Sashe 35
Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cike da kasaita take takawa har ta karasa jikin wardrobe dinta ta bude wata bakar Leda ta dauko Mai dauke da gorar magani ciki ta dagata Sama tana bin gorar da kallo sanan ta sauke lallausan murmushi ta juyo ta tako har wajenda ummaty ke tsaye itama ta tsaya,murmushi ta Kara saukewa a fuskarta ta daga gorar daidai fuskar ummaty,wadda gabanta ke tsananin faduwa tana karewa gorar kallo cike da tsoro..."wanan shine abinda zai fiddaki cikin matsalar da kike Shirin fadawa,idan har kika bawa zainul wanan maganin ya Sha bukatata ta biya to tabbas zan fiddaki cikin wanan Kullin Koda Nan gaba ne bazan taba saki ciki ba ummaty ki ceci Kanki ki ceci rayuwar iyayenki data zuriarku Baki daya kibawa zainul maganin Nan yau ayita takare idan ba haka ba Ina Mai tabbatar Miki komi Yana iya faruwa,Abu na karshe da zan sanar Miki shine idan kikace Zaki yaudareni to wallahi wallahi zakisha mamakina idan kingadama kije Kiki bashi kiyi dik yadda kikeso Amma idanuwana sunkai dubu akanki dik abinda kikeyi ko numfashi kika sauke me karfi sai an sanarmun Dan haka dabara ta rage ga Mai Shiga rijiya karbi"ta Mika mata gorar hannunta na rawa ta karba hawaye kuwa tamkar an bude pampo zuciyarta na Raya Mata abubuwa da dama ga recording tayi dik na maganganunsu Amma batasan ta yadda zaayi ta fidda kanta ba....ita kuwa gimbiya makulli tasa ta bude kofa tayi Mata nuni da ta fita......
*WANAN LITTAFIN NA KUDINE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619*
**********
tallabe take da warisah a jikinta wadda jikinta yayi zafi Rau alamar zazzabi cike da tashin hankali hajiya kubrah ta dubi Yar tata "ke warisah Wai bazaki fadamin abinda yake damunki ba so kikeyi ki mutu?wa kikedashi Wanda ya fini?Wanda kike ganin Zaki iya fadawa damuwarki bayan ni?dik yadda naso ki fadamin kinki fadamin dubi dik yadda kika koma fisabilliahi kifadamun ko menene damuwarki d'iyata Allah zai Miki maganinta Zanyi Miki"...ta karashe maganar cikin sigar lallashi,
Maimakon tace wani Abu sai kawai ta lumshe idonta tana murmushi,hawaye na gangarowa ta gefen idanuwanta masun zafin gaske a hankali ta daga hannunta ta dafe gefen kirjinta batare da tayi magana ba zuciyarta na gargadinta da kada ta Fadi abinda ke damunta idan haka ne har gara taje ta tari zainul ta sanar dashi dikda tanaji a jikinta bazai taba sauraronta ba ....
Jijiigata momy keyi da kyar ta bude idanuwanta wadanda suka canja kala sukai jajir hankalin momy ba karamin tashi yayiba warisat dinta ce dik ta canja haka?meke faruwa da yarinyar take boye mata Wanda yakesata tsananin Rama ga fari da take karawa da kyau na daukar hankali...dik yadda hajiya kubrah Tai lallashi fafur warisah Taki fada mata damuwarta saima mikewa da tayi ta fada toilet Dan tayi wanka...ta dauki lokaci cikin toilet kafin ta fito inda tabar hajiya kubrah Nan ta sameta ta rafka tagumi sai kawai Tai mata murmushi ta karasa gaban mirror dinta ta Shiga shafa mayuka kala kala masu dadin kamshi da turarruka ta shirya tsaf cikin doguwar rigar jallabiya red Mai stones masu daukar Ido ta yane kanta da gyalenta ta kawo maroon din janbaki ta shafa Sama sama ta zizara kwalli a manyan idanuwanta Wanda Tai masifar kyau tamkar ba ita ba....sallamar ya haris ce ta dakatar da ita daga maganar da Tai Shirin Yi ya nemi gefen gado ya zauna sanan ya kalli warisah ya tabe Baki cikin sigar tsokana yace "ko kyau"ta turo Baki
"Dama fa Kai zanje nema naji kamar kana cewa xaka Shiga gidan sarki"
"Ehh,ya akai"yace hade da tamke fuskarsa,
"Dama Ina son zuwa ne in duba jikin ya zainul"daga momy har haris kallonta sukai cike da mamaki sai Kuma suka basar haris yace "to muje kada ki Bata min lokaci"...
"Momy sai mundawo I love you kinji"cewar warisah tana murmushi tana kallon momy itama murmushin ta maida mata "a gaida bilkisu da rumana inaga zan sameku da yamma can",
",Owk momy"suka hada Baki tare suka daga mata hannu suka fice dakin ta bisu cike da kallon so da kauna.....
*********
Dik wani shiri hansa'u da yusha'u sunyi shi Suna makale suna kallon cikin dakin zainul abideen rikeda camera yusha'u ya dubi hansa'u suka hada Ido lokacin da ummaty ta Ciro gorar magani idanuwanta taff da hawaye....
"Ya zainul ga maganinka zakasha?idan bazaka sha ba bazan takuraka ba"tayi maganar ne don zainul yace Baya Sha,
"Mezai hanani Sha ummaty?maganin Nan ba yau kika soma bani ba ban Isa ince baxan Sha ba Dole insha bani"...ya karasa maganar Yana kallonta,...gabanta na tsananin faduwa ta Ciro gorar tana kallo,
Daga inda suke labe "yusha'u wanan ba gorar da gimbiya tabawa ummaty bace mu cika aiki kawai mu dauki wajen da ta bashi mu ruga mu sanarwa da gimbiya bilkisu halin da ake ciki".
