← Book details Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 49

Sashe 1

Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[1/23, 10:30 AM] 😍SLIMZY😍: *HASKE WRITERS* *ASSO...💡*

💞 *ZAINUL ABIDEEN💞*

*SLIMZY✍🏼*
*Wattpad@slimzy33*

*1*

Daga zaunen dayake saman wheel chair ya d'ago ido yana kallon ta yana saukar mata da murmushi me sanyaya zuciya, Tabare masa fuskar nan tayi wane zatae kuka

"Amma ni Yaa zain banace wai idan kanajin wannan abin ba ka dinga adu'a dan Allah" kanshi dayake a karkace ya k'ara juyarwa yawun bakin nashi suka k'ara gangarowa zuwa saman kirjin sa, da sauri ta sanya tissure ta share masa su ta wurga a kwando, lokaci d'aya k'wallan datake k'ok'ari tarewa ya silalo mata da sauri ta sanya bayan hannunta ta d'auke shi tana me kawar da kanta karya gani, wani azababben bak'in ciki ne ya taso mata ya tokare mata k'irjin ta zuwa wuya, da k'yar ta had'iyi wani yawu me d'acin gaske sannan ta furta

"Sannu yaa Zain, yanzu inane yake maka ciwo?" Kasa magana yae sabida abinda yakejin yana taso masa yana danne masa mak'oshinsa da k'yar yake numfashi ma, hannunsa yakai yana shirin mak'ure wuyansa da sauri ta rik'eshi ta soma karanto masa adu'o'in tsari tun yana k'ok'arin qwacewa harya hakura ya lafe tayi ta masa adu'a kusan 15mns ko ita gumi takeyi, seda taga ya lafe alamun yashiga duniyar bacci sannan ta sakeshi tasoma kuka wiwi tamkar wata zararriya, tausayi sosai yaa Zain yake bata d'an sarki guda d'aya, lamarinsa kullum sekace me ciwon iska, tayi wa Sarauniya maganar amasa na gargajiya amma ta kafe akan haka Allah ya haliccesa, wane ciwon ne bashida magani?" Jansa tayi zuwa cikin b'angaren sa har tsakiyar d'akinsa sannan ta kira fadawan sa suka kwantar mata dashi, kallon bafade d'aya tae tace dashi

"Nasan halin baccin sa baze wuce 1 houf ba bari zanje na dawo, idan ya farka kafin 1 hour ka aika akirani" tana gama fad'ar haka ta juya ya bita da harara, an baiwa yarinyar nan dama da yawa, harsu take commanding irin haka?.....

********
Hararar sa ta keyi sosai, yanayin kallon dake idanta kurin ya isa ya sanya kasha jinin jininka, sadda kanshi yae a k'asa cikeda rotso, besan kose yaushe ze dena tsoron ta ba, besan kose yaushe zata dena shiga rayuwar sa ba, meya mata ne wai? Aduk fad'in masarautar nan bashida abinda ya tsana da gani sama da ita, gata sekace aljana duk inda yae idonta na kasan

"Idan abinda nake fahimta daidai ne kana nufin bazaka sab'awa waccem jakar ba kenan?, so kake ka nunamun kai kanada taurin kai da kafiya ko? Dacen dawa kake amfani bada 'yar taka ba! Se yanzu danka gama rainan hankali zaka ce wai baka san yan da zaka datse alak'ar tasu ba" D'agowa yae ranshi ba dad'i, xuciyarsa tamkar zata fasa k'irjinsa tayo waje yace

"Kece kike amfani da ita bani ba, tun faruwar al'amarin nan roqon meye ban miki ba akan ki sake kuruwar yaron nan? Ya kamata kisani nifa ba yaronki bane ba, banida kuma almakashin datse wannan alak'ar kece kike dashi, keda kima dasa alak'ar tasu tun suna jinjiraye"

Cikin baqin ciki tabishi da kallo

"Amma ba haka mukai dakai ba, wannan aikin tare muka faroshi kuma da sanya hanmun 'yarka da ita akayi komai ko kanaso ko bakaso, idan ma so kake lallai seka had'a aure a tsakaninsu ka sani zan fasa k'wai kowama ya huta" Yanzukam idan shi yayi ja jajir

