← Book details Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 49

Sashe 12

Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ummaty takara natsuwa sosai tausayin gimbiya ya Shiga jikinta,"Dan haka nakeso ki taimakeni musamawa yaron Nan lafiya kinji?Dan kinfini kusa dashi ummaty ,zan karbo magani wajen kakana in Baki ki rinka bashi nasan zaisha idan kece ummaty,idan kikai min haka kingamamun komi a rayuwata matukar yarona zai samu lafiya"ta share hawayen dake zuba a idanuwanta,

Sosai tausayin gimbiya ya kamata sanan wani irin farin ciki ne ya ziyarci zuciyar ummaty na zainul zai samu lafiya ya warke kamar kowa mafarkinta zai Zama gaskiya kenan?

*SLIMZY😍*
[1/23, 10:40 AM] 😍SLIMZY😍: *HASKE WRITERS* *ASSO...*💡

💞 *ZAINUL ABIDEEN💞*

*SLIMZY✍🏼*
*Wattpad@slimzy33*

*Assalamualaikum zuwa ga masoyana Ina muku fatan alheri,wanan book din na zainul abideen na* *kudi ne Wanda ke bukata dari biyu ne kacal ka nemi* *wanan numbers* 08166177830 *ko* 07084161619 *daga* *wanan page din nagama bada free page zakuji shiru inawa kowa fatan alheri.....SLIMZY* ✍🏼

11
Murmushi kawai takeyi tana ayyanawa a zuciyarta zainul ya samu lafiya,wani irin farin ciki zata tsinci kanta a wanan ranan?lumshe idanuwanta Tai ta budesu sukai Ido hudu da gimbiya rumana wadda ta kafeta da idanuwa ko kiftawa batayi,samm ta manta a inda take ma saboda tsananin farin ciki ,sadda kanta Tai kasa bakinta yaki rufuwa "ranki ya Dade tabbas ke uwace ta gari nadade Ina Neman ganin ranan da zaayiwa zainul abideen magani ya warke Amma babu halin hakan saboda kasancewar ni ba kowa bace a cikin gidan Nan shiyasa ban taba tunkarar wani da maganar ba, alhamdulillahi tunda ke mamansa kinyi wanan tunanin Allah ubangiji yabamu nasara a wanan tafiyar gaskiya nayi matukar farin ciki da Jin wanan labari"ta karashe maganar cike da ladabi,

Murmushin nasara gimbiya rumana tayi hade da sauki sassanyar ajiyar zuciya wani farin ciki Yana ratsa zuciyarta tun daga kanta zuwa yantsun kafarta "Masha allahu shikenan ummaty Zanyi magana da Wanda zai rinka bashi maganin idan yaso sai ki rinka zuwa kina amsa a nan wajena kina bashi cikin sirri batare da kowa ya sani ba inada burin da fatan saidai Mai martaba yaga zainul ya tako da kafafuwansa har fadarsa"

"Allah ubangiji ya sa ranki ya Dadi,Allah ya Baki Lada"Tai maganar cike da farin ciki,....ledar dake gefe gimbiya rumana ta janyo ta Ciro turamen atamfofi guda biyu ta mikawa ummaty "amshi wanan ummaty ki kaiwa mamanki daya ki dinka daya kema kisa kinji?"

"Allah ya saka da alheri gimbiya ,Allah ya Kara girma da arziki ya Kara Miki lafiya da nisan kwana sanan Allah yasa kifi haka ya cika Miki burinki na alheri"...sosai gimbiya ke faraa ta kasa boye farin cikinta,...a zahirin gaskiya Bata taba tsintar kanta cikin farin ciki irin na yau ba,ita kadai tasan me take tunani kasan zuciyarta.

"Tashi kije kada ruwa ya tsareki kinji ki gaida innar Taki"to ummaty tace ta Mike rungume da kayan da gimbiya ta Bata ta fice gimbiya ta bita da wani irin kallo tana kada kafa fuskarta dauke da murmushin mugunta,cije lebenta tayi "hmmmm lallai nasamu cikar burina,yanzun ne nakeda damar da zan dama,yanzun ne nasamu yadda nakeso nake muradi farin cikina be wuce in bude idanuwana Inga yaron Nan rayuwarsa ta lalace ta kazanta fiye da wadda yake ciki,banida burin daya wuce a nunamin gawarsa a kwance ya mutu,shine babban buri na a rayuwa....Zanyi amfani da damata tun kafin ta kubucemin nasani inhar nayi amfani da wanan yarinyar to tabbas babu ranar da asirina zai tonu a hakan zamuyita tafiya babu Wanda zai fahimci wani Abu tattare Dani,gwauron numfashi ta sauke hade da janyo wayarta Tai dialing wata number,ta Dade tana waya sanan ta tsunke wayar cike da tsananin farin ciki....

