← Book details Sirrin Keta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 47

Sashe 35

Sirrin Keta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunanin abunda ya faru dawo mata kawai yakeyi roooh tafi tunawa dan kuwa zata iya cewa yayi mata babban temakon da bazata ta'ba mantawa dashi ba da tayi tunanin yana d'aya daga cikin wanda ze qi ta idan ya ganta amma sai taga ba hakan bane shima dai yasan halin mhamahn su ashe dai,,

Tunani tayi ta fama dasu kala kala har suka isa ,

Lokacin da zata fita tace ameed ashe qanin yalla'bai d'in nan yana da mutunci ashe baze tsane ni ba??

Ameed yace a kan me kike tunanin ze tsane ki??

Tace ameed naga ai ni talaka ce ba kowa ba kuma su masu kud'i ne kuma ba baqar fata ba kuma naga masu kud'i basa son talaka ya ra'be su amma kaga shi ya temake ni ai na zata yalla'bai ne kawai ze iya temako na,

Ameed yace ai kuwa dai basa gudun talaka madam dan kuwa a jinin mahaifin su suka d'ebi hakan dan kuwa shi baya aboki d'an me kud'i ma duk talakawa ne abokan sa yana temakon mutane sosai kuma suma y'ay'an sa sun gaje shi shiyasa duk inda kika shiga kika ce kanawan dabo babu wanda be san su ba duk kan su nan da kika gani sun iya temako yaran nan har qauyuka suke zuwa suna temakon marasa qarfi ita kanta mhamah tana da qoqarin wannan musamman ta 'bangaren lafiyar talakawa tanada temako sosai kuma tana da mutunci ga kirki amma fa idan bakayi mata ba taku batazo d'aya ba gaskiya baza ga mutuncin ta ba.

kuma bama wannan ba akwai wata alaqa a tsakanin yalla'bai da wannan qanin nasa wadda ko mahaifiyar su bata iya gane tsakanin su akwai qauna da kuma amana da yarda a tsakanin su na tabbata yadda yalla'bai yake sonki sosai d'in nan shima roooh haka ze d'auke ki ,.

Shiyasa ma kikaji yace d'an uwan sa baze bari mhamah tagan ki ba,

Bata iya cewa komai Ba ta shige gida,,,

Tana shiga umma tace munafukar allah kince aiki zakije ya akai kika shiga motar wani?? Iye?? Kin fara bambad'ancin ko???
Dama ace gandamemiyar mace kamar ki ba aure ai dole a ga ba daidai ba allah dai ya kiyaye mu da abun kunya,

Reetaj tayi kamar bataji ba ta wuce ammah tace haka dai kike so ayi ta zagin mu kin samu mutum nagari kamar muhsin amma duniya ta rufe miki ido kika qi aure yanzu kuwa ina zaki auru?? Ai kin gama cutar mu reetaj kin gama tozarta mu kin samu ma wani yazo shima kika ce ba kyaso kin yaudari muhsin kuma kin qi auren sa kin maidamu qananun mutane kin zubar mana da mutunci amma babu komai Allah ze saka mana tinda ai yana kallo yasan bamu da laifi iya qoqarin mu munayi amma mun had'u da kangararriya babu komai kije kiyi duniya ce reetaj,

Wuce wa tayi tana share qwallah damuwa tayi mata yawa tana shiga d'aki ta fashe da kuka........

Comment and share dan Allah🙏

Karku manta da sharhi🥰🥰🥰
https://facebook.com/groups/575599953675542/

*💫💫ANNURI WRITER'S ASS.*💫💫
(Annuri is the best)

*(A.W.A)*

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FEViiYLkmiwKIUEZc2PcLD

*SIRRIN QETA*

*Page* *47~48*

*by yar gatan annuri writers*

🎉🎉 *Indo ce..*🎉🎉

*بسم الله الر حمن الحيم*

Kuka takeyi sosai tana cewa Allah ka fitar dani daga wannan sharrin da zargin da akeyi min kafi ni sanin meya faru dani da kuma wanda ze faru Allah ka nesanta ni da wannan mummunar qaddarar har zuciya ta Ban ta'ba tunanin aika ta kuskure ba koda nayi ma ba"a sani na bane bani da laifi akan abunda ake tuhuma ta ba laifi na bane...

Surutai tayi ta faman yi har sai da tayi kuka me isarta ta share hawayen ta ta tashi,

da yamma ta fito wajen su huzaifa suna ganin ta abdullah yasa dariya yana cewa wato yaya kinyi wuyar gani sai da yalla'bai yayi sama jannati,

Dariya tayi tace wallahi kuwa abdullah gashi kuma na saba dashi sosai,

Huzaifa yace Allah yaya ko dai kun fara soyewa ne?

Wayyo huzaifa rufa min asiri kana son ganin mutuwa ta ashe?? Ai kuwa da daga ranar shikenan mutuwa tazo kawai kuyi tanadin makara da liqafani,,

Dariya huzaifa yayi yace yaya kina da tsoro da yawa ita soyayya ina ruwan ta da mutuwa wai bakya sauraran wasiyar hamisu breaker ne ??

