← Book details Sirrin Keta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 47

Sashe 22

Sirrin Keta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hmm... Cokaleti dai aikin kenan shan zaqi da zafi had'a gishiri da suga guri d'aya ,

Yayi dariya yace.. Kaka ta ba cokaleti ake cewa ba,

To koma dai meye ai ka gane me nake nufi yanzu bari in d'akko maka sai kai ta sha sannan mu gaisa muyi hirar yaushe gamo tinda yanzu bakwa ziyara jaaa"irai kaga iyayen ku kullum sai sun zo sun gaishe mu baqaramin abu bane yake hanasu zuwa kullum amma ku banda ku,

Shi dai murmushi kawai yayi,
Ta tashi ta tafi d'akko masa,
Ba zato ba tsammani yaga ayaana tsaye a kan sa ido ya zuba mata cike da mamakin duk tsiya dai yasan makaranta aka tura ta da alama dai gwangwaneta tayi,

Cike da tsiwa tace kaii me kake kallo ne wai.. meye ya kawo ka gidan nan??
Kace wani kakar ka.. ko ai kai yanzu baka da wata kaka duk sun riga sun sheqa kuma dama ba sanin ta akai ba hasashen ma da ake kawai y'ar yawon ta zubar ce tazo ta haifeshi kuma taci gaba da tafiya ka dena wani kiranta kakar ka kaje kai tambaya ina taka take amma ba wannan ba kaji ko???

Idon sa da suka qara rikicewa ya zuba mata cikin baqin ciki da 'bacin rai...

mahaifina????,

Gira d'aya ta d'aga masa alamar eh hakan take nufi ta qara da cewa wannan siyan ta akai ba ta asalin bace kaje ka nemo waccan shishshigin nan naka ya fara wuce gona da iri,

Baze iya jurar zaman gidan ba dan haka ya tashi ya tafi kafin kaka ta dawo,

Tana zuwa ta tarar da ayaana ta zabga tagumi,
Qarasowa tayi tace lafiya qawata ina yayan naki yake ??,

Kuka ayaana ta saki tana cewa yanzu kaka dan Allah meyesa bhaiya ze ci miki mutunci haka me kikai masa?? Wai harda cewa ke ba kakar sa bace Allah ya kyauta ki zama kakar sa wai ke siyo ki akai kuma ke y'ar yawon ta zubar ce baki da wani amfani saboda haka baze zauna a gidan ba cokaletin ki na banza allah ya kyauta yaci abun hannun ki qazamar banza anzo an jibge ki a gidan mutane baki da jikan ki na kanki sai dai kita cewa y'ay'an mutane jikokin ki to shi ba jikan ki bane kije ki nemo naki jikan,,,

Zaman y'an bori kaka tayi tana numfarfashi yanzu yaron nan ne ya fad'i haka??

Ayaana tace nasan dama bazaki yarda ba nima sai da ya qare min zagi sannan ya tashi yayi tafiyar sa ,

Kuka kaka ta farayi cikin baqin ciki da takaici. Tace ai kuwa sai na kira iyayen sa na tambaye su yaushe suka siyo ni kuma yaushe nake yawon banza,,

Koda ya isa samu yayi ya salalla'ba ba tareda ya bari kowa ya ganshi ba ya wuce sashin su,

Da daddare kowa ya hallara a cikin gidan suna hira sai ga kiran kaka yazo..
Abbhai ne ya d'auka cikin biyayya ya gaishe ta,

Bazan amsa ba yanzu haka alqawari yace y'ay'an nan??

Cikin rashin fahimta abbhai yace ummin mu ban gane ba meye faru ne ??

