← Book details Sirrin Keta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 47

Sashe 33

Sirrin Keta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Roooh yace ai kuwa in ba kishi ba babu abunda ze kawo hakan kawai mutum dan yayi abota da wata sai ace ya zama d'an iska kunga kuwa ai kishi ne yake kawo haka,

Fashewa tayi da kuka cike da baqin ciki tace ai kuwa duk sai na fad'awa mhamah kuma wallahi Allah ya kyauta in so wannan me kama da zaren kad'in koda shine autan maza kuma ko mazan sun qare bazan ta'ba son shi ba kuma sai na fad'awa mhamah,,

Ayaan yace maza karki bari na riga ki zuwa ,

Hararar sa tayi ta murgud'a baki tace mara tausayi kawai kana ganin duk ta had'a min gajiya amma mugu ko a jikin ka wai kai me tausayi ko ai kuwa zan fad'awa mhamah wallahi ka san ko wacece .
Nasan kuma kawai wata matsiyaciyar ce irin talakawan nan amma babu wata qawar ka me mugun hali kawai,

Roooh yace qaramar meyi kawai ashe dai kin san ba d'an iskan bane ,

Ayaan yace ai kunyi min maganin ta dai,
Daga haka yayi tafiyar sa,

Sithara tace nifa ban yarda ma bhaiya yana da wata qawa ba tinda kaji ma ita da kanta tace ba haka bane kawai inaga fad'e yayi,

Islam yace to dama mana kawai so yake ya kashe bakin tsanya gashinan ai ta kama kuka nasan kuma mhamahn ma babu abunda zata ce sai dai ta bata haquri,

Aslam yace shine darr dama ai mhamahn ce take qyale ta shiyasa ma ta raina shi da yawa ko kuma ince ma shine bashida yaji,

Haka sukai ta hirar su ba tareda wata damuwa ba kuma sun yarda da cewar bhaiyan su bashida wata qawa,

Da daddare ayaan ya shiga bedroom d'in mhamah ya tarar da ita tana zaune a bakin gado ayaana tayi filo da cinyar ta da alama dai hira suke wadda tayi musu dad'i kusa da ita ya zauna yace mhamah namaste shubrathrie,,

Murmushi tayi tace bethaa? mein thik hai our aap?

Yace mhamah mein achcha hoon ,

Tace masha Allah shiru ce ta biyo baya kafin ta kalli ayaana tace ayaana maza je wajen ammuu ,

Tashi tayi tana fakar idon mhamah tana harar sa be ko kulata ba har tayi ta gama ta fice,

Mhamah ta kalle shi tace bethaa ?? Wai fushi kake ne ??

Girgiza kai tayi tace gaskiya ne amma nasan dai baka so zuwa india ba ba??

Gyad'a mata kai yayi ,

Tace kayi haquri ai bazaka dad'e ba kuma zuwan naka yana da muhimmanci ne bethaa akwai buqatar qarin tsaro a tattare da kai,

Da mamaki yace tsaro kuma ?? Meyesa ,

Murmushi tayi tace ba lallai ka fahimce ni ba akwai wanda suke son sihirce ka ne shiyasa duk da nasan ba lallai yayi tasiri ba amma kasani sihiri mugun abu ne shiyasa papu yace kaje,

Shafa sumar sa yayi yace shikenan mhamah zanje amma dan Allah ki zo da wuri,

Shikenan bethaa naji dad'in hakan ka shirya a nutse kaji sannan kuma karka sa damuwa a ranka bana son hakan
Kuma naga kwanan nan kamar ka canja kodan bama kama bane haka ne ko meye dalili??

