Sashe 38
Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tausayinta ne ya lullube innah ta Shiga sharar hawayen da batasan suna zuba ba "kinadashi ummaty kingafa haris Shima Dan uwanki ne Kuma Yana kaunarki Shima inhar baya kaunarmu da hakan ta faru bazai biyomu har ya lallashemu ba,kingani ga Kuma abinda yace karki kuskura kice bakida Dan uwa a gabansa bazaiji dadiba kinji ki rungumi kaddarar da Allah ya jeho Mana da hannu biyu biyu sai Allah ya kawo Mana mafita,Kinga annabi ma yace Yana daga cikar imanin mutum shine yadda da kaddarar Mai kyau da Mara kyau me zaisa bazakiyi koyi da annabi ba kibi maganar daya fada umm?"...kuka ummaty takeyi ta fada jikin innah ta rungumeta ta cigaba da lallashinta ga jikinta yayi zafi Rau har asuba suna zaune waje daya Saida aka Kira sallar asuba sanan sukayo alwala din gabatar da sallar asuba....
*WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619*
********
misalin karfe Tara na Rana tana kwance kan tabarma kanta akan cinyar innah Tana fama da ita akan ta tashi taci abinci Taki tashi sai ajiyar zuciya take saukewa minti minti ga jikinta da yayi zafi sosai har kanajin hucin zazzabinta,
Haris ne ya shigo bakinsa dauke da sallama Yana sanye cikin kayan sanyi track suit jajaye Riga da wando sun matukar karbarsa innah ta amsa Masa sallamar cike da kulawa ya tsugunna a gabanta "innah barka da tashi, antashi lafiya?"
"Lafiya Lau haris ya dawainiya Allah ya saka da alheri yayi albarka"..
"Ameen"yace Yana sadda Kansa kasa minti minti yakan dago idonsa ya Saci kallon ummaty wadda ta lumshe idanuwanta tamkar me bacci,..
"Innah ummaty bacci takeyi ne?"
"Ehh inaganin Dan jiya daddare bamuyi bacci ba,kwana mukai batayi bacci ba tanata koke koke ga jikinta yayi zafi sosai zazzabi ke damunta bansan ya Zanyi da itaba"...
Cije lebensa yayi ya busar da iskar bakinsa "innah sai a hankali zuciyarta Babu Dadi ne nazo ne inji shawarar da kuka yanke Dan nasa har anfara gyaran gidan"...
"Toh shikenan Allah yayi albarka Babu damuwa insha allahu zamu zauna can din .."
"Zuwa gobe zanzo in kwasheku in maidaku can din Bari inje in Nemo Mata magunguna in dawo"
"To haris Allah ya saka maka da alheri"...
"Ameen innah"
Wasu hawaye ne masu dumi ke gudu a fuskarta dikda idanuwanta a rufe suke Tana sauraron dik tattaunawarsu...
******
Juyin duniyar Nan anyiwa zainul magana tun tashinsa yaki kula kowa tamkar kurma haka ya koma musu gashi tun jiya beci komiba ,har idan aka matsa Masa da magana sai ya sa kuka tamkar karamin yaro bakaramin tashin hankali iyayensa suka Shiga ba na wanan lamari musamman Mai martaba Wanda yayi iya bakin kokarinsa akan zainul Amma yaki koda kallonsa ne hakan Nan badan sunso ba kowa ya bashi waje...