"Bazan miki uzuri ba kika sako Ummaty acikin maganar nan, kece kika turata kece zaki warware komai, yanzu yara sunyi shak'uwar dabazasu iya rabuwa ba shine zaki tayarmun da hankali" A yamutse ta kallesa

"Da gasken kake mafarkin had'asu aure kake kenan, kasan Allah wlhy tsaf zan b'atar da Ummatyn inga k'arshen iskancinka" Mik'ewa yae daga zaman dayake ya bugi babbar rigarsa

"Ga fili gamai doki, wacce bata tsoron Allah kawai" yae ficewar sa,Koda ya fito hanyar fita yayi gidan gabaki daya saboda tsananin bacin ran da ya tsinci kansa....

*********
Tunda ta shigo gidan take kuka tamkar wadda aka aikowa da sakon mutuwa ko hijabin jikinta ta kasa cirewa neman waje kawai tayi gefen mahaifiyarta ta zauna Tana sharar hawaye....

Kallon ummaty takeyi cike da kulawa da tsananin tausayin Yar Tata,dakyar ta sauke gwauron numfashi takai hannunta kafadarta ta dafata ta Soma magana cike da kulawa, "ummaty lokaci yayi da Zaki daina zubar da hawayenki Domin rashin lafiyar zainul abideen,zuwa yanzun ya kamata ki fahimci cewar wanan lafiyar tashi daga Allah ce Allah ne kadai zai iya yi Masa maganin rashin lafiyar Nan tasa ba wani Dan Adam ba sai addua da zakiyi mishi na samun sauki daga ubangiji Amma kuka Babu abinda zai Miki sai Karin bakin ciki da damuwa da zai saki kinji ummaty?"ta karasa maganar cike da kulawa,

Idanuwanta sunyi jajir saboda kuka fuskarta jike da hawaye ta juyo ta dubi mahaifiyarta cikin shasshekar kuka "innah ki duba kiga halin da zainul abideen yake ciki Amma Mai martaba yakasa yin wani Abu dangane da rashin lafiyar ta dansa daya tilo namiji a cewarsa Wai rashin lafiyar ya zainul na asibiti ne bana gargajiya ba kullum saidai a daukesa a kaisa asibiti ayi gwaje gwaje a tilo magunguna a dawo batare da ansan takamai man abinda yake damunsa ba,yanzun Haka innah nabaro sa a kwance Yana bacci saboda ciwon nasa ya motsa dakyar nasamu bacci ya daukesa"ta karashe maganar cike da takaici ta Sanya hannunta ta share hawayen dake fuskarta,

Tsananin tausayi yasanya innah kasa magana kusan minti biyar idanuwanta na Kan Yar Tata Tana sauraren sautin kukanta dake fita,...ta lula duniyar tunani sallamar da sukaji CE dukkansu ya sa suka juya suna kallon hanyar shigowa,

Fuskarsa Babu walwala ya karasa shigowa cikin gidan inda suke zaune a tabarmar kaba a tsakar gidansu,yanayin fuskarsa kadai zaka kalla da kwayar idanuwansa kasan Yana cikin tsananin damuwa ,dukkansu hankalinsu na kanshi ganin yanayin nasa ba yadda ya Saba shigowa cikin gida ba,

Innah ce ta dubesa cike da kulawa tace "barka da shigowa sarkin dawaki"

"Barka"shine abinda yace mata a takaice,

"Ya Naga yanayin naka Sam ba a yadda ka fita ba ko wani Abu ya faru ne?"

"Babukomi kawaidai ranar garin ce yau sai a hankali kawomin ruwa insha"ya kauda maganar Yana Mai duban inda ummaty ke zaune wadda fuskarta Tai jajir saboda kuka....

"Ummaty lafiya na ganki haka?meyasameki fuskarki kamar kinyi kuka?"

Hawayen da take kokerin boyewa ne suka sulalo Mata a fuskarta tasa hannu ta goge hade da Jan hancinta,cikin sanyin murya irin nata ta Soma magana "baba wallahi dama rashin lafiyar ya zainul ce yau ma ta Kara tashi Dan yau bakaga abinda yayi ba wallahi gwanin tausayi baba"

Saida gabansa ya fadi Jin sunan zainul data ambata a bakinta Amma sai ya dake Yana Mai Kara fuskantarta"shine dik kikabi kika tada hankalinki kenan ummaty?ki kwantar da hankalinki zai samu sauki matukar Yana Shan maganinsa Wanda kike basa insha allahu zai samu lafiya kamar kowa kinji?"

