← Book details Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 49

Sashe 23

Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

********
Hankalinsu na kan katon tv plasma din da yake patlorn bakajin sautin komi sai karar fanka sai AC da suka kureta karshe ko Ina ya dauki sanyi dik hankulansu na kan American film din da suke kallo ....can gefe warisah ce zaune kunnenta makale da waya tanayi tana lumshe idanuwanta da alama tana Jin dadin wayar da takeyi....a hankali ta turo kofar falon bakinta dauke da sallama dukkansu Babu Wanda ya kula da ita balle yasan tayi sallama ko batayi ba har ta iso tsakiyar patlorn zata ketare ta wuce sashen zainul abideen,...kallon banza warisah ta bi ta dashi sanan ta katse wayar da takeyi tace cikin tsawa "dalla malama dakata"....cakkkk ummaty ta tsaya kamar an dasata "Baki iya sallama bane ballantana musamu arzikin gaisuwa?"...Tai maganar tana dagowa daga kishingiden da take.... wanan karon juyar da kanta ummaty tayi da niyyar wucewa,warisah ta Kara Kara dakatar da ita a Karo na biyu

"Halan ke dabbar Ina ce da anayi Miki magana kina kokarin wucewa?ko kurma ce ke?"

"Nayi sallama har sau uku ba kuji bane"Tai maganar ranta a tsananin bace Amma sai ta danne ta kakalo murmushi...

Mtswwww warisah taja tsaki ta zauna tana fadin "komi akayi da jaki sai yaci Kara"...itadai ummaty Bata ce komiba tasa Kai Tai shigewarta ko karasa wucewa batayi ba taji sautin muryar zahira tana fadin "turaren jikinta kamar na Yan bori wallahi dik ta cika Mana parlor Bari kugani"...ta Mike Tai hanyar window tana kokarin zuge labule tsuki warisah taja ta dubi baiwarsu dake rakube a gefe "ke hinde jeki ki hado mana turaren wuta kisa a wajen Nan dik ya dume da warin talauci"

Dukkansu Yan Matan dake parlon dariya sukeyi sosai Banda mutum daya wadda ta dubesu Rai a bace tace "haba Dan Allah wanan ba Yi bane wallahi ba girmanku bane,yarinya batayi muku komiba dik kunbi kum tsamgwameta fisabilillahi?"

Wani kallo warisah ta watsawa Mai maganar sanan tace "hafsaht ke dama ai ko da yaushe bamu San daidai ba kece kikasan dai dai Kuma kike kaunar mutane koh?Wai shin ma Ina ruwanki Dan antaba wanan kucakar?"

"To ku ma Ina ruwanku da ita idan ba sa Ido ba?mtsww sai shegen kishin tsiya "

"Kishin uban me zaayi da wanan jakar?"zahirah tace a fusace

"Kishi kuke tafiku kyau Kuma ya zainul ita yakeso zai aura"...yadda Tai maganar yasa su dukkansu shekewa da wata irin dariya suna rike ciki har suna hada Baki wajen fadin"tabdijan wanan zamuyi kishi Dan tafimu kyau?farar fata dai,maganar ya zainul Kuma mun bar Mata indai wanan ne"

Takaici ne ya Kara lullube hafsat ta Mike tsaye ta rike kugu "insha allahu wata Rana cikinku sai an samu wadanda sukai fada Akan ya zainul Bari dai yasamu lafiya "tana Gama fadin haka ta fice a fusace suka bita da hayaniya tamkar zasu tsaga dakin....