Baiwar gimbiya bilkisu ce ta turo kofar bakinta dauke da sallama ta shigo sanan ta tura kofar,...gefen wheel chair din da yake zaune ta zube a kasa dik kawo gaisuwar da takeyi be amsa ba kusan minti biyar da kyar tayi shahada ta bude Baki taace "ranka ya Dade dama jiya bakada lafiya dangane da abinda ya faru shine na tsinci wayar ummaty to ummah naso Kai mawa saidai nace Bari inkawo maka idan kace akai sai akai"...da sauri ya juyo gareta Yana kallonta har ta karasa zancenta yayi shiru bece komiba har ta fidda Rai zaiyi magana sanan ya mikar da hannunsa "mikomim wayar" Babu musu ta Mika masa wayar ya karba,
Gabaki daya ya maida hankalinsa kan wayar yayi kurrr da Ido Yana kallonta tamkar ummaty yake gani a gabansa har lubabatu ta Mike ta Kai kofa zata fice ya dakatar da ita da sauri ta tsugunna a wajen "Kar inji labarin cewar wayar ummaty tana hannuna idan har naji to tabbas kece kika fadeta Dan haka wanaan wayar itace zata debemun kewar masoyiyata"...Yana Gama magana ya daga Mata Kai alamar ta tafi ta Mike da sassarfa ta fita sukai kicibis da warisah xata Shiga wajensa....
*******
"Dik yadda zaayi ki tabbatar kin samomin wayar Nan a hannun yarinyar Nan Dan ban yadda da ita ba gabaki daya hankalina be kwanta da cewan da tayi in mallaka Mata wayaba"cike da tashin hankali take fadawa hansa'u wanan lamari....
Jijjiga Kai hansa'u takeyi cike da alhinin wanan maganar da uwargijiyata ke fada Mata zuciyarta cunkushe da tunanin yadda zata bullowa lamarin ta karbo.....
*HASKE WRITERS ASSO💡*
💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞
*SLIMZY😍*
[1/23, 11:42 AM] 😍SLIMZY😍: 34
Jiki a sanyaye ta shigo dakin bakinta dauke da sallama,kamar wadda takejin tsoro haka ta rakube daga gefe ta sadda kanta kasa gabanta na tsananta faduwa,...shiko wani mugun kallo yake jifanta dashi tun shigowarta dakin kusan minti goma Babu Wanda ya cewa Dan uwansa uffan yasa warisah sadakarwa bakinta na karkarwa "barka da tashi ya zainul ,ya jikin?fatan kasamu lafiya"ta dago manyan idanuwanta ta sauke Masa su,...wata muguwar harara da ya watsa Mata itace tasa hantar cikinta wani irin kuwwa Amma saita daure,ko tanka Mata beyiba ya maida Kansa gefe suna Nan zaune malam zubair ya shigo hannunsa dauke da robar ruwan addua na rubutu da yayo Masa Shima sallamar yayi ya shigo dakyar zainul ya bude Baki ya amsa Masa ciki ciki,malam zubairu bedamu da hakan ba ya cigaba da magana "ranka ya Dade ya karfin jikin? fatan kasamu lafiya, yanzun me kakeji?"ya Watso Masa tambaya Yana maida hankali Kansa,
Dakyar zainul ya bude Baki tamkar me ciwo a bakin yace "da sauki Babu abinda ke damuna"yace a takaice...
Gyada Kai malam yayi cike da gamsuwa "Masha allahu ga ruwan addua na kawo da turare Wanda Zan shafa maka hade yake da habbatusauda da zaitun ciki anjima da yamma Ma zanzo in shafa maka safe da yamma"... batare da yace komiba ya gyada Masa Kai,...sai kawai ya juya sashen da warisah ke zaune ta sadda kanta kasa Tana Wasa da yatsunta cikin daga murya hade da tsawa yace "ke uban me kikemun a daki har yanzun Baki fitaba?"...a firgice ta dago Dara daran idanuwanta Tana kallonsa "Ina magana kin kafeni da Ido tamkar wata mayya?xaki fita ko sai na Kira fadawa sun fiddaki?"...take idanuwanta suka kawo ruwa ta Mike jiki Babu kwari Tai hanyar fita,dakyar take Jan kafarta har ta Kai kofa ta juyo ta kallesa taga shi yake bin ta da mugun kallo, haka ta rufo kofar ta tsaya ta baya ta danne bayanta da jikin kofar Tana maida numfashi hawaye na sauka daga idanuwanta....shiru tayi tsaye har wajen minti arbain tana tsaye wajen Saida taji alamar motsi zaa fito sanan tayi saurin barin wajen.....