Gyada kanta tayi ciikin sanyin jiki ta bude baki da kyar ta amsa da "Allah yasa"

"Ameeen"innah ta amsa da shi Tana Mai mikawa mahaifin nata ruwa....

*********
Tunda garin Allah ya waye yake kwance a Kan gadonsa Wanda saidai a kwantar saidai a tayar bakinsa Yana Nan yadda yake kamar kullum a karkace miyau na zuba a gefen rigarsa ya zurawa kofar dakin idanu...

Turo kofar da akayi ne yasa fadawan dake dakin saurin Shiga taitayinsu hade da zubewa kasa lokaci daya suna kwasar gaisuwa...

"Barka da zuwa ranki ya dade sarauniya rumana uwar gida a wajen sarki Mai martaba"

Hannu kawai ta daga musu cike da Isa da izzah Wanda indai sarauta ce kallo daya zakai ma wadda aka Kira da sarauniya ka tabbatar da ta amsa sunanta....

Gefen gadonsa ta tsaya Tana karewa zainul abideen kallo Wanda bemasan tanayi ba idan har idanuwanta ba gizo sukeyi ba to tabbas ko motsa idonsa yau bayayi da alamar ciwon nasa Yana kusa,

Cike da tausayawa ta sunkuyo daida fuskarsa Tana Mai dubansa cike da kulawa a Fili take fadin "Allah sarki zainul Allah ya baka lafiya kamar kowa kaji?Allah ya yaye maka wanan ciwon naka ya tashi kafadarka"Tana maganar ne Tana shafa gefen fuskarsa Wanda da alamu bemasan tanayi ba,

Takai minti goma Sha biyar cikin dakin da kanta ta dagosa ta jinginasa da jikin gado takai hannunta gefen gadon ta dauko wani farin towel me kyau ta Shiga share Masa miyaun dake zulalowa daga bakinsa hannunta daya na kansa Tana shafa kansa cike da kulawa,

Baiwarta dake tsaye ta dubeta "zubamun breakfast dinsa Dan da alama beci wani Abu ba"

Da sauri ta juya table din da aka jera kulolin abinci Wanda dama Nan ne ake aje Masa abincinsa dik lokacin da aka tashi bashi saidai a Diba,ta dibo abincin ta zo har kasa ta tsugunna ta Mika Mata...

Bude kofar dakin akayi da sauri gimbiya rumana ta juya suka hada Ido da Mai martaba sarki gefensa wata matace matashiya ke biye da shi sai fadawa da bayi dake take musu baya,

Murmushi Mai martaba yayi lokacin da yake karasowa gaban gadon na zainul abideen,"Gimbiya rumana uwar zainul abideen yau da kanki Zaki bashi abincin?lallai kinaji da wanan yaro naki"

Murmushi ta sauke "barka da tashi ranka ya dade"

"Barkanki,ya jikin Dan naki?"...Nan da Nan fuskarta ta canja idanuwanta suka kawo ruwa ta sunkuyar da Kai batare da tace komiba,

Ganin Haka yasa Mai martaba girgiza kansa tausayinta da soyayyarta na ratsa sassan jikinsa yadda ta shaku da zainul abideen take kulawa dashi komi nasa itace ko kyamarsa batayi mahaifiyarsa batayi Masa hakan,kodan hakan nada nasaba da yadda ta shaku dashi tun daga haihuwarsa?kasancewarsa shine da namiji a fadin masarautar?

*********
Tunda ya doso harabar sashinta gabansa ke tsananin faduwa saboda fargabar yadda zasu kwashe shida ita...

Da sallamarsa ya Shiga babban parlorn nata Wanda ya kasance Nan ne wajen sirrin su Babu kowa bakajin sautin komi sai karar fanka dake gudu a parlorn,

Gefen kilisa ya nema ya tankwashe kafa zuciyarsa na harbawa sauri da sauri Tana tsaye ta harde hannuwanta ta baya,

Dakyar ya lalubo natsuwarsa cike da fargaba yace "sakonki ya ishemun na son ganina Ina fatan dai lafiya kika aika kirana"
Chapter 1 · 0% Book details