← Book details Sirrin Keta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 47

Sashe 4

Sirrin Keta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kallon da yake mata ne yasa duk ta kasa sakewa ga gabanta da yake faduwa musamman idan suka hada ido shiru motar tayi kowa da tunanin da yake ganin shirun yayi yawa yasa yacewa
Awaaz sunana muhsin kefa kanwa ta cikin fara a tace Awaaz yace suna me dadi ta baya fah ?? Banida suna
Wani kasalallen
Murmushi
Yayi mata yace ba dake nake ba sarautar mata da kanwa ta nake Awaaz ta juya ido tace sunan ta reetaj
Gaskiya sunan yayi dadi matuka kuma ya dace da ita baiwar Allah
Haka dai sukai ta hira su kadai reetaj dai bata saka musu baki ba gaba daya a takure take Awaaz ce tai masa kwatancen gidan ya kaisu har kofar gida ta bude ta fita tana one taku seven girgiz...
Cikin hanzari reetaj ta bude motar ta fito kusan gware sukai dashi yana kokarin bude mata motar kallo daya tai masa suka hada ido ta kauda kai tace zan dan wuce yayi murmushi
Yace baza ai min godiya ba?? A kagauce tace nagode yace ba sai kinyi godiya ba yimiki ai tamkar yiwa kaina ne kiyi hakuri idan nayi abinda ya bata miki rai ki yafeni dan Allah bazanso abinda ze bata miki raiba gimbiyar mata ko mene ne zanyi kokarin bijire masa
Fatana kiyi bacci cikin salama ya karashe maganar cikin murmushi da wata irin siga jiri jiri reetaj ta fara gani dafe kai tayi ta furzar da huci jin abun take kamar a mafarki
Har zata shige gida taji yace kisa damu a cikin addu'a idan kinyi sallar naga kina ta sauri lokaci ze kwace koh???? Kai kawai ta iya
Daga masa ya kara da cewa zan dawo gobe inga ya kika kwana ? Bata juyo dan gudun su sake hada ido dan bata bukatar hakan da bi bango ta samu ta shiga cikin gida
Kai tsaye dakin su ta wuce ta fige hijab da jefar sannan ta fito ta daura alwala ta koma bayan sun idar da sallah Awaaz take tambayar ta mene ya tsaidata a waje tace ba komai
Kawai dai nayi masa godiya ne Awaaz tayi dariya tace Allah yasa dai cewa yayi yana sonki yaya
Dogon tsaki tayi tace mahaukaciya zaki fara kenan
Tayi dariya tace wallahi zanfi kowa farin ciki yaya gaskiya karki bari damar ki ta subuce miki a kufule tace ke dalla
Ai wani baya cin rabon wani babu yadda za ai ki auri wanda ba shine mahadin rayuwar ki ba gwara ma
Kidena wannan haukan kinji tabe baki tayi tace mutum yanaso yana kaiwa kasu
Kamar yadda ya fada saida ya dawo yasa ayi masa sallama da reetaj batayi niyar fita ba Awaaz da innan suka saka ta gaba suka tursasa
Ba laifi ya iya kalamai masu sanya sanyin jiki cikin lokaci kadan reetaj taji ta fara sakin jiki dashi
Tin daka ranan yake zuwa gidan har su umma sun san da zamansa amma dai har yau be furta cewa yana sonta ba murna a wajen Awaaz ai ba magana
Ji take inama itace sai dai abunda yake bata haushi yadda reetaj take nuna kamar bata san ma da zaman sa ba inda itace kuwa da anga yadda akeyinta sai dai amma ita yamayi kadan a duk yadda takeson namiji ya kasance amma duk da haka
Da zata samu dama da ta dama

https://facebook.com/groups/575599953675542/

*💫ANNURI WRITER'S ASS.*💫
(Annuri is the best.)

