Sashe 26
Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS* *DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619*
*********
"Ke ummaty lafiyarki kuwa tunda kika dawo gidan Nan kike Abu zabure zabure kina magana ke kadai kamar wata zautacciya?"
Dan furgita ummaty tayi hade da juyowa ta dubi innarta dake gefenta ta kafeta da Ido sai kawai ta sakar Mata lallausan murmushi ta Dora kanta a cinyarta tana turo Baki "Kai innah nifa ba magana nakeyi nikadai ba"
"Karya nayi Miki kenan?ko Kuma baa kusa Dani kike maganar ba wani waje kikeyi daban,meye yake damunki ne haka "
"Innah wallahi Babu komi kawaidai banajin dadin Raina ne kwana biyu tun Akan maganar auren da baabah yace zaimum dik hankalina ya tashi"
Murmushi innah tayi "ke Kuma bakison maganar aure koh?idan an barki haka Zaki zauna kenan ko ummaty?ai aure ya Zama Dole kiyishi komi Daren dadewa Amma dai kiyi tunani Akan hakan tunda bazaki dawwama a gabanmu ba ko?
Gyada Mata Kai ummaty tayi jiki a sanyaye,tace "toh innah"ta kwantar da kanta a cinyarta ta sake lulawa cikin duniyar tunani.....babban tashin hankali ke Shirin fuskantosu matukar abinda babah kande ta fada gaskiya ne to zaa samu babbar matsala,...hanyar da zaa rusa ginin tafiyar shine abin dubawa Dan tasani tabbas yanzun Mai martaba bashida wani buri da ya wuce yaga zainul abideen ya warke ya taka da kafafuwansa,Kuma ta tabbatarwa kanta da cewar zasuyi amfani da makirci da kissa cikin ruwan sanyi zasu shawo kan Mai martaba akam yabari akai zainul abideen wajen magani,Kuma ana kaisa shikenan dik Shirin da tayi ya koma baya komi zai lalace....idanuwanta suka kada sukai jajir...kanta yayi zafi zuciyarta Babu abinda takeyi sai bugawa sauri da sauri...shin me ya kamata tayi shiri Akan hakan ganin tafiyar ta ruguje?zuciyarta ke ayyana Mata Tai amfani da mahaifinta Amma take wata zuciyar ta kwabeta da hakan Dan zargin da takeyi akwai makarkashiya tsakanin mahaifinta da gimbiya rumana saboda yadda tunaninta yake Bata dikda Bata Gama gasgata hakan ba hasashe takeyi tare da lalube cikin duhu....runtse idanuwanta tayi tamkar Mai bacci,Amma a zahiri zuciyarta tana can wata duniyar ta daban,ji takeyi tamkar ta bude idonta taga gari ya waye Dan ta samu babah kande Akan wanan maganar....
*********
Tun sassafe ummaty ta tashi saboda rashin samun isasshem bacci da batayi ba Daren jiya,da bacci ya sure ta take farkawa saboda mugayen mafarkai da takeyi da gimbiya rumana hankalinta ba karamin tashi yayi da hakan ba yasa ta Mike cikin Daren tayi sallolin nafila tana kaiwa Allah kukanta akan samun nasara da rinjaye Akan gimbiya rumana tana zaune Akan sallaya har akai sallahr asuba Dan hakan batasamu bacci ba yasa ta tashi idanuwanta sun kumbura ga ciwon Kai da take fama dashi sosai...
Ayyukanta na gida tayisu a gaggauce wanke wanke da shara hade da gyaran daki dama ta Dora ruwanta akan murhu kafin ta Gama Dan haka tana Gama aikinta ta surka ruwanta ta dauki bokiti tayi bayin wanka ....
*********
Mai martaba ne zaune a fadarsa zagaye dashi waziri ne,sarkin dawaki da sarkin aska yau harda maga takaddar fada dukkansu sun hallara saboda Kiran gaggawa da Mai martaba yayi ....
