← Book details Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 49

Sashe 30

Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Insha allahu zan samu sauki haris ,inajin dadin jikina sosai Ina matukar alfahari da wanan yarinyar da kake gani tabbas banida kamarta a fadin duniyar Nan"...wani kallo warisah ta wurgo Masa cike da haushin abinda yace...Wai wanan kucakar yake cewa bashida kamarta ?mtswww wata zuciyar tace toke warisah idan hakan ne menene naki ciki?kodai sonsa kikeyi..take ta Shiga girgiza Kai a zuciyarta tana fadin ah ah ah Allah ya kyauta,.wani kallo haris yayi Mata"ke meye hakan kamar wata Mara hankali kina zancen zuci kina kada Kai tamkar wata sabon kamu"
.zumburo Baki tayi ta Mike fuuuuu tana tafe tana kunkuni ta fice dakin ta bugo kofar dakin...shiko zainul Allah Allah yakeyi ta fita Dama Dan ganinta yakeyi tamkar wata bakar macijiya gefensa wani irin tsanarta ce ke yawo cikin jinin jikinsa,Abu daya ya hanasa korarta ganin tare take da yayanta da badan hakan ba dababu abinda zaisa ya barta Tai second cikin dakinsa...kauda tunaninta tayiy hade da Dan tsaki ya juyo ga haris Wanda ke famar daddana waya da alama chat ya Shiga yanayi....

*******
Har karfe bakwai na magriba tana gurin Hassan Mai shago Yana famar tattaba wayar ya Shiga Nan ya fita can dik wani Abu da take bukata ya saita Mata a cikin wayar sanan cikin kankanin lokaci ya koya Mata dik wani Abu da take bukata,sosai take murna tare da Jin wani nishadi a cikin zuciyarta dikda yadda take tsoron zuwa gida da wayar ga dare da tayi Dan haka Yana gamawa sauri sauri ta sallameshi ta karbi wayar ta Miki hanyar gidansu.....

*WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619*

"Assalamualaikum"...Tai sallamar muryarta na rawa ...."ke ummaty dakata Nan,daga gidan ubanwa kike a daidai wanan lokacin ?"ya daka mata tsawa wadda ta haifar mata da faduwar gaba lokaci daya hantar cikinta ta kada,ji takeyi tamkar ta saki fitsari s inda take a tsaye,kafafuwanta ne suka soma rawa bakinta na rawa muryarta na sarkewa ta dubesa a tsorace "baabah...daga gidan Mai martaba nake wajen ya zainul"Tai mgnr a tsorace...

"Daidai wanan lokacin ne zakice daga gidan Mai martaba kike?ummaty me kikeso ki Zama?wallahi ki Shiga hankalinki idan ba haka ba zan matukar Saba Miki ,kalli lokaci karfe bakwai da minti goma har anyi magriba Baki shigo ba kincemun daga gidan Mai martaba kike koh?to ki kama Kanki tun kafin in hanaki zuwa gidan Mai martaba gabaki daya"

"Kayi hakuri baba insha allahu baxaa Kuma ba"Tai maganar tana sunkuyar da kanta kasa jikinta sai rawa yakeyi...wani irin kallo yake bin ta dashi daga Sama har kasa idanuwansa suka sauka Akan ledar wayar dake hannunta.... gabansa ne ya Fadi ya dago Kai ya dubeta da kyau sanan yace "kwalin menene a hannunki?"ya jefa Mata wanan tambayar,.

A rikice ta dubesa bakinta Yana rawa "umm...umm...babah dama ummah rumana ta siyamun waya dazun tare da afnan"Tai maganar a tsorace..

Girgiza Kansa kawai yayi batare da yace wani Abu ba yasa Kai ya fice...

Kada Kai kawai innah tayi fuskarta Babu yabo Babu fallasa ts kalli ummaty dake tsaye kamar an dasata sanan ta kauda Kai cike da bacin Rai tamkar bazata ce wani Abu ba ,ita kanta ummaty Tasha jinin jikinta yadda innar tata tayi mata "ummaty me kikeso ki Zama ne?gabaki daya lokaci kankani kinaso ki canja halayenki ki rinka betawa mahaifinki Rai ko ummaty?kina ganin kin kyauta kenan?haba ummaty kin bani mamaki gaskiya banji Dadi ba karki kuskura kice Zaki sauya idan kika sauya bazakiji dadin mahaifinki ba da ni kaina nafada Miki",tana Gama maganar ta juya ta dauki Dan karamin bokiti da muciya a ciki ta nufi kitchen,..tsaye take hawaye na gudu a idanuwanta zuciyarta ta karaya da kalaman innarta,gabaki daya jikinta yayi sanyi har batasan lokacinda ta Soma kuka a tsaye ba tasa hannu ta share hawayenta sansn taja kafarta ta shige dakinta tana sharar hawaye....

********
Dik juyi idan yayi cikin dakinsa muryarta ce takeyi Masa yawo a cikin Kai Babu abinda yafi burgesa a tattare da yarinyar Wanda ya wuce murmushinta da manyan fararen idanuwanta wadanda sukeyi tamkar suna Jin bacci...dago Kansa yayi ya dubi agogon bango dake manne a dakinsa karfe takwas da Rabi dai dai ya Mike ya zauna Akan gadonsa Yana sanye da farar singlet da dogon wandonsa jeans....hannunsa ya Mika ya dauki rigarsa ya zura ya dauki wayarsa dake gefe da makullensa dake gefen gadonsa ya kwasa ya fice daga sashensa ya bullo ta kofar baya ya nufi parking space ...yasa key ya bude motar ya Shiga shirruuuu yayi bayan ya rufe kofar yana tunanin yadda zaayi yaje wajenta to idan yaje yace Mata mene?Yaya zaayi ya samu gidansu?ya furzar da isaka Mai zafi daga bakinsa yayiwa motarsa key ya fice gidan a guje batare da sanin inda ya nufa ba haka yake toki minti minti yakan ja tsaki shi kadai zuciyarsa sai Kara azslzalarsa takeyi da wutar kaunarta.....

