Sashe 40
Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tsoro ne ya cikata yadda yake maganar Amma kwarjinin da yayi Mata ya hanata cewar komi sai gyada kanta kawai takeyi cike da faduwar gaba..dago Kai tayi ta cikin glass din motar Tana duban waje taga gari har ya soma duhu alamar magriba tayi ta dubesa cikin marairaicewa "ya zainul magriba tayi inaso inje gida"
"Kinaso kije gida Koko muje Inga inda kike?"..take tsoro ya cikata tunawa da tayi haris Yana gidansu sanan bataso yarima zainul yasan cewar haris ne ya Basu wajen Zama da kyar ta hadiyi mugun miyau ta tattaro dik wata natsuwarta tana yake tace "ya zainul baba bayaso kowa yasan inda muka koma Ina ganin idan har ya ganmu zaiga kamar nice na biyoka na kawoka gidanmu"...wani irin kallo yake watsa mata Wanda ya sata Babu shiri ta Shiga taitayinta "nayi Imani da Allah baba Dan ya ganni a gidansa bazai taba korata ba domin Nima da'nsa ne kamar yadda kike yarsa Dan haka gyara Zama zakiyi ki Nuna mana hanya....sauke glass yayi ya yafito Dan liti dake gefen titi yanata rawar sanyi,a guje ya rugo ya zube a kasa "gani ranka ya Dade"
"Shigo ka jamu ummaty zata Nuna maka hanya"...da sauri ya zagaya maxaunin driver ya tada mota suka dau hanya...
*WANAN LITTAFIN NA KUDINE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619*...
minti minti yakan kalli agogon wayarsa Yana duban lokaci har yanzun Bata dawo ba cike da damuwa ya dubi innah wadda ke zaune tana Jan carbi yace "innah har yanzun ummaty Bata shigo ba kaddai tayi makuwar hanya"
"Bazatayi makuwa ba haris ai ummaty akwai ganuwar hanya inaga dai kila ta biya wani wajene"...gyada Kansa kawai yayi badan zucuyarsa ta aminta da fitar Nan tata ba fatansa da burinsaa Allah yasadai ba wani bane ya tareta Nan take taji wani kishi ya rufesa...zaiyi magana kenan wayarsa ta Shiga ruri Yana dagowa yaga sweet momy ... gabansa ne ya Fadi yasan zaisha fada Dan tun safe ya baro gida be komaba gashi mahaifinsa yau zai dawo lallai ya tafka babban laifi hakanan ya daure ya Danna recieve ya Kara a kunnensa "hello sweet heart"yace cike da zolaya
"Dik inda kake kazo gida Nanda minti goma Dan daddynka ya dawo tun dazun baka a gida idan ba haka ba saina sassaba maka shasha Sha kawai"ta kashe wayar cike da bacin Rai...bin wayar yayi da kallo ya tabe Baki gefe daya farin ciki ne ya cikasa na zai samu muradin ransa ummaty Dan yau baa kwana be fadawa mahaifinsa maganarta ba kuma yasan zai Goya mishi baya Dan haka mikewa yayi ya dubi innah "innah Bari inje gida momy na kirana daddynmu ya dawo daga London"
"Kai Masha allahu to a gaida gida ayi Masa sannu da zuwa kaji"
"Insha allahu zaiji innah"
"Ga ummatyn Bata dawo ba har yanzun"
.cije Baki yayi beso hakan ba Dan bayaji yau zai runtsa yadda be ganta sunyi sallama ba hakanan yayi hanyar kofar gidan,Yana fitowa yaja motarsa a guje ya bar kofar gidan daidai kwanar fita unguwar sukai clashing da motar yarima....kallo haris yabi motar dashi tamkar yasan motar saidai an tada kura baya iya hango lambar motar balle yasan waye....
Har kofar gida suka kawota sun Dade cikin motar suna musayar kalamai masu sanyi da ratsa zuciyar masiya ta bude kofar motar zata fita ya fizgota ta fada jikinsa ya kafeta da wani mayen kallo da narkakken idanuwansa a hankali ta Shiga kwace jikinta saboda yadda taji kasala na neman rufeta shi Kansa jikinsa a sake yake fitarta kawai ya gani a guje Tana murmushi shafa Kansa yayi Shima yana murmushin hade da lumshe shanyayyun idanuwansa....
