Sashe 15
Sirrin Keta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Umman su afiya tace a"a reetaj kar kiyi haka bakisan me hakan yake nufi ba sai Allah ba kyace kin haqura ba kin dad'e kina zuwa kin sha wahala da wulaqanci akan neman aikin sai yanzu kice kin haqura kina ganin su huzaifa zasu ji dad'i ? Bazasuji dad'i ba kuma ma gaskiya in kikai haka baki kyauta musu ba sun tsaya tsayin daka dan suga sun saki farin ciki be kamata ki watsa musu kasa a ido ba kiyi haquri dai reetaj me haquri yana tareda Allah karki karaya kawai kisa gaskiya da tsoron Allah a cikin lamarin ki kuma a ko ina kike a fad'in duniya kar ki manta da gaskiyar ki idan kikai haka Allah ze temake ki,
Gyad'a kai tayi tace toh yanzu umma sai in ta rubuta masa duk abunda ya faru?
Umma ta d'an yi shiru kafin tace eh haka ne ki rubuta masa kiga gudun ruwan sa tinda shine ya buqaci hakan a matsayin y'ar ciki na na d'auke ki reetaj bazan baki shawarar da zata zama nakasu a gareki ba ni dake da afiya a guri na duk d'aya ne ..
Amma yana da kyau kiyi tunani kuma kiyi shawara da zuciyar ki kuma ki fad'awa su huzaifa tinda sune abokan shawarar ki idan kinga rubutawar shine matsala kawai sai ki haquran Allah ya za'ba mana mafi alkhairi,
Reetaj da afiya suka amsa da amin,
Afiya tace nima dai yaya iya tawa shawarar kenan gaskiya abunda umma tace,
Dai dai lokacin abdurrahman ya shigo yace yaya ga huzaifa nan suna bayan layi suna buga ball har da su walid da su sadik,
Murmushi tayi tace nagode abdurrahman tashi tayi tace sai anjima umma nagode,
Umma tace babu komai sai kin qara shigo mana,
Toh kawai tace tayi waje,
A tsaitsaye ta samesu tsurkui tsurkui tayi dariya tace yauwa qanne na kunzo kenan dama... Gaya musu abunda yalla'bai yace tayi.. da mamakin ta sai taga suna ta murna su sadik da su umar harda tsalle da yake sune qananun ciki ,
Katse su tayi da cewa amma fah nace ni babu abunda zan rubuta na haqura da aikin,
Sororo suka tsaya suna kallon ta huzaifa yace haba yaya dan Allah meyesa haka? alamar bacin rai ta bayyana a fuskar sa ya wani had'e rai kamar gaske,
Su kansu su umar duk sai suka d'age mata qeya wai su basu yarda ba ta 'bata musu rai ,
Dariya tayi tace ohh ai na fasa umman su afiya tace min inyi kawai kuma zan rubuta kawai dama dan naji ta bakin ku ne yasa nace haka kuma naji dad'i,,
Sai a lokacin suka fara fara a huzaifa yace ai kuwa yau d'in nan za a fara rubutun barakiga inje in nemo qaton littafi, kafin tayi wani motsi ya tafi suka rufa masa baya wuce wa tayi cikin gida tana jinjina musu da suka fita hauka daga fad'a musu sai neman littafi ?,
Bayan magrib sai ga yusuf kimkim da littafi dindimeme yace yaya gashi inji huzaifa,
Kar'ba tayi tace kace masa na gode,
Bud'e littafin tayi tagan shi tar dashi sabo fil murmushi tayi tace to ni yanzu ta ina zan fara rubuta labarin nan????????????????????????????
