← Book details Sirrin Keta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 47

Sashe 23

Sirrin Keta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga haka ta haye sama tana huci sithara da roooh ne suka mara mata baya sai faman kiran ta sithara take mhamah ko kallon su batayi ba,

Sai da ta dangana da barandar ta ta sama sannan ta tsaya tana kallon qasa..
Roooh yace mham... Be qarasa ba ta katse shi da cewa...
yaa'' isaa' haka roooh bana buqatar kowa kawai ku tafi ku barni ni kad'ai kar ran ku ya 'baci yanzu,
Babu yadda suka iya haka suka baro ta sai kai kawo take ta rasa zaune ta kasa tsaye,

A qasa kuwa abbu ne yace gaskiya kun 'bata mata rai da yawa ba haka ya kamata kuyi ba,

ammuu ta ta'be baki tace dama mana ai duk me hankali indai yaji wannan zance yasan zance ne mara tushe ayaan baze aikata hakan ba amma su an fad'a sun yarda har suna 'batawa yaro rai beji ba be gani ba,

Bhabhai yace kina nufin dai mu bamu da hankali??

A"a d'an uwa ba haka nake nufi ba,

Abbhai ne ya kalle ta yace maza ki tattarasu ku koma ciki,

Yadda yace hakan tayi shi kuma ya maida kallon sa ga y'an uwan sa yace a nan dai qanwa ta tana da gaskiya sannan ammuu ma gaskiya ta fad'a yaya Almustafa kaine babba kai ya kamata ace ka fara tunani me zurfi dan shi dama d'an uwa na kawai koda yaushe a hasale yake amma tsakani ga Allah ya kamata muyi tunani a kai ayaan baze fad'i haka ba in da ace ayaana aka ce zan iya yarda amma ba ayaan ba , ya kalli bhabhai yace..
Haba d'an uwa na meyesa kake hanzari akan irin haka kawai dan kanajin cewa kaine ka haife d'an shikenan sai kai ta masa fad'a akan abunda kasan ko a wasan kwaikwayo baze yuwu ba?? bance ummin mu tayi qarya ba amma ku tambaye ta indai tace muku a gaban ta ya fad'a ta gani da idon ta taji da kunnen ta to na yarda amma itama fad'a mata akai fah ita ma ta fad'a mana kuma irin haka yaro baya buqatar hayaniya nasiha za muyi masa koda yana da laifi ku fahimta mana y'an uwa na ,

Abbu yace gaskiya ne wannan nima dai nayi mamaki sosai ya kamata muyi bincike kafin yanke hukunci kun ga yanzu kun 'batawa hindoo rai kuma ai ba kwace zaku ga laifin ta ba dan tayi magana a kan gaskiya kuma kun san bata goyon bayan yaro sai da dalili,
Bhabha yace eh gaskiya ne hakan ma amma yana da kyau ayiwa yaro fad'a idan akace yayi laifi musamman a wajen babba saboda sauran yaran ma duk me shirin yayi irin laifin ko makamancin hakan ze ji tsoro kuma koda be aikata ba ya kamata su san irin darajar da manya suke dashi,
Bhabhai yace ni kukan da naji ummin mu nayi shine ya tayar min da hankali,

Muryar roooh ce ta katse su a zuciye yace Gashi nan mhamah ma ranta ya 'baci baku san ko waye ya had'a munafurcin sa ya fad'a ba kawai kun yiwa yaya na fad'a ta yuwu ma wannan shaid'aniyar yarinyar ce ta had'a fad'an kuma indai na gane itace duk abunda nayi mata ita ta siya ta yuwu ma sai na kashe ta dan na riga nayiwa kaina alqawarin duk wanda ya ta'ba min yaya na bazan qyale shi ba,

Zuba masa ido sukayi shi kuwa ya wuce abunsa
Abbhai yace kaga irin ta ko shi wancan yafika zuciya d'an uwa na kuma gaskiyar sa dan kuwa ayaana sai dai Allah ya shirya kawai amma bata ji gaskiya....
Basu wani tsaya jajantawa ba suka ci gaba da hirar su...

Mhamah tana tsaye ayaana ta hawo kusa da ita ta nufa tace mhamah ?? Mhamah wai meyesa kike ta fushi haka??
Mhamah dai bata ko motsa ba bare ta sa ran zata kula ta zata kuma wata maganar mhamah ta dakatar da ita ta juyo tana zuba mata idanun ta masu kwarjini tace na sani..
Firgita ayaana tayi ganin mhamah tayi kamar ba ita ba a tsorace tace mhaa... Katse ta tayi tana nuna ta da yatsa tace....
Karki fad'a min komai na sani komai ummi tace anyi mata kece kika shirya kuma kika fad'a akwai abunda zaki fad'a min ne?? ???????
Ayaaan shine d'an da na fara haifa ina son shi fiye da duk wani zaton mutum zan iya jurar komai amma bazan juri ganin 'bacin ran sa ba ko meye zakiyi masa wannan a tsakanin ku ne amma karki sake ki had'a shi fad'a da iyayen sa ko ki aibata shi idan kikai hakan tabbas zaki gamu da 'bacin rai na..
Na tsani ko mene ne yasa shi damuwa,
Farin cikin sa shine farin ciki na rasa farin ciki na kuwa shine yake nufin rabuwa da farin ciki a cikin wannan gidan namu...
Ayaaana fashewa tayi da kuka tayi matuqar firgita da ganin yadda mhamah ta canja lokaci guda ta iya cewa bata ta'ba ganin 'bacin ranta irin na yau ba tinda take...
sai yau ta tabbatar da irin muhimmancin da ayaan yake dashi a gurin mhamah murya na rawa tace...
mhamah dan.....