********
"Kace yarinyar Yar sarkin dawaki ce?"dady ke tambayar haris bayan ya Gama rattabo mishi labari Dan haka da sauri ta kada Kansa..
Murmushi irin na manya daddy yayi "to alhamdulillahi indai yarinyar da kake magana ce tanada tarbiyya ummu Salma sanan shi Kansa sarkin dawaki mutumin kirki ne Dan haka Zan sameshi da maganar zuwa jibi.."farin ciki ne ya lullube haris har baya iya rufe bakinsa saboda farin ciki...yayita wa daddynsa godiya ,dik maganar da sukeyi momy batasan wainar da ake toyawa ba koda tayi sallama ta shigo patlorn shiru haris yayi gudun kada taji Aiko dady ya Shiga zayyano Mata....
********
Zazzabi me zafi ya rufeta a kuryar daki ta rasa yadda zatayi dik maganin duniya Tasha Amma yaki sauka ga mugun ciwon kirji gefe daya da take fama dashi kusan sati uku kenan Taki fadawa kowa dik ta rame ta fita hayyacinta...wayarta ta janyo ta Shiga foldern din hotuna ta bude wasu hotunansa ne guda biyu Wanda haris yayi Masa gab da zaiji sauki ta bude tana kallo tana murmushi warisah kenan wadda ciwon soyayya ke neman yin ajalinta ta shagala wajen kallon hotonsa Wanda ya zame mata kamar aikinyi bataci Bata Sha sai an tsareta...tari ne ya taso mata taitayi da sauri ta fada toilet Jin tamkar zatayi amai tarin bai sauka ba taji wani Abu na taso Mata daga makogwaro ta kakoshi kasa tamkar majina zaro Ido tayi lokacin da tayi tozali da gudan jini....ta kara kako wani Shima jinin ne innalillahi wa Inna ilaihi rajiun...Nan da Nan idanuwanta suka cicciko da hawaye daidai Nan momy ta turo kofar toilet din ta shigo tana Kiran sunan warisah.....
*HASKE WRITERS ASSO💡*
💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞
*SLIMZY😍*
[1/23, 11:43 AM] 😍SLIMZY😍: 36
"Innalillahi wa innah ilaihi rajiun shine abinda hajiya kubrah ke furtawa jikinta na tsananin rawa ta shiga cikin toilet din ta ruke warisah wadda dik ta galabaita saboda amai ga wata irin Rama da tayi wadda ita kanta bata lurada hakan ba sai yau "warisah meke damunki babyna?meyasameki haka?"..cikin tashin hankali takeyi mata tambayar...gaban warisah ne ya fadi cike da tsoro ta kalli fuskar momy sai ta kauda kanta gefe Dan bata shirya sanar mata da ta dade da hakan ba kuma Bata shirya fallasa sirrin zuciyarta ba Dan haka sai kawai dabara ta Fado mata ta danyi tari kadan sanan a wahale tace "momy wallahi wani irin tari ne nake fama dashi idan na Soma sai nayi amai kuma harda jini ciki inaga mura ce tayi mummunan kamani"..cikin rashin yarda momy ke kallon kwayar idanun warisah Tana so ta hango wani Abu Amma dik yadda ta Kai ga karantar ta takasa hango karya a kwayar idanun nata cikin mutuwaar jiki momy tace "Amma wanan wani irin tari ne kikeyi hadda jini guda guda da Dan yawa hakan?nasan cewar inhar mutum na tari me jini to zaiyishi Amma bada jini sosai ba naga naki yayi yawa shikenan Bari muje asibiti gobe idan Allah ya kaimu sai a Baki maganin taarin kinji?"gyada mata Kai warisah tayi fuskarta dauke da murmushi na dole har yanzun momy rike da ita take haka suka fito toilet din Tana karantar yanayin yartata Wanda samm Bata yarda zancen warisah ba koma menene dai zata kaita asibiti kuma likita zai bincike mata ita...
