← Book details Sirrin Keta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 47

Sashe 46

Sirrin Keta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin tarkacen kayan abincin sa ya zaro wata y'ar qaramar wuqa nufar inda take yayi da sauri ta tashi tana cewa yalla'bai lafiya ba dai yankani zakayi ba dai ko???

Taso bashi dariya amma sai ya cije yace eh ba yanka ki zanyi ba hatimin zanyi miki sai ki bawa kanki amsa,,

Zaro ido tayi tace kai??? Yalla'bai rufamin asiri,,,

Bata gama rufe baki ba yace naqi,

Aa yalla'bai temaka dai kai da kace sai y'an gidan ku ma ake yiwa shine kuma zakace zakayi min ka yanka jiki na da wuqa kuma ina zaune???
Tab..

To idan kika bari nayi miki ai sai ki zama y'ar gidan kema ,

Ahhh yalla'bai??? na shigenge tayaya zan zama y'ar gidan ku banda neman rigima???

Qasa yayi da murya yace to idan ya kasance d'aya daga cikin y'an gidan mu ya aure ki fa??
Kinga kuwa kin shiga cikin su,,

'Bata rai tayi tace yalla'bai wannan wace irin magana ce ni wallahi tayi min tsauri da yawa ni idan kana yi min irin ta bazan kuma zuwa aikin ba na haqura gobe ma ni bazan zo ba kuma yanzu zan tafi,,

Tattara inata inata tayi ta tafi gida,

Kamar yadda tace baza taje aikin ba bataje d'in ba,

Ya tabbatar da gaske take...
Irin tsoro da banbancin da take nunawa dangin sa abun ba qaramin damunsa yake yi ba.............

Suna zaune a falon su kowa tunani yake yi,

Kamar daga sama yaji armaaan yace bhaiya ka fad'a tarkon so ko???

Shiru yayi na wani lokaci kafin yayi murmushi yace qwarai d'an uwa na babu shakka na kamu da sonta...
Ina son ta sosai kuma bana jin zan iya rayuwa me dad'i ba tare da tana gare ni ba..
Soyayya ta a gareta ba irin ta sharholiya bace bhai zan aure ta......... wannan shine maudu'i na a yanzu shi na saka gaba kuma na riga nayi qudurin hakan...
Bhai ina jin tamkar itace zuciya ta..
Ji nake tamkar itace bugun numfashi na..
Ji nake tamkar idan bana tareda ita bazan iya rayuwa ba.....
Ina ji a jiki na cewa itace mahad'in rayuwa ta.........
Rayuwa a waje na bazata yuwu idan babu ita ba.....................................

Wani mugun jiri ne ya fara d'ibar ta wanda yasa ta dena ganin haske sai duhu zaman y'an bori tayi akan kujerar falon nasu tana dafe qirjinta da yake tsananin bugawa a hankali tace...
Bethaa..........

Mhamah?????

😜 ina son ku masoya na😂😂

Comment and share Dan Allah 🙏🙏🙏

Karku manta da sharhi🥰🥰🥰
https://facebook.com/groups/575599953675542/

*💫💫ANNURI WRITER'S ASS.*💫💫
(Annuri is the best)

*(A.W.A)*

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FEViiYLkmiwKIUEZc2PcLD

*SIRRIN QETA*

*Page* *59~60*

*by yar gatan annuri writers*

🎉🎉 *Indo ce..*🎉🎉

*بسم الله الر حمن الحيم*

Murmushi armaan yayi yace dama nasan haka zata faru....
Bhaiya nima ina sonta..

Bana d'aya daga cikin wanda zasu qi son abunda kake so ina bayan ka...
zanji dad'i idan farin cikin ka ya samu nima shine farin ciki na amma nasan akwai qalu bale a gaba tabbas bhaiya baka gudun abunda zeje yazo ???