Katse ta tayi da cewa kinyi kuskure kiyi gaggawar gyarawa ina so kije ki bashi haquri sannan ki fad'a wa ummin mu duk abunda kika fad'a qarya ne kinji ko???????????

Da gudu ta juya kai tsaye sashin su ta nufa a d'an qaramin falon sa ta tarar dashi yana zaune kan kujera yana danne danne,
A kan sa ta tsaya tana kuka taqi magana ido ya zuba mata yana mamakin abunda ya kawo ta yana shirin yayi magana ta fad'a jikin sa qanqame shi tayi tana ci gaba da rero baitukan kukan ta...
Shiru yayi mata itama batace qala ba sai kuka har bacci ya kwashe ta sai da ya kammala abunda yake sannan ya d'auke ta cilak ya sa'ba ta a kafad'a lokacin har dare yayi sosai kusan 12;00 ta wuce ...
Ba tareda tsoro ko shakka ba ya nufi shashin mhamah da ita... Haka ya wuce abbhai da bhabhai a falo ko kallon inda suke beyi ba ya wuce sunyi mamakin ganin su tare mutanen da basa iya had'a hanya,,

Mhamah tana zaune bakin gado tana lazumi ya shiga ya wani sauke rumfar ido mhamahn ma ko kallon ta beyi ba kan makeken gadon ta ya qarasa ya kwantar da ayaana ya lullu'be ta ya juya ze fita har yaje qofa mhamah ta kira shi...

Meri bechchaah""!!!!!

Tsayawa yayi kamar wanda akaiwa dole yace mhamah??

Murmushi tayi tace zo nan ka zauna,
beyi gardama ba ya zauna kusa da ita kamar bata san anyi ba tace me ayaana take a wajen ka kuma??

Mhamah nima ban sani ba kawai tazo tana ta kuka ne har tayi bacci ,,

Hmmm shikenan amma ranka ya 'baci ko??
Ka fad'a min gaskiya ya akai hakan ta faru shin kaine ka fad'a da gaske ?? Ko kuma ayaana ce dai??

Shiru yayi sai ma rungume ta da yayi yana zubda qwallah

Murmushi tayi tace kana da saurin kuka bhetaaa shiyasa ayaana take raina ka kayi shiru baka fad'a min ba?

Mhamaaah""

A shagwa'be ya kira sunan ta..
Ta amsa da uhmm ? Inyi shiru ko ??
To shikenan na dena magana kaima ka dena kuka komai ya wuce indai akan 'bacin ran da mahaifin ka yayi ne shima wannan ya wuce kaje ka kwanta kayi bacci ka huta gobe zaka fita da wuri nima in Allah ya yarda da wuri zan fita zanje asibiti zan duba marasa lafiya kaji kayi addu'a kafin Kayi Bacci... Ko dai inzo in raka ka??

Girgiza kai yayi alamar a"a,

Washe gari tin sassafe ayaana taje har gida ta gaya wa ummi cewar ai qarya take nan kuwa ummi ta fara kuka jage jage ...
Babu 'bata lokaci ta taso qeyar ayaana suka taho wai tazo bawa me gidan ta haquri ayaana kuwa sai zare ido take ganin aarmaan da roooh sai harara garke suke mata tasan su kad'ai ne zasu iya lallasa ta bhabhai da bhabha sun d'anyi mamakin jin cewa ayaana ce ta had'a wannan kitimurmura abbhai kuwa dama yasan halin kayar sa tinda shine ya haife ta shiyasa dama be gazgata lamarin ba tun farko yasan akwai lauje a cikin nad'i,

Islam ya kwashe da dariya ganin yadda kowa jikin sa yayi sanyi gashi dai ummin har yanzu kuka take tana cewa dole sai ayaaan yace ya yafe mata shi kuwa da alama allurar miskilancin nasa ta motsa yayi banza da ita sai qasa qasa yake da ido..
Aslam ya kalle shi yace kai kuma lafiya ???
Be dena dariyar ba yace abun ne ya kaimin harr... Mad'iga in gaya maka.. wai tazo tace an mata laifi yanzu kuma sai an yafe mata kaji wata fitina fah su su bhabhai basu sani ba wannan tsohuwar fa tafara rikicewa,

Ayaat ma dariya tasa tace wallahi nima naga alamar hakan ga dai yadda take kuka harda majinar ta abun ta,,
Suka kwashe da dariya duka yaran sai suka fara dariya ummi ta tsaya da kukan tana kallon su ganin da gaske suke yasa taqara fashe wa da kuka tana cewa yanzu saboda Allah dariya kuke min kaduba ka gani fah dan Allah,,

Ayaaan ne ya kira sunan islam a tsawace hakan yasa duk sukai shiru suna muzurai,

Da qyar suka samu suka lalla'ba ummi dan kuwa da gaske ta fara rikici su kansu su bhabha sai da suka jinjinawa lamarin ta... Bayan ta tafi aarmaan yaso ya casa ayaana amma ayaan ya hana dole ya haqura,,,

Reeetaj..

Cikin doguwar rigar atamfa ta shirya ta yafa mayafin ta a ka tayi kyau sosai duk da ba kwalliya tayi ba bama a nutse tayi shirin ba dan kuwa gani take ta makara mukullin mota ta d'auka ta fice tana sauri sauri karo tayi da yaya hafiz tace ina kwana yaya hafiz bata tsammaci ze amsa ba sai taji yace..
Lafiya reeetaj yaya ahmad fa fad'a suke akan wannan aikin naki bazaki iya haqura ba?? Karfa abba ya qara yin fushi dake ,
Chapter 23 · 0% Book details