← Book details Sirrin Keta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 47

Sashe 26

Sirrin Keta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka sukaita shagali kowa yayi farin ciki dama haka rayuwar gidan take basu san wani qunci ko damuwa ba basu da babba basuda yaro kowa abokin kowa ne tare suke wasa tare suke cin abinci basu da wanda yafi d'an uwan su shiyasa suke mutunta juna ga kuma so da qauna shiyasa ko abokai basu dasu a waje,
y'an uwan su da iyayen su sune abokan su.
idan ta raya musu haka kawai sukan saka gasa a tsakanin su wanda yayi nasara kuwa ze samu kyaututtuka daga y'an uwan sa babu irin wasannin da basayi shiyasa koda yaushe cikin farin ciki suke basu san 'bacin rai ba indai kaga wannan to ayaaana ce tayi aikin ta itace zata 'bata maka rai ko tasa wani ya 'bata maka duk da tasan inda take yin iskancin ta ayaan ne me haquri shiyasa duk tsiyar ta akan sa take qarewa sauran kuwa babu me raga mata .
duk da haka be hana su ganin girman na sama dasu ba.. babba babba ne a cikin su indai babban ka ya yanke hukunci a kanka koda da minti d'aya ya girme ka to ko iyayen su baza su ce dan meyesa ba kawai hukunci ya yanku domin shima ya isa ne .
dan haka lokacin wasa za"ayi wasa amma in ya wuce babu batun raini,,,,,,,

Comment and share dan Allah🙏🙏

Karku manta da sharhi🥰🥰
https://facebook.com/groups/575599953675542/

*💫💫ANNURI WRITER'S ASS.*💫💫
(Annuri is the best)

*(A.W.A)*

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FEViiYLkmiwKIUEZc2PcLD

*SIRRIN QETA*

*Page* *37~38*

*by yar gatan annuri writers*

🎉🎉 *Indo ce..*🎉🎉

*بسم الله الر حمن الحيم*

Washe gari kamar yadda tace da wuri zata da wurin tazo dan kuwa sai da ta rigashi zuwa,
Yana zuwa amid ya leqa yace madam ga yalla'bai nan da sauri ta tashi ta la'be yana shigowa tayi tsalle ta tafa hannun ta tare da cewa gashi nan!!! Da qarfi tayi maganar ai kuwa cikin sa"a ayaan ya waro ido ya qame a wajen ko motsawa beyi ba,
Reetaj da ameed suka fara dariya harda tafawa ayaan ya saki baki yana kallon su dama kitimurmura suka had'a masa kwata kwata beyi tsammanin ma reetaj tazo ba ashe ita shirin firgitashi take,

Ido ya zuba mata ganin yadda take dariya harda tsalle tsalle sai fari ciki take,
Murmushin ta akwai qawatarwa dariyar ta kuwa maqura ce wajen burgewa.
Ganin Farin cikin ta kuwa shine abu mafi kyawu a gurin mutum indai har mutum ne nagari reetaj yarinya ce wadda idan baka sata farin ciki ba ba zaka muzguna mata ba ban san da wane irin suna zan kira wanda ya zalumce ta ba amma tabbas babban asararre ne ko waye shi,,
Ina ma zan iya dauwamar da wannan farin cikin nata har abada .

Katse masa tunanin tayi da cewa yalla'bai kaga na tsora ta ka ko?? Kaje ka zauna kawai kaji yalla'bai kar ka gaji da tsayuwa,

Wuce wa yayi ya zauna ta jawo kujera ta zauna tana fuskantar sa tace yalla'bai ashe kaima kana da tsoro??

Murmushi yayi yace eh mana abu ne wanda baka ta'ba tsammanin ko da wasa ze shigo rayuwar ka ba kawai sai ka ganshi lokaci d'aya ya gifto maka kinga dole abun yazo maka a baibai,

Dariya tayi tace gaskiya yalla'bai ka bani dariya wallahi abun yayi zuma,,

Nima haka ya sani farin ciki dariyar ki tana bani dariya dama bazaki dena ba,,

Murmushi tayi tace to yalla'bai kaga wannan shine hukuncin ka na rashin zuwa da wuri har ka bari na riga ka zuwa,

Murmushi kawai yayi beyi magana ba,

Tace..
Yalla'bai yau kuma me zakasha kindirmo??

