Sashe 13
Sirrin Keta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ihun da taji ya dawo da ita daga kalle kallen wasu y'an mata ne guda biyu sai wasu wanda basu kaisu girma ba su kuma su uku da mata da maza..
Suka fito suna tsalle tareda ihu suna dariya da alama duniya ce tagama kai musu tsolo...
Kai tsaye wajen yalla'bai reetaj taga sun nufa nan fa d'ayar tayi tsalle ta fad'a kirjin sa yawan fara"ar sa ne ya qaru daga ganin su d'aya bayan d'aya sai da suka rungume shi har qananun yaran,
Dafe goshi reetaj tayi tace innalillahi yanzu ashe wannan yalla'bai d'in mutumin banza ne ashe ma d'an iska ne????? ,
Haka yake rungumar mata dan iskanci ??
Tana tsaye ta qara ganin wasu y'an samari su uku sun fito sai d'aya a bayan su abun da ya bata mamaki ganin su ma duk sai da suka rungume shi,,,
Zuwa yanzu reetaj ta fidda rai da komawa gida a cewar ta ta shigo inda ba'a fita,
Haka sukai ta fitowa kowa sai ya ringumi yalla'bai tin tana iya fassara abun har ta kasa fassara shi a matsayin komai sai ikon Allah,,
wani me kama da yalla'bai ne ya fito yana takawa cikin kasaita wadda da alama abun a jinin su yake,
Shima murmushi ne a kan fuskar sa ya rungume d'an uwan sa,
Runguma ta haqiqa me cike da so da qauna da kulawa da alama suna matuqar qaunar junan su ,
Sai a lokacin taga haqoran yalla'bai dariya yake sosai yayin da me kama dashi d'in yake magana kuma har lokacin suna rungume da juna har na wani lokaci kafin su rabe sannan me kama dashi d'in yaci gaba da magana yana dariya shi ma yalla'bai ya zuba masa na mujiya bayan ya gama ya d'an doki kafad'ar sa suka qara kwashewa da dariya suka qara rungume juna,,,,,,
Abun mamaki wata matar ce again ta 'bullo ta bayan sa itama babbar mace ce ..
Wayyoh Allah na yau naga ta kaina abun mamaki kuma duk shigar su ta kayan ball ce kuma dukan su inda matar nan ta farko tayi suma nan sukeyi ko me zasuyi oho,,,,
kuma shigar su duk iri d'aya sai dai banbancin kala ....
Reetaj ce take surutun ta ita kad'ai,
Matar kuwa dafa kafad'ar sa tayi
Hanun nata kawai ya kalla ya gane ko wacece ya riqe hannun nata sannan ya juyo rungume ta yayi tana murmushi ta shafi kansa kalma d'aya kawai ta furta tayi gaba abun ta,
Reetaj tace da alama wannan ce mahaifiyar sa dan naga ita kamar da alkunya a cikin lamarin ta amma ba irin ta farkon nan ba,
Bayan ita ma sai ga wata itama babba ce amma ba kamar ta farkon da ta biyun ba,
Itama rungume shi tayi tana dariya sannan ta sake shi tayi gaba,
Me kama dashi d'in ma dafa kafad'ar sa yayi ya fad'a masa wani abun sannan ya wuce,
Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke. wadda sukayi ta a tareda reetaj ,
Dafe qirji tayi tana cewa allah ya rufamin asiri basu ganni ba da tuni kwana na ya qare,
Shafar sumar kansa yayi ya furzar da huci ya taka da shirin shiga ciki wata budurwa ita kuma a lokacin ta sako kai,
Jin irin qarar tarkacen jikin matar nan yasa reetaj ta dawo hayyacin ta da sauri tana cewa wayyo Allah kodai gurina ta dawo abun mamaki sai taga ba matar bace ashe wata budurwa ce ita da gudu gudu ma take tafiya,
