Sashe 19
Sirrin Keta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tinda ya shigo takeson gaishe shi amma ta kasa yana matuqar yi mata kwarjini ita kanta har mamakin yadda bakin ta yayi nauyi take musamman idan ta tuna lokacin da take neman aikin sai tayi ta sokanabe ba tareda shakka ba kodan lokacin idon ta ya rufe?? Ko dan bata ta'ba tunanin yana jin hausa ba shiyasa take fad'an duk abunda yazo bakin ta? ,
Da kyar tayi ta maza tace yalla'bai ina kwana?
'Dagowa yayi ya kalle ta ya maida kai kan abunda yake yi,
A take tausayin kanta ya kamata wannan ba qaramin wulaqanci bane a gaida mutum yaqi amsawa ni dama me yakaini dama shiru na nayi in riqe matsayina dan ba tsara na bane iya d'auka ta aikin da yayi ma na samu,
idon ta duk sun ciko da qwalla take wannan tunanin,
Rashin sani yafi dare duhu ita reetaj a nata tunanin bata kai matsayin da zata gaishe shi ya amsa ba..
Shi kuwa a bangaren sa ya amsa ne shiyasa ya d'ago ya kalle ta.. da baze amsa ba zeyi kamar be san anayi ba...
shi bud'ar baki yayi magana shine abun tashin hankali a wajen sa kwata kwata baya son magana ya yarda ya rubuta komai tsawon zance amma be yarda ya fad'a da baki ba wanda ya zauna dashi kuma ya nutsu ya karance shi ciki da waje shine ze iya gane yaren sa ya kanyi magana da ido sau goma beyi magana da baki sau biyar ba yawanci idan kaga maganar shi ma to shi da d'an uwan sa aarmaan ne shine kawai yake iya sashi magana,
(Da sauran kallo...... Reetaj kinada sauran aiki...)
Shirun ce taci gaba da wanzuwa babu me cewa qala sai dai aikin sa da yakeyi kawai dube duben takardu da kuma danne danne a laptop da danna waya aikin kenan,,,
Reetaj kuwa kanta na qasa sai tunane tunane take..
'Dan guntu ne ya shigo yana cewa madam lokacin shan shayi yayi,
Ido ta zuba masa cikin rashin fahimta..
Tace kamar ya??
Yace lokacin breakfast na yalla'bai yayi,
Iyyee?? Nice ma zan had'a masa shayin kenan kamar wani d'ana ko kuma wani qaramin yaro,
Ba d'an guntu ba har ayaan sai da ya kalle ta qasa yayi da kai yana murmushi a ransa yake tunanin ni dai a rayuwa qaddara ta had'ani da yara kala kala jiya wata ta zuba min gishiri a shayi yau kuma wata da yunwa ma takeso ta barni,
Turo baki reetaj tayi tace toh ina kayan shayin??
Nuna mata komai d'an guntu yayi..
ta d'akko tana mitar cewa shi kuma wannan kamar wani d'an yaye da abincin sa ma yake zuwa..
Kofi ta samu ta tsiyaya shayin sannan ta d'ebi madara ta zuba ta had'a da milo duk wani abunda ta gani na had'in shayi sai da ta zuba sannan ta ajiye masa kan tebur d'in da yake gaban sa ,
Qarewa shayin kallo yayi aransa yana jinjinawa kato'bara irin tata ,
Abunda ya bata mamaki ganin ya d'auki shayin ya miqo mata,
Jikinta ne ya fara tsuma a tsorace tace yalla'bai kayi haquri idan beyi dad'i ba ko in fifita maka??
Ganin be fasa miqo mata ba yasa ta kar'ba cike da zullumi wayyo Allah daga fara aikin yau har na fara hauka karfa nayi abunda ze kore ni,
Tashi yayi ya nufi inda kayan shayin yake da kansa ya had'a bayan ya tsiyayi ruwan shayi ya had'a da madara ...
Reetaj ce ta katse masa hanzari da cewa yalla'bai bansan meye ba amma meyesa kake had'a wani shayin?? Zazzaro ido tayi ganin ya d'auki wani kantu soyayye ya zuba da yawa a cikin shayin... Kasa shiru tayi tace yalla'bai meye kuma wannan kamar kantu dai wanda na sani kuma a cikin shayi? wannan wane irin abinci ne ??
Shiru yayi mata ya koma ya zauna yana shan abunsa da cokali hankalin sa kwance daka gani kasan yana jin dad'in abunsa,
Har wani yatsine fuska take a ganin ta ko da duka aka had'a ta ba lallai ta iya sha ba amma shi har wani lumshe ido yake...
Abun ya bata mamaki sosai har ta kasa dena kallon sa shi kuwa ko a jikin sa,
'Dan guntu ne ya shigo yace yalla'bai komai lafiya??
Ganin reetaj da kofin shayi a hannu yasa ya tambaye ta me yafaru?
Tace na bashi yaqi sha kuma ya bani,
Kallon yalla'bai d'in yayi sannan yace yalla'bai yana nufin ki shanye shayin..
Leqa kofin yayi yaga had'in shayin nata sai ya kwashe da dariya,
Abun ya bata takaici sosai sai dai tabishi da ido tana cewa ni wannan d'an guntu ya cika fitina ko meye sunan sa ma oho,
Mutuwar zaune tayi da taji yana magana cikin harshen hausa wadda dakaji kasan haye yayi ba gado ba kuma be ma gama qwarewa ba kanaji dai kasan ba bahaushen bane yace..
Suna na ameeed ne madam ba d'an guntu ba ,
Sakin baki tayi ido da hanci tana kallon sa cikin mamaki tace wai kana nufin kaima kanajin hausa!??