Fans d'in reetaj ta ina ya kamata ta fara ne🤔🤔🤔
Camment and sharhi dan Allah🙏🙏🙏🙏
https://facebook.com/groups/575599953675542/
*💫💫ANNURI WRITER'S ASS.*💫💫
(Annuri is the best)
*(A.W.A)*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FEViiYLkmiwKIUEZc2PcLD
*SIRRIN QETA*
*Page* *19~20*
*by yar gatan annuri writers*
🎉🎉 *Indo ce..*🎉🎉
*بسم الله الر حمن الحيم*
Washe gari suna zaune a qofar gida tareda su huzaifa kamar yadda suka saba,
Kallon huzaifa tayi tace.. Huzaifa nifa ina tantama akan yalla'bai d'in wai anya kuwa mutum ne ?? Jiya nakasa bacci wallahi kawai tunanin sa nake nayi mafarkai kala kala masu yawa kuma duk a kansa nakasa gane meye hakan yake nufi ko dai wani sauyin qaddarar ne ya qara riska ta?? Naga abun mamaki sosai wanda ban ta'ba gani ba a lokacin da naje gidan su,,,
Dariya su huzaifa suka sa sai da sukayi me isar su sannan huzaifa yace banda abun yaya kin bi mutum har gidan su kuma mutumin da bakisan ko waye shi ba ?? Ai ko meye kika gani kece kika siya da kanki ,
Sadeeq yace ni wallahi har na qagu ma inji me tagani ,
Hararar sa tayi tace to uban son zance,
Rausayar da kai tayi tace ayyah kuma na b'ata masa rai bawan Allah yanzu ko a wane hali yake ciki??
Kuma inaga ma fah baya magana huzaifa kamar kurma ne dan naga baya cewa komai ,
Dariya huzaifa yayi yace alabar yaya ko dan naci dariya,
Kasha takaici dai gara kawai..
Kai kaga yadda mata suke rungumar sa ma kuwa?
Tantirin arne kawai sai fad'in ran tsiya ni kuwa banason me irin wannan halin nidai da nasamu ya sakamin hannu bazan bari ya qara ganin fuska ta ba ma ,
Wallahi duk wanda ya fito sai kaga ya rungumeshi harda mazan ma narasa wannan wace irin d'abi"a ce nifa tsoro ma suke bani bama kamar matar nan ta iya yiwa mutum mugun kallo..
Yasin kuya.. Da farko da na fara ganin ta yadda ta kafe shi da ido nazata cinyeshi zatayi ni nazata ma irin mutanen nan ne masu cin mutane ,
Dariya huzaifa yake sosai ba tareda ya dena ba yace ...
Yaya kema fah kinsan ina kika kai kanki..
yadda naji baba dattijo yace fah shid'in ba indiye ne komai nasu yake yi dangin sa ma haka kuma na tabbata wannan gidan da kikaje sune kika gani dan Allah yaya kar su tsorata ki har kisa damuwa a ranki ki dena wani tunanin sa bare har kiyi mafarkin sa dan Allah,
Kuma be zama lallai ace kurma bane yaya ina shakka...
Gaskiya nafi tunanin kawai tabbata ce ta sa shi haka...
Amma dai ban sani ba maji ma gani dai allah ya kaimu litinin d'in da rai da lafiya inaga zaki gane idan kurman gaske ne idan ma kwanton 'bauna yayi miki zamu gane,,
Tace Allah ya kaimu kuwa..
Idan yayi wasa sai na sashi hawan jini d'an rainin hankali ,
Sadik yace idan kuma shine ya saki to munje ganin likita,
Kaiiii meye kace iyeh ????,
Ta tambaye shi tana zare masa ido,
Gimtse dariyar sa yayi yace ba magana nayi ba ,,
Qwafa tayi tace da ka fad'a mana idan ba tsoro ba ?
Huzaifa yace tsoron ne ma yaya,,,,,,
Haka sukai ta hira har ta gaji ta koma gida,
Da daddare ta dakko qur'anin ta zatayi karatu tana bud'ewa wata takarda ta fad'o da sauri ta d'auka ta fara warewa karo tayi da rubutun da babu makawa tasan na yaya muktar ne,
Murmushi ta saki tace Allah sarki yaya muktar har yanzu baka dena so na ba nima kuwa insha Allah bazan dena son ka kaine wanda nafi qauna a cikin y'an uwa na,
Fara karantawa tayi kamar haka....