Abun da ya d'aurewa reetaj kai matuqar kama da matar yarinyar take gashi irin shigar su d'aya kafar da qunshi ga tarkacen kayan ado ta d'aure gashinta da qaramin ribas sai wata sarqa a wuyanta yanda kaga shigar waccan matar komai da komai ita ma haka take gashin ta wanda ya kusan kama qugunta sai tsalle yake a bayan ta,
Reetaj tace inaga dai wannan itace y'ar wannan matar ,
A memakon rungumar sa da taga sunayi sai taga ta had'a iya qarfin ta ta bangaje shi har sai da yayi taga taga kamar ze fadi' sai ya tirje ,
Bata waigo taga halin da yake ciki ba tayi gaba abunta sannan ta d'ago masa hannu cike da alamar tsiwa tayi magana ba da hausa tayi ba shiyasa reetaj bata gane me take cewa ba... Shi kuwa rakata yayi da ido har ta 'bace sannan ya shiga ciki,
Ajiyar zuciya reetaj ta sauke ta jingina da motar sa tace aikin banza.. Aikin banza.... Gaskiya nima cikakkiyar mahaukaciya ce gaskiya ya kamata naga likita banda tsabar shahara irin tawa mutumin da bayajin hausa nakewa hausa ba dole yaqi kulani ba ? Toh yace min me ma banda haukana kuma na manta da turanci ma sai nai ta masa hausa ashe fah bayaji aikin banza inaga da tini ya samin hannun ma na tsaya shirme,
Dafe goshi tayi tareda cewa ohhhh na shigenge ai kuwa fah inaga yalla'bai d'in nan kurma ne baya magana..
naga dai shi da y'an uwan shi ma be bud'i baki yayi musu magana ba sai dai murmushi da dariya ai kuwa hakan ne ma..
ayyahh Allah sarki har yabani tausayi bawan Allah shiyasa sai ai ta magana yayi shiru Allah sarki gashi saurayi me tashe amma gashi kurma,
Be wani b'ata lokaci da shiga cikin ba ya fito shima cikin irin nasu shirin ya nufi inda suka nufa ,
Reetaj bata damu da ganin me sukeyi ba dan haka tayi zamanta a wajen duk ta shagala sai kallon tsuntsaye take dan ita dai a rayuwa tana qaunar tsuntsu shiyasa taji zaman wajen yafi mata da'di ,
ta shiga shauki da farin ciki sosai wanda ta dad'e batayi kamar sa ba,
Kwata kwata bata tunanin tafiya gida ta manta a inda take ma ta manta kuma lokaci tafiya yake bata ta 'bata lokaci me yawa a wajen ba,
Bataji takun mutum ba tana cikin yin baya baya taji tayi karo da wani juyowa tayi a firgice taga yalla'bai ne jikin sharkaf da ruwa ya jike har d'iga yake ,
Baya tayi da sauri tana cewa yi hakuri yalla'bai,,,,,,,
Bata ta'ba zaton zataga wani a kusa ba ashe tareda wannan matar yake ,
Tinda ta d'ora idon ta akan reetaj duk wani annuri na kan fuskar ta ya gushe musamman da taji tanayi masa magana ,,
Idon nan nata ta tsura masa tanai masa kallon tuhuma,
Sunkuyar da kai yayi kamar munafuki,
Cikin yaren su take magana..
Koda reetaj bataji amma ta gane tambayar sa take wacece.
dan haka tayi qarfin hali ta tuno da turancin nata da take mantawa dashi tace.
Dama ina neman aiki ne a wajen yalla'bai shine ze sa min hannu kuma sai ya tashi tafiya ni kuma da yake inason sa hannun sosai shine na kasa haquri na biyoshi nan ,
Wani mugun kallo matar ta watsawa reetaj har saida akuyar cikin ta tace ummeeeeee!!!!!