*********
Bayan sallar isha'i ummaty ce zaune hannunta rike da littafin adduoi na hisnul Muslim tana Dan dubawa,minti minti takan sauke ajiyar zuciya hade da lallausan murmushi,...innarta dake zaune gefe tana cin tuwo miyar taushe tana cin abincin ne Amma hankalinta gabaki daya Yana wajen Yar tata,ko meyasa yau tunda ta dawo take farin ciki oho?hakan bazai rasa nasaba da kyautar da gimbiya tayi Mata ba,ta Kai lomar tuwo bakinta a Karo na farko ta Kara dago fuskarta har yanzun wanan murmushin na Nan manne a kyakkyawar fuskarta wanan yasa innah yin gyaran murya,da sauri ummaty ta dago fuska ta kalli innar sai Kuma ta maida kanta kan littafin da take dubawa lokaci lokaci,
"Ummaty Wai nikam lafiya yau naganki cikin tsananin farin ciki haka?kekadai zaune tun dazun Ina lura da yadda kike murmushi tamkar wadda akaiwa goron albishi"...cikin tsananin farin ciki ummaty tace "innah kedai Bari wallahi gimbiya rumana Yar aljannah ce insha allahu,Wai kinsan me?"...sai Tai saurin dakatawa da maganar,tunawa da kalmar gimbiya da tayi,"ummaty banaso kowa yasan da maganar Nan dagani sai ke so nakeyi kawai Mai martaba yaga zainul ya taka da kafafunsa har fadarsa .....sai kawai ummaty Tai shiru,
"Kinyi shiru ummaty me gimbiyar tayi hakan"

"Yadda take kyautatawa jamaat gidan da al'ummar wanan gari gabaki daya,bakiga yadda take raba kyaututtuka ba dik Dan Allah ya bawa ya zainul lafiya,Kai Allah ya saka Mata da alheri,gaskiya tana matukar kaunar yaron Nan nata zainul abideen"

"Ameen ameen ummaty dik shine yasa kike tsananin farin ciki haka?gabaki daya murnarki yau Taki boyuwa ummaty,Baki da burin daya wuce ace zainul yasamu lafiya"hannuwanta tasa ta rude fuskarta rufff tana dariya cike da kunya,itama innar dariyar tayi ta cigaba da cin abincinta.

*******
Yau tunda safe yake kiraye kiraye daga cikin dakinsa kasantuwar fasawansa sun danyi nisa sai Kira yakeyi babu Wanda ya amsashi,..breakfast dinsu sukeyi hankali kwance kamar basajin Kiran da yakeyi daga cikin sashinsa,

"Mtswww gaskiya wanan ya takura Mana,dubi yadda yake Kira sai kace wani makaho tun dazun kake Kira babu Wanda ya amsa ai kasan babu me zuwa wajen naka"ta Kai kofin tea bakinta,...Kara Kira yayi a Karo na uku, zahira ta ajiye kofin tea dinta "idan bamuje wajensa ba bazamu samu sukuniba da wanan Kiran nasa,Dan hakan Bari inje Inga menene yake kiran"...tabe Baki Tai kawai batare da tace komiba.

Kofar dakin ta tura hade da yin sallama a gaggauce,Yana zaune saman wheel chair dinsa Yana gab da fadowa zahira ta Shiga "lafiya kaketa faman kwalawa mutane Kira haka Kuma kasan masu hidimar taka babu kowa?"...a hankali ya sauke idanuwansa akanta tana rike da kwankwaso tamkar me shirinfada "gyaramun zamana nakeso ayi,ko kafar Nan tawa data lankwashe idan ba hakan ba zan Fadi"...tsaki tayi cike da takaici taje tana kokarin gyara Masa kamar yadda yace,...Jin zahira shiru yasa warisah biyo bayanta taga meke faruwa,...daidai Nan ta shigo dakin tana raba idanuwa,turus tayi a tsaye ganin yadda zahira ke kici kicin gyara Masa zama dik tayi zufa,dakyar tasamu ta gyara shi ya zauna dakyau,
"Ke Kam da ba aikinki ba meya kaiki yin wanan aiki?ai be kamace ki ba zahira Aida saiki Kira wadanda keda alhakin kulawa dashi ko Kuma ya Kira wahalalliyar tasa ta karaso ta Dora daga inda ta tsaya"

