← Book details Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 49

Sashe 17

Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Nima kinsan tun yaushe na tashi daga baccin Ina kallon kyakkyawar fuskarki kina tunani kin hada zufa?...da alamar ummaty tana cikin tsananin damuwa...menene damuwarki ummaty na"yayi maganar idonsa akanta,sai kawai ta shagwabe fuska tamkar zatayi kuka "nifa ba tunani nakeyi ba kallonka nakeyi kana bacci da alama kanajin dadin baccin,sanan banida wata damuwar data wuce inganka ka Mike kana tafiya da kafafuwanka kamar kowa,sanan gabobin jikinka da Basu aiki kana motsa su cike da karfi da koshin lafiya dik shine ya dameni"idanuwanta suka ciko da hawaye....harga Allah ya yarda da batun nata Dan yasan batayi Masa karya Dan haka sai ya tausasa muryarsa cikin sigar lallashi "meyasa Zaki damu bayan yayan naki yafara samun lafiya?bakiga yadda nai kiba na canja ba?sanan inayin magana na Dan tsawon lokaci batare da hardewar harshe ba?ga canji Nan da mukasamu sakamakon samun lafiya da nayi?"ya tsura Mata Ido...share kwallar data zubo Mata tayi saboda tausayinsa daya lullubeta....take shawarar da zuciyarta ta Bata dazun ta Fado Mata,Dan haka batare da Bata lokaci ba ta dauki Jakarta ta Ciro gorar maganin ta rike a hannunsa ta dubesa,yanayin yadda yayi da fuskarsa kadai ta fahimci Yana cikin tashin hankali Dan ta lura Koda take basa maganin ba son Sha yakeyi ba gabaki daya ma nature dinsa ne beson Shan magani ko kodan Kona asibiti aka bashi haka yakeyi sai kawai ta Dan hada Rai "ga maganinka yau na amso maka kwana biyu baka Sha ba ya kamata kasha"Tai maganar cikin faduwar gaba,
Shi Kansa faduwar gaban takeyi Amma bashida zabin da ya wuce Shan maganin kodan yasamu lafiya da farin cikin ummaty sai kawai ya daga Kansa ta tallabosa ta kafa Masa a Baki ya shanye take....hade da yamutsa fuska Yana lumshe Ido "halan maganin bashida Dadi koh?"Ta jefa Masa tambaya saboda ganin yadda taga yanayi da fuskarsa,girgiza Kai kawai yayi "ai ummaty ko menene idan akace magani ne to tabbas bashida Dadi badai kashashi Dan kaji dadiba sai dai kashashi Dan biyan biyan bukatarka.."

*WANAN LITTAFIN* *NA* *KUDI NE GA ME BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN 08166177830 KO 07084161619*

********
cikin awanni da Basu wuce biyu zuwa uku ba gabaki daya halittar zainul abideen ta canja sakamakon wanan magani da yasha har wani kumfa ke fita daga bakinsa tamkar yasha guba....dik wani mahaluki dake cikin gidan Saida hankalinsa ya tashi na ciki Dana waje jamaar gidan kowa ya hallara a babbar fadar sarki inda aka shimfideshi masu kuka nayi masu furgici nayi kowa hankalinsa a tashe yake musamman gimbiya bilkisu wadda ta kasa boye furgicin ta sai sharar hawaye takeyi cike da faduwar gaba..

Rungume take dashi tana shafa sumar Kansa gimbiya rumana yayinda anty Zahra yayarsa ke matsa Masa kafafuwa "ummah ya dace ayi wani Abu wanan Karon akan wanan rashin lafiyar ta zainul gaskiya"gabaki daya fada kowa ya Shiga maganganu cike da gamsuwa akan maganar ta Zahra shidai Mai martaba tsananin bakin ciki ya hanasa magana hajiya Kaka ta dubi gimbiya rumana "ke rumana me kikaga ya dace ayi akan hakan ni yaron Nan gabaki daya abun nasa tsoro yake bani tamkar Mai ciwon aljanu ko tabin hankali,wani lokaci ki ganshi cikin lafiya harda Yar kiba yayi Kai ni wanan abun ya fara bani tsoro"