Shiru yayi mata sanin bazeyi magana ba yasa ta canja magana,

Washe gari,

Tana zaune a bakin gado tayi tagumi kawai tunanin ta yadda za ayi zuwa kamfanin yayi mata dad'i idan baya nan ita da bo kowa ta sani ma a ciki ba sauqin ta d'aya dai ameed yana nan amma duk da haka rayuwa zatayi mata babu dad'i dan kuwa ko ina ta shiga indai ta tuna yayi nisa da ita sai taji babu dad'i,

Wayar ta ce ta fara qara ta d'auka ba tareda ta duba ba dan kuwa ba a hankalin ta take ba,

Muryar sa ce ta doki dodon kunnen ta..
Namaste reeetha ,
Ya dai kina damuwa ko???

Aa yalla'bai bana wata damuwa kawai dai ina tunani ne,

Murmushi yayi yace to naji ba kya damuwa amma ai kina tunani ko?? Ki dena tunani da yawa yana sa ciwon kai idan ya tsanan ta ma har haukata mutum yake,
Amma dai zaki raka ni airport ko?

Kaii kai??
Yalla'bai ni a suwa tareda y'an uwan ka fa zakaje ,,

Eh tare dasu mana ke ina ruwan ki da hurumin su nidake zamuje su kuma zasuje daban shikenan??

Aa gaskiya yalla'bai nidai bazanje ba gaskiya kaje tareda y'an uwan ka ni dai ina gida gaskiya tsoro nake ji,

Tsoro dai in kika sake shine zeyi ajalin ki kuma sai kinje inyaso ki kwanta a tsakiyar titi mota ta lamutse ki ko?? Ya fad'a yana dariya,

Turo baki tayi tace a"a nidai gara ma karna fita nasan ko mutuwa nayi ina gida,

Ha"ha sai fa kinje ba a yi min gardama ki fito ina qofar gida kuma ki tawo da shirin ki dan bazaki koma ciki ba,,

A zabure tace yalla'bai wane gidan kuma??? Na shiga uku na shikenan na mutu yalla'bai ka gama kashe ni yalla'bai wayyo Allah so kake ace bin maza nake ne ?? baka san inada y'an sa ido ba masu d'iban duk abunda nayi su fad'a a gidan mu su yad'a a duniya so kake ace bin maza nake ko???

Dariya yayi yace eh idan sun fad'a ma bin mazan kike shikenan ke dai tinda kin san ba haka bane kuma kin san Allah ma ya sani meye na damuwa kina da tsoron mutum da yawa ya kamata ki zama y'antacciya daga duk wani me so yaga kukan ki reetha mutum idan kika fiye nuna kina tsoron sa shikenan yaga lagon ki zeyi qoqari har yaga ya kai ki qasa..
Ki fito ina jiran ki y'an uwana basu san ina nan ba fa, so nake inyi sauri kar suyi ta jira na,

Jikin ta yayi laushi sosai ta d'auki hijab ta zura ta fita,

Innan ta tare ta tace to bita zaizai ina kuma za aje??

Shiru tayi tana tsilla tsilla da ido musamman da ta kalli ammah taga tana jifan ta da wani shegen kallo,

Sunkuyar da kai tayi innan tace magana fa nake,

Innan zan d'an fita ne am..a.aiki zanje,

Innan ta yamutse baki tace allah ya tsare agogo sarkin aiki ba dai zakiyi aure ba kullum a aiki zaki qare ,

Ficewa tayi cikin sauri tana mita banda abun yalla'bai da ranar Allah ze wani zo qafar gidan mu kuma yace wani in rakashi shidai ya rantse sai yasa ta a cikin chakwakiya qila ma da wasa yake,

Leqowa ta farayi taga mutum jikin mota hannun sa hard'e a qirjinsa sanye yake da baqaqen kaya doguwar riga ce me tsaga a gefe sai wandon ta ko kad'an ba a ganin fuskar sa yayi wani nad'i ya rufe ta ruf idanun sa kawai ake iya gani,

Zuba masa ido tayi dan kuwa badan ta karanci idanun sa ba ba lallai ta ganeshi ba dan kuwa idanun sa tinda take bata ta'ba ganin me irin su ba kamar ba na mutane ba,

Ganin ta daskare a wajen yasa ya taka ya isa inda take kashe mata ido yayi yana murmushi,

Firgigit tayi tana zaro ido tace yalla'bai meye hakan??? Kake wani qifilfila min ido??
nifa na d'auka ma da wasa kake ashe dai ka zo ya akai kasan gidan mu??
Kuma wannan wace irin shiga ce???

