Sashe 25
Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Miyau ne yadan gangaro Masa ta gefen fuskarsa rabonsa da hakan tun kafin ciwonsa ya tashi shekaran jiya Dan hakan sai gimbiya rumana ta dubi ummaty "ummaty Baki ganin miyau ya gangaro Masa gefen fuska bazaki goge ba?"..Satan kallon zainul ummaty tayi batare da gimbiya rumana ta lura ba sai kawai taga ummaty ta turo Baki gaba hade da hararar inda zainul yake dik a idon gimbiya rumana da halima ta juya taje ta dau karamin towel tazo daidai fuskarsa taga idanuwansa a lumshe sai tasa towel din a hankali tana gogewa kamar tana taba kashi ta cillar dashi gefe....mamaki ne da al'ajabin ummaty ya lullube gimbiya rumana Amma ta kasa magana
Halima ce ta katse shirun"brother"ta Kira sunansa ya bude Ido a hankali...
"Kaga nazo maka da kilishi zansa babah kande ta kawo maka harda yougourt na siya maka"...murmushi yayi cike da faraa yace a hankali "nagode"....
Sun Dan jima kafin halima tayiwa zainul sallama ta nufi sashen Mai martaba...
Ummaty kuwa suna fita ta gyarawa zainul abideen kwanciya ta gyara Masa fuskarsa ta fito da ruwan adduwarta daya jikasa da ganyen magarya ta dibo a Kofi ta tallafosa jikinta ta Mika Masa Babu musu ya kwalkwale hade da rufe idanuwansa da yakejin bacci sosai...baai minti biyar ba yayi bacci,kamar jira takeyi ta fice Tai inda babah kande take...
*********
Wajen zaman nasu Nan ta sameta ita kadai ta rafka tagumi,har ummaty ta zauna babah kande Bata saniba,Saida ummaty ta Dan dabota
"Baba kande wai tunanin me kikeyi ne har nazo Baki saniba?"...a tsorace babah kande ta juyo ganin ummaty ce yasa ta sauke ajiyar zuciya "ammah anyi ja'irar yarinya saikizo ki tsoratani?"
Turo Baki ummaty tayi Tana gyara hijjabinta "to ba tunanin marigayi mijinki kikeyiba bakisan nazo ba"...sosai tabawa baba kande dariya yadda Tai maganar,itakuwa ummaty dama hakan takeso saitace "bani labarin tunanin me kikeyi?"
Wanan karon canja fuska baba kande tayi "tunanin rayuwa nakeyi yarnaj,yadda rayuwa ta canja ta tabarbare ake zaluncu kala kala akecin amanar zaman tare"
"Ban ganeba baba kande fahimtardani""""
Ajiyar zuciya baba kande tayi "ummaty na amince da hankalinki da natsuwarki yasa zan gutsira Miki kadan daga cikin abinda nasani game da gidan Nan saboda inaso a cikin kwanakin Nan idan Allah ya nufa ki ceto wanan yaron zainul abideen Nima insha allahu zanbaki gudun mawa da goyon baya dari bisa dari da taimako da zan amso Miki kala kala ganin munsamu nasara'
Wani farin ciki ne ya lullube ummaty duka jikinta ji takeyi kamar an watsa Mata ruwan sanyi Amma saita boye farin cikin nata Dan kada babah kande ta fahimci tasan wani Abu tunda so takeyi ta kyankyasa Mata komi...
Ruko hannunta baba kande tayi "kafin inbaki labari da sirrikan gidan Nan zan fada Miki wata magana da ja jiyo a sashen gimbiya rumana Wanda tunda nake da ita ban taba fallasa sirrinta ba....Amma banaso kiyi mamaki ko ki tsorata kinji?"ummaty ta gyada Kai cike da kosawa....
