← Book details Sirrin Keta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 47

Sashe 8

Sirrin Keta Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Wannan ta wuce a kwana a tashi muhsin da yake me wayo ne da dabara ya gama siye zuciyar reetaj sosai take sonsa abun yayi wa awaaz dadi sosai ko babu komai yayar ta zatayi aure su huta da mitar kakar su da yayan su da kuma bakin mutane
A haka har tafiya tayi nisa kowa yasan da batun muhsin a dangin su haka shima nashi barin duk sun san labarin ta sunyi sabo sosai suna shan soyayyar su sai dai ba ko yaushe reetaj take son surutu ba ko takurawa shiyasa wani lokcin idan ya kira sai dai ta bawa awaazhaka kuma duk maganar da sukai dashi sai ta fada mata dan amintar dake tsakanin su tafi karfin kawaye koh yaya da kanwa ,

https://facebook.com/groups/575599953675542/

*💫ANNURI WRITER'S ASS.*💫
(Annuri is the best.)

*(A.W.A.)*

*SIRRIN QETA*

Page 4

*by yar gatan annuri writers*

*Indo ce*

*بسم الله الر حمن الر حيم*

Da misalin 9:26 suna kwance awaaz tana kallo suna ta'ba hira kadan kadan wayar reetaj tayi qara dauka tayi ganin muhsin ne yasa tasaki murmushi,
Dagawa tayi takara a kunne bayan sun bata lokaci suna wayar har ta fara gajiya sannan sukai sallama kallon awaaz tayi tace,
Awaaz wai yace gobe mu shirya wai zanje mugaisa da mamin sa.
Murmushi awaaz tayi tace toh meye kuma naga kina... Ke dallah ni ba abinda nake kawai ni kunyar zuwa nake ma. Yar dariya tayi kafin tace kaji fah wai kunya kunyar zuwa to ranan da aka kaiki cikin su fah?? Babu wata kunya kawai ki shirya da wuri ni idan na tashi ma wuni zanyi ina kwalliya ta gama magana tana dariya, duka reetaj ta kai mata tana cewa kefa bakida hankali , kaucewa tayi tana cewa a to ni meye nawa a ciki mudai yan tayi dadi da ze temaka ma yasa mana auren nan da sati biyu da nafi kowa farin ciki, pillow ta dauka ta maka mata tana cewa dan ba bikin ki bane muguwa to sai an tiga naki kafin nawa ko kuma a hada lokaci daya,
Tabe baki awaaz tayi tace kina kokko.. Ni bari ma kiga yanzu zanje in fadawa umma da ammah gobe zamu fita tashi tayi tana rawa tare da wakar (kahona pyaar hai) har ta fita reetaj kallon ta kawai take cike da takaicin iskanci da take mata kamar wata kakar ta ko abokiyar wasa ,
Jin yar dariya kasa kasa yasa ta waiga su fatima ta gani suna kishin kishin filo ta dauka ta wurga musu tana cewa ni sa'ar ku ce dan me garin ku salma filon yafi samu ta miqe tana cewa allah ya isa na,
Reetaj tace me kika ce bansani ba ta fada kafin tayi hanyar fita, jikin reetaj yayi sanyi sosai tabi salma da kallo fatima kuwa kyakyacewa ta kara yi da dariya reetaj ta harare ta tace, banace kude dariyar banzar nan ba ko mahaukaciya kuka maidani?? Bata dena ba saima ci gaba da tayi tsura mata ido reetaj tayi tana tunanin yaushe da wane lokaci suka raina ta haka ?? Ashe dai da gaske idan mace batayi aure akan lokaci ba kimar ta raguwa take gashi dai qiriqiri salma tana mata allah ya isa abun kamar a mafarki yaune karon farko da tafara kwadayin taga tayi aure bayan abubuwa iri iri da suka shude zuciyar ta tafara kunci kawai sai ta danne ga dariyar da fatima take tana qara tunzura ta amma kawai sai tayi shiru har cikin ranta bataji dadi ba neman yin kuka take awaaz ta shigo tana murna ,
Dariyar fatima ce ta fara katse ta ta kalli reetaj tace lafiya dai me akai ganin babu alamun wasa ko walwala a fuskar yar uwar ta yasa ta kalli fatima tace ke dan uwarki dariyar me kike shanye dariyar tayi tace abun dariya akai, kanta awaaz tayi ta kama ta ta dirka mata duka a baya, ai kuwa ta fashe da kuka tayi hanyar fita , awaaz tace sai naci ubanku marasa mutunci ai tinda naga salma tana murgude murgude ita kadai nasan da abunda sukayi,