Yayi dariya yace eh mana ina tareda yalla'bai ai dole inji hausa ,
Cikin takaici tace kuma shine kukai ta wahalar dani ashe duk kunajin hausa meyesa kaqi yimin hausar to??
Hahaha yalla'bai be bani damar hakan ba madam sai yace inyi hausa nakeyi ko wane yare ma sai da izinin sa nakeyi'''
Dafe goshi tayi tace ni wannan mutum da wane suna ya kamata a kiraka saboda biyayya ??
Yace madam karki damu suna na ma kad'ai ya ishe ni indai biyayya wa yalla'bai d'in mu ne yanzu na fara dole inyi masa biyayya a sanadin sa nima na zama wani da kamar ba mutum ba haka nake banida komai haka nake shan wahalar rayuwa gashi hidima da yawa akaina ga mahaifiyata ga mahaifina ga qanne na uku mata mahaifina kuma makaho ne amma ya mutu ma yanzu.. inada matata da y'ay'a na biyu haka zanyi ta wahalar neman yadda zan temake su gashi ni kad'ai garesu basu da wanda zeyi musu na shiga wahala sosai a lokacin amma a sanadin yalla'bai na y'antu yanzu nima nazama mutum gashi har na baro qasata nazo qasar ku aiki har na tawo da iyali ta ai yalla'bai shine yayi min komai madam yalla'bai mutumin kirki ne akwaishi da temak.......
Ayaan ne ya katse shi ta hanyar kiran sunan sa... Ameeed!!!!
Zabura yayi yace yalla'bai...
kallon da yayi masa ne yasa yayi saurin cewa.. Yalla'bai yace a dena baki labari,
Murmushi tayi tace hakan ma nagode,
Haka reetaj take zuwa aiki tana shan wahala da ayaan dan har yanzu bata gane kansa ba inda Allah ya rufa mata asiri ma bashi da fad'a ko tayi ba daidai ba baze ce bari ba bare yace dan me yasa babu wata magana da take had'a su ko me zatayi baze ce mata cikal.. Ba ga shiru tayi yawa idan suka zauna sai kace duwatsu reetaj taso ta shiga cikin mutane dan rage kewa amma sai ma qara quntata da tayi babu um babu um um haka suke zaune gashi kullum lokaci qara tafiya yake wani lokacin har kuka take ta share hawayen ta...
Inda ma take jin dama dama ameeed yana da d'an banzan surutu idan suka samu sake sukanyi surutun nasu kafin su fara hawar masa kai ya tsawatar musu yanzu sun zama abokai da shi da ita yana d'an nuna mata yanayi da kuma d'abi"un ayaan d'in,
Awaaz....
Zaune take kan hamshaqiyar kujerar dake falon ta hakince tana taunan apple cikin nutsuwa..
Asabe y'ar aikin ta tana mata tausa yayin da samira take mata fifita da wani d'an mafici kamar wata basarakiya asabe tana cikin aikin ta awaaz ta hankad'ata da qafa a jarabe tana cewa bakida hankali? haka ake tausan dan uban ki??
Asabe tace kiyi haquri ranki yadad'e kuskure nayi tashi tayi ta yarfa mata mari tana cewa.. Ni!!! ??? Nii zaki fad'awa kuskure ?? Kuskure kikai??? ance miki an d'akko ki ne dan kiyi kuskure?? Matsiyaciya?? Baki san aikin ki ba ko?? An kawo ki ne fa dan kiyi aikatau ki samu kud'i ba kyauta ma zakiyi ba ko nawa ne biyanki fah za ayi qwalamammu ku baro gidan iyayen ku saboda maita kuzo qwalamar kuma kuce baza kuyi aikin ku ba ???
Muhsin ne ya fito yana tambaya lafiya??
A hasale tace kaga wannan qazamar yarinyar wai har ni zata fad'awa wai kuskure tayi?
Ohhh my love ki dena biyewa yaran nan mana gwara ki fad'a a hukunta su ko kuma idan basuyi miki ba a kawo miki wasu kud'i ne fa za a biya su ba wani abu ba wannan ai beci ki d'aga murya a kai ba muryar ki fa abune me daraja ba akan ko wane abu ya kamata a jita ba yayi magana yana sakar mata wani sassanyan murmushi...
Wanda yasa lokaci guda taji zuciyar ta tayi sanyi. A shagwa'be tace my dear ai yaran ne sai da haka banason raini su kuma kucakan banza gani suke kamar daidai suke da ni,
Inaa haba haba waye ya isa ya had'a kansa dake sarauniyar mata ai babu shi kuma ba a yishi ba ki dena ma tunanin zasu had'a kansu da ke ai wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa haba babbar yarinya,
Farrrrr tayi da ido tana wani sakaran murmushi gaskiya na mori miji ga kyau ga iya komai ya iya soyayya gashi ya iya kalamai masu dad'i da zaqi gaskiya ne wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa ko a yanzu nayiwa reetaj fintinkau,
Murmushin gayya ta saki zata qare a wahala zata qare a biye biyen titi ni kuma na aure muhsin d'in gashi yanzu nazama tamkar sarauniya shi kansa duk abunda nace shine.. ga y'an aiki tamkar bayi.. na taka nera na hau nera na murza nera na zama manya ba sa"ar yara ba gaskiya ina ga babu wanda yakai muhsin kud'i a qasar nan nayi babbar sa"a nayi dace dama ai muhsin dani ya dace ba da bagidajiya ba,,
Sake wani murmushin tayi muhsin ya kama hannun ta suka wuce bedroom...
(Ni kuma nayi kwana....)