Lallai kam tana wasa yarinyar nan bata san duk inda ta shiga ina sane ba bata san ina bibiyar ta ba kenan ?? Hmm nida nake da d'an uwa ss ai banida matsala ko ina zaki cikin tsaro kike,

Tafi tayi masa ya juyo sannan tace tunanin me kake ?? Bani amsa ta mana,

Eh nasan gidan ku mana wannan shigar kuma mafi yawanci inayin ta ne idan zan shiga asibiti to yanzu kinji amsa mu tafi ko???
Ko in d'auke ki?

'Dan tsaki tayi yana wani turo baki tace kai dama ai wata rana kunyar ka kad'an ce,

Bin bayan ta yayi ameed ya bud'e musu gidan baya saida ta shiga sannan ya shiga suka d'au hanya,

Comment and share dan Allah🙏🙏

Karku manta da sharhi🥰🥰🥰
https://facebook.com/groups/575599953675542/

*💫💫ANNURI WRITER'S ASS.*💫💫
(Annuri is the best)

*(A.W.A)*

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FEViiYLkmiwKIUEZc2PcLD

*SIRRIN QETA*

*Page* *45~46*

*by yar gatan annuri writers*

🎉🎉 *Indo ce..*🎉🎉

*بسم الله الر حمن الحيم*

Shiru motar babu wanda yake magana kowa da tunanin da yake yi,

Ameed ne ya katse shirun da cewa yalla'bai wallahi dad'i nakeji idan na ganku tare da madam wallahi kuna matuqar sajewa kuma fa nasan baza taji dad'i ba in ka tafi kawai yalla'bai ka tafi da ita,

Watsa masa idanun sa yayi yana had'e fuska yace gidan wace qaniyar zan kaita idan na tafi da ita?? Papu zan kaiwa ita ko kuma nanie zan bawa ajiyar ta ??
Ko kuma gidan sirikan ka zan kaita ince musu ga matar ka ta biyu in yaso su yanka ka suyi miya da kai,,

Ameed da sauri yace a'a yalla'bai dan allah kayi shiru da kayi irin wannan maganar wallayi gara kawai kayi shirun ka abun ka dama kai salihi ne ko magana baka yi,,

Ayaan yace da kace ai yanzu kuma ina magana ta...
reetaj ta katse shi da sauri tace iyye? Ameed rufamin asiri ni meye ze kaini india ma ni ai ko a qafa ake zuwa bazani ba waye nake da shi a can ?? Me na ajiye da zanje d'akkowa ??
Kaga wannan bakin naka sai yasa muyi had'ari ba tareda munje inda zamu ba ma kayi shiru kawai ka kula da abunda kake yi ni bana fatan ganin ranar ma da zata kaini india bazan je ba,,,

Ido ayaan ya zuba mata yana wani murmushi na yaro baka da wayo aransa kuwa yana cewa..
Zakije india kuwa reeetaj kawai ki jira lokaci amma tabbas lokacin ze zo dole ma zakije da yardar Allah...

Be gama tunanin ba ta katse shi da cewa yalla'bai ya da kallo na haka kuma??
Bana son yawan sa ido fah,

Gyara zama yayi yana cewa ansa idon..
Naki ne idon ko nawa???

Wurqile ido tayi zuwa sama tace eh naka ne amma dai ai ni kake kallo.. Nifa yau dukan ka ma ka 'bata min rai kamar in rufe ka da duka,,
Chapter 33 · 0% Book details