*********
Zaune take gefen gadon zainul abideen rike da hannunsa fuskarta samm Babu walwala ko kadan Tai shiru tana Kare Masa kallo yadda ya rame daga Daren jiya zuwa wayewar gari,....murza Masa hannuwansa takeyi da yatsunta Yana Kara lumshe idanuwansa da alama yanajin dadin yadda takeyi Masa,...cikin wata iriyar murya a dashe yace "ummaty kina Sona?"...da sauri ta saki hannun ta kalleshi a tsorace gabanta yayi mummunan faduwa....Bata taba tunani ko a mafarki zataji wanan kalmar daga bakinsa ba Koko zaiyi Mata wanan tambayar da taji dirarta cikin zuciyarta,....gabaki daya a rude take ta kasa magana jikinta ne ya soma rawa....shi kuwa ya zuba Mata manyan idanuwansa. Farare Tass ya kasa kunne yaji me zatace ,sai kawai tasunkuyar da kanta kasa jikinta bai daina rawa ba....sosai taso bashi dariya dik da yadda yakejin jikin nasa Babu Dadi bai hanasa yin murmushi ba yace "kinyi shiru?tunda bazaki amsa ba mubar maganar kawai ammah ga hannuna rikemun ki cigaba da yadda kikemun inajin dadin hakan"...a hankali yadan dago hannunsa dikda nauyin da hannun yakeyi Masa yau itace Rana ta farko daya dagasa sosai Amma Yana rawa Kar Karrrr Karrrr.....shiru tayi ta kasa dago kanta sai zuciyarta dake bugawa tamkar zata fasa kirjinta ta fito....dakyar ta Dan dago idanuwanta ta kalli hannun da yake Mika Mata,Dan haka sai ta tsinci kanta da dago hannunta a hankali ta ruko hannunsa masu shegen taushi kamar auduga ta rike ta Shiga Yi Masa kamar yadda ya Umar ceta....wani Abu ne ke yawo a ilahirin jikinta tamkar shocking take taji wata irin kasala na neman saukar Mata...dakyar ta iya motsawa ta dago kanta suka hada Ido ya lumshe Mata idanuwansa Wanda suka sa lokaci daya jikinta ya karasa mutuwa wani irin bakon yanayi fiye da Koda yaushe taji a cikin jikinta....suna cikin wanan yanayin aka bude kofa hade da sallama da sauri Tai kokarin kwace hannunta sai kawai taji Allah ya bashi ikon riketa gammm rukon da bazata iya kwacewa ba...

Karasowa tayi cikin dakin tana sanye da doguwar rigar Abaya baka Tasha kwalliya Tai masifar kyau sai kamshi take zubawa bayi ne biye da ita sunkai biyar ko wacce da abinda take rike dashi haka ta nemi waje ta tsaya Amma idanuwanta karr Akan hannuwansu da take kallo....daya daga cikin bayi ce ta zube a kasa tace "barka da war haka zainul abideen Dan sarki jikan sarki magajin sarki...da daya tamkar da dubu a dik fadin wanan masarautar ,dik wani namiji a bayanka yake Dan Kaine magajin sarki.....ranka ya Dade Yar sarkin kudu ce ta kawo ziyara wanan masarautar gimbiya maryama diyar sarauniya zainab aminiya ga gimbiya rumanah ummanka,tun jiya ta sauka a wanan gida Mai albarka Amma kasantuwar ta gaji batasamu tazo bangaren magajin sarki Dan duba jikin nasa ba Allah yaja zamaninka ,Allah ya Kara maka lafiya ya kawo karshen wahalarka"....har wanan baiwa ta Gama magana idanuwan zainul abideen a lumshe suke Saida yaji shiru sanan ya budesu hade da sakin lallausan murmushi....itama murmushin ta maida Masa sanan cikin siririyar muryarta tace "barka da warhaka ya zainul"

Gyada Mata Kai yayi sanan ya bude Baki a hankali yace "barkanki dai maryama"....

"Ya jikin naka?"Tai tambayar a takaice....

"Da sauki"kawai yace hade da rufe idanuwansa yanajin dadin rikon da ummaty Tai Masa....ta dauki lokaci sanan tace"Allah ya Kara sauki"

Dukkan su dake dakin sukace "ameeen"...batare da Bata lokaci ba ta saci kallon zainul da idanuwansa ke rufe tamkar me bacci ta kalli ummaty ta Dan tabe Baki ta juya Tai hanyar fita Yan rakiyarta suka take Mata baya...

