Sashe 15
Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*********
Koda ta je da maganin wasiwasin bashi maganin take tayi ga faduwar gaba data tsinci kanta ciki da ta dubi gorar sai hotonta yayita yawo a idanuwanta ta rasa a inda tasanta....dakyar Tai shahada ta tsiyayo maganin a cikin Kofi Dan kadan ba kamar yadda take bashi ya shanye dukaba ta fara bashi ta gani ko aljanun nasa zasu tashi?tausayi yake Bata sosai bataso tabashi su tashi su wahal dashi ta Mika Masa Babu musu ya karba ya shanye....shi Kansa fargabar Shan maganin yakeyi Dan dai kawai Kar yayi Mata musu ne bayason bacin ranta bayaso tace Tana kokarin Taimakonsa Yana gwasaleta shiyasa...ya runtse idanuwansa wasu abubuwa nayi Masa yawo akai tamkar tsutsa ganin yadda yakeyi yasa ta furgita da sauri ta Shiga tambayarsa ko lafiya?saidai ya kada Mata Kai kawai kusan minti talatin a hakan ganin Yana kokarin fita hayyacinsa yasata saurn Ciro MP3 ta kunna tasa Masa suratul baqara a cikin kunnuwansa dikda hakan gabanta bai daina tsananin faduwa ba ta kafesa da idanuwa ko kiftawa batayi a hakan taga bacci ya daukesa....sassanyar ajiyar zuciya ta sauke ta dauko gorar maganin tana kallonta tamkar me Shirin gano wani Abu...kome zuciyarta ta Raya Mata oho sai kawai ta Mike tsaye tana jinjina Kai a hankali idanuwanta suna Shirin kawo ruwa....
********
"Gimbiya meye hadinki da ni ne da Yar Dana Haifa kikeda niyyar sai kin halakamu hankalinki zai kwanta?"
Wata uwar tsawa ta daka Masa "Kai sarkin dawaki me kake nufi da kalamanka?ka iya harshenka idan ba hakan ba zansa a datse maka shi Dan na lura kwanakin Nan kanada son ka rinka jefamun maganganu marasa Dadi ka manta da wadda take gabanka?ko ka manta da wacece gimbiya rumana matar sarki abdulazeez?ko ka mance da iko da mulki da izzah irin tawa?wadda cikin minti goma zuwa ashirin idan nayi niyya Zanyi abinda sarki zaisa a ratayeka?Dan hakan ka iya kalamanka idan kana gabana matar sarki nake"ta maida kanta gefe tana huci tamkar wata zakanya....ganin yadda take mazurai tana hura hanci yasa hankalin sarkin dawaki tashi lokaci kankani ya nemi dik wata natsuwa tasa ya rasa ya rasa dalilin dayasa wanan matar take amfani da mulki da kissa da tuggu irin na Mata Akan kowa a masarautar Nan babban tashin hankalinsa da damuwarsa be wuce yadda sarki da gimbiya bilkisu da dik wasu a Hali na gidan sarki da mutanen gari suka dauki soyayyar duniya suka Dora Mata ba rashin sanin ko ita din wacece...da sunsan yadda take a wajensu da tuni sun Nemi tsari daga sharrinta,dafinta yafi dafin maciji gimbiya rumana hawainiya ce me rikida dik yadda ta gadama zata rikidar maka Kuma cikin seconds da Basu wuce talatin ba dik bukatar datazo maka da ita Dole ka amince da ita saboda sanin ilimin magana da sarrafata da wayau tsantsa da Allah ya Bata...
"Sarkin dawaki"ta Kira sunansa a kausashe Wanda Saida hantar cikinsa ta kada Bata jira amsawarsa ba ta cigaba da magana...
"Ka bini a hankali idan ba hakan ba daga Kai har yarka Kuna cikin balai Dan gab kuke da ku tsinci kanku a cikin Rami ana muku tambayoyi,Dan da zarar asiri ya tonu to Babu makawa sarki zaisa a kasheku daga Kai har yarka Kuma dik yadda kaso da ka tonamun asiri inada hanyoyi da dama da zambi in Kare kaina batare da nasamu wata matsala ba Dan hakan Ina Mai Baku shawara a wanan tafiyar Babu bijirewa sanan Babu kin bin umarnin gimbiya rumana hakan tamkar Wasa da rayuwarku ne.....
WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU CE KACAL TA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619
**HASKE WRITER ASSOCIATION* 💡
*
*ZAINUL ABIDEEN*
*SLIMZY😍*
[1/23, 10:42 AM] 😍SLIMZY😍: 14
Ajiyar zuciya yayi Yana Kare Mata kallo yadda take kumfar Baki saboda masifa...karara ya hango rashin Imani a fuskarta tunda ta furta hakan to zata aikata,Dan haka bazaiso asiri ya tonu ba Dan Babu wadda yakejin tausayi kamar yarsa ummaty wadda take tsananin Shan wahala akan zainul a tunaninta dik abinda takeyi tana yinsa ne Akan samun lafiyarsa .."Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun"ya fada a fili ya furzar da wata iska Mai zafi daga bakinsa...
"Ranki ya Dade yanzun me kikeso ayi"yadda yayi maganar a sanyaye sarkin dawaki sai ya baka tausayi gabaki daya a rikice yake,ita kanta yadda yayi maganar yaso Bata tausayi Amma rashin digon Imani a cikin zuciyarta yasata Kara tamke fuskarta ta dubeshi Babu walwala "dabara ta rage ga Mai Shiga rijiya ai,inma yayi tsalle ya fada,ko Kuma ya taka a hankali ya Shiga,gargadi na gareka na karshe shine kada ka kuskura kace zakayimun Wasa da hankali hakan babban gangancine ga rayuwar zuriarka gabaki daya sanan kada ka kuskure ka sanarwa da yarinyar Nan kasan tsakanina da ita kamar yadda batasan tsakaninka Dani ba na fada maka"...
Zufar dake karyo Masa yasa hannnunsa ya share Yana Shirin Yi Mata magana ta Nuna Masa kofa"ga hanya ka fita nagaji da Jin muryarka a Nan saina nemeka wani lokaci"...jiki a sanyaye ya fita dik jikinsa Babu kwari tamkar Wanda akaiwa duka haka yakejin Kansa,dakyar yaja kafarsa ya bar gidan gabaki daya...
********
Hasa'uh ce makale a jikin sashen gimbiya rumana tana kaiwa da komowa jiran shigowar ummaty kawai takeyi kamar yarda uwargijiyarta tabata umarni Akan ta tabbata taga shigowarta Dan tabata sakon da aka kawo shi Akan lallai ta bashi yasha zataga abun mamaki,tana Nan tsaye ummaty ta shigo sauri sauri tana Shirin wucewa kamar daga sama taga hansa'u a gabanta da sauri taja da baya saboda yadda ta tsorata,wani kallo hansa'u tayi Mata sai Kuma ta tabe Baki "meye na ja da baya sai kace Kinga abun tsoro?ko gudun bayi kikeyi?nagadai banbancina dake a gidan Nan shine uniform Amma ai aikin bautar kikeyi Zaki ganni ki wani ja da baya kamar Kinga dodan jiya"daga ganin yadda take magana Taji haushin yadda ummaty taja da baya,ita kuwa ummaty dariya tabata Dan harga Allah Bata ganta ba Dan haka murmushin Nan nata Tai Mata hade da cewa "Allah ya huci zuciyarki hansa'u wallahi tsoro naji Dan bansan da zuwan naki ba kiyi hakuri"ta kureta da Ido
Sake tabe Baki hansa'u tayi "komadai menene kyaji da iyayinki ni gimbiya rumanah ke kiranki tana wancen sashenn"ta Nuna Mata kebabben sashi inda Nan gimbiya ke Zama dik lokacinda zata Bata magani tabawa zainul,Jim abinda hansa'u tace yasa ta tsinci kanta cikin tsananin faduwar gaba,gabaki daya yanzun ita batason muamala da gimbiya rumana Dan akwai abubuwa da dama da takeji a jikinta dangane da wanan matar....inhar maganar bawa zainul magani ne gaskiya ita zuwa yanzun ta hakura da samun lafiyarsa gara ya zauna a hakan da yadda yakeshan wahala dik lokacin da zaisha wanan maganin gashi uwa uba ta rasa dalilin dayasa maganin da gimbiya rumanah ke karbowa ya zainul yayi iri daya da Wanda mahaifinta ke karbowa shekara da shekaru Yana Bata Akan nema Masa magani ita kanta ya daure akan wanan lamarin,da wanan zancen zucin nata ta Isa sashen da gimbiya ke jiranta da sallamarta a bakinta ta Shiga ta nemi kasan carpet inda tasaba Zama idan ta shigo ta zauna "ranki ya Dade gani ance kina kirana inji hansa'u"Tai maganar tana dukar dakai