"Na jiyo gimbiya rumana da yarta halima suna tattaunawa akan sun samu sabon Malami Wanda zaakai zainul abideen wajensa da sunan Yi Masa magani a nakasta rayuwarsa batare da kowa ya fahimta ba,Dan yanzun haka halima taje fada wajen sarki zaafada Masa a juyar Masa da hankali a karasa nakassa zainul abideen dikda a kwance yake so akeyi ya rasa hankalinsa gabaki daya"...zumbur ummaty ta Mike cike da tashin hankali tana kallon babah kande a rude,
"Nace kada ki tsorata ki saurareni tsaff ingama Mana insha allahu munada mafita"...bakin ummaty na rawa jikinta nayi muryarta har hardewa takeyi "baabah kande "ta Kira sunanta dai dai Nan wata baiwa ta karaso wajen sai suka canja hirar "ummaty gimbiya rumana na bukatar ganinki a sashenta"
Takaici ne ya lullube ummaty na Bata gamajimzance ba ankirata ba lallai su hadu ba Dan yamma tayi sai kawai ta bude Baki zatayi magana babah kande ta rigata ta hanyar fadin "gatanan zuwa,ummaty je Kiran uwargijiyata"Dan hakan ba musu ummaty ta wuce hankalinta a tashe...
*WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619*
*******
Gefen carpet ta zauna kamar yadda ta Saba "gani ranki yadade"
Cike da kulawa murya kasa kasa gimbiya rumana tace "ummaty Kinga nakiraki koh"...ummaty tagyada Kai,
"Dazun ne Naga kinyiwa yarona abinda banji Dadi ba yasa nakiraki intambayeki dalilinki nayin hakan kamar kina kyamarsa bayan ba hakan kikeyi Masa ba"...murmushi ummaty tayi har zuciyarta taji Dadi tarkon da ta Dana ya Kama gimbiya rumana Dan hakan saita daure fuskarta,ta nisa hade da sauke ajiyar zuciya "ranki ya Dade ba kyamarsa nakeyi ba,kawai dai Nima nafara gajiya da jinyar ne, masifar haushi yake bani wallahi banida yadda Zanyi ne yasa nake zuwa ramki ya Dade Amma na gaji"ummaty kawai sai ta saki kuka hawaye Sharrrr sharrr a fuskarta ta cigaba da Fadi cikin kuka "kiyi hakuri ranki ya Dade idan na Bata Miki Rai saboda danki ne"
Wani sanyin dadi ne ya lullube gimbiya rumana jin furucin ummaty Akan zainul abideen wato tagaji dashi?Kai taji dadin wanan lamarin tabbas yazun tasan hakarta zata cimma ruwa Dan dik abinda tace Yar tayi zatayi babu musu...
Ita kuwa ummaty kasan zuciyarta tamkar ya Kama da wuta takeji dikda tasan tarkon da ta danawa gimbiya ya kamata Kuma zata yarda da ita dari bisa dari yanzun.....dik ta kosa ta fita taje wajen baabah kande su karasa maganarsu Dan yanzun tasan ta Gama da gimbiya yanzun Target dinta na gaba kawai zata Dora.....

💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞
*HASKE WRITERS* *ASSO💡*
*SLIMZY😍*
[1/23, 11:10 AM] 😍SLIMZY😍: 23
Sauri sauri ta fito sashen gimbiya rumana har tana hardewa kamar zata Fadi kasa,bayin dake zagaye da sashenta suna kaiwa da komowa suka bi ummaty da kallo hade da girgiza Kai,...daya daga cikinsu ta kalle Yar uwarta murya kasa kasa tace "uwaliya ko Kinga wanan yarinyar kullum sai na ga gilmawarta a sashen gimbiya rumana ko me take zuwa Yi oho"
Wawwaigawa wadda aka Kira da uwaliya tayi sanan Tai kasa da murya tace "saade indai wanan ne ni ba kwanan Nan na soma gani ba koma menene zai bayyana Nan bada jimawa ba,babban abinda ya bani mamaki ma jiya fa na gansu tare da babah kande?"
Dafe kirji saade tayi "wace baba kande?"sai Kuma ta tabe baki hade da girgiza Kai cike da tsaigumi tace "su kadai sukasan me suke kullawa"
"Idan tayi wari zamuji,yanzun idan kanason kanka da arziki da mutunci ka Kama bawan Allah ka kayi shiru kasa Ido ka baza kunnuwa"suka tafa hade da sakin dariya..
"Umm Bari kigani inje inyi abinda gimbiya tace kafin ya nemeni kinsan halinta"a tare suka juya suka watse wajen kowa yayi hanyarshi...
