← Book details Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 49

Sashe 32

Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*WANAN LITTAFIN NA KUDINE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619*

sosai haris ke jan ummaty da Hira da tsokana tun Bata kulasa har ta sake dashi Tana bashi amsa da dariya sosai yayinda zainul ke gefe kamar ya fashe da kuka bini bini haris ya sako zainul cikin maganarsu bakin ciki yasa zainul lumshe Ido Yana baccin karya..."muje ki rakani ladan dariyar da nasaki Dan Dole ki biyani dariyar da nasaki"yayi maganar cike da barkwanci

Cikin faraa tace "indai wanan ne me sauki ne muje"ta Mike ya Mike ya dubi zainul "laa yayi bacci idan ya tashi kice natafi"ta gyada Masa Kai ta dauki wayarta tabiyo bayansa...yanajin karar rufe kofarsu ya bude idanuwansa da sukai jajir ya bi kofar da kallo cike da takaici....

Har mota ta rakasa ya bukaci numberta dakyar ta basa Saida ta Gama ja Masa aji sanan ta koma shi Kuma ya wuce...

Tana sako kafarta cikin gidan Kiran gimbiya rumana ya shigo wayarta dikda number ta gani tasan itace Dan daga ita sai haris keda numberta....wani irin faduwar gaba ta tsinci kanta tana bin Kiran da kallo har ya tsinke sai a Karo na biyu ya Danna recieve ta Kara a kunne a sanyaye tace"assalamualaikum barka da yammaci ranki ya Dade"

"Barkanki dai ummaty kintafi ne ko kina Nan?"

Dan yatsina fuska ummaty tayi Tana tsaye "Ina Nan ranki ya Dade"

"Ina bukatar ganinki yanzun a sashina zamuyi magana Mai muhimmanci"...Tana Gama maganar ta kashe batare da jiran cewarta ba Dan hakan ummaty tabi wayar da kallo tana nazari...sanan tayi murmushi ta Shiga danne danne Nan da Nan ta Shiga recording sanan tayi sashen gimbiya rumana.....

*WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619*

*TEAM...UMMATY/HARIS*🏃🏻‍♀

*Team gimbiya rumana*🤥

💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞

*HASKE WRITERS ASSO💡*

*SLIMZY😍*
[1/23, 11:18 AM] 😍SLIMZY😍: 29

A tsaye ta sameta tana kallon window dakinta hannuwanta rungume a bayanta....cakkk ummaty ta tsaya daga kofar dakin gabanta na tsananin faduwa dakyar ta hadiye wani mugun miyau ta furta "assalamualaikum"batare da ta karasa shigowa dakinba,

A hankali gimbiya rumana ta juyo fuskarta dauke da damuwa ta saukewa ummaty idanuwanta wadanda suka canja kala sukai jajir tamkar wadda tayi kuka,kallonta takeyi ido cikin Ido yayinda kirjin ummaty ya cigaba da bugu sauri da sauri....tsoro ya cikata tamkar ta saki fitsari takeji a wajen saboda tsananin tsorata da tayi da yanayin na gimbiya rumana addua ta shigayi cikin zuciyarta hade da tasbihi kala kala Tana mai neman tsari da Sharrin gimbiya rumana...katse mata tunani tayi ta hanyar Kiran sunanta da wata iriyar murya bakinta har Yana sarkewa ",ummaty"....dammm gabanta ya Fadi ta dago Kai da sauri bakinta Yana karkarwa ta amsa "na'aaam ranki ya Dade"

"Ya kika tsaya daga bakin kofa kamar wadda zaa cinye ki shigo Mana"...jikin ummaty na tsananin rawa kafafuwanta dakyar take dagasu ta tako a hankali tana tafiya gimbiya rumana na bin yadda jikinta ke rawa da idanu har ta karaso tsakiyar falon ta durkusa Akan gwiwoyinta ta sunkuyar da kanta...cije lebe gimbiya tayi cike da takaici sanan tayi gyaran murya ta matso daf da ummaty "ummaty ya Naga dik kin tsorata kin furgita lokaci daya kafafuwanki har rawa sukeyi"ta jefa mata tambaya Tana bin yanayin nata da kallo...

"Ummaty yanayin ki Yana Nuna min tamkar akwai wani Abu da kikeyi Wanda bakyaso insani dik a rude kike"...