Gyaran murya Mai martaba yayi sanan ya fara maganar dalilin tarasu a wanan lokaci...komi ya kwashe dangane da maganar ciwon zainul da Kuma shawarar da halima ta kawo na kaisa a nema Masa magani shine yake neman shawararsu....take waziri ya amshi maganar kafin kowa yace wani Abu yace cike da zumudi "alhamdulillahi ranka ya Dade wanan shawara tayi ya kamata gaskiya a duba lamarin yaron Nan Dan sarki jikan sarki a cikin wanan Hali na rashin lafiya Wanda ya Dace tun tuni ayi wani Abu akai ai ni harga Allah naji dadin wanan shawara"
Sarkin aska ma cikin tsananin murna da farin ciki yayi naam da maganar da Mai martaba ya kawo Banda sarkin dawaki Wanda yayi sumar zaune tunda Mai martaba ya rattabo wanan zancen hanakalimsa yayi kololuwar tashi Dan yasan Babu tantama wanan makircin na gimbiya rumana ne da halima su suka hadashi don suga bayan zainul,baisan lokacin da zufa ke keto Masa ta ko Ina a jikinsa ba har ya manta a inda yake zaune Saida ya tsinkayo muryar Mai martaba yanayi Masa magana "sarkin dawaki menene shawararka Akam wanan lamarin?"ya jeho Masa tambaya idanuwansa akansa...
********
Idanuwanta a rufe ta Fado cikin gidan kamar wadda aka korota sai waige waige takeyi kamar Mara gaskiya burinta be wuce su hadu da baabah kande ba Dan haka Bata ma Yi hanyar sashin gimbiya bilkisu ba sai tabi ta wata karamar hanyar da zata sadaka da bayan kitchen da inda bayi na gidan suke taruwa da kuyangi,tasan zata iya samunta a wajen saidai Bata so kuyangin gidan su fahimci akwai wata alaka tsakaninta da baabah kande Dan gudun gulma....saita makale jikin katamga tana leke ko zata hangota,....ta bayanta aka dafa kafadarta Wanda yasata sumar tsaye batare da ta waigo ba,...gabanta ya tsananta faduwa Amma hakan be hanata jarumtar juyowa a hankali taga waye ya dafa kafadarta ya ganta a makale a wanan wajen ba,ganin babah kande yasa ta sauke nannauyar ajiyar zuciya hade da dafe kirji tana sauke numfashi a hankali......
*WANAN LITTAFIN NA KUDINE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619*
💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞
*HASKE WRITERS* *ASSO💡*
*SLIMZY😍*
[1/23, 11:11 AM] 😍SLIMZY😍: 24
Shiru kowa yayi Yana sauraron shawarar da sarkin dawaki zai bada wadda dukkansu sunsan cewar dik abinda yace dashi Mai martaba ke amfani,Dan ko waziri Yana matsayin waziri ne Amma Mai martaba baya amfani da maganarsa kamar yadda yake amfani da ta sarkin dawaki ballantana wani galadima Wanda tuni sarki yayi fatali da lamarinsa...
Gyaran murya sarkin dawaki yayi tare da tattaro dik wata jarumta tasa yace "a bisa shawarar da kowa ya bada da wadda sarki ya kawo wadda gimbiya halima ta bada to a gaskiya nidai tawa Tasha bamban da ta kowa"dukkansu sukai saurin dagowa suna Bim sarkin dawaki da kallon mamaki da al'ajabi shi kuwa Mai martaba maida hankalinsa yayi sosai Yana gyada Kansa hade da cewa "umhmm sarkin dawaki muna sauraronka meye shawarar taka?"
"A bisa alamu da suka Nuna na jikin wanan yaro zainul abideen alamu sun Nuna Yana samun sauki sosai magungunan da aka canjo Masa ake basa na asibiti sun karbesa Kuma ana samun cigaba sosai a jikin nasa,yaron yayi lafiya sosai ya murmure tamkar ba shi ba,abinda ya rage Masa be wuci samun kafarsa ba Dan yadda na lura har magana yanayi sosai Dan hakan nake ganin idan aka kaishi wajen masu maganin Nan ba lallai bane maganin ya karbi jikin nasa a bisa dalili ko sanadim hakan sai ya kawo rikicewar jikin nasa ni a ganina a Kara Masa lokaci zuwa ya gama Shan magungunansa na asibiti mugani ranka ya Dade"...sosai Mai martaba ya gamsu da bayanin da sarkin dawaki ya bashi Dan haka ya gyada Kansa ya juyo ga sashen da waziri ke zaune ya kasa kunne yaji me sarki zaice..."a bisa kwakkwarar hujja da sarkin dawaki ya kawo Kuma shawarar tasa Mai kyau ce inaga zamuyi amfani da shawarar tasa mugani zuwa Nan da wata uku"...
