← Book details Sirrin Keta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 47

Sashe 9

Sirrin Keta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*💫ANNURI WRITER'S ASS.*💫
(Annuri is the best)

*(A.W.A)*

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FEViiYLkmiwKIUEZc2PcLD

*SIRRIN QETA*

*Page* *5*

*by yar gatan annuri writers*

*Indo ce*

*بسم الله الر حمن الر حيم*!!

Ranan kwanan farin ciki reetaj tayi haka ta tashi zuciyar ta wasai,
Yaya muktar kuwa ai ya samu abun yi..
Tana zaune tana karatun alqur'ani Awaaz ta fado kanta ,
Zare ido tayi kafin tace wanne irin hauka ne wai haka ina karatu kawai ki jibgo min a ka gaki wata sambadediya dake, Awaaz tayi dariya tace gaskiya ina tayaki murna "yaya wallahi kin samu miji wanda ba babu kamar sa" murmushi Reetaj tayi tace Allah yabaki lafiiya Awaaz, Amin ta fada tana juya ido taci gaba da cewa wallahi yaya kina da sakaci ma allah naga kamar bakya son kulawa da yaya muhsin kamar ba.. Koda yake ke dama duk kanki sai a hankali wallahi yaya nifa banason abunda kike haba kamar ba wayis ba ?
Ture ta reetaj tayi tace keh ware can da yawarki ,
Nifa duk wannan iskancin naki bayi zan ba gwara kiyi shiru wani wayis can ni banason wayon y'an wuta,
Awaaz tayi tsaki tace bazaki taba gane wa ba wallahi yaya, wata rana kuwa zaki sa yagaji da wannan mugun ajin naki bama jan aji bane wannan kawai ke... To nayi shiru dai amma yaya yakamata ki dinga kulawa dashi yadda ya kamata,
Dogon tsaki reetaj taja kamar bazatayi magana ba tace kehh.. In dinga kulawa dashi shidin jariri na ne iyeh??
Mamin shi keda alhakin wannan bani ba kulawa kulawa wacce kulawa dai awaaz?
Tsaki awaaz tayi tace hakan dai.. Ke yaya wai bakya ganewa ne bawai wani abu fah kamar jariri ba kawai dai ki dinga nuna masa soyayya shine ki fahimta mana yaya dan Allah,
Murmushin takaici tayi tace kinga ni banada yanayin yin hakan kin gane??
Awaaz tace ai kiwa kina tare da wahala babu wanda ze soki da wannan duhun kan naki kamar baki taba shiga class ba,
Reetaj dai taji tayi magana amma bataji abunda tace ba dan haka tace me kikace??
Ba dake nake ba kawai kici gaba ,
Reetaj bata kara kula ta ba,
Har wani lokaci sannan suka fara hira awaaz bata sake sako mata maganar muhsin ba dan tasan fada zasu karayi ,,

Haka rayuwa taci gaba da tafiya lokaci yana kara wucewa kwanaki da watanni suna shudewa kullum dai awaaz bata da magana da ta wuce fadawa reetaj akan ta riki muhsin hannu bibbiyu ita kuwa gani take tinda dai tasan tana sonshi kuma da gaskiya da amana wace irin riko kuma zatai masa bayan haka,
Ita dai awaaz ta kasa fahimtar ta musamman da taga ansa lokacin auren su gashi har yana tawo wa,
Reetaj kuwa lamarin awaaz har mamaki yake bata tai ta tunane tunane da sake sake ta damu da muhsin fiye da zaton mutum ,
Yanzu ko shiri basayi sosai kullum cikin magana awaaz take ita kuwa reetaj sai ta nuna bata juri hakan ba,
Yauma sun fito zasu makaranta ta tsaya hira da yaran layin su awaaz ta fara masifa kamar ta cinye ta in banda abunki kizo mu wuce kin zauna kula wa yan nan kaskantattun yaran ga wanda ya kamata ki kuladashi kin kasa sai wasu banzaye,
Reetaj taji ba dadi amma sai ta danne kawai inda sabo ta saba da wannan halin na awaaz,