Bhabhai ne ya kar'be wayar yasa handsfree yadda kowa ze ji yace ummin mu me yake faruwa ne ??
Tana kuka ta zayyana musu abunda ayaana tace mata a matsayin ayaan ne ya fad'a,

Ai kuwa take ran ko wannan su ya 'baci,

Bhabha ne yace a nemo masa ayaaan ba musu Abeei ya tashi jiki ba qwari yaje ya kira d'an uwan sa,

Abbhai da abbu da nasiha zasuyi masa amma bhabai da bhabha suka fara fad'a ta inda suke shiga ba tanan suke fita ba,

Sunkuyar da kai ayaan yayi hawayen baqin ciki suka sheqo masa,

Bhabhai yace kukan banzan me kuma zakai min anan ??

Bhabhai nifa ban sani ba bance mata kom....

Tsawa bhabhai ya daka masa kana nufin qarya zatai maka ummin ??
Ya d'aga hannu ze sheqe shi da mari..

mhamah ta dakatar dashi cikin tsawaa tace.....

Meri!!!! Patteei!!!!!!!

Sai da kowa ya firgita saboda yadda tayi magana cikin qaraji musamman ma ganin wanda take dokawa tsawa haka shine yafi firgita yaran su da suke wajen.................................

Reetaj jikin ta na d'ari d'ari ta shiga gidan a falo ta tsaya ta tambayi y'ar aiki matar gidan..
Tace tana sama sai dai a sanar mata ,

Reetaj tace to dan Allah jeki ki sanar mata,

To wacece zance mata ??

Kice mata reetaj ce ,

To ta juya ta tafi kiran awaaz ko mazauni basu bata ba ,

Haka take ta tsayuwa har ta gaji sai ga y'ar aikin tazo tace mata wai tace me ke tafe dake ??

Cikin mamaki reetaj tace meke tafe dani ko dai bata gane wace ba kice mata reetaj ce fah yayar ta ko gurin zama fah baku bani ba kun barni a tsaye kuna min wata tambaya ,

Samira tayi dariya tace kiyi haqiri haka tsarin uwar d'akin mu yake idan muka baki wajen zama ba tareda izinin ta ba shikenan tamu ta qare har sai tace mu karrama mutum sannan mukeyi da alamu ma ke baki da wata daraja a gurin ta ba ma lallai ta fito ba ,

Mutuwar tsaye reetaj tayi saboda mamakin irin wannan sabuwar rayuwa da awaaz ta tsirarwa kanta saboda rashin tsoron allah,
ko zata wulaqanta wani ai ni beci ta wulaqantani ba ko dan gashi ma y'ar aikin ta ma bata qyale ni ba bare ita??
Nima me ya kawoni gidan awaaz tinda nasan ita da gaske ta tsane ni ta manta da duk irin shaquwar da mukayi abun duniya ya saka ta cikin rud'ani?

Samira ce ta dawo tace ..
Tace ke d'in me kike buqata wane temako zata baki ??

Hawayen da suka cicciko idon ta ne suka gangaro tace babu komai dama na dad'e ban ganta ba shine nace bari nazo mu gaisa amma zan tafi sai anjima ,
Aa ki tsaya ai tace in qarasa dake falon ki zauna ,
Reetaj ta so tafiya amma allah ma ya sani tana son ganin y'ar uwar ta shiyasa tabi bayan samira,

Kan sofa ta zauna tana tsammanin fitowar awaaz..
Tin tana sa rai cikin qaramin lokaci har lokaci ya girma tafi minti 20 kafin ta fito cikin wata shiga ta alfarma taku take cikin kasaita kamar wata giwar sarki tana taunar cingam qaras qaras ,

Murmushi reetaj take da ganin ta tace awaaz sai kika ganni kwatsam ko??

Ko kallon ta batayi ba sai qwalawa samira kira da tayi ,
Samira tazo jikinta na tsuma tace gani ranki yadad'e.
Awaaz tace bani kuncin ki ,
Haka samira ta miqo mata fuska ta zabga mata tafi sannan tace.
Nace miki ko wace qazanta nake d'orawa a kan kujera ta ??me yasa zaki sa wannan mara galihun ta zauna min a kan kujera??
Samira tace kiyi haquri ranki yadad'e,
Baiwar Allah ki sauka ki zauna a kan carpet,
Zamewa reetaj tayi ta zauna a qasa,
Awaaz ta hakince a kan kujera sannan ta kalli reetaj cike da qasqanci tace ke kuma ina jinki kinzo dandalar arziki ne ??
Kodai wata alfarmar kikazo nema??