A tare suka hada Baki "Allah ya Kara mishi lafiya ranka ya Dade"gyada Kai kawai Mai martaba keyi batare da ya amsa ba daga waziri har sarkin aska rasa bakin magana sukayi kowa da abinda ke cikin zuciyarsa har Allah Allah sukeyi su fita a tare a fadar su zanta,kasa hakuri waziri yayi ya dubi sarkin aska bayan sunfito suka tsaya can nesa da fadar damuwa ce dauke da fuskarsa yace "sarkin aska Anya wanan mutumin Babu wani Abu da yake shukawa a wanan masarautar kuwa?wanan Abu akwai mamaki tsantsa da al'ajabi...dubafa kagani ko akan rashin lafiyar yaron Nan zainul shekara da shekaru ace ana Abu daya sarkin dawaki shi ke dakatar da Mai martaba akam dik wata shawarar arziki da zaa bada sai ya kawo cikas a ciki?Anya wanan tafiyar Babu wata kulalliya da manakisa kuwa?"
"Hmmm waziri kenan ni ai abun ne ya isheni kaga na kasa ko kwakkwaran motsi har ya Gama rattabo iyayinsa nasan Mai martaba bayansa zaibi shiyasa ban tsaya dogon bayani ba nace shawarar tayi Dan nasan ko munce wani Abu bazai amfani dashi ba sai abinda sarkin dawaki yace gara karma in Bata bakina"
Cikin tsananin bacin Rai waziri Yama rasa abinda zaice cewa kawai yayi "Allah ya kyauta toh"...
"Ameeen "yace kawai ya juya abinda cike da bacin rai....
********
"Baabah kande wallahi harga Allah kinbani tsoro bakiji yadda zuciyata ke harbawa ba"ta turo Baki,....dariya sosai babah kande tayi "kagamum ja'irar yarinya sai kace Kinga dodo ko wata aljanah zakice na Baki tsoro?"
"Umm babah kande ni dik ba wanan ba kinsan yadda na Shiga tsananin damuwa daga jiya zuwa yau?"hmmm Allah ko baccin kirki banyi ba tunani kawai nakeyi akan abinda zai biyo baya ba Dan gimbiya inhar hakan ta kasance to tabbas ta mamayeni"
"Ki kwantar da hankalinki ummaty inaji a jikina Babu abinda zaisamu zainul abideen alfarmar annabi da alkurani domin Allah zai kareshi tunda bashida hakkinsu ko kadan Dan haka kibi komi a hankali Banda garaje sanan babbar shawarar da zam Baki shine kiyi taka tsantsan Akan komi zakiyi karki kuskura ki hada Kai da kowa wajen wanan tafiyar karkice Zaki nemi mataimaki bayan Allah domin zaa iya Gina Miki rijiya ki fada....Kinga gimbiya rumana?macece shedaniya ga wayau zata iya amfani da wata damar Dan sanin sirrinki da asirin ki gabaki daya bazaki San yadda zatasamu komiba saidai ki wayi gari cikin masifa baa fata Dan haka ki iya takunki ummaty"
Sosai jikin ummaty yayi sanyi da kalaman baba kande,iska Mai zafin gaske ta hurar daga bakinta sanan tace cikin sanyin murya "baabah kande insha allahu Zanyi yadda kikace Kuma da izinin Allah fatana be wuce gimbiya ta wayi gari zainul ya taka da kafafuwansa ba insha allahu yanzun Ina cikin tsananin damuwa damgane da abin Nan data bullo dashi"ta dubi babah kande tamkar zatayi kuka,
Tausayinta ne ya lullube babah kande "ki kwantar da hankalinki nace Miki akwai wani shiri Dana shirya a zuciyata matukar hakan ya kasance ,balle Ina fatan Allah ya kawo sanadim da zaa fasa wanan shiri nasu...