Girgiza kai yayi,

Tace to shayi da kantu??

A"a

To shayi ba madara??

A"a

To yalla'bai ka fad'a min mana'

Sai lokaci yayi,

Ta'be baki tayi tace komai dai lokaci lokaci naga agogo ma"

Shiru yayi mata jim kad'an tace yalla'bai ina da magana,

Ina ji ,

Tace..
yalla'bai wai iyaye nawa ne a gidan ku nifa wallahi kuna burgeni wani lokacin amma tsoron ku nake ji,

To ikon allah me ya kawo wannan tambayar kuma??

Turo baki tayi tace yalla'bai ni dai in baza ka fad'a min ba shikenan,

To shikenan su uku ne ta wata fuskar kuma su hud'u mata ma haka
Mhamah Ammuu Ummuu Annaa
Bhabha Bhabhai Abbu Abbhai,,

Kaiii to yalla'bai naji sunan su kusan d'aya kamar ma babu banbanci??

Akwai mana bhabha shine baba bhabhai qaramin uba Abbhai na qasa dashi shi kuma Abbu ba a gidan su yake ba babban aminin bhabhai ne amma zuwa yanzu shima d'an uwa ne tinda mahaifiyar sa kakan mu ya aura har a yanzu matar sa ce shiyasa muke kiran sa da uba shima,

Ahh? To yalla'bai kenan cikin su su waye iyayen ka na asali ??

Mhamah da bhabhai
Ammuu da Abbhai sune iyayen arman
Anna da bhabha sune iyayen abie
Abbu da ummu sune iyayen hanan ita kad'ai ce y'ar su mu kuma muna da qanne shikenan?

Aa..
yalla'bai to kuma kaida mahaifin ka meyesa kake kiran sa qaramin uba??

Saboda ba shine babba ba indai mutum ya girme ka kawai ya girme ka bhabha shine sama da bhabhai shiyasa muke kiran sa haka,

Wannan shine tsarin gidan mu shiyasa qannen mu suke kirana bhaiya su kira arman bhai kuma dukan su babu wani banbanci,

Gaskiya yalla'bai tsarin gidan nan naku sai yasa mutum ciwon kai kenan kana nufin ka girmi d'an uwan ka me kama da kai d'in nan ? nifa na zata ma tagwaye ne,

Girgiza kai yayi yace.. Aa kowa iyayen sa daban kuma ba tagwaye bane
Na girme shi amma girman ba wani bane an haife mu rana d'aya a gida d'aya kuma a lokaci d'aya,

Kaiii ta fad'a tana dariya kafin tace yalla'bai kenan duk a wannan gidan aka haife ku?

Aa ba ma a qasar nan aka haife mu ba a india aka haife ni nayi karatu na duk a can duk wani matakin karatu na acan na kammala sai kuma na qara yi a germany ba fannin mu d'aya da arman ba shiyasa karatun mu bezo d'aya ba,

Kenan ma bakayi karatu a qasar nan ba ?

Eh,

A"ahh?? to yalla'bai akwai wata tambayar ka ta'ba cemin kai bahaushe ne ko? To kuma ya akai naga bakayi kalar mu ba?? Kuma meyesa naga baka son yin turanci ??

Saboda ba yaren mu bane, kuma ba"a yinsa a gidan mu kwata kwata daga hausa sai hindi sai larabci
Murmushi yayi yace mhamah ta mahaifiyar ta da dangin ta duk suna india dangin mahaifin ta kuwa sune *kanawan dabo* haka shima mahaifina shi ake wa laqani da *kanawa* ko kuma *dabo* shine sunan ahalin mu mahaifiyar sa kuma buzuwar agadez ce ko hausa bataji sosai,
to yanzu ai kinji koh?? Shikenan??

