← Book details Sirrin Keta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 47

Sashe 6

Sirrin Keta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar yadda awaaz ta bawa muhsin shawara yayi amfani da ita kuma ya cima nasara
Baka tatan abba yaji anzo wajensa neman aure har da bada shedar sun fahimci juna kuma suna son junan su abba yayi farin ciki matuka yasa albarka tareda sallama musu reetaj abunda yarage kawai sa ranar aure da sauran al'adu bayan wani lokaci kuma a daura aure,, suna kwance awaaz tana aikin kallon indian film reetaj kuwa duba sakon whatsapp take amma tayi sallama tace kuzo inji abban ku gaban ta ya yanke ya fadi dandanan jikinta yayi sanyi haka kawai dakajin kiran taji ajikinta akwai matsala awaaz kuwa tasan komai dan haka tayi saurin durowa daka gado tana cewa abban namu sabbin kaya yasiyo mana ne? Ammah
Idan mukaje kya gani keh taso mana reetaj kinaji kuma kinyi zamanki, jiki ba kwari ta sakko suka rufawa ammah baya can gefe ta ragube abba yace masha Allah wato mamana yau anzo min da kyakkyawan labari na neman auren ki kuma... Katseshi tai da cewa aure??
Aure fa abba kuma ni? Neman aure fah !!! Murmushi irin na manya abba yayi yace kinji mamaki koh? Shine masoyi mafi gaskiya mama na wanda ze soki dan Allah wanda yake sonki dan kuyi rayuwar ibada ba ta 'bata lokaci a titi ba insha Allah yaro ne me hankali da nutsuwa da kamala shiyasa ma na riga na amince da abunda suka zo min dashi kuma na bayar dake wa dansu muhsinu yanzu akwai alk'awarin auren wani a kanki babu ke babu wani sakarci ko kula wani saurayin wanda bashine wanda zaki aura ba
Kar kiyi mamaki ko kuma kiji ba dadi abisa saurin yarda da nayi kin san nine mahaifin ki bazan miki abunda ze zama ba dai dai ba amma duk da haka tinda kece zaki zauna dashi yana da kyau kiyi tunani tin kafin tafiya tayi nisa idan bakyaso ko kuma kinga yanada wani aibu koh abunda beyi ba toh kisanar dani ni kuma in Allah ya yarda zan dauki matakin da yadace kinji koh, gyada kai tayi da kyar alamar to. Abba yace Allah yayi miki albarka amin suka amsa tashi tayi a daddafe ta fice tana biii bango dan gaba daya batajin ta jitayi kafafunta suna neman su gaza daukar ta da kyar ta karasa kan gado ta zube tunani barkatai suka fara yomata kwana abun mamaki shi ba a mafarki ba shi ba a gaske ba wai da gaske muhsin din da tasani ne yayi mata wannan qanqancin ko kuwa wani ne wai da gaske ta tabbata yana sonta kenan ba shirmen awaaz bane? Kodai awaaz din ce ta fadawa abban wani abu? To meyesa muhsin ze nemi auren ta ba tareda amincewar ta ba? Meye dalilin sa da ze tabbatar da tana sonshi? Kenan makaryaci ko kuwa?? meye hakan yake nufi? Ko kuwa dai wannan shi yake nufin kundin kaddarar ta ya bude? Toh wai yanzu taya zata iya rayuwar aure ma? Kuma da muhsin din da a matsayin aboki take daukar sa ya za'ai ta fara sonshi? meyesa zeyi mata haka kodai tacewa abba karya yake bata sonshi? Ko kuma aibunsa zata fad'a kamar yadda abban yace ? Toh idan hakane me zatace na aibun sa? A duk iya dadewar ta dashi bashida wani abu na rashin tsafta wanda ba dai dai ba yanzu ina zatasa kanta taji sanyi???? Yanzu haka rayuwar ta zata cigaba ba tareda wani kwakkwaran farin ciki ba rayuwa da wanda bakaso ai masifa ce wai ma meyesa muhsin yake zaton sonshi take?????? Wannan tarin tambayoyi da tunani da zuciyar ta suke antaya mata takasa samun cikakkiyar amsar su gashi tana matukar bukatar amsar cikin sauri tashin hankali wanda ba'a sa masa rana yau kenan
A wannan daren reetaj bacci sai barawo awaaz ma jikinta yayi sanyi ganin halinda yar uwar ta tashiga ta tausaya mata sosai amma tasan na iya lokaci ne kawai idan ta fahimci komai zata dena wannan tunane tunane tin da asbahi da ta idar da sallah ta fara mita ai kuwa
Zan nuna wa muhsin din nan nafishi hauka banda mara mutunci haka ake soyayya ko anayin ta dole ne munafukin banza a sanyaye
Awaaz tace dan Allah yaya kidena fadan haka ba laifinsa bane, tsawa ta daka mata keehh!! Rufemin baki!!! Ke dama ai bakisan ciwon kanki ba kawai.
Gyara kwanci awaaz tayi tace alabaki hakuri tsaki kawai tayi zuciyar ta na cigaba da kuna tabbas taji haushi da bakin ciki akan abun ji take da zatayi tozali dashi da sanyin safiyar nan kamar ta kashe shi zatai se dai munafukin ba zuwa zeyi ba yasan bashida gaskiya,