Murmushi yayi yace na shirya tsaf na shirya wa ko mene ne duk wani 'bacin rai ko qunci baze sa na fasa ba na riga nayi wa kaina alqawarin samar mata da farin ciki har lokacin da zan bar wannan duniyar kayi min fatan alkairi kawai d'an uwa na,,,,

Armaan yace to allah ya taqaita fitina,,,

A falo kuwa ammuu bayan tayi zaman y'an bori kan kujera kuka ne ya qwace mata cike da tausayawa take cewa mhamah ayaan mhamah baza ta amince ba ayaan meyesa so zeyi maka irin wannan yankan qaunar tabbas mahaifiyar ka baza ta amincewa hakan ba ni dama na sani shiyasa tin farko banso suyi abunda sukayi ba shiyasa ban goyi baya ba amma sai da hakan ta faru yanzu ga irin ta nan ina me cike da tausayin ka d'ana...
ina jin tsoron makomar da wannan abu ze janyo amma Allah shine yasan sirrin dake 'boye a cikin wannan al'amarin shi yafi mu sanin abunda yake nufi da hakan...
Amma tabbas lokacin shiga wata waa'qi'ar yayi....

Jikin ammuu yayi matuqar sanyi ta tsora ta sosai abun ya dame ta ta rasa waye zata fad'awa taji sanyi........

Zeeeny ce gurfane a gaban bokan su tayi masa bayanin komai da irin abunda take so yayi,

Y'an tsubbace tsubbacen sa ya hau yi dan da nan jikin sa ya hau tsuma alamar tsoro da razani ta bayyana a gare shi...

Ido zeeny ta zuba masa tace ya akai ne meye ya faru???

Tunanin abunda ya gani yake yi lallai wannan mutuwa ta ta kawo min har inda nake wannan mutumin ai baze sihirtu ba amma dai bazan bari wannan dukiyar ta wuce ni ba kuma ban san tsoro ba ni sai yau d'aya bazan bari suga gazawa ta ba bazan nuna tsoro ba kuma sai na tatsi rabo na nima saina kar'bi kud'ad'e yanzu kawai cewa zanyi ta kawo kud'i komai ze yuwu zatayi nasara dama irin su haka kawai suke son ji,,,

Kallon ta yayi a dake yace kamar anyi an gama zaki samu duk biyan buqatun ki idan akwai abunda yafi wannan ma zaki samu saboda ke d'in me sa'a ce babu abunda ze gagare ki yanzu kawai kud'i zaki bayar masu yawan gaske dan kuwa wannan lamari sai an dage an tashi tsaye,,,

Batayi gardama ba ta shaqa masa wasu da cewar zata dawo,,,,,

Reeetaj zaune suke a ofishin yalla'bai sai surutu take masa ita da ameeed shi kuwa sai dai idan sun bashi dariya ya dara kawai,

Kallon sa tayi tace yalla'bai??? Wai kai har yau baza ka canja ba ne??? Nifa na gaji da ganin ka da irin kayan nan saboda haka tashi yanzu muje a gwada ka ayi maka shadda ka saka ranar jumu'a d'in nan...

Zeyi magana ta katse shi da cewa...

Aaaa yalla'bai dan Allah kar kace komai...
kawai ka tashi muje har na siyo maka shadda nasan fara zatayi maka kyau dan haka kawai d'inki ya rage kuma saura ka qi sakawa kaji ko???
Tashi muje yanzu jiran ka nake akwai wani me d'inki a unguwar mu can zamuje kawai yayi maka d'inkin,

Yamutsa sumar sa yayi yace ohhhh yanzu...

Saurin katse shi tayi da cewa Tsaya yalla'bai baka qoshi da shayin bane?? Idan shayin zaka sha sai kasha a mota amma yanzu baka da wani uzurin da zakace baza kaje ba kuma saura idan munje kayi min wannan yaren naku hausa kawai zaka dinga yi kar kayi wani yare har su gane kai ba bahaushe bane kaji???