Kamshin turarenta ne ya gauraye ko Ina yasasu saurin diban inda sukejin kamshin,ko kallonsu batayi ba Tai gaba abinta bayi na biye da ita,dukkansu basusan shigowarta ba sunbar patlorn lokacin da ta shigo Dan haka kowa kallon mamaki yake bin ta dashi Allah Allah suke Tai nisa suyi magana ,
Jikin zahira har rawa yakeyi wajen fadin "tabdijan Amma fa ta hadu"...wani kallo warisah da hafsat sukai Mata hafsat ta dauke kanta warisah ce ta kasa hakuri tace"kedai Taiwa kyau ni batamunba batafini kyau ba"tana fadin haka ta Mike ta fice abinta....

********
Ganin yayi bacci yasata mikewa a hankali ta zare hannunta daga nasa ta tsaya tsaye Kansa tana murmushi ta girgiza kanta ta juya a hankali take takun nata Dan kada ta tasheshi Koda taje kofa a hankali taja kofar ta sulale Tai cikin gida....

*WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN* *BAYANI 08166177830 KO 07084161619*
*********

Firar dankali tsohuwar keyi a ta bayan babban dakin girki na cikin masarautar tana zaune kan kujerar ta sanye da kaya irin na manyan kuyangi tsofaffi wadanda suka Dade a cikin gidan har suka hayayyafa a ciki Kaya ne irin na gargajiya irin na saki na da Wanda tsofaffi ke sawa kalar blue kamar Koda yaushe a jikinta ta dukufa tana firar dankalin turawa ummaty ta karaso wajen da faraarta hade da sallama tace "assalamualaikum baba kande"

"Waalaikumussalam ummaty barkanki da zuwa "baba kande tace fuskarta dauke da faraa tana cigaba da firar dankalinta...

Gefen baba kande karamin benci ne ummaty ta gyara ta zauna "baabah dankali kiketa ferewa haka da laasar din Nan?"

"Ehh wallahi Wai bakin can Yan Mata sukeso a soya musu Wai bazasuci tuwon shinkafa ba daddare shine akace infere insa a ruwa sai inbawa Mai suyar da yamma sai ta soya musu"...

Dan Bata fuska ummaty tayi tace "shine sai a saki?"

"Ya Zanyi ummaty?ai aikinmune bauta gidan Nan shekara da shekaru karki wani damu kinji"

"Toh Bari in tayaki muna Yar hirarmu ko Yar tsohuwar?"

Dariya sukai gabaki daya ummaty ta dauki wuka ta dau dankali ta Shiga ferewa....sun dau minti biyar a hakan ummaty tace "baabah nabar zainul yanata bacci a daki nayo Nan muyi Hira kafin ya tashi yasa rigima har ummansa taji takirani taimun fada"Tai maganar tana dariya...

Jinjina Kai baba kande tayi ta cigaba da firar dankalinta tana Yar dariya...."ammah kinsan wani Abu baabah?"

Baba ta dago Kai tana kallon ummaty alamar tana sauraronta...

Ummaty ta cigaba da magana "dik gidan Nan Babu Wanda yakei ummah rumanah son ya zainul tana matukar ji dashi sosai wani lokacin har tausayi take bani sai kiga tamkar ta cire ciwon ta maida jikinta idan ciwonsa ya tashi....kwanakin Nan tana Shiga damuwa sosai akansa"...

Jinjina Kai babah kande tayi ta dubi ummaty tana rike da dankali tace "yarinya ce ke ummaty"

"Babah bangane ba me kike nufi?"...

"Karki damu Zaki fahimci abinda nake nufi Nan gaba,Zaki fahimci tsananin soyayyar da gimbiya rumana keyiwa zainul abideen sanan Zaki San komi dangane da yaron da mahaifinsa da mahaifiyarsa...."

Cikin rashin fahimta da tsananin fargaba ummaty ke kallon baba kande tana sauraronta...shiru tayi na Dan lokaci tana nazarin kalaman babah kande Wanda ta ninke ta Dasu a baibai....Bata fahimci komiba a furucin dik yadda taso ta kasa....cije lebenta tayi Tana son Karin bayani Amma zuciyarta ta haneta da hakan Dan kada baabah kande ta fahimci wani Abu ....sai kawai Tai murmushi tace"tsohuwa ni ban fahimci wanan furucin naki ba wallahi kinyimun magana da yare irin naku na tsofaffi"ta turo Baki gaba...
Chapter 23 · 0% Book details