"Kin tabbatar ba ita bace?"ta gyada Masa Kai murya kasa kasa "wallahi ba ita bace"...
Tanaji tana gani ta Mika Masa gorar ya rike ta rike ya Shiga kwankwadar ruwan maganin da gimbiya tabawa ummaty har yasha rabi tari ya sarkesa cike da tashin hankali ta rike gorar tanayi Masa sannu....
Suna Gama sanar mata da Nuna mata videon gimbiya bilkisu da fiyya suka Mike s kidime suka runtuma a guje zuwa sashen zainul abideen cikin tsananin tashin hankali ,
Bankado kofar da akayi ce ummaty ta Mike a kidime gorar ruwan maganin da sauran suka Fadi jikinta suka watse....shiko zainul na kwance shame shame Babu alamar numfashi s guje gimbiya ta shake ummaty "asirinki ya tonu munafukar Allah lallai mutum Sai Allah dama kece silar ciwosa?"
Dafe kirji warisah tayi daga kofar dakin da suka shigo tare da haris ......
*WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619*
💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞
*HASKE WRITERS* *ASSO💡*
*SLIMZY😍*
[1/23, 11:40 AM] 😍SLIMZY😍: 32
Kakkafe idanuwan ummaty sukayi saboda yadda gimbiya bilkisu ta shaketa ta Shiga kakari tamkar wadda zata sheka lahira cikin azama haris yayi kansu da sauri ya ruko hannun gimbiya bilkisu "ammiey ki tsaya Zaki kasheta kinsassauta rukon Nan kada yarinyar Nan ta bakunci lahira Dan Allah"
Idanuwa jajir take bin haris da kallo hawaye taf ciki "menene amfanin makashinka Yana tare da Kai haris?ko kasan cewa shekara da shekaru nake zargin akwai Wanda yake kullawa yaron Nan wanan masifar inata addua yau Rana tsaka Allah ya Toni asirinta na tsaneki na tsaneki ummaty allah ya tsine Miki albarka bakida wani amfani a wanan duniyar Wanda ya wuce in kasheki matsiyaciya dangin matsiyata"...kan haris daurewa yayi saboda furucin da gimbiya bilkisu keyi Amma hakan be hanasa sa karfinsa wajen kwatar ummaty ba cikin kankanin lokaci ya fizgota ta fada jikinsa sumammiya safiyya wadda ke tsaye a gefe saboda tsananin zuciya Tai kukan Kura tayi kan ummaty,wata uwar tsawa haris ya daka Ma safiya 'ke dakata kina hauka ne?meye haka?meye ribar Yi Mata taron dangi idan aka kasheta wani sabon laifi ne"Yana maganar cike da fushi Yana rungume da ummaty wadda ke numfashi Sama sama idanuwanta a rufe hawaye masu dumi ke bin gefen fuskarta....
Gimbiya rumana a firgice ta shigo sashin tana zarar idanuwa zuciyarta na bugawa fat fat saboda furgici Amma ganin halin da ake ciki ta danne sai kawai tayi kan zainul abideen tana sharar hawaye "Allah sarki Dan ummah ni dik ba ta kowa nakeyi ba ta yarona nakeyi ta ran magajin sarki nakeyi shi kadai gareni idan aka kashemun shi an cuceni"tana rusa kuka musaddik ne ya shigo da sauri ya sunkuci zainul abideen a kafadarsa yayi sashin Mai martaba dashi be tsaya ko Inaba sai bedroom din sarki Nan ya shimfide shi ya bude windows hade da kunna fanka saboda yadda yake fidda numfashi tamkar me ciwon asthma kimfaffaki ke fita daga bakinsa....
Gabaki daya gida ya rikice Nan da Nan dangi duka fara hallara gidan sarki harda Yan kallo na nesa Dana kusa cikin gari ya dauka cikin mintuna da Basu wuce goma Sha biyar ba labari ya karade garin da kewaye cewar angano Wanda yayi silar ciwon Magajin sarki ummaty Yar gidan sarkin dawaki wasu suna yarda da maganar wasu Basu yarda da cewar ummaty zata aikata hakan ba duba da kananun shekarunta....
********
Cikin awa daya fada ta cika dankammm har Babu wajen Zama xuriar gidan Mai martaba kowa ya iso da labari ya cin Masa harda sarkin dawaki Wanda Yana kasuwa akayi Masa Kiran gaggawa Wanda ko da ya karaso cikin fadar ya tarar da mahaifiyar ummaty ta rigashi isowa yadda yaga wuri makil da mutane ya tabbatarwa da Kansa shikenan tafaru takare (Billy galadanci)Wai anyiwa Mai Dami daya sata dama yasan ko ba Dade ko banjima akwai wanan ranan,Jin yakeyi tamkar ya saki fitsari lokacin da ya hada Ido da gimbiya bilkisu ta watsa Masa wani kallo Mai tattare da tsana da kyama besan lokacin da ya sadda Kansa kasa ba Yana ambatar sunayen Allah s zuciyarsa... Hawaye ne kawai ke gudu a fuskar innah wadda ta rasa abin cewa ji takeyi tamkar ta hadiyi zuciya ta mutu Dan bakin ciki ta tabbatar wa da kanta sharri akayiwa ummaty ba gaskiya bane wanan labarin da ake yadawa... Zaman sarkin dawaki a fada shi ya hargitsa fadar aka soma CeCe kuce surutu hade da zage zage kawai ke tashi har kusan minti biyar....