Zama tayi kusada reetaj tace yaya na fada masu sunce allah ya kaimu har ma da addu'a sukayi mana ,
Murmushi ta kakalo tace to jeki kiyi kallon ki kawai ni kwanciya zanyi batayi musu ba ta koma ta kwanta
Har bacci ya fara daukar ta yaya muktar yazo yaye dan mayafin da ta lulluba dashi yayi yana cewa kehh! Ke!!! Matar muhsin tashi mana,
Tana jinsa tayi masa banza tana takaicin yaye mata lullubarta da yayi zama yayi gefen ta yana cewa wai sai ta kama ta lullube ta kudundune a zafin nan kuma a hakan bacci zatai awaaz tace a haka ma zata kwana, tsaki yayi yace ai kuwa wataran zaki mutu a cikin malullubi, turo baki tayi tace yaya muktar nifa ba iya bacci idan ban lulluba ba, yace kuma a lokacin zafi allah ya baki lafiya mahaukaciya, tace amin ai addu'a kayi,
Toh ni ba addu'ar ce ta kawoni ba maza tashi kije ki zubomin abinci, abinci kuma da tsohon daren nan ?? Ance miki dare yayi ne ? Ko da yake kin lullube fuska ba dole kirasa ina kanki yake ba ? Tace ina sane ai a hayyaci na nake , dariya yayi yace toh yimin kwana kinji maza cene karya nayi, sakkowa tayi tana cewa ni bance ba. Maida hankali yayi akan awaaz da ta kurawa waya ido ga iyafis a kunne , duka ya d'ad'a mata yace shiyasa kanki yake ciwo ai dare yayi me makon kiyita tasbihi da istigfari sai ki zauna kina kallo a waya! Zakizo kice kanki na ciwo inba ko sannu yarinya ,
Reetaj tace yauwa yaya muktar shiyasa nake son gaskiyar ka haka take kullum batada aiki sai kallon wasu banzayen yan india da yan america bama kamar yan indian ma da dogayen kafafun su,
Dariya muktar yayi yace lallaima bama ni kike so ba gaskiya ta kike so koh ?
Awaaz tace eh mana yaya ai bata sonka dama nasani ai idan na fada bazaka yarda ba"
Tana magana tana susar cinyar ta inda ya doke ta reetaj tace kidai ji da susar cinyar ki,
Langabar da kai tayi tace yaya muktar gaskiya hannun ka akwai zafi wallahi gaba daya wajen rad'ad'i yake ,
Yace haka nake so ai kamar ma wani ya sakoki cikin zancen idan ma bata sona ina ruwanki meye naki a ciki ? Tsakanin mu nida itane kuma ko shaidan bashida guri"'
Reetaj tayi dariya tace gaya mata dai yaya na na kaina,
Gwatsile fuska awaaz tayi tana maimaita abunda reetaj tace kafin tace kema ze dawo kanki ne ,
Reetaj tace inaaa yarinya ai bama fada nida yayana na gold tabe baki yayi,
Suka cigaba da hira babu zato babu tsammani ya daka mata tsawa ta firgita tuni tayi kasa rajaf ta zube ,
Awaaz ta tuntsure da dariya, reetaj kuwa kokarin tashi tayi tana rike kugu tace haba yaya muktar meye hakan dan allah ware idanun sa yayi akanta yace dan iskanci ba tin dazu nace ki kawomin abinci ba kikaqi ,
Shagwabe fuska tayi tace toh ai babu abincin ma mun cinye" kam bala,i ai kuwa wallahi da sai kin dafamin wani a daren nan,
Turo baki tayi tace to dawasa ma nake, yace kimayi da gasken fita tayi ta kawo masa yace yauwa nagode matar muhsin,
Kwanciya tayi ta ja abin lullubar ta tace idan ka gama tsokanar sai da safe,
Washe gari tin da awaaz ta tashi take falli taqi zama waje daya sai sukursukur take tana herere,
Reetaj kuwa duk jikinta a sanyaye yake bazatace bata murna da zuwan ba bazatace tanayi ba,
Misalin 3:00 yayi parking a kofar gidan su kiranta yayi ta dauka yasanar da ita cewa yazo toh kawai tace,
Awaaz tace yaya kefa yanzu se kinyi wannan mugun jan ajin naki gaskiya tashi mu tafi, ko kulata reetaj batayi ba tacigaba da buga game awaaz kuwa hoda ta qara tasha kwalliya sosai ,
Tayi kyau sosai
