← Book details Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 49

Sashe 46

Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*******
Ummaty na azhkar din safe kamar saga sama taga mutum sanye da farar jallabiya hakan ta tsorata ta taja da baya kadan tana zaro ido "ya zainul daga Ina kake da safiyar nan?"be Bata amsar abinda ta tambayesa ba ya ce 'banaso ku Kara cikakkiyar awa daya cikin gidan nan ga mota nan a waje na kawo zata kwashi kayanku wadanda kukeso"gaba yayi ya barta nan a zaune ya nufi dakin da yake tunanin nan ne na sarkin dawaki...shima yayi mamakin ganin zainul ya shaida Masa abinda ya kawosa beyi Masa musu ba ya shaidawa innah itama Shiri ta shigayi suka Shiga shirye shirye ummaty kuwa dik yadda taso ta hada ido dashi ko zataji sanyi ya ki Bata dama kauda kansa yakeyi dikda shima Babu abinda yake bukata sama da ganin kwayar idanuwanta Amma takaicin abinda tayi jiya shi ya sa wani kishi ke damunsa yayi hakan ne Dan ya kuntatawa haris Dan yasan tabbas zaizo zai kuma tarar da basa nan sai yaga ta iskanci....

Tsaye yake jikin Shiga kofar gidan ya juya baya ta tako har inda yake ta tsaya gabanta na tsananin faduwa ga wani tsoronsa da ya cikata "ya zainul"ta kirasa muryarta na rawa..."menene Ina jinki"....yace a takaice cikin wata irin dakakkiyar murya ..kasa cewa komi tayi kawai ta rakube gefensa ta wuce hawaye na sauka a idanuwanta wani irin ciwo yakeji ya ga ummaty a wanan halin baya kaunar ganin hawayenta saidai Dole ya dau mataki kanta Dan ta Bata Masa Rai....

Ko kafin bakwai sun Gama kwashe Kaya tas sun nufo gidan Mai martaba da Kaya Niki Niki nan zainul ya zage dashi aka Shiga kwashe kayan zuwa cikin gidan da maaikatan cikin gidan

********
Zaune suke suna breakfast shida daddynsa a parlor ,daddy ya nisa yace "haris inaso kafin inkoma Italy ayi bikinka menene shirye shiryen ka?".. Dadi ne ya lullube haris bakinsa ya kasa rufuwa ya durkusar da kansa cike da kunya Yana jujjuya cokali cikin tea shiru yayi sanan yace "daddy nima hakan nakeso wallahi tunda ankai kudi sai ayi maganar aure ayi shirye shirye daddy da kayan akwati ko?sai a tsaida Rana "

"Ehh hakan nakeso Bari Zan Kira abbanka da mukaje tare mu koma gobe Akan maganar yanzun zanyi maka transfer din million biyar cikin account Dinka sai ka dauki kanwarka kuje siyayyar Kaya idan Basu isaba Zan Kara muku"...hajiya kubra ce ta shigo parlorn jiki a sanyaye tun jiya ta rasa abinda keyi Mata dadi ta nemi kujera ta zauna "alhaji saidai inji Kuna maganar aure daga Kai sai Danka Baku sani cikin lamarinku yanzun haris ne zai dau warisah su je siyayyar kayan aure inada Rai"

"To momyn yara ai gani nayi bakison auren kince Babu ruwanki shiyasa kawai nace muyi nida yarona".murmushi tayi wanan karon "to yanzun da ruwana a tsundumani dumu dumu ciki"...wani Dadi ne ya lullube haris ya rungume momy Yana dariya cikin zolaya ta dungure Masa Kai "kaga ja'irin yaro wato ka gaji da zama da momy aure kakeso Koh?"dukkansu sukasa dariya cike da farin ciki suka cigaba da breakfast dinsu a tare...

"Ina babyna ne Wai"daddy ya tambayi momy...

