Nan wanan wani irin bamzam Hali ne kikedashi?mukami kikafishi ko uban me kika fishi?Ina lura da dik abubuwan da kikeyi a gidan sarki ki Shiga hankalinki nafada Miki"

Zuburo Baki warisah tayi ta Mike fuuyhhh tabar patlorn tabar mahaifiyarta na zazzaga masifa Akan abinda takeyi....dik zuciyar hajiya kubrah Babu Dadi Babu yadda ta iya da warisah dik yadda taso ta lankwasata Bata lamkwasuwa Babu abinda take jiye Mata sai gaba....mtswww Tai tsaki tabar patlorn tabita daki.....

*********
Tunda ta shigo gida ta dubi fuskar mahaifinta gabanta ya Fadi,ta juyo ta dubi mahaifiyarta wadda ke zaune kan tabarma fuskarta dauke da tsananin damuwa tasan akwai matsala a kasa....kirjinta ke bugawa sauri da sauri hakan be hanata durkusawa gabansu ba bakinta na rawa tace"barkanku da gida"mahaifiyarta ce ta amsa cike da kulawa sabanin mahaifinta da ya amsa Babu yabo Babu fallasa gwaggo hauwa ko kauda kanta gefe tayi ta janyo karamin radiyo dake gefenta ta Kara a kunnenta tana sauraren zaben almuru...

Ta Dade tsugunne sanan ta Mike da niyyar zuwa Tai alwalar magriba kamar yadda takeyi idan ta dawo...da wata iriyar murya mahaifinta ya kirata "ummaty"...gabanta ne ya yanke ya Fadi ta tsaya cakkk na Yan dakiku sanan ta juyo a tsorace tace "naam"Baki na rawa....a hankali ta karasa gabansa ta tsugunna kirjinta na dokawa sauri da sauri.....

*WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN* *BAYANI 08166177830 KO 07084161619*

*HASKE WRITERS* *ASSO💡*

💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞

*SLIMZY😍*
[1/23, 10:44 AM] 😍SLIMZY😍: 18

"Ummaty umarni nakeson Baki akan zuwanki gidan Mai martaba inaso in datse alakarki da gidan saboda inason hadaki aure da modibbo Dan kanwata"

Wani irin faduwar gaba ne ya ta tsinci kanta wanda hakan Saida ya haufar Mata Zama daga durkuson da takeyi badan ta shiryaba,jikinta ne kawai yake rawa tamkar an watsa Mata ruwan kankara kallon fuskar mahaifinta tayi idanuwanta a waje,yadda taga fuskar tasa Bata taba ganin hakan ba ya Kara rikita Mata tunani sanin halin mahaifin nata da waye shi yasa wasu zafafan hawaye Wanda Bata shirya saukarsu ba suka fara zuba Akan kumatunta dakyar ta bude Baki tace "baabah menene dalilin hakan?"

"A matsayinki na Yar Dana Haifa Baki Isa in yanke hukuncin ki tambayeni daliliba Dan nikeda iko dake bakece keda iko Dani ba kinaji ko"

Kanwar babansa ce ta gyada kanta tana watsawa ummaty harara wadda ke zaune dabas a kasa tamkar an tureta a kasa,hawaye ke gudu a idanuwanta tamkar an bude famfo wasu gumi ke karyo Mata ta ko Ina, mahaifiyarta na gefe tana jinjina Kai cike da damuwa hankalinta ba karamin tashi yayi ba Dan tasan halin ummaty Sarai wajen saka Abu a cikin ranta.."Zaki iya tashi kitafi na sanar dake hakan ne da wuri kafin lokaci yayi Dan a yadda na tsara inaso kibi hauwah kutafi can anka ki zauna wajen yayana"...da sauri ta dago kanta bakinta Yana rawa zatayi magana gwaggo hauwa ta tarbi numfashinta "ke Mara kunyar inace ana magana kinason tsoma Baki?yaran zamani?mahaifinki na magana kina neman gaddama dashi?to Bari kiji Baki isaba mun rigada mun yanke hukunci Bari kiji Kuma Baki Isa mu fasa abinda mukai niyya ba saboda wani banza can Wanda kike wahala akansa yaro musaki yaki warkewa sai aikin banza kikeyi iyayensa basusan kinayi ba"
Chapter 19 · 0% Book details