← Book details Sirrin Keta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 47

Sashe 44

Sirrin Keta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Itama reetaj fashewa tayi da kuka tana cewa kai yalla'bai meyesa zaka wani rungume ni ance maka nima irin ka ce nifa musulma ce fa ko ka manta ne nifa ba arniya bace fa,

Dariya ya shiga qyalqyalawa har sai da tayi shiru ta zuba masa ido tana mamakin dariyar tasa,

Meyesa kuma kake dariya??

Saboda ni arne ne ba musulmi ba y'an uwa na ma haka ni gunki hanumam nake bautawa mhamah ta kuma ghanesh bhabhai kuma shiva...

Katse shi tayi da cewa dariya ma kake yi ?? Ka maida abun wasa ma kenan bakaji abunda ayaana ta fad'a bane yalla'bai nifa na lura kawai neman makasa ta kawai kake yi ka kawo ni gidan ku ka ajiye ni kawai salon su kama ni allah ka maidani gidan mu inyi kuka na sosai dan Allah yalla'bai kanaji tace zata gayawa mhamah shine kuma kake ma dariya abun ka?????

To reetha idan banyi dariya ba kuka kike so inyi??

To yalla'bai ta tafi fa taje ta fad'a ,

Girgiza kai yayi yace baza ta iya ba
Bata son duk wani abunda ze 'batawa mhamah rai nasan bazata fad'a mata ba gara ta bari abun a zuciyar ta amma nasan baza ta iya fad'a ba,

Nidai yalla'bai ka maidani gidan mu dan Allah wallahi ina jin tsoro kuma nasan za suyi min fad'a,

Sai a lokacin ya tuna hakan da sauri ya saka doguwar jallabiya ya fice yana cewa tsaya in d'auko mota .

Be wani dad'e ba ya dawo yace ta taso hanun ta ya riqe har cikin motar tana shiga ya rufe ya koma mazaunin sa ya kunna mata wuta armaan sai qwala masa kira yake,,

Reetaj tace yalla'bai d'an uwan ka yana kiran ka,

Qara manne ta yayi yana cewa ke sharewa batun sa kinji idan na dawo duk wadda za ayi sai ayi ,

Sai da ya kaita har qofar gida ya tabbatar ta shiga sannan ya juyo ,

Ayaana

Taqi saurarar kowa sai faman kuka takeyi ta kulle kanta a d'aki tunani da dama suna nema su sa kwanyar ta ta tsage meyesa ayaan ze kasan ce haka!??? Idan ta fad'awa mhamah wane irin baqin ciki zatayi jin cewar d'an ta da take matuqar qauna ya kasan ce d'an iska ne lallai zatayi 'bacin rai da yawa dan haka ta yankewa kanta shawarar baza ta fad'awa kowa ba ,

Zeeny.

alina tayi iya shige da ficin ta ta nemo musu wani bokan wanda ake cewa har yafi wancan qwarewa dan haka akai masa laqani da mugun dodo abun take so da zafi zafi dan haka har sun sa ranar zuwa dan ganawa da shi su kai masa buqatun su,,

Muhsin ..

zaune suke shida mosoyiyar sa fauza..

Sai 'bata rai take yi ita a dole yasa musu ranar aure kawai ya aure ta shine in ba haka ba akwai matsala,

Muhsin yace na rasa ina zan sa kaina na kasa gane meye mafita gaba d'aya gashi kwanan nan mami na ta takura min akan cewar awaaz bata haihuwa ita kawai jikoki take son gani,,,

Wani makirin murmushi ta saki tace gaskiya ne na kasan ce me matuqar sa'a wannan babbar dama ce a gare ni wannan ne lokacin mu da ya dace ka gabatar dani a wajen ta,

Muhsin yace kamar ya kenan ??? Kina ganin zata yarda na qara aure ne ???