"Warisah bacci takeyi ninarasa meke damun wanan yarinyar inaga wajen likita Zan maidata Dan nagaji"

"Gaskiya momy"cewar haris Yana Kai farfesu bakinsa..

*******
Tryin number halima Zahra ta karayi ganin yadda gimbiya rumana ke numfarfashi ta nufi wajen mahaifinta yaki sauraronta so takeyi akaita asibiti Amma yaki tayi Kira na biyu kenan taji sallamar halima cikin dakin...ta shigo sanye da hijabi fuskarta a kumbure idanuwanta sunyi jajir yaranta biye da ita da sumayya da samir sanye da kayan sanyi....

Kallo Zahra Kebin halima dashi Baki bude har ta shigo...cakkkk ta tsaya halima tana bin mahaifiyarta da kallo cike da mamaki da tsoro ta zaro ido zatayi magana samir ya ce "laaaa ummu dubi ojuju"ya kwashe da dariya Yana tabo Yar uwarsa...
.
"Meya samu ummah ?ya na ganku a wanan sashin da Babu kowa?na shigo uwale tacemin Kuna nan?"

Takaici ne ya lullube Zahra ta Shiga zayyanowa halima abinda ta sani daga farko har karshe "innalillahi wa innah ilaihi rajiun...na Shiga uku ni halima wanan wace irin bakar Rana CE nagani a daidai wanan lokacin jiya nima muka samu matsala da prince da mahaifiyarsa ta ce sai ya sakeni jiya shine ya sakeni harda duka".. wata irin zabura Zahra tayi ta Dora hannu aka "nashiga uku na lalace wace irin mummunar kaddara ce ta samemu?"

******"
Parking haris yayi a kofar gidan ya kashe mota ya fito Yana sanye da track suit kansa da hular sanye me rubutun later U a jiki ya nufi kofar gidan saidai Kato padluck da ya ganine ya sanyashi yayi turus yayi maza ya Ciro wayarsa ya kalli agogo karfe Sha daya da Rabi....Ina sukaje?....ya tambayi kansa cike da tashin hankali zuciyarsa ce ta Raya Masa Kila suna gidan Mai martaba.....ya juya kawai ya nufi motarsa ya Shiga ya tadata ya bar kofar gidan....

*KUYI HAKURI DAN ALLAH BANI DA BAKIN DA ZANBAKU HAKURI AKAN WANAN LAMARI WALLAHI KWANA BIYU BANI DA LAFIYA NE SAI A HANKALI SANYI YAZO SHIYASA KUKE JINA SHIRU WALLAHI...AMMA INSHA ALLAHU SAURAN PAGES DIN NAN DA YARAGE ZAKUJII*

*HASKE WRITERS ASSO💡*

💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞

*SLIMZY😍*
[1/23, 11:50 AM] 😍SLIMZY😍: 42

Tarba suka samu ta musamman daga bangaren gimbiya bilkisu wadda dama tasan tun bayan fitar zainul can ya nufa ko baa fada mataba shiyasa ko kafin su iso an gyara sashen gimbiya rumana dikda dama ba wani Abu ya sameshiba sanan anyi breakfast dasu abinci kala kala aka Shiga shigowa dashi sashen gimbiya rumana Wanda ya kasance yanzun sashen sarkin dawaki da iyalensa....Baki bude innah take bin bayi da kuyangi ganin yadda wanan ya shigo wanan ya fita da abinci kala kala...kallon ummaty tayi suka hada ido ummaty ta sakar Mata murmushi tana Jin wani irin sanyi a cikin zuciyarta da wata natsuwa ta musamman data tsinci kanta ciki "Niko wanan abincin da ake shigowa dashi ummaty ai yayi yawa Ina zamu kaishi daga Baki na sai naki saina babanku?"itadai ummaty murmushi tayi batare da tace komi ba...janyo plates innah tayi tana Shirin serving dinsu wata baiwa ta shigo da sauri ta amshi plate din "ranki ya dade ba aikinki bane wanan hidimar tawa ce sunana iklima nice Mai aikin na sashen dik abinda kuke bukata nice zanyi muku"...innah galala tayi tana bin iklima da kallo wadda ta cigaba da aikinta tayi serving dinsu abinci kowa ta dire Masa a gabansa...tea ummaty ta dauka ta kurba ta ajiye cup din kenan haris yayi sallama cikin dakin Saida gabanta ya fadi da sukai ido hudu ta kauda kanta....innah da ke zaune sai faraa takeyi ta dubi haris "ah ah harisu sai kaje can baka ganmu ba ko?wallahi zainul abideen tun asuba ya je ya kwasomu kamar masu Shirin barin gari"...murmushi haris ya kakalo ya Dan tsugunna "innah Ina kwana"