*******

Gabaki daya hankalinta yaki kwanciya tunanin yadda zaayi ta fito ta sanarwa da ummaty kudurinta akan zainul abideen kawai takeyi Dan gabaki daya ta Gama kololuwar tunani Akan kawai ta fito ta sanarwa da yarinyar kudurinta dan wanan wahalar da takeyi shekara da shekaru ta Isa ta kasa kasheshi shi a wahale ita a wahale gara kawai tunda ummaty ta Nuna gajiyarta akan jinyar tasa gara ta sanar Mata da su kasheshi kawai ita ta huta da jinya itama ta ciwwa burinta...da wanan tunanin ta kwana tare da kosawa ummaty ta iso gidan Dan ta sanar Mata da bukatar ta...

*WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619*

*HASKE WRITERS* *ASSO💡*

💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞

*SLIMZY😍*
[1/23, 11:13 AM] 😍SLIMZY😍: 28

Tafe yake Yana tuki cikin kwanciyar hankali gabaki idanuwansa akan tukin da yakeyi suke a zahiri Amma hankalinsa gabaki daya ya karkata akan yarinyar gabaki daya ya rasa natsuwarsa tun ranan da ya fara sanyata cikin idanuwansa yanzun menene abunyi?zuciyarsa ke tambayarsa shin gidansu yarinyar zakaje daddaren Nan?idan kaje kace mata mene? gabansa ya Fadi sai kawai ya Kar kata kan motarsa ya canja hanya ya dauki hanyar GRA gidan anty Zahra be dau lokaci ba ya iso gidan yayi horn Mai gadi ya leko da Kansa yana kallon kotar haris ya Kara horn da karfi ya haske masa Ido da gudu ya ruga ya wangale masa gate din,ya take motar ya Shiga s guje "barka da zuwa ranka ya Dade" komi bece Masa ba ya kulle motarsa ya barsa Nan tsaye ya kada Kansa ya koma maxauninsa kan benci...

Kallon tv yaran sukeyi lokacin da yayi sallama cikin patlorn a guje suka ruga suka rungumeshi suna ihun "oyoyo oyoyo uncle haris ya dawo "

"Welcome back uncle haris"cewar Yar Macen ya dagata sama Yana dariya "oyoyo surayya Ashe kin gane uncle haris"...ya ruko hannunsu suka karaso patlorn saiga Zahra ta fito rike da nuaiym a hannunta "ah ah haris Ashe Kaine nakejin ihun su surayya "

Shafa Kansa yayi "nine anty Zahra"

Da faraar ta takaraso patlorn ta Mika Masa nuaiym tana fadin "su haris manyan gayu yau Kaine a gidana yaushe rabo?"

"Kai anty ai Ina zuwa sosai kawaidai so kike kiyimun sharri"sukasa dariya tare,Kiran me aikinta tayi ta kawo Masa kayan motsa Baki da kular abinci ta dire Masa a karamin table din dake gabansa....yanaci suna Hira sama sama har ya gama...

"Hmmm haris kodai daga wajen zance kake?"Tai maganar cike da tsokana...

Shafa Kansa yayi "anty ni ai Banda budurwa yanzun ne dai nasamu"

"Kai Dan Allah haris?kace zamusha biki alhamdulillahi Kaine namiji na farko da zaka fara aure a family dinmu gaskiya naji Dadi"Tai maganar cike da zumudi...

"Kaga anty Zahra harkin fara maganar aure bayan ban gabatarwa da yarinyar Ina sonta ba yanzun haka na fito da niyyar zuwa gidan ne nafasa Dan bansan mezance Mata ba idan naje"

Dariya sosai anty Zahra tayi "Kai haris dadina dakai shirme?au baka fada mata ba?Yar gidan waye to?a Ina take?"

Shiru yayi Yana shafa Kansa sanan yayi murmushin gefen fuska "ummm ummaty ce yarinyar sarkin dawaki",

Dafe kirji anty Zahra tayi hade da zaro Ido "ummaty haris?"

Kallonta yakeyi fuskarsa Babu yabo Babu fallasa "batayi bane anty Zahra?"

"Ah ah haris wallahi tayi nayi mamaki ne da kace kana son ummaty naganka Dan gayu kana son social life ita Kuma yarinyar akwai kunya da natsuwa gashi Bata fiye gayu ba,Amma naji dadin wanan maganar wallahi zainul nayi mata shaawa saboda yadda take wahala dashi Amma kaga auren zainul be kamaceta ba wallahi saboda lalurarsa kaje ka nemi soyayyarta Allah ya shige Mana gaba"

Farin ciki ne ya lullube haris har fuskarsa ya kasa boyewa "anty Zahra nagode Amma su mama nakeji fa"

"Karka damu Mai martaba zai tsaya maka Nima Kuma Ina tare da Kai"

"Nagode anty Zahra Bari inzo inkoma dare nayi"

Mikewa tayi tallabe da nuaiym tace "bazaka jira abbansu ya shigo ku gaisa ba ya kusa fa?"

"Nidai ah ah kya gaisheshi zan dawo jibi insha allahu",

"Ok"har wajen mota ta rakashi sukai sallama Tayo cikin gida cike da zumudin wanan labari...

*******
Chapter 30 · 0% Book details