Murmushi fauza tayi tace ai shine nace maka ga dama ta samu kar mu bari ta qwace mana zamuyi amfani da rashin haihuwar awaaz domin cimma burikan mu ba ce mata zakayi kai tsaye zaka qara aure ba ai kace mata tinda abun ya kasance haka kawai ka yanke hukuncin zaka aure ni domin farin cikin ta da yuwuwar za"a samu qaruwa wannan shine kawai ka fahimta ???

Wani sukurkutaccen murmushi muhsin yayi yace Allah sarki awaaz yarinya tana can tana fi'ili ni kuma zan auri masoyiya ta bata sani ba ma kuma da munyi aure kika haihu shikenan mami duk wata qaunar ta kanki zata koma duk da tana son awaaz sosai amma nasan zata soki fiye da awaaz d'in idan kika sama mata jika,,,

Fauza ta murmusa tace mami idon ta ya rufe da neman zuriya ta damu akan haka sosai zata samu abunda take so daga gare ni a yayin da idanun ta suka rufe bata ganin kowa sai jikan ta ni kuma zan cika muradi na..
Muhsin gaskiya awaaz ta biya ni ban san da me zan saka mata ba gaskiya da ta zama silar aure na da kai nagode mata sosai Allah yabar qauna kace ina gaishe ta dan Allah,

Muhsin ya d'an zaro ido yace tabb ban shirya rigima ba gaskiya bazan 'bata mata rai ba ban da lokacin rarrashi ai har a gama komai ayi auren har a haihu baza ta san anyi ba bare ma ta sako ni gaba.......

Mhamah...

Ta kasa zama sai kai kawo take a d'akin ta roooh Da aslam suka shigo ganin haka yasa roooh yace mhamah me yake faruwa ne ???

Ohh Allah roooh ban san meyesa bethaa ya bud'e qofar baya ba.. amma dai haka kawai inaji a jiki na kamar ba haka nan bane hankali na ya kasa kwanciya...

Shiru tayi kafin ta qara cewa da yuwuwar mad'aukar gidan tana aiki kuwa???
Da alama zan bincika in gani,,,

Gaban sa ne ya fara fad'uwa yayi shiru ya kasa cewa komai.........

Aslam da be qara sa shigowa ba yanajin abunda mhamah take cewa hannu ya d'ora a kai yana zazzaro ido yace................

Har sun qwalala ido suji abunda ze ce 👭to qwalelen ku😜😜🤪🤪🥴🥴🥴😝😝

Comment and share dan Allah🙏🙏🙏

Karku manta da sharhi 🥰🥰
https://facebook.com/groups/575599953675542/

*💫💫ANNURI WRITER'S ASS.*💫💫
(Annuri is the best)

*(A.W.A)*

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FEViiYLkmiwKIUEZc2PcLD

*SIRRIN QETA*

*Page* *57~58*

*by yar gatan annuri writers*

🎉🎉 *Indo ce..*🎉🎉

*بسم الله الر حمن الحيم*

..tinda mhamah take irin wannan maganae tabbas akwai wani abunda bhaiya yayi to yanzu meye abunyi ??? Ya kamata in riga mhamah zuwa na gani abunda ya faru in yaso kawai sai na goge komai kafin tazo,,,

Fasa shiga yayi da gudu ya nufi d'aki na musamman wanda aka tanada dan madaukan tsaron gidan da na'urori kuma da yake shine shugaba ta wannan fannin shiyasa yake iya sarrafa komai shi ya karanci wannan idan ba shi ba duk yawan y'an gidan babu wanda ze iya kowa da fannin da yafi qwarewa sai dai mhamah itace y'ar komai da ruwan ka tana iya komai kuma a sannu a nutse saboda Allah ya bata kaifin basira takanyi nazari sosai akan abu kuma cikin ikon Allah sai ta gane inda ya dosa,

Jikin sa har 'bari yake ya fara dube dube cikin sa"a kuwa komai ya bayyana ganin bhaiyan sa ya rungumo mace daga motar sa abunda ya d'aga masa hankali sosai ido ya zaro yana cewa bhaiyaa???
Qara zuba wa na'urar ido yayi har lokacin da ayaan ya shige d'akin sa da yake mad'aukar hoton d'akin nasa bata aiki hakan be bashi damar ganin abunda ya faru ba zazzafan huci ya furzar yace da sauqi ma ai magana yayi wa roooh ta bluetooth da suke amfani dashi ko a cikin gidan su musamman idan zasu rarrabu sukan yi amfani dashi dan sanin halin da d'ayan su yake ciki a razane yace roooh mhamah fa?? Wallahi akwai matsala bhaiya na gani da mace fa kuma a cikin gidan nan ,..