ita kuwa reetaj daka hoda sai man le'be da kwalli batayi wata kwalliya ba
Saida awaaz ta dameta da naci sannan ta dauki hijab ta zura tsakar goda ta fito su umma suna zaune suna hira jikin bango ta rabe kamar zatayi kuka tace umma zamu tafi murmushi umma tayi tace toh allah ya kiyaye kuce muna gaisa su ,
Ammah ma murmushi tayi har cikin ranta takejin farin ciki tareda fatan aurar da y'ar tata nasiha tayi musu umma ma ta dora akai kafin suyi musu addu'a sannan suka fita,
Ganin sun fito yasa ya bude mata gidan gaba mazaunin dan zaman banza amma sai tayi kamar bata gani ba ta bude baya ta shiga, awaaz tace yaya? Kishiga gaba mana, tace ke barni anan awaaz tayi tsaki tace bara ni in shiga toh, reetaj tace kishiga mana maza, muhsin yace yauwa kanwa ta kyaleta tinda bataso,
Awaaz ta shiga gaba batareda wani darr ba takaici ya hana reetaj magana ,
Hira suke sosai harda zolayar ta ita dai sai dai tayi murmushi,
Haka har suka isa
Muhseena tanajin hon din dan uwanta ta fito da gudun ta kai tsaye gaba ta nufa ta bude awaaz murfi tana murna,
Awaaz kuwa yauqi kawai take tana wani murmushi wanda ita da mahaliccin ta ne kawai sukasan ma"anar, sa
Zagayowa muhsin yayi yace wato kinga auntyn ki har kin manta dani koh??
Dariya tayi tace eh mana kaida kullum tare muke kwana,
Ganin ya bude bayan motar ne yasa ta saki baki tana cewa yaya toh banda abunka me zaka dauka a nan tinda ga anty na ?
Ganin awaaz ta fito yasa tayi shiru tana binsu da kallo ta kalli awaaz ta kalli reetaj,
Awaaz tace toh ga antin taki nan,
Maida hankali tayi kan muhsin tace yaya da gaske?
Gira ya daga mata
Tayi sufa ta rungume reetaj har saida suka kusa faduwa,
Dariya kawai reetaj keyi lokaci daya taji muhseena ta shiga ranta ,
Jan hannun ta tayi suka shiga gidan tana kwalawa mamin su kira mami ta fito tana fara'a cikin murna ta doso inda suke,
Reetaj dai sunkuyar da kai qasa tayi mami ta kama hannun ta ta kaita gurin zama ta zaunar da ita,
Itama ta zauna sannan tace sannun ku da zuwa awaaz ce ta amsa reetaj kuwa shiru tayi,
Muhseena tace mami kunyar ki fa takeji gaskiya surukar nan taki ta hadu mami,
Mami tayi dariya tace jaa"ira kefa in aka biye miki baza ai wani abun kirki ba,
Gurin muhsin ta koma tace yaya wai dan allah karya nayi ai gaskiya nake fada koh?
Yace eh mana
Mami tace kai da allah kuyi shiru mu gaisa kun cika mata kunne da surutu,
Shiru sukayi kafin reetaj tace ina wuni
Mami ta amsa tana qara fadada fara'ar ta tace lafiya lau ya mutan gidan ya manya?
Reetaj tace lafiya lau,
Masha allah ya fama da yara nasan shi akwai takurawa ta fada tana kallon sa,
Reetaj tayi murmushi
Shi kuwa cikin shagwaba yace kai mamina nifa ba yaro bane,
Mami tace eh mana ai naga alama,
Awaaz ma gaishe ta tayi ta amsa tareda tambayar ta yasu umma tace lafiya lau,
Tashi muhsin yayi ya nufi dakin sa
Mami tasa aka cikasu da kayan ciye ciye da na sha bata sake taci ba dan ba maramin kunyar mamin takeji ba,
Muhseena kuwa surutu kawai take zubawa awaaz tana taya ta mami tayi qoqarin jan reetaj da hira sai dai taqi magana sai dai murmushi kawai,,,,
Har suka tashi tafiya.
Tasha kyaututtuka daka mami harma da muhseena awaaz ma ba"a barta a baya ba bayan sunje gida a gajiye take shiyasa,
Kwanciya kawai tayi tana hutawa kafin wani lokaci ,
Ba wanda awaaz bata bawa labarin halaccin da mami tayi musu da karramawa ba sunji dadi sosai
Kuma muhsin ya qara daraja a wajen su ,
Ita kanta reetaj ji take kamar tafi kowace mace sa'ar miji da dangin mijin ma"
Idan ta tuna murmushi kawai take tanajin soyayyar sa har cikin qashin ta,
https://facebook.com/groups/575599953675542/
Chapter 8 · 0% Book details