*******
Gurfane take a gaban gimbiya rumana tana kwararo Mata bayanin yadda zatai amfani da maganin na zainul abideen dik yadda zata bashi ta sanar Mata komi,sanan ta Dora da,
"Maganar kunna karatun alkurani kidaina saboda nayi magana da malamin me bada wanan magani akan cewar zainul Yana dauke da bakaken aljanu a tare dashi,wanan maganin daya bada shine zakiyi mishi amfani dashi musamu waraka da haske,idan kina kunna Masa karatun alkurani fushi sukeyi Suyita bashi wahala kala kala shiyasa kikaga Koda yaushe cikin tashi ciwonsa yakeyi,sanan Abu na biyu ya sanarmun da cewar Koda munsamu ciwonsa na tashi idan muka bada maganin muyi hakuri na Dan lokacine zamuga ya daina Kuma aljanum zasuyi nisa dashi insha allahu,Ina fatan kin fahimta"...ajiyar zuciya ta sauke ta gyada Kai cike da natsuwa.."tashi kije Allah yayi albarka ki tabbatarda kinyi yadda akace"

"Insha allahu...ta Mike jiki babu kwari

******
Zahira Tai murmushi,"Taimakonsa kawai nayi a matsayinsa na Dan uwana,Kuma iya abinda Naga zan iya din kenan Dan wallahi inda taimakon ya wuce hakan bazanyi ba"...turo kofar ummaty tayi bakinta dauke da sallama Yana zaune Yana bin kowaccensu da Ido cike da takaici na abinda kannen nasa sukeyi Masa,...kallo ta Shiga binsu dashi daya bayan daya.
"Malama kallon me kikeyi man haka irin na rainin wayau?ko kina tunanin zamu cutar dashi ne?to Taimakonsa mukai dan da yanzun kimzo ki taddashi a kasa warwas "cewar zahira tana watsawa ummaty harara

"Ke kika tsaya kula lamarinta har kikasan tana kallonki,tunda kinyi taimakon da kikai niyya Kuma Dan Allah kikayi to Allah ya Baki Lada,nikam tunda babu niyya dama ko tabasa bazanyi ba Dan tsoro nakeji ko da wata najasar a jikin nasa ya shafamun mtsww"Tai gaba abinta zahira ta take Mata baya...

Tsananin bakin cikin da takaici yasa zainul abideen zubarda hawaye besan yanayi ba,gudu kawai hawaye keyi a fuskarsa zuciyarsa Tai Masa bakin Kirin saboda bacin Rai,....kallon yadda yake hawaye ummaty tayi kadai tasan bacin Rai ne yaja Masa hakan,tausayinsa ya lullubeta ta rasa yadda zatayi sai kawai ta janyo kujerar ta ta zauna daf dashi tana kallonsa cike da tausayawa "ya zainul menene Naga hawaye suna sauka a kwayar idon jarumin namiji kamarka?meyasaka kuka"a shagwabe Tai maganar itama tamkar zata fashe da kuka.

"Nima bansan daliliba ummaty...Abu daya nasani shine ban taba bakin cikin kasancewata cikin wanan halin ba kamar na yau,Shima bawai nayiwa Allah butulci bane,saidan abinda kannena jinina sukaimun da kansu ummaty"

Hannu tasa ta Shiga share Masa hawaye Tana girgiza Kai,sosai ya Bata tausayi "kayi shiru insha allahu ciwonka yazo karshe ya zainul zakasamu lafiya kamar kowa kaima har ka taimakawa wani Dan Adam din kaji?"...cikin tsananin bakin ciki yake kada Kansa kawai wani irin tsanar yaran ce ta darsu cikin kahon zuciyarsa...

********
Tayi zurfi cikin tsananin tunani tana jingine da jikin kilisa irinta sarakai ,ummaty kema bazan taba barinki rayuwarki ta tafi a hakan ba saina bibiyi rayuwarki na tabbatar da cikar burina sanan zansamu kwanciyar hankali dik wani taku ko numfashin da Zaki sauke tamkar akan idanuwana zakiyi shi Dan bazan taba Bari wanan Karon asamu matsala ba....ta lumshe idanuwanta ta budesu sunyi jajir tasa hannu ta dauki apple ta gutsira tana taunawa a hankali...tabbas tayi amfani da wayau da hikima da shekaru akan yarinyar tayi amfani da kalaman da babu yadda zaayi yarinyar ta tsallake umarninta...yanzun komi na ragamar zainul Yana hannunta sai yadda tayi...wani murmushi ta saki Wanda iyakarsa fuskarta tana ayyana abubuwa da dama a zuciyarta...
Chapter 12 · 0% Book details