Murmushi kawai roooh yayi dan kuwa shi ya dad'e da sanin reeetaj baibaita maganar yayi kamar yadda sukeyi idan basa son wani ya fahimce su zasuyi magana da hausa amma babu lallai ka gane me suke nufi sai kayi dogon nazari..
Muna jone e. Wuta.. Zalla

Aslam yace yanzu ma kuwa dan Allah kar ka bari ta zo yanzu...
Kafin ya rufe baki yaga mhamah tazo wajen qofar tana qwanqwasawa tare da kiran bethaa zubewa yayi a wajen yana juya kai a mutuqar razane yake cewa...

Mhamah ha"ha dan Allah karki shiga bhaiya kar ka bud'e fah mhamah a"a mhamah kiyi haquri dan Allah mhamah'"""

Duk yabi ya kid'ime sai surutai yakeyi ya ma manta cewa abun ya riga ya faru tin d'azu kawai yana kallo ne bayan an gama....

Qoqarin tafiya zuwa d'akin mhamah takeyi anan ne fa roooh shima ya fara gigicewa tsawa ya daka wa aslam da ya kasa ta'buka komai...
Kayi da wuri manaa!!! Baka da lokaci fa!!!!!
Kana ihu akan abunda ya wuce,,,

Juyowa mhamah tayi ta gwarara masa ido cike da tuhuma tace...

Da sauri aslam ya tashi yana cewa yanzu yanzu ma kuwa roooh dan Allah karka bari tazo qoqarin goge duk wata hujja da zata nuna alama ya farayi,,,

Da waye kake magana haka?????

Da sauri ya tsige bluetooth d'in ya soka a aljihu ya fara Kame kame cike da rashin sanin abunyi mham... Mha.. Da.. Au..

Tsawa ta daka masa yayi saurin dawowa hayyacin sa besan lokacin da ya zundumo mata qarya ba ba tare da ya shirya ba yace da ni kad'ai nake dama mhamah dama ina son zuwa saudi arabia ne to.. Ku..kuma. Dama.. Fa ina son gaya.. Gayawa...

Katse shi tayi da cewa bhaiya ba???

Da sauri yace ehh mhamah ko zaki fad'a masa bana so yace a"a,

Kai 'bace min anan kaje ka gayawa bhaiyan ka duk abunda yace dashi zakayi amfani banada ikon da zance kaje ko in hana ka zuwa duk abunda yace kawai shikenan bani waje banida lokacin shirmen nan naka mutum sai zafin rai kai kad'ai ma kana yiwa kanka fad'a,

Ficewa tayi..

da sauri ya mayar yace aslam ka gama ???

Ha"ha roooh kai ma kayi wani abu mana kaja hankalin ta ,

Roooh yace ina zuwa maza ka raba min wutar gidan duka,

Kamar yadda yace haka aslam yayi ,

Kashe wutar da akayi kuwa yayi nasara wajen daqile mhamah,,,

Kafin ta qarasa shukreey tace mata ammuu tace dan Allah tazo wai ayaana sai kuka take ta rasa yaya zatayi mata,

Hakan kuwa shine ya mantar da mhamah akan abunda take son yi har su aslam suka kammala abunda zasuyi,

(Kunci sa"a yalla'bai d'in naku ya tsira wannan karon😎😎 amma in kere na yawo zabo na yawo wata rana za"a had'u😂😂)

Reetaj..
Chapter 44 · 0% Book details