← Book details Sirrin Keta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 47

Sashe 24

Sirrin Keta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Langa'bar da kai tayi tace babu yadda na iya ne yaya hafiz dan Allah karka hanani kai min fatan alkhairi kawai bazan iya zaman gidan ba koda yaushe cikin qunci nake Abba ma nasan baze yi fad'a ba insha Allah,

To shikenan ki kula,

Toh nagode wuce wa tayi ta shiga mota ta fece,

Lokacin da taje yalla'bai be iso ba hakan yasa suka fara sharholiya ita da ameeed labari yake bata akan qasar su ita kuwa sai dariya take dan ameeed akwai shi da bwarkwanci,

Shigowar yalla'bai ne yasa ya tashi yana cewa barka da zuwa yalla'bai yanzu ma zan koma kan aiki na ai dama kawai ina bawa madam labari ne shin....
Ayaan ya katse shi da cewa to waya tambaye ka??? 'Dan magananniya kai!!!!!

Sum..sum.. Yayi ya zirare ya kwarare qwalale ya fece ,

Reeetaj ta kwashe da dariya har da tafa hannu gaskiya yalla'bai ka cije shi wallahi yalla'bai d'in nan wani lokacin d'an rainin hankali ne a haka kamar baya magana amma wai d'an magananniya hahahah gaskiya ya bani dariya amma sai yabar ni ni kad'ai ba um.. Ba um.um yayi shiru abun shi...

Badan ta gama surutun ba ayaan ya katse ta da cewa ai ina jinki duk abunda zaki fad'a ki fad'a mana ai bani nace kiyi shiru ba kunne ne fa me ji,,

Zaro ido tayi tace wayyoh yalla'bai Allah ya baka haquri ni wallahi wani lokacin mantawa nake kanajin hausa wallahi sai inga wani lokacin kafi kama da irin mutanen nan masu bautar gunki,,

Dariya sosai ta bawa ayaan sai da yayi me isar shi sannan yace ai ni ba jin hausa nake ba ni cikakken bahaushe ne,,

La ilaa yalla'bai kuma meyesa kake dariya??

Kafe ta yayi da ido yace kuka kike so inyi ??

a"a amma dai da se kayi shiru ba se kayi dariyar ba shirme fa nayi ai ba abun dariya bane yalla'bai ,,

Shafar sumar sa yayi yana tunanin irin giyar da tasha kafin ta fito dan ya lura yau a kwazare take,,,

Yalla'bai in tambaye ka??

Gyad'a mata kai yayi,

Tace meyesa yau ka makara ??

Tofa ikon Allah yau kuma zarrah zata gwada min!

Kamar baze yi magana ba yace na tsaya kashe rigimar kaka ta,

Dariya reeetaj tayi tace kace kaima kana da taka rigimammiyar wallahi tsofaffin nan sai du"a'i,

Ohh na cika surutu wallahi bari dai inyi shiru kar yalla'bai ya kore ni daga haka bata sake magana ba ta dawo kamar dai yadda take daa'

Ameeed ne ya shigo yace madam lokacin breakfast... Toh ai na sani nima ai na gane lokacin jeka kayi aikin ka kawai.. Da d'an ficicin kanka zaka min iyayi,

Shidai yalla'bai beyi magana ba fulas ta d'auko zata zuba masa shayi kamar daga sama taji yace...

Reeetha??

Daskarewa tayi a wajen a hankali ta d'ago tana kallon sa,
Murmushi yayi yace yau bazan sha shayi ba,
Fiki fiki ta farayi da ido wai ku gizo suke mata amma sai taga da gaske shi d'in ne yake magana,

ganin ta kasa abun arziki yasa ya tashi sa kanshi ya had'a kindirmon nono ne me zafi ya d'e bi gishiri ya maka a ciki ya motsa ya koma ya zauna ya fara shan kayan sa,,,

Yalla'baiiii????

