← Book details Sirrin Keta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 47

Sashe 39

Sirrin Keta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da haka sukai sallama,

Kamar yadda ya fad'a hakan ce ta kasan ce ameed ya kawo mata tayi murna sosai,

Danne danne takeyi tana kallon hotuna kala kala inaga ta iya cewa babu ce kawai babu a ciki hotuna harda nasu tin suna yara,

Tana cikin danne danne ta kai wajen video gasu nan iri da kala ba na komai bane yawanci na cikin gidan su ne na sharholiyar su,

Abunda mamaki ganin yalla'bai yana tiqar ball kamar ba shine ba,

Ta fad'a tana riqe ha'ba ta qara da cewa kuma wallahi shine har ma da mhamah harda duk kowa ma na gidan su bhabha ne kawai babu?? harda wasu y'an yara ni ban ma san su ba dama ba iya su roooh bane qannen sa ???
Kuma fa da alama taurarin ciki shi da ayaana ne dan kuwa sunfi kowa iyawa,

Ci gaba tayi da bud'e wasu video d'in wasu kuma ba na ball bane wasan kricket da irin su golf harda su wasan tsere da sauran su kamar ba mutane ba sannan kuma dukan su babu qarami babu babba ,

Ajiyar zuciya ta sauke tace da alama dai babu irin wasan da basayi.. gaskiya akwai farin ciki da walwala da qauna a wannan ahalin kar Allah ya kawo ranar da zakuyi baqin ciki inama dai ace farin cikin ku ze d'ore baze samu tangard'a ba kamar dai yadda mafi yawancin farin cikin gidan mu ya d'aid'aice ,
Kuma awaaz ce silar komai ita kuma ko a jikinta,

Share y'ar qwallar da ta ziraro tayi tana ci gaba da kallon su..
Su shida ne zaune a wajen hutawar su shunsha anko wanda da alama haka al'adar su take su shidan..
sunyi rukuni suna hira,

aslam yace..
nida na shiga wata unguwa naga wai wani mutum daga ajiye mashin d'in sa ya shiga masallaci zeyi sallah kafin ya fito sun d'auke mashin d'in wallahi yana fitowa kawai sai dai yaji hammatar sa tana shan iska ,,,

Kwashewa sukayi da dariya ayaat tace kai bhai Aslam Wallahi mutuncin ka sai du"a"i.
sithara tace kaii ni y'ar bhabha anayi ina shan mama,

A hanzarce islam yace A"uzubillah"
Ke iskancin naki ma har yafi na Aslam d'in ,

Dariya sukeyi sosai.
roooh yace kaji shegiya ke ko kunya ma bakyaji??
Ke bama shayin kike sha ba tsabar kin raina mana hankali ,

Ayaana tace wallahi da gaskiyar ta kowa fa yasha na lokacin sa itama ku barta ta qara ,

Aslam yace ke dama ai indai hauka ne baki da tsara,

Ayaat tace dama dai bhaiya yaji ki ya casa ki,

Ayaana ta ta'be baki tace wani bhaiya can?? 'Dan rainin hankali da jar fuskar sa wannan mugun miskilin ma har wata casa mutum ze iya yi??

Sithara tace kaiiya ai bhaiya ko?? garantin miskili ne yayi ta wani manyance amma idan aka saka gasar rawa har yafi bhai iyawa ,

Roooh yace wallahi kuwa d'aid'ai ne zasu zo kai d'aya da bhai amma koda yaushe shine a sama sai an gama kuma yayi ta wani qasa da ido ,

Aslam yace to yanzu gulma kuke ko munafurci??

Islam yace duk wanda ka za'ba ,

Aslam yace qananun arna kuje gaban sa kuyi mana,

Sithara tace to bazamu iya bane ???

Ayaana tace tambaye shi dai,

Cikin d'aga murya ayaat tace singham!!!!!!!....

