← Book details Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 49

Sashe 11

Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murya na rawa ta Kara dubansa "ya zainul kafadamun menayi maka yau kaki kulani wallahi hankalina ya matukar tashi ya zainul kaji?na Bata maka Raine?idan na Mata maka Rai kayi hakuri bazan sake ba"Tai maganar tana shasshekar kuka,kamar daga sama ta tsinkayi muryarsa a dishe
"Ummaty babu abinda na tsana a rayuwata sama da injuya gefen dama da haguna bangankiba,banji motsinki ba sanan Banga ko inuwarki a kusa Dani ba,tun bayan tashina jiya da yamma bangankiba zuciyata bataimun Dadi ba,naso ace Naga tafiyarki munyi sallama dake shine zaisamun salama da kwanciyar hankali"share hawayenta tayi ta sauke sassanyar ajiyar zuciya,
"Kayi hakuri ya zainul kasan yanayin tafiyar tawa,da yamma tayi nake haramar tafiya gida kafin magriba ta riskeni Akan hanya,da Naga kana bacci shine kawai banyi yunkurin tashinka ba na kimtsa natafi kawai kayi hakuri daga yanzun ko dare zankai inhar kana bacci bazan tafi inbarkaba batare da munyi sallama ba"

"Yanzun wanan hawayen na menene kikeyi?umm?

Turo Baki tayi "ba Kai bane tunda Nazo kaki kulani sai dauremun fuska kakeyi?Kuma fa da har naji tsoro nafara tunanin kila kadaina kula ni ne"

"Komi girman laifin da zakiyi ummaty baxaki tabayin laifin da ni zainul abideen zan kasa bude Baki inyi Miki magana ba,bazan jure ba bazan iyaba,bana tunanin akwai wanan ranar a rayuwata Koda kuwa kinyimun babban zunubin da ya dace ingujeki infita hanyarki,Amma bazan iyaba....shin tayaya ma zaayi nakasasshe kamar ni ingujeki ummaty?dik fadin duniyar Nan bayan iyayena yanzun Kam banida tamkarki ummaty...babban tashin hankali bai wuce idan na tuna watarana Zaki aure kibarni ba a cikin wanan halin ,nakan tsinci kaina cikin tsananin takaici da bakin ciki,duniyata takanyi mun duhu komi bana iya gani bana iyaji,dikda nasan wanan ranan tana zuwa,Amma burina be wuce inhar ban warkeba zuwa lokacin to Allah yasa in mutu in huta..."

"Shhhhh ya zainul banason Jin wanan kalmar daga bakinka karkasake fadamun irinta idan ba hakan ba Zanyi fushi Kuma Zanyi kuka"Tai maganar tana shagwabe fuska,

Murmushi yayi "banason hawayenki ya diga ko kadan ta dakililina Dan ban cancanci hawayen kyakkyawar budurwar yarinya kamarki ya zuba akan nakasasshe kamata ba,Niba kowa bane yanzun a wanan duniyar,dani da babu dik daya ne tunda babu wani Abu na amfani da nake amfanawa alummah sai ma wahala da nake Basu"sosai tausayinsa ya kamata ta matso daff dashi tasa bakinta daidai fuskarsa ta hura Masa iska ya lumshe idanuwansa ya budesu lokaci daya Yana kallonta,

"Ko bakada amfani a wajen jamaa,to kasani ni kanada amfani a wajena ya zainul Dan inada yakinin tabbas zaka warke zaka Kuma taka doron kasa insha allahu"...murmushi yayi Wanda iya fuskarsa ya tsaya,wani irin zafi zuciyarsa takeyi Masa dik lokacin da ya kalli Kansa ya ga bashida wani Abu da yakeyi Wanda ya wuce zaman daki,kwanciyar kan gado sai cin abinci,Kashi da fitsari dik taimaka Masa akeyi wajen yinsu,me yakai wanan bakin ciki a wanan rayuwarsa?abubuwa biyu da ko wani Dan Adam idan zai yisu sai ya kadaice shi sai an taimaka Masa,tunda ya taso ya girma ya tsinci Kansa kwance a gadon jinya har zuwa wanan lokacin shekara da shekaru saanninsa dik suna karatu wasu ma sun Gama Amma shi gashi kwance a gadon jinya....hmmmm baa mamaki da ikon Allah Dan shi ikon Allah sai kallo,babu abinda zaice a rayuwarsa saidai kawai alhamdulillahi...ya lumshe idanuwansa ya Dade kafin ya budesu sunyi jajir ya saukesu akanta yaga itama shi take kallo fuskarta tamkar me Shirin yin kuka,

