← Book details Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 49

Sashe 28

Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Ummaty matso ki karya nasan kila bakici wani abuba kika fito saboda sauri kizo wajen rigimammen Nan Dan ummah"

Dan Bata fuska tayi ummaty hade da fadin "wallahi nskoshi ummah,"

Kallonta sosai gimbiya rumana keyi tana nazarin fuskarta sanan tace"ummaty yadai naga kin Bata fuskarki hakan?kodai akwai wata damuwa ce",

Kara natsuwa ummaty tayi Tai shiru tamkar zata fashe da kuka ta soma magana cike da ladabi"ranki ya Dade kinsan yau da gobe sai Allah Kuma batabar komiba "...,gimbiya rumana ta gyada kanta "haka ne ummaty menene Ina sauraronki"ta maida hankali sosai kan ummaty,

"Kawai dai gajiya ce nafara gajiya da jinyar Nan ranki yadade inaso Nima in natsu a gidanmu Kinga kullum Kara girma nakeyi Kuma iyayena ko basuyi mun magana ba bazasu so inzauna hakan batare da nasamu miji nayi aureba,ranki ya Dade bazan boye Miki ba zainul danki ne bansan ya zakijiba Amma nagaji da jinyar Nan dik ya siremun wani irin haushinsa nakeji"ta karasa maganar tana zubar da hawaye ta Dan dago idanuwanta jike da hawaye ta dubi gimbiya ta sadda kanta kasa tana sharar hawaye...sosai ta hango tsantsar yadda a fuskar gimbiya rumana...ga yadda ta maida hankalinta sosai akanta da yadda tayi da fuskarta tana sauraronta...a zahiri ummaty sharbar kuka takeyi Amma kasan zuciyarta wani irin farin ciki ne kwance saboda burinta be wuce gimbiya rumana ta gama yarda da itaba yadda zata gudanar da aikinta cikin sauki....

Ajiyar zuciya gimbiya rumana ta sauke Dadi cike da cikinta Amma sai ta danne gudun kada ummaty ta fahimci wani Abu "haba ummaty kiyi hakuri Mana har musamu yasamu sauki?Kinga yanzun akan Shan maganinsa yake Kuma kece nasamu kike taimaka Masa har ya warke Dan Allah ki Kara hakuri kinji ummaty nasan jinya Babu Dadi kiyi hakuri kinji"

Share hawayenta ummaty tayi "ranki ya Dade kullum bada maganin Nan nakeyi Amma Babu sauki ranki ya Dade har na soma gajiya wallahi wasu abubuwan inayinsu ne donke Dan iyayensa musamman ke da kikemun alheri kikasan inayi"...

Dadi ne sosai ya Kama gimbiya rumana "yauwa ummaty ko kefa to kiyi hakuri ki cigaba dayi ko Dan ni din kinji?kinsan magani ba daga farawa ake warkewa ba sai an daure,Kinga ga wani maganin ma ankawo dama nace idan kinzo zan aika kiranki kizo sai kibashi"

"Ranki ya Dade naso ace inada wayar sadarwa idan dik abinda kikeso ki kirani saiki fadamun da ki rinka aikawa kirana tunda kince bakyaso kowa yasan kina Taimakonsa a fili sai bayan ya warke ansamu biyan bukata koh?Kinga idan kina aikawa kirana may be a fahimci wani Abu Amma shawara ce"

Kasa boye farin cikinta gimbiya tayi jikinta har rawa yakeyi "daama inataso intambayeki ko kinada waya Ashe Baki da ita budurwa kamarki Babu waya?be yuwuwa tunda afnan Ma auta tanada ita saike budurwa dakee?,zan aika zuwa yamma kafin kitafi a kawo Miki waya"...

Zaro idanuwa ummaty tayi "ranki ya Dade babana yace sainayi aure fada zaimun ki rufamin asiri"

Murmushin kasaita gimbiya rumana tayi "inajinki kamar Yar Dana Haifa Dan haka kome Zanyi Miki kyautatawa ce kema kinamun Kuma inajin Dadi... kibarni da sarkin dawaki nasan yadda zan bullo Masa"...tsoron fadan mahaifinta takeyi Amma saita danne tana addua cikin zuciyarta Allah yasa kada yace ita tasa aka sai Mata....ita kuwa gimbiya rumana kissima yadda zata bullowa sarkin dawaki takeyi yadda zata furgitashi batare da yayi wani tunani ba...

Janyo gorar maganin ummaty tayi ta Dan yatsina fuska "ranki ya Dade ni wallahi dama kinzo munje tare Kinga muna Hira sai inbashi maganin a matsayin ruwa yadda zaki Dan zauna zanji Dadi"..satar kallon gimbiya tayi sai taga tayi murmushi "kema kin iya rigima ummaty to ai idan mukaje tare zai fahimci wani Abu"

Ummaty tana sane tace hakan Dan gimbiya rumana ta Kara yarda da amincewa da ita,ta Kuma ga alamar hakan yadda gimbiya dik ta rude jikinta sai rawa yakeyi fuskar Nan dauke da farin ciki Wanda ta kasa boyewa...turo Baki ummaty tayi hade da mikewa 'bari inje ummah nasan Yana can Yana nemana"..ta danyi tsaki ta dauki gorar magani tasa a hijabi "ummah sai anjima"

",Toh ummaty kibiyo idan Zaki tafi gida"...

Ummaty na fita gimbiya rumana ta janyo wayarta ta Kira waya da alamar shago takira tana tambayarsu wayar da suke da ita a kasa zata Aiko driver da kudi ya karba...tana gama wayar number sarkin dawaki tayi dialing...

*WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619*

*******
Bata karasa fitowa sashen gimbiya Ba sukai kicibis a hanya da baabah kande batace Mata komiba hannunta ta Kama ta jata sukai wata hanya Dan nesa kadan shiru Babu kowa sai dawaki dake kuka a wajen,

Gora ta Ciro a hannunta daga hijjabinta ta dubi ummaty tana waige waige "kalli gorar Nan",da sauri ummaty ta kalla ta xaro Ido hade da Dan furgita ta Ciro ta cikin nata hijabin taga Babu banbanci a kidime tace "babah kande wanan gorar fa?iri daya ce data hannuna"

Gyada mata Kai babah kande tayi Tana murmushi "ki kwantar da hankalinki nasamota ne a dakin gimbiya saboda mu rinka musayar magani Koda kinje Zaki iya Ciro wanan ta hannuna ki bashi memakom waccan,nayi ma wanan sheda yadda bazaki makuwa ba wanan ruwan na maganine adduoi ne sosai na tsari da karya sihiri shi Zaki bashi memakon na hannunki"

Sosai ummaty ta rude "menene faidar samun gorar iri daya?"

"Ummaty ke yarinya ce bakisan gimbiya rumana ba tanada masifar wayau dikda Naga alamun ta yarda dake Amma hakan bazai Hana Tasa ai mata gadinki ba Kinga koda Tasaka a sa Miki Ido zaaga ai gorar ce kike bashi maganin Kinga bazaa ganeba ,dikda kema kinada basira da hikima Amma zata iya Miki wayau Dan ta wuce dik inda kike zato,kibar ganin daga ke Sai ita kukeyi zata iya sa Miki Ido ta ko wani siga",

Ajiyar zuciya ummaty ta sauke ",lallai nagodewa Allah da ya hadani dake babah kande,gaskiya kinfini hikima kinfini basira dikda kin tsufa,Koda yake kin haifeni Dole ne kifini hangen nesa"

",Kema da Taki basirar da hikimarki domin samun gimbiya ta yarda da mutum take ba karamin Abu bane Dan dik inda kika bullo mata tanada wayau zatasa Miki Ido sai daga karshe ta Nuna Miki tasan komi Dan hakan kika taka tsantsan",

",Insha allahu baabah kande idan tasan wata batasan wataba yanzun haka zata saimun abinda zan yaketa dashi batare da ta Ankara ba",

"Mekenan Yar Nan?"

"Wayar salula babah kande,kedai zanbaki labarin yadda zaayi yanzun Bari inje Dan nasan bawan Allahn can Yana can Yana jirana, zaice wanan ta canja besan shi nakeson cetowa ba"

",To adaiyi a a hankali kizo Kuma mu tattauna akan wayar "

"Insha allahu natafi sainazo"ta juya da sauri tabar baabah kande wajen tana bin ta da kallo tausayi yarinyar take Bata harga Allah shiyasa tasa mata hannu Dan anason jefata a halaka batasani ba harda ubanta...ta kada Kai kawai tabar wajen...

*******
Sarkin dawaki s firgice ya nufo gidan Mai martaba Jin Kiran gimbiya na gaggawa gabaki daya a tsure take dik tunaninsa tasan shi ya warware tafiyar Kai zainul wajen Mai magani Dan haka hantar cikinsa a kade ya iso gidan.. gaba daya ya furgita da lamarin gimbiya ga babban tashin hankalinsa besan me yarsa takesonyi da waya ba da takeso a siya mata waya Rana tsaka a haka ya karasa sashen da suka Saba haduwa da gimbiya rumana....

*WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619*

💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞

*HASKE WRITERS ASSO💡*

*SLIMZY😍*
[1/23, 11:12 AM] 😍SLIMZY😍: 26

Ko wannensu shiru yayi Yana sauraron abinda Dan uwansa zaice,musamman sarkin dawaki Wanda zuciyarsa ke harbawa tamkar ta fasa kirjinsa ta fito... gabaki daya ya zabge ya rame sosai kamar Wanda yake rashin lafiya, danasani da nadamar abubuwan da suka aikata shida gimbiya rumana kawai ya sashi wanan ramar ta Babu gaira Babu dalili... gyaran murya tayi cike da izzah da Isa irinta masu mulki ta kada kanta kadan fuskar Nan kamar Koda yaushe dauke da murmushin Nan nata Mai tsada Wanda ya kasance dabiarta ce hakan..."sarkin dawaki kaji Kira daga sama ko?daga gimbiya rumana wadda ta kasance ta hannun damanka a baya yanzun Kuma kake gudunta ko ganinta baka kaunar Yi koh?"hmmmm ta sauke lallausan murmushi "bedameni ba saboda nasamu nasara na Kuma cinmma burina ko ince Ina gab da cin ma burina Dan Ina hango nasara Nan kusa kadan tunda Yar taka itace ta kasance babbar aminiyata yanzun ta hannun damana nake juyata yadda na gadama batare da tamun gaddama ba,dikda itama a tafin hannuna take Dan yanzun dik motsinta zan Sanya idanuwana gaba da baya Dan a rinka bibiyar takunta dikda na yarda da ita Dan ita din yarinya ce mara wayau shiyasa nayi nasarar saurin juyar da hankalinta"... hannu tasa ta dauko kofin lemo dake gabanta ta Dan kurba kadan ta ajiye sanan ta nufasa tana me binsa da kallo yadda ya firgice Babu abinda yakeyi sai zufa...

"Kiranka nayi inbaka umarni Akan inaso kabar ummaty da waya domin nicenan nace tafara tuntubarka da maganar waya kace bazata rikeba har saitayi aure menene dalilinka na hakan"
Chapter 28 · 0% Book details