Abun mamaki kafin kace me kowa ya d'au matsayar sa wani yana danna waya me hoto kuwa har ya fara d'auke d'auken sa
Me yin kamar yayi bacci yayi me shiga bayan kujera ya 'buya ya 'buya,,

Dariya ayaat ta saki tana cewa kuji fah kunce zaku iya fad'a a gaban sa amma kuma yanzu bama sunan sa na asali aka fad'a ba duk kun firgice matsorata ,

Islam yace yanzu dama yarinyar nan shirga mu kikayi??

Tace to eh mana tinda gashi har ka gani qananun marasa yaji kawai ,

Roooh yace ai kuwa zaki ga yaji yanzu ,

Kafin tayi wani qoqari sunyi mata qawanya sithara tace yanzu dai sai dai in kin qware taki ta fishshe ki ,

Fakar idon su tayi ta zura da gudu ta fita tayi hanyar da zata maida ita cikin gida suka mara mata baya,

Karo tayi da Abhie ta shiga bayan sa ta 'buya su kuwa duk suka tirje a gaban sa ,

Dariya yayi yace mazaje wai yau me kuka sha ne naga kamar bakwa cikin hayyaci ,

Roooh yace ka dai gan mu nan ni nan ciyawar rabbana na zuqa ingaya maka gaskiya shiyasa ka ganni a make,

Aslam yace ni dama kullum ai a shaye nake ni meye ma bana sha insha shayi insha coffee insha madara insha ruwa insha... Kai ni in gaya maka tsohon d'an shaye shaye ne nan da kake gani na ko d'azu sai da nasha rake ,

Sithara tace ni kuma kawai wata y'ar guntuwa roooh bhai ya d'an zuqa ya rage min kaga yanzu ma ganin ka nake sama a qasa fuskar ka rabi ta haana rabi ta Abhie na,,,

Dariya abhie yayi sosai kafin yace to Allah ya shiryaku y'an gwafar na gwafara,

Reetaj dariya harda hawaye ita babu abunda yafi bata dariya irin na me shan mama da kuma wanda ya fito yaji hammatar sa tana shan iska..
Lallai ta gazgata fad'ar yalla'bai da yace idan suka had'u basu da dama ,

Haka rayuwar take tafiya lokaci yana qara wuce wa,

Sai da ta gaji da laptop d'in sannan ta bawa ameed ya mayar ,

Tana zaune tana wasu y'an aikace aikace muhsin yazo ameed ya shigo ya yace madam. Wannan ma"aikacin da kika sa aka dawo dashi nan yazo yana so ya ganki ,,

Shiru tayi kafin tace ya yanayin aikin nasa yanayi cikin aminci kuwa??

Ameeed yace e madam gaskiya baza"ace a'a ba dan kuwa tinda aka kawo shi nan banji wani laifi da yayi ba,

Tace to da yuwuwar ya gyara halin sa kenan??

Ameed yace banida tabbas madam dan a yanzu kafin ka shedi mutum sai ka fara tabbatar da abunda yake aikatawa bansan abunda yake qudire a zuciyar sa ba madam,

Ta jinjina kai tace shikenan jeka zanyi tunani a kansa idan da yuwuwar ganin sa to?

Fita yayi ya sanar masa abunda madam tace muhsin yaji takaici sosai a ransa yake ayyana kud'i da iko ma sunyi a rayuwa yanzu gashi wata y'ar qaramar cikar yarinya tana raina masa hankali dan yaji mutanen da suka santa sukan ce yarinya ce amma har wani sai tayi nazari ma zata bashi amsar shiga,

Jin bata kirashi ba shiru shiru yasa yace wa ameed ya koma ya qara tambayar ta,

Komawar yayi ya gaya mata,

Dafe goshi tayi tace ahh ameed yanzu na riga na tashi tafiya bazan tsaya sauraran sa ba kawai yaje ya gyara mu'amalar sa da mutane shine idan kuma ya matsu da gani na ya fad'a maka meke tafe dashi sai ka tura min,