Shima wani kallo tayi masa ta wuce ta gefen sa sauran y'an uwan sa ma duk suka wuce suka barshi a wajen ,
Ta bud'e baki zatayi magana ya watsa mata idanun sa masu matuqar kaifi wanda suka fara rikid'a ,
Had'iye wani qullutu tayi muquuttt .. Tana zazzare ido,
Kafin tayi aune taga masu kula da gidan sun zagaye ta kansu a sunkuye da alama umarnin sa kawai suke jira ,
Babban su ne ya d'ago ya kalle shi a yanayin fuskar sa ya gane me yake nufi dan haka yacewa reetaj maza kibar wajen nan umarni ne,
Shi kuwa yalla'bai tafiyar sa yayi ya barta ,
Sanin ba hankali garesu ba ma'aikatan zasu iya cicci'bar ta yasa babu musu ta shige mota ta fice ,
Koda taje gida tunanin abunda ya faru take ta faman yi yau taga abun mamaki wanda a tsawon rayuwar ta bata ta'ba ganin haka ba ashe shi muhsin da yake ta cika bakin mahaifiyar sa tana son shi sosai a kwai wanda suka fita wai ma wannan abun so za"a kirashi ko hauka?
Bata da me amsa mata tambayar dan haka tayi shiru...
Tunanin abun ya hana ta sakat idan ta rufe ido fuskar yalla'bai kawai take gani musamman lokacin da yake dariya da kuma lokacin da tabari wannan matar ta ganta tabbas alamar bacin rai ya bayyana a kan fuskar sa sosai.
Gaskiya ban kyauta masa ba karfa hakan ya zama rigima a cikin su. gashi allah sarki da alama me haquri ne. In ba dan haka ba ai wulaqancin yarinyar nan ma kawai ya ishe shi jaraba idan da ba me haqurin bane,
Zaro ido tayi tace wai ni kuwa ze saka min hannun kuwa naga ya fusata sosai wallahi wayyo Allah na gaskiya ya kamata na bashi haquri ai kuwa gobe da wuri zan shirya inje karma lokacin tafiyar sa yayi,
Kashhh ta fad'a lokacin da ta tuna gobe asabar ayyah shikenan na gama yawo ai kuwa ba lalle yasa min hannun nan ba ko dai haqura zanyi??
Girgiza kai tayi tace a"a be kamata na haqura cikin sauqi haka ba kamar ba nice reetaj d'in nan ba wadda ta fuskanci komar maza da yawa ?
Gaskiya zanyi qoqari sosai ko zan iya bugawa dashi har na samu nasara.. Toh amma fa shi ba kamar kowa yake ba da alama.
amma dai hakan zan jaraba insha Allah,,,,
Haka tai ta tufka da warwara ita kad'ai,
shigowar su fatima ne yasa ta daidai ta nutsuwar ta duk wata shiririta ta dena,
Kamar yadda suka saba binta sukai da kallon banza da habaice habaice ita dai batece kuci kanku ba ,
Comment and sharhi dan Allah🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏
https://facebook.com/groups/575599953675542/
*💫💫ANNURI WRITER'S ASS.*💫💫
(Annuri is the best)
*(A.W.A)*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FEViiYLkmiwKIUEZc2PcLD
*SIRRIN QETA*
*Page* *21~22*
*by yar gatan annuri writers*
🎉🎉 *Indo ce..*🎉🎉
*بسم الله الر حمن الحيم*
Katse wayar tayi ta rungume ta ta fashe da kuka,
Su fatima sukai shewa salma tace wata gwauruwa dai idan tayi wasa hawayen ta zasu qare ta rasa na kukan munafurcin ranar da za a kaita gidan miji,
Fatima tayi dariya tace lallai kuwa ashe zaki mutu indai kika zauna jiran ranar da za a kai wannan gidan miji ai gwauron gwauron ne in gaya miki ..
Yanda ta fito haka zata koma tazo abanza ta koma wofi hahahaha,