Har garin yakusa wayewa sannan bacci ya sake daukar bata dade da komawa ba taji yaya muktar yana kwala mata kira,
A firgice ta sauko tana mutstsuka ido tayi hanyar tsakar gida tana had'a hanya
Cike da zolaya yace amarsu ta ango yaushe ne bikin??
Kallo me kama da harara tai masa tace dama tambayar kenan ka tashe daka bacci na?
Yace eh mana banyi dai dai bane ?? Oh ina ga dai mafarkin sa kike wayyo banso na tasheki ba gaskiya
A hasale tace toh wai meyesa zanyi mafarkin sa wai mene na tsokana ta nifa ba nice nace inason shi bama kawai zaka zo kana tsokana ta nidai gaskiya kadena banaso,
Toh akan me zandena ai sai inda maina ya kare ni ai abun farin ciki ne yasameni kanwata zatayi aure daka yau ma yaya ta ce ke ba kanwa ba ya karasa magana yana kyalkyala dariya, kamar zatayi kuka tace amma da umma dan Allah kuce yadena tsokana ta dan Allah,
Murmushi umma tayi tace ai gaskiya yake fada reetaj meyesa bazeyi farin ciki ba ai nima kaina ina bayan sa dole muyi murna,
Kuyi murna umma saboda za aimin auren dole ko me? Ko akan ku nake zaune duk kun takura min,
Sai yanzu ammah tayi magana tace ke wai kunya haukace zaki fadawa mutane maganar banza anan ,
Dariya yaya muktar yayi yace fada mata dai amman mu kema kin sani kawai borin kunya kike ni kuwa dai baza a hanani magana ba nida baki na kansa tayi tana kai masa duka ta fashe da kuka tana ni wallahi duk sainayi maganin ku dakai dashi din tinda baku da mutunci shi yazo yamin sharri kai kuma zaka rinka tsokana ta shigowar yaya hafiz ne yasa ta saurara fuska a hade yace ke lafiya kasa magana tayi,
Muktar yayi caraf yace yaya hafiz wai dan nace Allah yasanya alkairi shine take duka na harda zagi
Dariya shima yayi yace toh ai abun ba na zafi bane reetaj meye aciki daka an daura fah shikenan an wuce me wahalar ,
Sake rushewa tayi da kuka tana cewa wallahi na lura duk yan gidan nan bakwaso na kuma saina fadawa... Kafin ta fadi wanda zata fadawa muktar yace kaji yaya hafiz wai seta fada masa kayi shiru kar azo da police a kwashe ka yaya hafiz yayi dariya yace abun har yakai ga haka reetaj??
Zundumawa tayi da gudu tayi dakin su kan gado ta fada ta dora daka inda ta tsaya ,
Sukuwa dariya suka sake fashewa da ita harda tafawa
Yaya hafiz yace kaga yarinya dan Allah god'iya da ita amma wai dan anyi zancen auren ta take mana kuka, umma tace ai kune manyan banza inaku ina tsokanar kanwar ku ?
Muktar yace ahh. Tohh. Umma kawai sai mu zuba ido ai gwara mu dan taba muma kinga da wani ya tsokane ta ai gwara mu tsokane ta , umma tace Allah ya shirya ku manyan kwali, awaaz dai tanajin ta tana kuka amma batayi magana ba dan kada ta hauta da fada sai fa tayi me isarta duk yadda akai da ita ta karya taqi haka nan suka qyale ta makarantar ma cewa tayi bazata ba,
Cikin sa"a da yamma sai ga muhsin yazo da yusuf yazo ya fada awaaz tayi karaf tace kace bacci take.
Zumbur ta tashi tace dan wayece miki bacci nake mayafi ta dauka ta rataya ta fita idon ta kozai kozai daka ganta kasan tayi kuka tagaji tayi laushi sosai,
Tinda ya ganta ya fara tsumayin masifa dan awaaz ta sanar masa da yabi a hankali zesha fada gyara tsayuwa yayi yace barka da fitowa sarau.... Kai rufe min baki malam , toh na rufe, jikin bango ta jingina tana girgiza kafa batace komai ba shikuwa kallon ta yake yana mamakin rigima irin tata ,
Ganin shirun yayi yawa yace barka da yamma, bazan amsa ba banda karamin tunani irin naka haka ake so? Kai ina ganin ka kamar wani me hankali ashe duk ba haka bane?
https://facebook.com/groups/575599953675542/

*💫ANNURI WRITER'S ASS.*💫
(Annuri is the best.)

*(A.W.A.)*

*SIRRIN QETA*

Page 3

*by yar gatan annuri writers*

*Indo ce*

*بسم الله الر حمن الر حيم*

Wai angaya maka ni irin sakarkarun yan matan nan ce ? Toh Ni ba tsarar ka bace dan haka karka kara zuwa gidan banason iskanci.kawai saboda tsabar rainin hankali har zakaje kacewa abbana wai soyayya ma muke da kai a yaushe ka taba cemin kana sona ko ni ta ta'ba ce maka ina sonka kawai dan ta qare maka sai tsiyar ka ta qare a kaina toh wallahi kashiga taitayin ka ko kazata neman kai ake dani a gidan mu ko kuma kana ganin kamar sun gaji dani ne iyeh??
Sai a lokacin muhsin yayi magana yace wai dama haka kike da rigima???
Chapter 6 · 0% Book details