Ta'be baki tayi tace can ta soye qalau shima can ya yanka dashi da wasiyar tasa indai akan yalla'bai ne gara ma kawai in mutun in san mutawar nayi amma soyayya da yalla'bai yafi had'arin gingimari masifa kwata kwata ma babu had'i tsakanin biri da gada shi ba tsara na bane kawai addu"ar da zakai min Allah ya bani dai dai dani me gaskiya da amana kawai wanda ze riqe ni tsakani ga Allah kuma ya soni da gaskiya shine kawai,,

Huzaifa yayi murmushi yace yaya kenan shi so ai besan wani tsara ba indai ta wannan ne shiyasa ake cewa so makaho ne wasu suce mahaukaci ne amma dai kawai mu sai muce Allah ya amsa addu"ar mu yabaki miji nagari irin wanda kike so me gaskiya dan kuwa yanzu soyayyar gaskiya tayi qaranci a rayuwar nan sai dai Allah yayi mana me kyau kawai,

Reeetaj tace amin dai wai amma huzaifa yaushe ne ka fara wa"azi akan soyayya??
Kai ma dai da alama ka fad'a ko???

Dariya yayi yace haba yaya ba wannan fa ni kunyar ma y'an mata nekeji,

Dariya tayi tace to Allah ya had'a ka da tagari dai amma kanajin kunyar y'an mata ai ba kanta,

Kai haba yaya dan Allah kiyi shiru nifa yaro ne fa gaskiya ki dena min irin wannan hirar sai na girma,

Murmushi tayi tace Allah ya sauwaqe maka kai dai ,

Hira sukai sosai kafin ta koma gida,

washe gari,

Jikinta duk a sanyaye haka ta shirya ta wuce aiki babu abunda ya sauya a ciki komai da yalla'bai yake yi shine aikin da yake jiran ta tsarawa da tacewa da kulawa da gabatarwa da duk wani abunda ya kamata komai sai da izinin ta,,

Kan kujerar da ta saba zama ta zauna tana kallon kujerar sa ganin fayau wajen yasa taji hawaye na neman zubowa ko ina ta kalla a wajen sai dai taga fayau sai take ganin office d'in ya zama kango ji take kamar ya tafi kenan ta saba idan yana nan tayi ta rawar kai da girin gid'ishi amma yanzu sai dai kawai tayi aiki tuquru kuma ita kad'ai abun zeyi mata wahala sosai ,

Haka dai ta lalla'ba tayi abunda zata iya ta wuce gida ba tareda lokacin tafiyar ta ma yayi ba,

Muhsin..

suna zaune shida awaaz suna kashe love wayar sa tayi qara yayi saurin d'auko ta ganin me kiran yasa qirjin sa ya bada rasss...

Kallon awaaz yayi sai wani yauqi take tana bashi labari da sauri ya d'aga ya kara a kunne.. Banji abunda akace ba sai dai naji yace to shikenan Alhaji ina zuwa yanzu ma kuwa babu damuwa ai,

Kallon sa awaaz tayi tace waye yake neman ka kuma ??

A diriri ce yace yi haquri my sweetheart wallahi yalla'bai na ne yake kira na cikin gaggawa kin san dai wanda ya qauna ce ka koda baka qarqashin yanzu dole zaka dinga ganin girman sa shiyasa ban san kuma wace alfarma yake nema ba ya kamata inje yanzu,

Awaaz ba dan ranta yaso ba tace gaskiya ne yayi kyau hakan sai ka dawo Allah yasa dai samuwa ce,

Muhsin ya saki wani d'aid'aitaccen murmushi cike da salo yace amin my love baza kiyi min rakiya ba??

Tashi tayi tana cewa bari na raka ka to sarakan rakiya,

Eh mana idan ina tare dake ne sam bana son abunda ze rabamu shiyasa nafiso ki raka ni har sai kinga na 'bace wa ganin ki ki raka ni da addu'ar ki da fatan alkhairi da wannan kyakkyawan bakin naki,

Tayi wani farr da ido tana murmushi sai wani taku take d'aya da d'aya,

Kamar yadda ya fad'a har sai da taga ya 'bace sannan ta koma ciki,

A wani d'an madaidaicin mall yayi parking ya fito ya kutsa kai ciki kan wani tebur me kujeru biyu ya nufa inda wata kyakkyawar budurwa take zaune tana danne dannen waya gami da taunar cingam daka ganta dai kasan irin gogaggun y'an matan nan ce,

Zama yayi yana cewa baby na ya akai kiran gaggawa haka?? Lafiya dai ko??
Ina tare da awaaz kawai naga kiran ki da fa ta gani??

Wani shu'umin kallo ta bishi dashi kafin tace kana tambayar lafiya ma?? Ina fa lafiya take??

Gyara zama yayi yana subhanallah babu lafiya ga sarauniyar mata ina naga ta zama me yafaru ne ??

Tace nifa na fara gajiyawa gaskiya..
Na kasa gane ma asalin irin son da kake min haba ka sani na sani soyayya muke ta a mutu amma kaje ka auri wata wai ma me ya had'a ka da ita??
Ka sani dan kai ne naqi aurar kowa na tsaya jiran ka har yanzu meyesa kake nema ka manta dani ne??
Nifa gaskiya na gaji ina buqatar nayi aure ya kamata kasan duk yadda zakayi ka aure ni dan kuwa in ba haka ba to tabbas zanje in gayawa matar ka cewar kana soyayya dani kuma zamuyi aure bayan haka ma muna hutawa har kayi min ajiya,
Chapter 35 · 0% Book details