Zaro Ido ummaty tayi hade da dafe kirji"haba ranki ya Dade?Nina Isa inyi wani Abu batare da sanin uwata uwargijiyata ba ?Babu wani Abu Wanda Zanyi shi batare da sanin kiba ranki ya Dade farin cikinki shine farin cikina banida wani aiki Wanda ya wuce bin umarninki ko wani iri ne ranki ya Dade wane ni?"

Murmushin Jin Dadi gimbiya rumana ta sauke hade da sassanyar ajiyar zuciya "kin tabbatar dik abinda nasaki Zaki iya yinsa?kin tabbatar idan na bude Miki sirrin zuciyata Zaki rike mun Amana bazakici amanata ba ummaty kin tabbatar Zaki kasance tare Dani har karshen rayuwarmu Babu abinda zai Shiga tsakanina dake na cutarwa ummaty?Zaki taimakeni ta ko wani Hali ummaty?"ta karasa maganar muryarta Tana rawa tamkar zatayi kuka ita kanta kalaman gimbiya rumana da yadda muryarta ke rawa sun sanyaya mata jiki sun karya Mata zuciya har idanuwanta suka ciko da hawaye...tasa hannu ta share batare da gimbiya ta ganiba Amma bangaren zuciyarta ta tuna mata da niyyarta na kubutar da zainul da sauran zuriar gidan daga muguntarta lokaci daya tausayin gimbiya ya gushe cikin zuciyarta ta Kara samun karfin gwiwa....style tayi tamkar Tana duba agogo ta tabbatar da wayarta tana kan recording taji wani sanyin dadi cikin zuciyarta na burinta dake Shirin cika...gyaran muryar gimbiya ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tsunduma tayi furgigit ta dago kanta taga ita take kallo ta sadda kanta kasa zuciyarta na tsananin harbawa..."ranki ya Dade Babu wani Abu Wanda Zaki umarceni inyi Miki shi banyishiba a lokacin da kikeso domin inajinki tamkar uwar data haifeni Kinga kuwa uwata Bata Isa ta bani umarni in kalli idonta ince baxanyi Mata shiba bazan iyaba ranki ya Dade dik wani abinda kikeso ki fadeshi Kai tsaye batare da wani tunaniba Zaki sameni me gaskiya da rukon Amana ranki ya Dade",

"Kin tabbata?"

Gyada mata Kai tayi"insha allahu ranki ya Dade"...mstsowa tayi kusa da ummaty ta zauna daf da ita har numfashinsu Yana Karo da juna...

"Ummaty Abu na farko shine inaso infito fili insaki aiki Akan zainul abideen saboda Naga boye boyen bazai yuwuba hada kanmu nidake shi zaisa inci nasara har incinma burina Akan bukatata,ko nawa ne daga naira daya zuwa million dari zsn Baki inhar zakisa mun hannu mu salwantar da rayuwar zainul abideen"

A firgice ummaty ta dago Tana kallon gimbiya rumana dikda batayi mamaki da wanan maganar daga bakinta ba a zahiri dama abinda take expecting kenan Amma s fili saita nuna mata furgici hade da zaro Ido take tasa hannu tana murza idanuwanta Wai alamar ko mafarki takeyi....rukota gimbiya rumana tayi yadda taga dik ta firgice tamkar zararriya batare da sanin cewar ummaty pretending kawai takeyi ba "cool down ummaty ki kwantar da hankalinki,nasan zakiyi mamaki akan wanan maganar da kikaji daga bakina nasan bakiyi zaton haka ba saboda yadda zainul yake a wajena koh?"...ummaty ta gyada Kai hannunta dafe da kirjinta har zuwa lokacin jikinta be bar rawa ba....