Ameed yace to madam ,

Fita yayi ya fad'awa muhsin abunda reetaj ta fad'a a karo na biyu rai a 'bace ya bar wajen ya juya baya ita kuma ta fito tayi tafiyar ta,,,,,,,

A kwana a tashi babu wuya da ikon Allah gashi har yalla'bai ya dawo saboda rigimar da ya sakawa papu tinda ya kira reetaj yaji tana kuka shikenan ya tashi zaune tsaye,

Shida ita baza ka banbance wanda yafi farin ciki ba kwanan sa biyu ya koma kan aikin sa itama reetaj bata fasa zuwa ba,

A kwana na hud'u ne ta shigo office d'in bayan ta zauna tace yalla'bai ina kwana??

Ayaan yace sathie lafiya lau ,

Wani kwali ya miqo mata me d'an girma wanda aka nannad'e shi tsaf da leda me qyalqyali kai tsaye dai kamar irin kyauta da ake shiryawa,

Kar'ba tayi tace yalla'bai wannan fa na meye??

Naki ne yaune shekarun ki ta qaru da guda d'aya yau ranar zagayowar shekarun ki dan haka wannan kyauta ce a gare ki,

Da sauri tace a"a yalla'bai kar muyi haka dan allah ni a suwa zaka bani kyauta dan allah kar ka bani ,

Murmushi yayi yace sathie wannan itace kyautata ta farko a gurin ki dan Allah kar ki qi kar'ba bazan ji dad'i ba idan baki ansa ba ,

Jiki a sanyaye ta d'auka tace na gode yalla'bai Allah ya tsare ka da dukkan wani sharri ,

Amin ya amsa mata ..

Shiru ce ta biyo baya reetaj taqi magana shi kuwa kallon ta kawai yake yi yana jinta har cikin ransa.
'Dan murmushi yayi yace sathie bani labarin abunda ya faru da bana nan,

Rausayar da kai tayi tace yalla'bai ba ayi wani abu ba fa kawai duk ya wuce,

Yace Uhm to shikenan hakan yayi,

Zeeeny da Alina

Ne a hanyar su ta zuwa tsibirin bokan su ,

Bayan sun isa wata mata ce tayi musu masauki tana musu maraba ta basu wajen zama a cikin y'ar bukkar da yake tsubbun sa...

Ta fita ta kawo musu ruwa ko kallon sa basuyi ba matar ta gaishe su basu amsa ba saima tambayar ta da Alina t
https://facebook.com/groups/575599953675542/

*💫💫ANNURI WRITER'S ASS.*💫💫
(Annuri is the best)

*(A.W.A)*

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FEViiYLkmiwKIUEZc2PcLD

*SIRRIN QETA*

*Page* *51~52*

*by yar gatan annuri writers*

🎉🎉 *Indo ce..*🎉🎉

*بسم الله الر حمن الحيم*

Salamu"alaiki sathie kina lafiya??

Da sauri ta tashi daga kwance ta zauna tace lafiya lau yalla'bai wannan kiran daren fa?? Bakayi bacci ???
Bafa ni kad'ai ce ba ina tareda qanne na kuma duk abunda nayi sai sun fad'a su sa ayi min fad'a kuma ran ammah ze 'baci yalla'bai dan allah kawai sai da safe,

Da sauri ya dakatar da ita da cewa ai baki ji amsa ba karki kashe..
Nayi bacci na farka...
Kira a daren nan kuma kawai ji nayi alaqar mu taqaru shiyasa na kira ki inji kina lafiya nasan dai bakiyi bacci ba kike ta tunani ko??

A qagauce tace eh yalla'bai,,,

Ha"ha nifa bana son sunan nan yalla'bai ko dad'in ji babu ya kamata ki fara kirana ayaan kamar yadda suna na yake dan kuwa baki da wani dalilin kira na yalla'bai saboda mun qara alaqantuwa sosai shiyasa ma na canja miki suna na maidake sathie dan haka nima ki cemin ayaan sakk,,
Chapter 39 · 0% Book details