*(A.W.A.)*

*SIRRIN QETA*

Page 2

*by yar gatan annuri writers*

*indo ce*

*بسم الله الر حمن الر حيم*

Reetaj ce zaune gaban madubi tana kwalliya sai faman gyara gashin kanta take "
Awaaz kuwa tana gefe ta zuba mata na mujiya kamar ta hadiye ta kasa shiru tayi ta kalle ta tace.. Yaya? ' dan kallon ta tayi kawai ba tareda tayi magaba hakan yasa awaaz cigaba da magana
Cikin murmushi tace yaya da ace nice da kyawun ki koh? Ai kawai ba'a magana ma kinga gashin nan naki wallahi inda nice ke koh kitso ma bazanyi ba bazan daura dankwali ba ma in rinka cancarewa abina lokaci na ne amma ke yaya gaki kyakkyawa amma ke baki damu da duk wani kyale kyale ba ..
Adan harzuke reetaj tace ehh bandamu ba kinji banason wannan surutun banzan naki kinaji ?? Meye wani abun burgewa kina yawo ba dan kwali wai idan zakiyi haukan nan naki bakyayin tunani ne?
Tabe baki awaaz tayi tace ai fah dama nasan aikin kenan daka magana ta fatar baki abu yazama na masifa' reetaj tace nice masifar ?? ' shiru tayi
Tana murguda baki' reetaj tace allah ya shiryeki awaaz. Juya ido tayi tace amin ya allah kinaji kuma wayar ki tana kara kinqi kulawa . Dafe goshi reetaj tayi tace ohh Allah na inaga wannan uban takurar ne nifa wallahi gaba daya yafiye takurawa .
Dogon tsaki awaaz taja tace wallahi kidena irin haka yaya!!
Babu dadi fah yanzu sabida Allah saurayi kamar yaya muhsin ai ba irin wanda ake jawa aji bane kodan kinga yana sonki ne kike wulakanta shi?? Amma mutum hadadde ga kyau ga kudi ga iya salo amma duk hakan baya jan hankalinki kai yaya dan Allah nifa wallahi banaso ki masa abunda ze kaurace mana babu lallai kisamu wanda ya kaishi ma bare wanda yafishi kuma wallahi wulakanci babu dadi yaya kiji tsoron Allah """ reetaj tayi tsaki ta jefa mata kwalbar turare tana cewa jarababbiya zaki fara kenan dalla maza ki daga kiran kice masa bacci nake '
Babu yadda awaaz ta iya haka ta daga kiran gami da sallama. ya amsa cikin farin ciki yace kina lafiya?
Lafiya lau amma ba itace ba.
Da mamaki yace da gaske kodai na takura miki ne gimbiya??? Sakin baki awaaz tayi tana kallon reetaj '
Ita kuwa jin haka yayi mata dadi sosai tayiwa awaaz alamar tayi magana .
Yawu ta hadiya muqut.. Kafin ta kakalo murmushi tace haba dai ni na isa ince ka takura min ai babu takura tsakanin mu, yayi murmushi yace naji dadin haka ba kadan ba ya su umma ??
Suna lafiya lau yayi kyau shiru ne yabiyo baya kafin yace yaushe zan ganki ne gimbiya?" Ido reetaj ta zaro tana kallon awaaz cike da son taji abunda zatace. Awaaz tace koh ya....
Saurin katse ta tayi ta hanyar yimata dak'uwa ,, tayi saurin cewa uhm duk lokacin da kaso , yayi murmushi yace bakyason magana sosai, shiru tayi. Ya kara da cewa ko ba haka bane gyada kai tayi tace eh haka ne, yace toh shikenan sai na kara kira sai anjima koh ?? Awaaz tace eh.ohh. Allah ya kai mu, ya amsa da amin kafin ya kashe wayar, kwashewa sukai da dariya reetaj tace kiji fah dan Allah wai yana wani gimbiya gimbiya kuma koh muryar gimbiyar be sani ba hamago, ta karasa tana dariya, awaaz ma dariya tayi tace wai da gaske muryar mu tana kama?? Tabe baki tayi tace toh oho dai nima ban sani ba amma dai kinga shi be gane ba ,
Awaaz tayi murmushi tace yaya dan Allah ki riqi yaya muhsin hannu biyu, murmushi reetaj tayi tace toh awaaz hmm ke nema kike kisani a matsala wai gani kike sona yake koh kuwa kin zata ma soyayya muke?? Ni kawai dai ina mutunci dashi ne kuma shima nasan haka yake dauka ta ,
Awaaz tace toh idan hakane meyesa ze kiraki gimbiya ?
Ban sani ba amma ta yuwu kawai sunan yana masa dadi ne kawai kidena wannan mugun zaton naki awaaz dan Allah koh so kike in kamu da son wanda baya sona toh ni koma yace yana sona bazan so shi ba kinji ki fadawa wanda raki yake so bazan taba sonshi ba tinda son ba hauka bane daka mutunci sai so kawai saboda ma bashida kunya!? Allah yasa ma naji yace yana sona inyi rugu rugu dashi yadda bama ni ba ko wace mace ma tsoron ta zeji kiji kuma ki gane , ta yuwu ma bashida kanwa mace shiyasa yake mutunci damu har yake kiranki kanwar sa ni kuma gimbiya amma ba dan komai ba...
Hmm abun takaici fadar awaaz kenan lokacin da take shirin fita
Reetaj ta rakata da harara tace shashasha,,
Chapter 4 · 0% Book details