Reeetaj ta kira shi tana zuba masa na mujiya

Comment and share dan Allah🙏🙏🙏

Karku manta da sharhi🥰🥰🥰
https://facebook.com/groups/575599953675542/

*💫💫ANNURI WRITER'S ASS.*💫💫
(Annuri is the best)

*(A.W.A)*

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FEViiYLkmiwKIUEZc2PcLD

*SIRRIN QETA*

*Page* *35~36*

*by yar gatan annuri writers*

🎉🎉 *Indo ce..*🎉🎉

*بسم الله الر حمن الحيم*

Wai anya kuwa kai mutum ne??

Murmushi kawai yayi bece komai ba.
Taci gaba da cewa yalla'bai yanzu dan Allah wannan abinci ne?? Nifa wallahi wani lokacin tsoron ka ma nake ji.

Meyesa ?

Yalla'bai wallahi wani abun in kayi kamar ba mutum ba,

Ohh kiyi shiru kawai zaki samin ciwon kai,

To yalla'bai Allah ya baka haquri,
Nayi shirun ma,

Tin da mhamah ta nuna wa ayaana 'bacin ranta an samu sauqin fitina amma bayan kwani biyu da zafin ta ta dawo,

Yalla'bai kuwa har ya fara sabawa da 'baran'batamar reeetaj,
Yauma ta gama har ta gaji be kula ta ba bacci yayi awon gaba da ita tana zaune kan kujera take ta faman zabga gyangyad'i gashi kujerar babu makarai kamar zata wuntsilo qasa hankalin ayaan ya gaza kwanciya kallon ta kawai yake dan kuwa gani yake da ya juya zata fad'o shi kanshi be san dalilin da yasa ya damu da ita sosai ba haka kawai yake jin baze iya jurar ganin wani abu ya same ta ba gani yayi ta kusa shan qasa be san lokacin da ya matsa kusa da ita ba rungumo ta yayi a hankali yayi mata masauki a kan kafad'ar sa ya kwantar da ita yadda zataji dad'in baccin ita kuwa bata san anayi ba sai ma qara jan numfashi da take shi kuwa danne dannen sa yake ba tareda damuwa ko tunanin gajiya ba har wani lokaci,
Ameeed ne ya shigo da sallama cakkk ya tsaya yana zarowa yalla'bai ido cike da mamaki yace yalla'bai meye hakan abunda ban ta'ba gani ba.

Tsakin da ayaaan ya zabga ne yasa yayi saurin kama bakin sa yace yalla'bai ana neman iso ne zeeeny ce wannan me nacin tsiyar nan kusan kullum sai tazo na hanata shigowa yanzu yalla'bai me zance mata??

Kace ta shigo.
To yalla'bai..

Zeeeny cikin farin ciki ta shigo tana taku qaras qaras sai wani fi'ili take a ranta kuwa tasa aniyar gogewa wannan bagidajiyar y'ar aikin tasa hadda sai ta nuna mata ita qaramar y'ar bariki ce sai wani juya idanu take tana fari dasu ta shigo tareda sallama cikin wata maqalalliyar murya,
Suman fad'uwa qasa ne kawai batayi ba ganin reetaj kwance sha'be sha'be kan kafad'ar ayaaan a tsaye ta daskare tana jin wata wujujuwa a cikin kanta da yake qwararriya ce ta ta fannin bariki dan da nan ta sauya salo tayi kamar bata damu ba ta danne zuciyar ta,,
Cikin harshen turanci tace barka da wannan lokaci ayaan kana lafiya?

Remote d'in kira ya danna ameeed ya shigo da sauri,
da hausa ayaan yace kayi magana da ita dan naga kamar bata jin hausa,
Maida hankalin sa yayi kan reeetaj yana gyara mata d'an kwalin ta da ya rufe mata fuska jin ta motsa yasa yayi saurin hura mata iska a hankali sauke ajiyar zuciya tayi gami da shaqar daddad'an numfashi ta sauke a hankali shi kuwa ya zuba mata ido kamar wani wanda ake ce yana kauda idon sa za a d'auke ta.