********
Koda suke fito da kaya daga gidan haka jamaa sukai cirko cirko kofar gidan cike da tsaigumi wasu na murna wasu har zubda hawaye sukeyi cike da jimami da tausayinsu dik yadda makota sukaso da su ji inda zasu koma Babu Wanda suka fadawa dakyar ummaty ta fito ta Shiga motar abokin Haris al'ameen Wanda sukazo tare dik zazzabi take fama dashi gashi ta zabge ta rame sosai.....tayi fari sosai ta cikin glass take kallon unguwar Tana zubda hawaye cike da takaici haka suka tattara sukabar unguwar....
Gida ne Mai kyau Dan karamin daidai zamansu da Dan madaidaicin parlor Mai kujeru set daya da dining area yayi kyau sosai tare sukai gyaran gidan da haris da al'ameen har suka Gama sanan suka fice tare...
"Innah nikam bansan da wani Baki zamuyi wa haris godiya ba"
.jinjina Kai innah tayi "wallahi kuwa hidimar tayi yawa ummaty nikaina narasa bakin magana saidai muce Allah ya saka mishi da alheri"
Kwalla ce ta ciko a idanuwan ummaty ta marairaice "innah yanzun shikenan bazan sake ganin ya zainul ba?wallahi nadamu jiya har mafarkinsa nayi bansan halin da yake ciki ba innah Allah sarki Babu me tayashi Hira innah"....shiru innah tayi tana sauraronta tausayin Yar tata ya Kara kamata sai ta danne Dan kada ta karya mata zuciya "hakuri zakiyi ummaty kiyi addua idan kinada rabon Kara rayuwa dashi zakiyi ummaty Koda zumunci ne Dan zainul abideen yanzun yafi karfinka kinji?"...gyada mata Kai ummaty tayi Tana share kwallar dake zubo Mata dai dai Nan haris yayi sallama hannunsa dauke da take away biyu da drinks da sallamarsa ya shigo innah ta karba Masa cike da kulawa....
*******
Bayan sati daya da faruwar lamarin cikin kankanin lokaci zainul abideen ya warke tasss sai Dan abinda baa rasa ba domin yanzun da kafafuwansa yake takawa kowa sai Sam barka yakeyi..
Ta fannin gimbiya rumana kuwa ta Gama haukacewa hade da furgicewa dik Wanda tasa binciken ummaty baa samu inda suke ba gashi abubuwa sunyi mata yawa ta rame sosai ta danyi Baki tunda ta ziyarci wajen bokanta ya sanar da ita ta tabbatar da ta samu yarinyar Nan domin Nan da kankanin lokaci asiri zai iya tonuwa...
Cikin tsananin tashin hankali take duban yusha'u Wanda yake durkushe a gabanta "yusha'u idan har kasamomin inda ummaty take to tabbas nayi maka alkawarin gida harda kujerar makka matukar ansamu abinda akeso ka kokarta"
"Ranki ya Dade dik garin Nan Babu inda ban leka ba neman su Amma bansame suba hatta unguwar da suka Bari nayi bincike Babu Wanda yasan inda suka koma ranki ya Dade dikda an tabbatar mun ba garin suka Bari ba"
Sintiri ta shigayi cikin patlorn tana shawagi dik ta fita hayyacinta babban tashin hankali take ciki tasani tabbas bokanta bai taba buga kasa ya fada Mata karya ba to yanzun menene abunyi?"
*******
Shigowar haris ya Sanya momy dago idanuwanta ta cikin farin glashi tana watsa Masa harara sanan ta kalli agogon hannunta "karfe nawa yanzun haris?daga Ina kake?shin Wai ma in tambayeka kasamu aikine yasa cikin sati dayan Nan baka wuni a cikin gidan Nan?idan ka fita tun safe sai dare bansan gidan uban da kake zuwaba"tayi kwafa,
. Shafa Kansa ya shigayi ya sani bashi da ta cewa Dan beda gaskiya Dan haka sai ya kaskantar da muryarsa "kiyi hakuri momy wallahi kwana biyun Nan muna can inda al'ameen yake gini muna lura da wajen kinsan ya kusa sure momy"