Akwana a tashi ba wuya da yardar allah lokacin bikin reetaj da muhsin yazo har ya rage sauran wata biyu .
Tana iya farin ciki amma sai dai akwai abunda ke damunta wannan kuwa ba komai bane sai canji da take gani a wajen muhsin nema yake ya koma wani muhsin din daban ba wanda ta sani ba abun yana damunta amma ta kasa fadawa kowa awaaz ce dama abokiyar hirar ta ita take fadawa matsalar ta to amma yanzu da ta fada awaaz cewa zatayi ita taja wa kanta ba wani ba idan batayi sa a bama ta iya cewa allah ya kara , tana zaune ita kadai a daki yaya muktar ya shigo,
Bata lura dashi ba har yaje kanta ya tambaye ta tagumin me kike? turo baki tayi tace ba komai, ki fadamin gaskiya shiru tayi,
Hakan yasa ya nemi guri ya zauna yace to yanzu fadamin naga kamar kwanan nan bakya walwala sosai ko akwai wata matsala ne,
Nifa nace ba komai yaya muktar meyesa kake damuna wai se kace karamin yaro ka fiye tsokana,
Toh shikenan nidai kar kije garin tunane tunane zuciyar ki ta buga yanzu ki mutu yarinya,
Murmushi tayi tace yaya muktar wai kai ance maka ni yarinya ce da wayo na fah bana tsoron mutuwa ni ai,
Oh hakan da kika fada yayi nuni da kina cikin damuwar dai kinga ko a yanzu na nuna miki wayon naki be kai nawa ke ba yarinya to ai nima ba yaro bane ko kin manta na girmeki??,
Yatsine fuska tayi tace wani giman ka can dame ka girme ni din har zaka wani nuna min zarrah? Giman da befi na minti bakwai ba,
A,ah minti daya da sakanni biyu,
Ya fada yana hararar ta, dariya ta danyi tace dududu shekara nawa kabani?? Shekara.... Duka ta kai mata yace ke dallah ba saikin fada ba so kike su (yar mutanen kt suji su raina ni...lol..)
Kwafa tayi tace da kabari na fada mana janta yayi da surutu har ta fara fada masa damuwar ta yaya muktar nifa wallahi duk muhsin ya canja kamar bashi ba,
Yanzu..

Mu hadu a comment
https://facebook.com/groups/575599953675542/

*💫ANNURI WRITER'S ASS.*💫
(Annuri is the best)

*(A.W.A)*

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FEViiYLkmiwKIUEZc2PcLD

*SIRRIN QETA*

*Page* *6*

*by yar gatan annuri writers*

*Indo ce*

*بسم الله الر حمن الحيم*

Yaya muktar yanzu fa kwata kwata kamar be damu dani ba ko kirana da yake daa, yanzu bayayi nifa gaskiya abun yana damuna kuma na tambaye shi ko laifi nai masa amma yace babu komai yaya ina tsoro kodai ya dena sona ne ? Yanzu kenan ya zanyi idan hakan ta faru?? Shiru yaya muktar beyi magana ba. Hakan yasa ta dago kai tana kallon sa shima idon sa na kanta ya ware su tarr a ka naga ganin ya kame ne yasa ta kama hannun sa ta jijjigashi tana cewa kayi magana mana kayi shiru,
A hanun nasa da ta rike taji jijiyoyin sa suna tashi dan da nan idanun sa suka fara rinewa zuwa kalar jaaa,
Nutsuwar ta ta mayar kansa a matukar tsorace anan ta fahimci yadda zuciyar sa ke bugawa da karfi kuma cikin sauri sauri,

Hankalin ta ya fara tashi, da kyar ya samu ya yaki zuciyar sa da take bugawa a dari da sittin yace reetaj ina zuwa zanyi magana dake in anjima yanzu bana cikin yanayi,
Cikin mamakin abunda bata taba gani daka yayan nata ba tace yaya toh wai hakan me yake nufi baka da lafiya ne? Kai kawai ya iya girgiza mata. tace ohh na gane ranka ne yabaci ko?? Marairaicewa tayi tace hakuri mana yaya nifa ban zata ranka ze baci haka ba ai ba sai ka damu har haka ba yaya kawai ma ta wuce ni banida wata damuwa, ya gyada mata kai yace idan nasha ruwan sanyi zanji dadi ina zuwa,
Yaya to ka tsaya in karbo maka a wajen umma ,
Rufamin asiri kar kije dan allah,
Da mamaki tace meyesa dafe goshi yayi a kagauce yace kin fara damuna reetaj idan kikaje suka ce miki bacin ran me nake kice musu me??
Lakwas tayi kafin ta kara wani kokari ya fice a dakin da daddafe bango ya samu ya sirare ya kwarare ya zirare ya fece daka cikin gidan dan gudun kar wani yaga halinda yake ciki,
Da fari reetaj tayi mamaki kuma tayi jimami gami da tunani kala kala amma washegari da tagan shi tangaras ta tabbatar wa kanta kalau yake kawai dai bacin ran ne ,

Kamar dai yadda reetaj ta fada ba abunda ya canja saima kara cigaba yake,
Chapter 9 · 0% Book details