Kuka ta fashe dashi Mai ban tausayi "kafin ayi wani Abu yanzun mujira zuwan likitan nasa tunda Naga kamar yasamu bacci sanan likitan nasa na hanya yanzun haka idan ya duddubabshi yayi Masa allurar da yakeyi Masa Yana samun sauki kafin musan abunyi ko"

Ajiyar zuciya hajiya Kaka tayi cike da alhini "haka ne mujira zuwan nasa"....baafi minti goma ba sai ga likita,abinda yasaba sai shi yayi Masa wato allurar baccinsa Nan take ko yayi bacci dama ya soma baccin,masu kula dashi suka gyara Masa jiki aka daukesa akai dakinsa dashi aka kwantar dashi kowa da fargaba zuciyarsa....

********
Hajiya kubra mahaifiyar warisah itace zaune tare da gimbiya bilkisu kallo daya zakayi musu kasan suna cikin tsananin damuwa duba da yanayin fuskokinsu..."nikam hajiya bilkisu mezai hana yaron Nan a canja Masa asibiti ko Kuma a nema Masa maganin gargajiya?Dan wanan abun ya isheni gaskiya haba kullum jiya iyau yaro Kara girma yakeyi da shekaru ansa Masa Ido cikin lalura?idan kasar waje zaa kaisa akaisa idan Kuma masu magani zaa nema a nema gaskiya nagaji idan bazakiyi wani abuba ni zan tari Mai martaba Akan maganar"

Share hawaye gimbiya bilkisu tayi "ki tareshi da maganar ko ki samu hajiya Kaka Akan hakan Amma ni nagaji da kafiyarsa Dan dik abinda Zanyi ko ince saidai yace ciwon zainul bana gargajiya bane na asibiti ne"

"To idan na asibiti. Ne a kaisa wasu Mana ga asibitocinan a kasashen duniya sai Wanda akaje dikda cewar anyi yawon na asibitin har angaji a gwada wasu Mana ai akwai kwararru. Likitoci zagaye da duniya"

"Toh zaayi Masa din"....

*******
Tsura Masa idanuwa tayi Tana Kara nazarin abinda yake faruwa ta Gama fahimtar inda komi ya dosa a cikin wanan masarautar....Dan hakan abinda takeso tasani tasanshi,...ta gyara zamanta da kyau "insha allahu komi yazo karshe zainul....zuciyata ta aminta da zargin da nakeyi a kwanakin Nan gaskiya ne...Dan hakan insha allahu zaka warke zaka taka da kafafuwanka cikin kankanin lokaci..."ita kadai take sambatu tana zaune a gabansa tana gadinsa dik ta kwarkwance gabaki daya ta rasa meke Mata Dadi...insha allahu tasamu mafita akan komi batare da gimbiya tasani ba.....saidai tana cikin tsananin tashin hankali can kasan zucuyarta damuwace dankare wadda batasan meye mafitarta ba.......

WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN 08166177830 KO 07084161619

*ZAINUL ABIDEEN*💞

*HASKE WRITERS* 💡 *ASSO*

*SLIMZY😍*
[1/23, 10:43 AM] 😍SLIMZY😍: 16

*HAPPY BIRTHDAY..my exceptional sister,she's one in millions,my wonderful sister she's* *smart and strong,I just can't resist her😍,I am so glad u are with me,I really luv u as u plainly can see😉so have a great BIRTHDAY SOFFY* *GALADANCI...I luv u FURATY...🤭*

*********
Bayan kwana biyu,

Zaune yake Akan wheelchair dinsa jikinsa ya fara kyau sosai Dan tun ranar da gimbiya ta bada magani Bata Kuma badawa ba saboda yadda burinta ya cika ganin yadda ya koma lokaci kankani Dan haka ba karamin farin ciki tayi da hakanba