"Lafiya kalau haris ya maman naka?"

"Lafiyansu kalau tace a gaisheku"...ya koma kujera ya zauna Yana jifan ummaty da wani irin shu,umin kallo ita ko gabaki daya ta rikice da kyar take cusa abincin a cikinta...innah ce ta katse shirun "haris a zuba maka abincin ka karya Mana"...siririyar ajiyar zuciya ya sauke "na karya innah kafin na fito"

"Toh shikenan"ta Mike ta bar musu parlorn ta nufi daya daga cikin dakunan....tasowa yayi daga inda yake zaune ya dawo daf da ummaty ya zauna Yana fuskantar ta da wani irin mayen kallo ko kifta idanuwansa bayayi,dik ta takura da irin kallon da yakeyi Mata ga wani irin bugawa da zuciyarta keyi...turo Baki kadan tayi ta jefa Masa harara ta dakko cup din tea zata Kai bakinta ya rike da sauri tai Masa wani irin kallo "ka rike mun cup Ina cin abinci idan tea din yayi Sanyi bazan iya Sha ba"kallonta kawai yakeyi batare da yayi magana ba,daga labulen dakin da akayi ne yasasu duka su biyun juyowa a tare hannun haris na jikin cup din ummaty....zainul ne tsaye a bakin kofar murmushi yayi "sorry bros na shigo banyi muku sallama ba hope banyi laiifi ba "ya karashe maganar Yana murmushin gefen fuska,gyada Masa Kai haris yayi shima Yana murmushin "yanzun nake Shirin shigowa wajenka dama idan na gama da nan din"

"Owk sai ka shigo"zainul yace a takaice sanan yayiwa ummaty wani irin kallo ya fice,...Ido ta bishi da shi har ya bace Bata sani ba Saida haris ya Dan tabo ta sanan Tai furgigit ta dawo da hankalinta tana sauke numfashi..cije lebe haris yayi cike da kishi yace "ummaty nasan zuciyarki Bata tare Dani gangan jikinki ce take tare Dani sanan inaji a jikina bakya Sona ummaty"a sanyaye yayi maganar Yana furzar da iska daga bakinsa

Tausayinsa ne ya lullubeta ta dubesa da Lulu eyes dinta "meyasa zakace haka ya haris bayan kana Shirin aurena sanan kace bana sonka?"

"Bakya Sona kinadai tausayina ummaty sanan kona aureki gangar jikinki kawai zan aura amma ruhinki da zuciyarki tana can wani waje daban"...mikewa yayi ya zura hannunsa cikin aljihunsa sanan yace"yau su daddy sukace sunaso suzo a tsaida ranar aurena dake so nazo in shaidawa baba ne kuma Naga kamar Baya nan Amma ki shaidawa innah"

Dakyar ta hadiye miyon da ya makale Mata a makoshi tace "toh"hanyar waje yayi ta bishi da kallo ya fice ko waigenta beyi ba,wani irin kuka ne ya taso Mata ta toshe bakinta ta fada Kan kujera tana rera kuka Mara sauti....

********
Chapter 46 · 0% Book details