"Ya zainul lafiya?kayi shiru sai tunani kakeyi fa,dubi yadda idanuwanka suka canja kala lokaci kankani haba ya zainul"

"Ummaty tunanin rayuwata kawai nakeyi yadda nakeyinta,sanan babban damuwata yanzun be wuce yadda kika kashe karatunki tun bayan Gama secondary dinki last year Baki koma makaranta ba kina Nan zaune tare Dani babu dare babu Rana Anya ban Shiga hakkinki ba kuwa"

Girgiza Masa Kai tayi "baka Shiga ba ya zainul kadaina wanan tunanin ka kwantar da hankalinka kawai har Allah ubangiji ya amshi adduarmu ya baka lafiya kaji".

"Ameeen ummaty Allah ubangiji ya Nuna min wanan ranar ya bani ikon saka Miki da abinda kikaimun in kula dake tamkar fiyya da afnan da Aysha kannena na cikina kinji?"farrrrr Tai da idanuwanta ba karamin kyau Tai Masa ba,baisan lokacin da ya tsinci Kansa cikin sakin murmushi ba,

Zahira ce tai kasa da murya yadda babu Wanda zai jiyota,"Anya kuwa ummaty da ya zainul ba soyayya suke ba warisah"

"Natayasu murna idan ma soyayyar sukeyi Dan sun dace sosai tunda akwance yake ita Kuma kwadayi na bibiyat shegiya"

"Ni Kam ya zainul na balain yimun kyau warisah"....wani kallo warisah Tai Mata sanan ta saki wani malalacin murmushi,

"To ko kina cikine?idan kinaciki kawai akai magana wajen Mai martaba a hadaku aure Kinga jinyar ta dawo hannunki kenan,idan Kuma dukamku kukesonsa Mai martaba zai aura muku shi Dan nasan tabbas Neman nayi akeyi dashi"

"Amma kinsan wani Abu kuwa?wallahi ya zainul da lafiyarsa kalau har dambe Mata zasuyi akansa,saboda koba komi shidin kyakkyawa ne uwa uba ga mulki ga dukiya ga Kuma sarauta da yakedaita Kinga ba karamin farin jini zaiyiba"

"A wajenki kike ganin hakan,ko Kuma kina cikin wadanda zasuyi damben akansa koh?"tabe Baki tayi Tana ci gaba da tazar gashin kanta dake kwance agadon bayanta,

"Rabani da zancensa ki kakomin wani zancen Dan baya gabana ko kadan zahira,Dan ni Ina mantawa Allah yayi ruwan tsiransa a cikin gidan Nan wallahi,ni Banda ammiey ta hanani tafiya da tun jiyan nasan inda dare yamun,Dan haka ki rabu Dani da zancensa"

Murmushi kawai zahira tayi ta ta lumshe idanuwanta ta budesu tana ayyana abubuwa da dama cikin zuciyarta...

*******
Mai martaba ne tallabe da zainul a jikinsa Yana karewa Dan nasa kallo cike da so da kauna,dik wata gaba ta jikinsa ta sadarwa wadda take bugawa hade da numfashinsa to tana bugawa ne tare da soyayyar da'nsa kwaya d'aya dilo jinin jikinsa Wanda ya dauki so da kauna na dik duniya ya Dora Masa,ya dauki buri masu yawan gaske Akan wanan da'n nasa daya tilo sai kaddarori da jarabawa tazo mishi a hakan,Amma hakan besa yaji son dam nasa ya ragu cikin zuciyarsaba,sai ma karuwa da yakeyi fiye da baya ga tausayi irin na iyaye na da da mahaifi da yakeyiwa Dan nasa,kallon da yakeyi Masa ko kiftawa bayayi yayi yawa,...gefe da gefenshi Zahra ce babbar yarda sai me bi Mata halima sai gefensu gimbiya rumana ce cikin Shiga ta alfarma Tasha alkyabba irin na matan sarakai na wanan lokacin,

Halima ce ta dubi mahaifin nasu tace"Abbu wanan kallon yayi yawa da kakeyiwa zainul sai kasa dik yaron yaji wani iri ya fara daukar Kansa wani abun na daban ranka ya Dade"Tai maganar cike da tausayawa,...Zahra ma karbe zancen tayi "idan anayi Masa hakan ana karayar Masa da zuciya ne Abbu sai yaga tamkar shidin bazai warke ba kamar kowa"