Qullutun Baqin ciki ne ya toshewa zeeny maqoshi ji take kamar ta kurma ihu da kyar ta iya daurewa tace kayi haquri da kai nake son nayi magana,,,

Duba agogon sa yayi sannan ya kalli ameeed da harshen hindi yayi magana,
Ameeed ya maimaita mata cewar yalla'bai namu yace babu lokacin ki a yanzu kya iya dawowa wani lokaci..
Ki fita yanzu yanzu yalla'bai baya buqatar ganin ki,

Babu abunda be ziyar ci zeeeny ba indai na 'bacin rai ne kamar ta tashi sama ta fita kai tsaye parking sface ta nufa ta d'auki motar ta ta wuce gidan da suke tantirancin su ta nufa ta samu alina tana shaye shayen ta saida ta kora itama sannan taji dama dama tace alina ?? Ni ze ciwa mutunci ayaaan be san wacece ni ba ko??

Alina tace eh da alama dai meye faru kuma yanzu??

Zeeny tace wannan munafukar sai da nace miki zanyi maganin ta kikace ba matsalar ta bace yanzu gashi nan ta mallake min zuciyar sa zuwa fa nayi na tarar da ita sai bacci take a kan qirjin sa alina meyesa ze min haka?? ya wulaqanta ni a gaban wannan me gadin nasa yaci zarafi na kawai dan yaga ina son shi?? Alina meyesa hakan take faruwa meyesa alina yaqi fahimta ta be saurare ni ba bare ma ya fahimce ni alina yanzu ya zanyi? meyesa ayaan ze gagare ni ???
Ki fad'a min alina meye zanyi yanzu ??
baya son gani na kwata kwata ni kuma sai na same shi ko ta tsiya ko ta arziqi,

Alina tace qwarai ma idan baki samu ayaan ba ai bamu cika ba wallahi zeeeny sai munyi maganin sa ke dai yanzu ki nutsu kawai naga ba a hayyacin ki kike ba idan muka nutsu zamu tattauna a kai yanzu dai ki tashi ki shirya dan kuwa *babban yaro* ze zo gurin ki ki masa tanadi me kyau gaskiya karki bamu kunya ki cire duk wannan damuwar dalla ki raqashe tareda shi har tsawon kwana yana tare dake yarinya ai ke baki da matsala ayaan d'in banza tinda ga wanda ze d'ebe miki kewa ki manta dashi kawai in kin gama kya fara tunanin sa yanzu dai ga wannan ki fara sha tukunna miqa mata kofin hannun ta tayi.
Ta kar'ba ta shanye qyatt,

Bayan tayi baccin me isar ta a hankali ta farka jinta a jikin mutum yasa ta firgita zaro ido tayi tana kallon sa shima kallon ta yake fuskar sa d'auke da murmushi yace kin tashi??

Janye jikin ta tayi tana murtsike ido tace ba gashi ka gani ba ?? Ko mene ya kawo ka kusa dani ma??'

Shafar sumar sa yayi yace kin fiye bacci da yawa kuma kina bacci a kan kujera sai kin je kin fad'o kodai a kawo miki gado???

Zaro idon ta da sukai wuri wuri tayi kafin ta langa'bar da kai tace nifa.. haba yalla'bai ni dai.. Ka dena ... Nidai .. Ka dena yi min magana...

Ya d'an yi dariya yace hmmm??,
To shikenan Zan dena maganar
https://facebook.com/groups/575599953675542/

*💫💫ANNURI WRITER'S ASS.*💫💫
(Annuri is the best)

*(A.W.A)*

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FEViiYLkmiwKIUEZc2PcLD

*SIRRIN QETA*

*Page* *35~36*

*by yar gatan annuri writers*

🎉🎉 *Indo ce..*🎉🎉

*بسم الله الر حمن الحيم*

Wai anya kuwa kai mutum ne??

Murmushi kawai yayi bece komai ba.
Taci gaba da cewa yalla'bai yanzu dan Allah wannan abinci ne?? Nifa wallahi wani lokacin tsoron ka ma nake ji.

Meyesa ?

Yalla'bai wallahi wani abun in kayi kamar ba mutum ba,

Ohh kiyi shiru kawai zaki samin ciwon kai,

To yalla'bai Allah ya baka haquri,
Nayi shirun ma,
Chapter 24 · 0% Book details