Duban duniyar Nan ummaty tayi bataga baba kande ba hankalinta ba karamin tashi yayi ba gashi yamma tayi batare da ta so hakan ba haka ta hakura ta juya a sanyaye ta nufi sashen gimbiya bilkisu Dan ganin halin da zainul abideen yake ciki....
********
Durkushe take a babbar fadar sarki gaban Mai martaba mahaifinta gefe daya gimbiya rumana ce zaune tana kada kafafuwanta fuskarta dauke da murmushi ta dubi halima tace "halima ya dai akwai magana ne Naga kinyi shiru tamkar kinada bukatar wani Abu"
Gyara Zama halima tayi hade da gyaran murya tace "dama nazo wajen abbah ne da wata magana dangane da lil bro zainul"
Jin hakan yasa Mai martaba maida hankalinsa sosai kan halima,
"Au Ashe zuwan ba namu bane,zuwan na mahaifinki ne da d'an uwanki to sai ki fada mishi ai ba kiyi shiru durkushe ba"
Murmushin manya Mai martaba yayi cike da zolaya ya dubi gimbiya rumana 'yanzun dai kishi kikayi saboda d'iyata tace wajena tazo miyi magana ba wajenki ba koh"
Farrr tayi da idanuwanta tana murmushin kasaita baiwarta nayi Mata fifita a hankali sanan tace cike da kissa "to ai gatanan ga ka koh?saima nabaku wuri idan sirri ne,saidai Abu daya zaisa inzauna don maganar ta shafi yarona shiyasa"...dukkansu dariya sukayi sanan Mai martaba ya dubi halima hade da maida hankalinsa sosai "Ina sauraronki sadiya"
"Ranka ya Dade Akan maganar ciwo zainul ne nazoda wata muhimmiyar magana,...maganar ciwonsa ne nake ganin ya Dace zuwa yanzun a nema Masa maganin gargajiya"
Mai martaba ya gyada Kansa cike da gamsuwa da maganar da halima tayi,ita Kuma ta cigaba da maganarta "akwai wani Malami Wanda ya kware Akan harkar magungunan gargajiya Dana musulunci Wanda prince ya sanshi shine yake bani labarin cewar shine ya warkar da kanin mahaifinsa lokacinda ya samu tabin hankali,zuwa biyu kwata kwata akayi yasamu lafiya,shine nace ya hadani dashi Zanyi maka maganar idan har ka amince a dauki zainul abideen akaisa can ko Allah zaisa mudace ko zai Mike da kafafuwansa"
Gimbiya rumana ta karbe zancen cike da farin ciki "alhamdulillahi Kai naji dadin wanan labari Allah yasa karshen wahalar yaron Nan ne tazo"...
Shiruuuu Mai martaba yayi na Dan wani lokaci Yana nazari,yayinda zuciyoyin su suke bugawa sauri da sauri cike da faduwar gaba suna sauraron amsar da zataa fito daga cikin bakinsa...kimanin minti goma Sha biyar bece wani Abu ba sai cannnn yayi Yar gyaran murya yace "halimatu saadiya naji zancenki naji shawararki Kuma ya yaba da ita....saidai ni bana gaggawar yanke shawarar batare da nayi nazari akanta ba Kuma nayi shawara da abokanan shawarata....
Gimbiya rumana bataso hakan ba zuciyarta batayi Mata Dadi ba taso ace ya amince take batare da Bata lokaci ba,Amma Bata baci ba tasan yadda zata bullowa lamarin Dan hakan sai ta dubesa "ranka ya Dade ya kamata ka duba lamarin yaron Nan kasan halin da yake ciki shekara da shekaru,watakila warakarsa ce tazo ,watakila wahalarsa tazo karshene yasa Allah ya bawa halima ikon zuwa gareka da maganar...Dan Allah abbam zainul a duba lamarin Nan na yarona a nemawa magajin babansa magani Shima ya samu lafiya kamar kowa"cike da damuwa take maganar tamkar zatayi kuka,...tausayin ya ne ya lullube Mai martaba sai kawai ya gyada Mata Kai tare da cewa"zaa duba ki kwantar da hankalinki uwar zainul abideen"
"Magajin babansa Kuma ba"cewar gimbiya rumana tana dariya....Nan suka kauda maganar suka dauko wata hirar,Saida aka Kira magriba sanan halima Tai haramar tafiya gidanta....