Murmushi irin na manya Mai martaba yayi ya dubi gimbiya rumana dake tsaye tana famar sheki tana zuba kamshi "kinji abinda yaranki suke cewa Akan kaminsu ko?basaso Ina karya mishi gwiwa Wai"

"To ai Kaine ranka ya Dade gaskiya baayin haka,yaro ai karfafa Masa gwiwa akeyi yadda ka kafesa da Ido ai saikasa yarona yayi kuka ka rungumesa tamkar jariri umm?bayan yarona ya girma?inasaka ran idan ya warke yayi aure insamu jikoki?kaga ranka ya Dade Bari ma in koma kusa da abuna ga abincinsa Nan inbashi yaci ya koshi ya kwanta ko zainul?"ta karasa maganar tana kallon kwayar idon zainul din ,sai kawai yayi dariya dukkansu Suma dariyar sukai ,halima ce ta duka da kanta ta Shiga zuba abinci a plate ta mikawa ummahnsu ta zuba ruwa a glass cup Shima ta Mika mata.gimbiya rumana da kanta take bashi abincin har ya koshi ,dik abinda sukeyi da dramar da yakeyi idan yanacin abinci dik mahaifinsa na tsaye akansu Yana kallo Yana famar zuba murmushi soyayyar iyalinsa na Kara Shiga zuciyarsa...

A tare suka fito dakin,a kofar daki ummaty ke tsugunne yayinda gimbiya rumana ta kalleta fuskarta dauke da murmushi,ummaty ta gaidata ta amsa cike da kulawa har sunyi gaba ta sa baiwarta ta dawo ta sanarwa da ummaty akan idan zata wuce gida ta biyo sashinta zata bada sako takaiwa innarta.

*******
Yammaci nayi ummaty ta Shiga haramar tafiya gida musamman da ya kasance yau garin akwai hadari hadari kada ruwa ya rutsata,dik inda hankalinsa yake a tashe yake babu abinda ya tsana sama da yamma nayi ummaty ta fara hada kayanta na tafiya gida,gashi yau garin akwai hadari ba yamma bace tayi Amma gida take haramar tafiya Dan kada ruwa ya tareta,
"Ya zainul kaga akwai hadari kaji?kayi hakuri zuwa gobe insha allahu da wuri zan shigo zan xauna har dare babana zaizo ya tafi Dani kaji?"Jin hakan yasashi Dan sakin fuska sukai sallama ta fice.

********
Durkushe take a gaban gimbiya rumana zuciyarta sai lugude takeyi Mata tamkar zata tsaga kirjinta ta fito,ta rasa dalilin dayasa ta tsinci kanta cikin wanan yanayin na tsananin tsoron matar,kodan jiya ta zare Mata Ido ne yasa hakan oho Allah yasadai ba laifi ta sakeyi ba Dan harga Allah yanzun ummaty ta tsorata,

"Akan maganar jiya da mukai dakene Akan ciwon yarona zainul abideen"gaban ummaty ya yanke ya Fadi,
"Kamar yadda na fada Miki zan tuntubi mahaifinsa Akan ciwon nasa da mukai magana kikace bana asibiti bane na gargajiya ne shine nai Masa magana"
Ummaty ji tayi tamkar ta saki fitsari saboda tsananin tsoro,
"Be amince da hakan ba ummaty Amma ni tausayin yaron nakeyi har cikin Raina ummaty"idanuwan gimbiya suka kawo ruwa tamkar zataiyi hawaye,...ummaty ta natsu tana saurarenta,
"Dan haka na yanke shawarar nemawa zainul abideen magani Kota halin Yaya ne inhar zai warke banida farin cikin daya wuce hakan,na kwana da tunanin abun a zuciyata,sanan na auna hankalinki da natsuwarki nasan bazaki tabayiwa zainul wani Abu na cutarwa ba,...shiyasa na yanke shawarar nema Masa lafiya cikin sirri tare dake tunda mahaifinsa be yarda da wani maganiba sai na asibiti,Kuma Kinga rukon yaron Nan a hannunna yake tun Yana yaro ummaty,nasan uwarsa tanasonyi Masa magani Amma tanayimun Kara irin na hausa fulani shiyasa tasa Ido"
Chapter 11 · 0% Book details