*WANAN LITTAFIN NA KUDINE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619*

"dik wata soyayya da zakiga ni rumana Ina nunawa zainul abideen to ba soyayyar komi bace face ta karya,banida wani buri a duniya Wanda ya wuce ni rumana Inga gawar zainul abideen a kwance Dan bana kaunarsa harabada bazan taba kaunarsa ba nayi nayi in rabasa da duniyar gabaki daya nakasa shine na biyo ta wanan hanyar na nakassa rayuwarsa nakeso tunda na kasa kasheshi ya Kare rayuwarsa a kwance,to yanzun babban tashin hankalina be wuce ganinsa ya fara warkewa ba shiyasa nakeso mu hada Kai dake mu shekasa lahira ki taimakeni ummaty banaso yaron Nan ya warke ya gaji sarautar garin Nan shine babban bakin cikina kiji tausayina Kinga ni ban haifi da namiji ba"Tana kaiwa Nan ta fashewa ummaty da kuka ta Sanya gwiwowinta a kasa a gabanta.. ummaty kuwa dake zaune tayi sandare take taji duniyar na jujjuya mata tamkar wadda Tasha kayan maye...Amma ganin gimbiya rumana gabanta Tana rokonta yasa ta tattaro jarumta tayi saurin rukota tana kokarin xaunar da ita "haba ummah darajarki da martabarki ta wuce kiyi durkuso a gaban ko waye ballantana ni ranki ya Dade umarni ya kamata kibani ba rokoba Dan kinfi karfin hakan,ni kaina neman maraba nakeyi domin nagaji Dan haka ki kwantar da hankalinki zamu yardar da kwallon mangwaro mu huta da kuda"....tsananin farin ciki yasa gimbiya rumana rungume ummaty a jikinta tana shasshekar kuka......

*******
Tafe take Tana hurga kafa domin tunda ta fito daga gidan Mai martaba ta kasa sukuni tunani kawai takeyi Babu kakkautawa lallai duniya Babu gaskiya yanzun da wata ce ita saboda kwadayin abin duniya zata bada hadin Kai wajen cutar da Dan uwanta musulmi?gimbiya rumana ta Bata mamaki matuka taci amanar gimbiya bilkisu kuma taci amanar Mai martaba koda yake batayi mamaki ba domin Dan Adam a wanan rayuwar ba abin yarda bane zaiyi abinda yafi haka mutum Sai Allah...aikuwa idan hakan ne to tabbas zata shayar da ita mamaki Dan saita tona mata asiri ta maidata abar kwatance...da wanan tunanin ta shawo kwanar hanyar gidansu,tun daga nesa take kallon dalleliyar motar Tana tunanin waye ta sani da irin waccan motar wadda ke kofar gidansu s Parke?harta karaso ta kasa tunawa Dan hakan ganin ba kowa yasa tasanya Kai cikin gidansu hade da sallama....turuss tayi tsaye tana binsa da kallo zaune Akan tabarma gefen Inna yanacin latas tsayawa tayi Tana kallonsa mamaki ya hanata magana shiko cike da barkwanci yace "ummaty kinyi mamakin ganina a Nan na rigaki zuwa koh?kin manta kece kikacemun innah latas zatayi shiyasa na rigaki zuwa na cinye duka"ya karasa maganar Yana daga mata gira daya,

Saroro tayi tana cigaba da kallonsa,...innah kuwa dariya tayi sosai sanan ta dubi ummaty "ke Kuma inbazaki shigo ba ki koma saikace haris din ne Baki saniba kin wani tsaya kina kallonmu"...jiki Babu kwari ta shigo cikin gidan ta wuce dakinta ta barsu Nan zaune suna hirarsu...

Koda sarkin dawaki ya dawo sallar magriba farin ciki yayi sosai da ganin haris yazo Wai saboda ummaty...addua ya shigayi cikin zuciyarsa Wanda ya barwa Kansa ita kawai....

*******

Sosai hankalin halima ya tashi Tana rike da Muhammad "ummah gaskiya kin tafka babban kuskure na saurin yadda da wanan yarinyar har kika kwashe sirrinki kika fada mata ummah meyasa?"halima ta dafe Kai cike da bacin Rai...

Girgiza kafa gimbiya rumana tayi Tana murmushin kasaita "ki kwantar da hankalinki sanin Kanki ne kusan Rabin maaikatan gidan Nan sun San koni wacece Amma shekara da shekaru Babu Wanda yayi yunkurin tonamin asiri Dan haka nasaka Mata matakan tsaro hagu da dama gabas da yamma kudu da arewa sanan na Dana mata tarko da su yusha'u Dan haka idan tayi yunkurin tonamin asiri itace zata kwana cikin balain...
Chapter 32 · 0% Book details