( amincin Allah ya tabbata a gareki kyakkyawar qanwa ta fatan kina cikin farin ciki da kwanciyar hankali a koda yaushe hakan shine farin ciki na naji a wajen su huzaifa cewa kina neman aiki nayi farin ciki matuqa da jin hakan ina miki fatan nasara a duk inda kika dosa qanwa ta sai dai roqona d'aya ne a gareki dan Allah ki kare mutuncin ki komai wuya komai rintsi karki sake ki watsa kimar ki karki bari wani abu ya zama ya ta'ba darajar ki reetaj ko menene kiyi yaqi dashi iya qarfin ki,
Na barki lafiya yayan ki muktar yake miki fatan alkhairi, )
Tafin hannu tasa ta goge hawayen da suka zubo kan fuskar ta,
Murmushi tayi tace nayi maka alqawari yaya na zan kare mutunci na da izinin Allah ko meye yake qoqarin ta'ba kima ta zanyi yaqi dashi kamar yadda kace ko nayi nasara ko shi yayi zan riqe kaina tamkar amanar da kabani yaya na zan jajirce a kan kaina domin banida wanda zemin hakan sai ni zanyi qoqarin hakan insha Allah koda hakan ze zama sanadiyar barin numfashi daga gangar jiki na,,,
A kwana a tashi babu wuya da yardar Allah gashi har litinin ta zagayo ,
Da wuri ta shirya tsaf ta d'auki mukullin mota ta fice tana addu"a har ta hau kan titi ,
Sai da ta biya ta gaida baba dattijo sannan ta wuce office d'in yalla'bai sai da wannan guntun mutumin ya sanar dashi zuwan ta sannan yayi mata iso,
Da sallama ta shiga kamar kullum ko kallon hanyar beyi ba haka bakin sa gammmm kamar be ta'ba buduwa ba babu alamar yanada niyyar amsar sallamar ta bata damu ba ta shiga a tsaye ta tsaya qiqam tace ina kwana yalla'bai,,,,,
Yalla'bai dai ko kallon ta beyi ba hakan yasa ta qara tunowa da turancin ta a karo na biyu ta fara yi masa bayani akan tazo neman aiki ne ,
'Daga mata hannu yayi kafin ya matsa wani abu kaman remote 'bagat sai ga d'an guntun mutumin nan ya shigo,,
A lokacin ne wani abu ya faru wanda yayi matuqar bawa reetaj mamaki ganin yalla'bai ya bud'e baki yana yiwa mutumin magana cikin yaren su ,,,,,,,
Bayan ya gama mutumin ya juyo kan reetaj cikin harshen turanci yayi mata bayanin abunda yalla'bai yace ...
Yalla'bai yace ki fita karki kuma zuwa inda yake bazaki samu aiki ba dan haka ki haqura ki koma gida ki zauna sannan a wannan kamfani namu ba a buqatar wani ma aikaci duk muna dasu babu wani gurbi dan haka aiki baze samu ba ki gaggauta fita,
Wannan shine saqon isarwa wa ke daga bakin shugaba na,
Jiki a sanyaye reetaj tace kodai zuwa gidan su da nayi ne ranshi ya 'baci sosai haka har yake jin hanani aikin ??
Allah sarki kayi haquri nima ba a son raina hakan ta faruba kuskure ne ,
Su'bul'bul ta fita ranta duk babu dad'i yanzu shikenan ta rasa aikin haka zata koma zaman gidan zaman baqin ciki wunin takaici kwanan 'bacin rai ??
Sai da ta zauna ta gama kukan ta a mota sannan ta tafi ,