********
yau ma kamar kullum ummaty shiri takeyi dan zuwa gidan Mai martaba kasantuwar tayi Rana saboda makara da tayi...tsaf ta shirya cikin jallabiya budaddiya baka Mai stones jajaye fuskarta Babu wani make up Dan ita dama bameson kwalliya bace sai kawai ta yane kanta da gyalen jallabiyar ba karamin kyau tayi ba a gaggauce ta Shiga dakin innarta inda ta tarar Dasu da kanwar babanta da tazo daga garinsu,har kasa ta tsugunna ta gaishesu tare suka amsa cikin sakin fuska....tana Dan tsugunne jimm kadan ta dago Kai ta dubi mahaifiyarta"innah inaso zan tafi gidan Mai martaba yau nayi Rana saboda na makara"

Innah ta bude Baki zatayi magana kanwar babanta ta karbe maganar cike da masifa "Ina Kuma zakije da sassafen Nan har kina cewa kin makara?ummaty wanan wani iri yawo ne kikeyi?tun kwana biyu da nazo kike fita da sassafe bakya dawowa sai yamman maraice a cewarki kina gidan Mai martaba ko,kodai aikatau kikasamu a can din ne?"tana dubanta cike da son Karin bayani,
Tura Baki ummaty tayi cike da Jin haushin abinda gwaggonta tace sai kawai ta daure tace"gwaggo hauwa ba aikatau nakeyi ba ya zainul nake zuwa jinya da debe Masa kewa"Tai maganar a sanyaye

"Jinya?au ummaty har yanzun kina zuwa jinyar wanan yaron da baasan ranan warkewar tasa ba ko?kinki cigaba da makaranta kin maida lokacinki da komi naki ga wanan nadaddem yaron da ke kwance kamar gawa ko?to ki Shiga hankalinki kisan abinda ya kamaceki ba ki zauna kina bautar banza ba,Dan bautar banza kikeyi kinki cigaba da karatu ke Kuma ba kawo miji kikaiba kina wahala Akan Wanda yafi karfinki,na tabbatar da ko warkewa yayi wanan yaron yayi Miki nisa bazai aurekiba wlhy kidai Gama wahalar,lokacin da zai warke ke ki rasa ma nema,Kinga kinyi biyu Babu kenan...Dan Allah dubi dik yadda kika Kare kika kanjale saboda jinya kankanuwar yarinya dake,kodayake harda kwadayi Dan Inba kwadayi ba Banga abinda kike tsinta ba a wanan shirgin"tunda ta soma zazzaga masifa daga ummaty har innarta Babu Wanda yace komi har tayi shiru sanan ne innah tace a sanyaye "hauwa nikam a ganina taimako ne yarinyar takeyi ai ko?"

"Dik fadin gidan sarauta Wanda ke cike da jamaa kala kala babu Wanda zai taimakesa sai ita?bashida maaikata ne ko fadawa dazasu kula dashi da har sai ita ta je ta Kula dashi?wallahi Ina jiye muku masifa irinta gidan sarauta Ina jiye muku abinda zaije ya dawo garin kwadayin abin duniya Tam"

"Insha allahu babu abinda zai faru hauwa,ki rinka kyautatawa Dan uwanki zato na alheri...wanan yarinya bamu Isa mu rabasu ba tunda tun suna kanana suke tare har ciwon Nan ya samesa,sun matukar shakuwa da juna, shiyasa Nima nabarta take zuwa din"

"Toh ta daibi a hankali ku taka a sannu nidai shine shawarar da zambada,"

Gwaggo ta dubi ummaty dake tsugunne kanta a kasa Tana Wasa da yatsanta ta tabe Baki tace "tashi kije Allah ya tsare adaibi a hankali"....a sanyaye ummaty ta dubi innar tata suka hada Ido ta gyada Mata Kai alamar taje saita Mike ta fice zuciyarta babu Dadi...

**********
Zaune take kan babban gadonta a kuryar dakinta kofarta ma a rufe ko Ina a rufe yake sai karar fanka da AC kawai ke tashi ga sassanyan dadin turare da aka turare dakin dashi ko Ina ya dauka kamshi ne kawai ke tashi wayarta makale a kunnenta da alama waya takeyi Mai matukar muhimmanci tunda har ta killace kanta haka Babu kowa ga yadda take wayar kasa kasa....
Chapter 17 · 0% Book details