Reetaj tana murmushin ta wanda baka iya fassarashi a lokacin da take cikin baqin ciki ta girgiza kai tace a"a kawai nazo mu gaisa ne ,

Awaaz tace ki fad'i gaskiya karkiji kunya ta idan te mako kikazo nema ,
A"a awaaz nifa banzo neman komai gurin ki ba kawai gaisawa zamuyi,

Awaaz tayi qaras qarassannan tace shikenan ai mun gaisa sai ki tashi ki tafi tashi tayi ta watsa mata kud'i sababbi y'an d'ari d'ari tace gashinan ki kwashe sai kiyi na mota ko ki rabawa qolawan ki,

Tayi gaba tana cewa asabe maza a tsaftace falon nan da Alla a fesa turare a gyara kan kujeran can da ta zauna,

Murmushi reetaj tayi tace nagode sosai awaaz amma bana buqatar wannan kud'in naki dan a motar Dabo aka kawo ni su kuma qolawa na sun fi qarfin d'ari d'arin ki dan su ba yara bane daga haka ta fice tana sharar qwallah ,

Awaaz kuwa suman tsaye tai jin wanda reetaj ta ambata DABO??
Ai kuwa tana yawan jin dabo a bakin muhsin kuma yace mata masu mugun kud'i ne qirjin ta ne yafara bugawa rass rasss tayaya hakan zata faru ina reetaj zata samu motar Dabo ai kuwa qarya take gaskiya qarya take bazan yarda ba,
Awaaz ta gazgatawa kanta cewa qarya reetaj take dan haka abun be dame ta ba ko banza dai ta muzguna mata kuma ta nuna mata iyakar ta ta nuna mata yanzu tafi qarfin ta ta riga ta wuce tsara murmushin qeta ta saki sannan ta juya taci gaba da tafiya,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,

Comment and share dan Allah🙏🙏🙏🙏

Karku manta da sharhi🥰🥰
https://facebook.com/groups/575599953675542/

*💫💫ANNURI WRITER'S ASS.*💫💫
(Annuri is the best)

*(A.W.A)*

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FEViiYLkmiwKIUEZc2PcLD

*SIRRIN QETA*

*Page* *33~34*

*by yar gatan annuri writers*

🎉🎉 *Indo ce..*🎉🎉

*بسم الله الر حمن الحيم*

Mhamah..
Jikinta har kakkarwa yake saboda tsabar b'acin rai...

Kar ka sake ka dokar min d'a,

Ta fad'a tana zazzaro masa gwara gwaran idanun ta wanda suka wadatu da gazal,

Abbhai ne ya kalle ta cikin takaici yace wa kike daka wa tsawa akan d'an ki haka??

Akan me bazan yi tsawa ba?? Akan me zan bari a dokar min d'a na akan abunda ba shi ne ya aika ta ba ??
Ba zan lamunci hakan ba kuma duk wanda ya sake hannun sa yayi gigin ta'ba min d'a na rantse bazan qyale shi ba ,

Bhabha cikin 'bacin rai yace yanzu kenan kina nufin idan d'an ki yayi laifi ba za a hukunta shi ba ko baza ai masa fad'a ba?? Mu zuba ido kike nufi ??

Bhabhai yace haka kike so kiji ko to idan shi bata haife shi ba mu ta haife mu uwa ce a wajen mu,

Qasaitaccen takun ta tayi d'ai d'ai har sau uku kafin tace idan d'a na yayi laifi indai har nasan yayi bazan ta'ba hanawa a hukunta shi ba kafin ma wani yayi qoqarin hakan da kaina zan hukunta shi amma ban yarda a d'ora masa lafin da bashi ne yayi ba kuma duk wanda yake da shirin hakan yayi ni kuma zan baku mamaki,
Chapter 22 · 0% Book details