A tsaya yalla'bai ba shikenan ba,
wai qannen ka guda nawa ne naga suna da yawa?

Gaskiya ina ga yau aljanun tambaya ne akanki reetha,

Langwa'bar da kai tayi tace yalla'bai ni dai idan baza ka fad'a min ba inyi tafiya ta gida "

Ohh" Allah na yarinya ta sani sai faman surutu nake"

Yace..
suna da yawa kamar yadda kika fad'a amma bazan fad'a miki adadin su ba wata rana zaki san su da kanki,

Zaro ido tayi tace yalla'bai meyesa zaka ce haka?? Nida ba zuwa gidan ku nake ba bare ko kace nifa y'ar aikin ka ce yalla'bai ko ka manta ne???????

Murmushi yayi yace ban manta ba sai dai in kece kika manta inyi miki tuni,

Yalla'bai to wane tuni kuma??

Lumshe ido yayi ya qara bud'e su sannan yace..
Ke ba y'ar aiki bace kin dad'e da wuce wannan matsayin.. Saboda
Koda yaushe qara alaqantuwa muke.. a waje na kullum qara matsayi kike kuma ina ganin alaqar mu baza ta warware ba ta d'auru kenan kiyi tunani kema zaki gane hakan,

Shiru tayi tana tunani na wani lokaci kafin tace..
Yalla'bai nifa kaina ya kulle na kasa fahimta wai wace irin alaqa???? kuma wane matsayi??

Yace kiyi tunani zaki gane..

To amma dai kar kiyi ciwon kai ina d'aukar ki a matsayin qanne na yadda kike da wannan rawar kan nan haka suke yadda kika maidani kaka suma haka suka maidani akwai su da fitina ga surutu rawar kai shiyasa nake kallon ki tamkar d'aya daga cikin su yadda kika ganki d'in nan suma haka ne,,

Jikin reetaj yayi sanyi sosai tunani kala kala suka fara bijiro mata sam takasa fahimtar inda maganar sa ta dosa haka kawai batasan dalili ba...
tayi laqwas tinda tayi shiru ko magana bata qara yi ba har abun yana nema ya zame mata damuwa,

Duk Yana lure da ita daga baya ma cewa yayi ta tashi ta tafi,
Batayi musu ba ta tashi,

Fitar ta keda wuya sai ga muhsin Allah ne yayi baza su had'u ba dan kuwa gaf da juna suka wuce babu wanda yaga d'an uwan sa,

Wajen ameed yaje yace inason ganin yalla'bai,,

koda yaje ya fad'a ya dawo yace ka shiga,

A wannan karon yalla'bai kamar ba shi ba yayi kicin kicin da rai ya hakince a kan kujera ya had'a girar sama da qasa,,

Muhsin jiki na d'ari d'ari ya shigo yace sannu yalla'bai,

Ko kallon sa ayaan beyi ba,

Ya nufi kujerar da reetaj ta tashi yana qoqarin zama,

Ayaan ya d'ora qafar sa akai yana bin shi da wani shegen kallon yace...
Waye ya baka izinin zama???

Kayi haquri yalla'bai babu kowa,

'Dan ma dannin sa ya danna ameed ya shigo da sauri yana cewa yalla'bai gani,

Cikin harshen hindi yayi masa magana shi kuma ya maimaita da hausa,

Ka din tunanin waye ya tashi daga guri kafin ka zauna idan kaga ba tsarar ka bane sai ka canja mazauni sannan idan ka shiga gurin manya kadinga sanin ya kamata ka fara neman izinin zama in ance ka zauna sai ka zauna sannan kanemi izinin magana,

Wannan shine abunda yalla'bai ya fad'a ka kula,,

Muhsin yace yalla'bai ina neman izinin zama,

Ameed ya kalla ameed yace bazaka iya zama ba yalla'bai be bada damar hakan ba ,

A quntace yace yalla'bai zan iya magana??

Yanzu ma ameed ya kalla ameed yace ana sauraren ka,
Chapter 26 · 0% Book details