Gyad'a mata kai yayi ya tashi tana gaba yana binta zangai zangai ,

Ameed ne direba yayi shiru kawai ya zubawa sarautar Allah ido dan kuwa shi be ta'ba ganin mutumin da ya mallaki lokacin yalla'bai ba ma bare kuma nutsuwar sa tunanin sa da hankalin sa ra"ayin sa kusan ma ace rayuwar sa gaba d'aya duk da bashi da fad'a bashi da hayaniya ba tashin hankali amma yana da tsauri kuma baya son a gardama kuma yafi son abunda ya fad'a kawai shine
Amma duk wannan zamanin an wuce reetaj ta gama malleke komai wai yau yalla'bai ne yake bin wata mace yuuu yuuu kamar wani bawan ta,

Koda suka je me d'inkin yana ganin ta dashi yace reetaj ina kika samo mana ba indiye kuma???

Zaro ido tayi dan kuwa a nata nazarin idan beyi yaren su ba baza'a gane ba indiye bane ,

Sunkuyar da kai qasa ayaaan yayi yana wata y'ar miskilar dariya tare da bawa shiriri ta irin na reetaj jinjina da ban girma ban da quruciya mutumin da idan baka san asalin sa ba baza ka ta'ba cewa yama had'a iri da baqar fata ba shine wai baza a gane ba bahaushe bane,,,

Hararar sa reetaj tayi ya dena dariyar sannan tacewa salisu kai dai kawai ka gwada shi kayi masa d'inki ba sa ido akace kayi ba kaji ko??

To salisu yace yana rawar jiki ya auna ayaan bayan ya tambaye shi irin d'inkin da yake so reetaj d'in ce tayi tsaram tace ayi masa mara ado kawai asa masa ma'ballai masu kyau irin d'inkin da yake wa yaya muktar d'in ta,

Salisu ya amsa da cewa gobe za a kar'ba ,

Gida ta wuto daga can shi kuma ya koma tare da ameeed ,

Ranar jumu'at......

Ya sha farar shaddar sa kamar sabon ango tayi masa matuqar kyau sai bazama qamshi yake yi ya fito duk suna falo tinda mhamah ta gansa taji zuciyar ta ta buga ido ta tsura masa tana mamakin abunda ya canja mata d'an ta daga d'abi'ar sa ta daa' wadda babu yadda ba'ayi ba akan ya canja yaqi haka ranar nan tayi danbun bhabhai wai har dashi ake ci abun ya bata mamaki matuqa mutumin da babu yadda bhabhai d'in sa beyi dashi ba akan ya dinga cin irin abincin da yake ci amma yaqi wai meye yasa hakan ne?????????

Ayaaat ce ta kalle shi sama da qasa tace bhaiya sai yanzu ka fito a asalin bakanon ka,

Dariya yayi yace Allah ko??

Sthara tace bhaiya kuma wallahi kayi bala'in kyau anya kuwa ba eh...a...haa.. Ba...,

Ke bana son is...k..a ya fad'a yana hararar ta ,

Khaireey yace bhaiya wallahi kayi kyau sosai kamar ranar auren ka ,

Kai shakiyi ka ta'ba ganin ranar ne da har kake wani qissimawa harda d'orar wa???

Ammuu tayi murmushi me cike da tausayawa tace da gaske ne bhaiya kayi kyau sosai kuma ka tambayi mhamah kaji,,,

Kallon ta yayi tayi masa murmushi hakan ya nuna masa alamar ya had'u,

Qarasawa yayi wajen ta ya zauna yace mhamah zan fita,

Kansa ta shafa tace Allah ya dawo da kai lafiya ka kula kaji ko? Amma dai kayi kyau wannan jumu'ar ta yau ta kasance ta musamman ce...
kowa zeyi mamakin ganin ka haka kamar yadda nima nayi..
ka fita da addu"a kiyayewar Allah tana tare da kai insha Allah,
Allah ya kare ka yaro na,,,,

Murmushi yayi ya amsa da amin sannan ya fita kowa sai da ya yaba wannan kwalliya tashi,
Chapter 46 · 0% Book details