*******
Wajen karfe daya na dare juyi takeyi kawai Amma bacci ya kasa daukanta gabaki daya hankalinta na wajen shi dik motsinta da bugun zuciyarta hade da saukan numfashinta Tana yinsu ne tare da soyayyar zainul abideen wadda take yawo a cikin jinin jikinta da b'argonta...gyara kwanciyarta tayi ta Mika hannunta gefen drawer din gadon ta ta janyo wayarta ta shiga typing massage jikinta har rawa takeyi....
It's seems like I can do without u ya zainul I luv u beyond ur expectations save my life...it's warisah....ta dade Tana karanta massage din tamkar bazata tura ba haka tayi shahada ta tura massage din hade da runtse ido...
Wayarsa ce tayi haske alamar massage ya shigo lokacin Yana zaune kan dadduma ya idar da sallah Yana tasbihi da rokon Allah gefensa alkurani ne me girma a kusa dashi wayar tasa take,Dan haka da sauri ya dauki wayar ganin wanene yayi Masa massage da wanan Daren zuciyarsa na darrrr darrr ya bude massage din ganin bakuwar number ce yasashi saurin fara karantawa...Saida ya Kare karantawa ya tabe bakinsa ya wulla wayar kan gado hade da dafa kansa cike da takaici ya rasa yadda zaiyi da wanan yarinyar kamar mayya metake nufi da wanan massage din?shine zatacewa ya ceci rayuwarta?Aiko indai soyayyarshi ce to gaskiya Yana tsammanin zata mutu,...zuciyarsa ke ayyana Masa Anya yarinyar nan zata barshi yasha ruwa?ta barsa da abinda yakeji Mana a jikinsa na rashin masoyiyarsa a tare dashi lokacin da yafi bukatarta?...inaga idan har be yi mata mummunan rashin mutunci ba bazata sakar Masa Mara yayi fitsari ba Yana neman mafita akan ummaty Tana kokarin hasa mishi wata sabuwar wuta...Dan tsaki yayi hade da yin auzubillahi minasshaidanin rajim..ya Kori shaidan sanan ya janyo alkuraninsa ya bude suratul yaseen Yana karantawa....
********
Ko kafin safiya jikin warisah yayi zafi sosai Amma Bata fadawa kowa ba sai aukin Shan magunguna da takeyi Wanda ba likita ya rubuta mata ba yau ma hakan ta kasance kusan karfe goma na safe Tana nade cikin bargo rike da waya tana jiran tsammanin massage dinta Koda na zagi ne tasamu taji sanyi...
A parlor hajiya kubrah ta shirya tsaf cikin leshinta me kyaun gaske da tsada suna breakfast itada daddy mahaifinsu soyayye Irish da kwai da pepe soup din kayan ciki suke breakfast dashi....a yangance take cin abincin lokacin da daddy ya kurbi tea ya ajiye cup ya dubeta yace "momyn Yara wai Ina babyna ne?tunda na dawo sau daya na ganta,yanzun gashi muna breakfast ban ganta ba Ina ta shiga ne?ko tana gidan Mai martaba ne?"
"Tun jiya nakeson sanar dakai batada lafiya yanzun haka Shirin da nayi kenan da nagama breakfast zanje in lallabeta taci ko kadan ne inkaita likita ya cajemun ita dikda tace tana fama da tari"
"Toh hakan nada kyau nima idan an sakko masallaci anjima Zan dauki alhaji madu muje nemawa Dana aure"
Cikin rashin fahimta momy ke kallon daddy Wanda ke aika pepe soup bakinsa "ban gane nemawa Danka aureba,Dan alhaji madu ne zaiyi aure?"
Nisawa yayi kadan "ai alhaji madu bashi da yaro namiji karami ne Ina nufin haris Mana ya samu matar aure"
"Wai haris nawa kake nufi?tabdijan wacece matar da har ni besanar Dani ba Kai ya sanar da Kai?wato inda baka fadamin ba sai kun gama abinku zanji kenan"