"Dawo kusa Dani Mana d'iyata ummaty,banaso kina banbanta Kanki da diyan Dana Haifa inajinki tamkar su fiyya afnan halima Aysha da zahrau yarana matso kusa"Tai maganar fuskarta a sake,Dan hakan a d'arare ummaty taja jiki ta matsa kusa da ita kasan kujerar datake zaune ta sunkuyar da kanta gabanta na tsananin faduwa
Dafa kanta gimbiya tayi Tana murmushi "kokefa ummaty,nasa ankiraki ne saboda wani rubutu da malam ya Aiko dashi zaabawa zainul Akan aljanum Nan nasa masu tashi su gajiyarmun da yaro yace kada a wuce yau baa bashi ba idan har aka bashi zaaga abun mamaki"Bata fuska ummaty tayi batare da tace komiba tunawa da tayi da irin wuyar da zainul Kesha idan aka bashi maganin Nan
"Ummaty ko bakison yayan naki ya warke ne umm?Naga kinyi shiru"
Da sauri ummaty ta kada kanta tana kakalo murmushin Dole "ah ah ranki ya Dade sai nafi kowa farin ciki idan hakan ta kasance"
"Yauwa ko kefa,Dan hakan ki Mike tsaye wajen jajircewa Dan uwan naki yasha maganin Nan kinji"
"Toh"shine abinda tace Amma badan yakai zuciyarta ba ta karbi maganin sukai sallama tasaka a jaka Tana tafe tana zancen zuci,yanzun tana zuwa ta bashi wanan maganin jikinsa zai rikice Yar hirar da sukeyi yanayi Mata murmushi tanajin Dadi a ranta asa dik yakiyi yayita ciwo,Anya zata yarda ta Kara bashi wanan maganin akai akai kuwa?dikda na neman lafiya ne?zuciyarta ta fara yi Mata waswasi Akan maganar maganin Nan,ya kamata ace aljanu yanzun sunyi nisa dashi tunda ya kwana biyu Yana Shan maganin Amma da yasha sai aljanun sunzo,sanan Kuma basason karatun alkurani?tabbas aljanu basason karatun alkurani Amma idan akasa musu korarsu yakeyi,ta tuna malaminsu ya taba sanar Dasu a islamiyya da su yawaita karanta alkurani ko saurarensa hakan na nesantamu daga aljanu,shedanu,da shedanun mutane....ajiyar zuciya ta sauke..idan hakane kuwa zata cigaba da sa Masa karatun alkuranin Koda a boye ne Kuma zata tsaya da bashi maganin taga yadda jikinsa zaiyi...da wanan tunanin ta karasa cikin gidan ta Shiga sashen ammiey da sallamarta....
*WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI...08166177830 KO 07084161619*
*********
Shiri sosai fiyya sukeyi itada afnan da Aysha kannen zainul abideen zasuje wajen bikin diyar sarkin kudu Wanda ya kasance babban amini ga mahaifinsu Aysha ta dubi fiyya tana dariya kasa kasa "ya fiyyah wanan kyau haka karfa kije kiyiwa uncle nurah kishiya,Dan kina haduwa da wani Dan sarkin a wajen ya kyalla Ido ya ganki babu makawa abbah zaice zai aura Miki shi"cike da zolaya Tai maganar tana gimtse bakinta,wani kallo da fiyya Tai Mata yasata ta Sha jinin jikinta Dan tasani Sarai fiyya batason raini shiyasa Bata cika Wasa da su ba,ganin hakan yasa afnan maida maganar datayi niyyar yi a cikin bakinta itama tana dariya kasa kasa