← Book details Sirrin Keta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 47

Sashe 40

Sirrin Keta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushin da bata shirya masa ba tayi kafin tace Allah yalla'bai nidai bazan iya ce maka ayaan ba..
To amma meyesa ka canja min suna??
Amma dai sunan ya min duk da ban san ma"anar sa ba nasan dai bazaka fad'a min sunan banza ba,

Murmushi yayi yace naji dad'i da kika fahimci hakan,,
To kina dai farin ciki ko??

Shiru tayi kafin tace yalla'bai nifa ina tsoron kar da yaran nan su je su ce ina waya da maza,,

Ohh ya'ilaah kina da tsoro da yawa meyesa kika bari qannen ki kuma qananun yara suka raina ki???

Yalla'bai babu yadda zanyi ne nima,

Ki zama kamar ni..
Ki jaraba hakan indai suka ga kin canja zasu d'anyi shakkar ki..
Kinga ni tare nake wasa da qanne na amma babu raini a tsakanin mu...
Amma gaskiya sun raina ki da yawa.
Da zaki iya ki dinga jan girman ki ko haqoran ki sai sunyi da gaske zasu gani ki dena sakar musu fuska ki dena nuna kina jin tsoron su ko wani sharrin su a gani na tin sunayi a marmarce har zasu gaji su dena indai kika nuna musu matsayar su,

Shiru tayi tana tunani kafin tace zan iya kuwa ???

Cikin sauqi ma kuwa ke jajirtacciya ce amma kin bari tsoro ya samu gurbi a zuciyar ki in kuwa hakan taci gaba da faruwa yaran nan har abunda yafi haka zasuyi miki dan na lura kamar basu da kunya yanda kasan ba a gaban mahaifiyar su suka taso ba ,

Ai kuwa yalla'bai zan jaraba Allah yasa su dena dan kuwa wallahi bani da sakat sun saka min ido da yawa,

Hmm karki wani damu dasu yanzu ki fad'a min babu wata damuwa??
Nifa wallahi na qagu in dawo amma ya zanyi sai haquri amma dai na kusa dawowa bi'izinillah,

Tayi murmushi tace Allah ya dawo da kai lafiya babu wata damuwa,,

Kin tabbata??

Eh amma ba sosai ba,

Murmushi yayi yace to shikenan meye ya rage ya zama sosai d'in ??

Turo baki tayi tace kawai banajin dad'in kad'aici ne banida abokin hira sai dai nayi tagumi kawai na rasa abunyi sai dai tunane tunane shine kawai yake damu na ,

Indai wannan ne baki da matsala indai abunyi kike nema zan sibaro miki laptop d'in camera man sai kiyi ta aikin abu d'aya har ki gaji dan kuwa inaga harda hotunan aljanu bazaki rasa ba komai d'auka yake wani kisha dariya wani takaici,,

Dariya reetaj tayi har ranta taji dad'i dan kuwa tana shiga damuwa sosai da farin ciki tace yalla'bai nagode gaskiya to yanzu a ina zan same ta????

Kai tsaye yace gobe da misalin qarfe 03:15pm ameeed ze kawo miki ita ki shirya,

Murmushi tayi tace to yalla'bai nagode sosai,,,

Murmushi yayi shima yace meye na godiya kuma sathie??

Da haka sukai sallama,

Kamar yadda ya fad'a hakan ce ta kasan ce ameed ya kawo mata tayi murna sosai,

Danne danne takeyi tana kallon hotuna kala kala inaga ta iya cewa babu ce kawai babu a ciki hotuna harda nasu tin suna yara,

Tana cikin danne danne ta kai wajen video gasu nan iri da kala ba na komai bane yawanci na cikin gidan su ne na sharholiyar su,

Abunda mamaki ganin yalla'bai yana tiqar ball kamar ba shine ba,

Ta fad'a tana riqe ha'ba ta qara da cewa kuma wallahi shine har ma da mhamah harda duk kowa ma na gidan su bhabha ne kawai babu?? harda wasu y'an yara ni ban ma san su ba dama ba iya su roooh bane qannen sa ???
Kuma fa da alama taurarin ciki shi da ayaana ne dan kuwa sunfi kowa iyawa,

Ci gaba tayi da bud'e wasu video d'in wasu kuma ba na ball bane wasan kricket da irin su golf harda su wasan tsere da sauran su kamar ba mutane ba sannan kuma dukan su babu qarami babu babba ,

Ajiyar zuciya ta sauke tace da alama dai babu irin wasan da basayi.. gaskiya akwai farin ciki da walwala da qauna a wannan ahalin kar Allah ya kawo ranar da zakuyi baqin ciki inama dai ace farin cikin ku ze d'ore baze samu tangard'a ba kamar dai yadda mafi yawancin farin cikin gidan mu ya d'aid'aice ,
Kuma awaaz ce silar komai ita kuma ko a jikinta,

Share y'ar qwallar da ta ziraro tayi tana ci gaba da kallon su..
Su shida ne zaune a wajen hutawar su shunsha anko wanda da alama haka al'adar su take su shidan..
sunyi rukuni suna hira,

aslam yace..
nida na shiga wata unguwa naga wai wani mutum daga ajiye mashin d'in sa ya shiga masallaci zeyi sallah kafin ya fito sun d'auke mashin d'in wallahi yana fitowa kawai sai dai yaji hammatar sa tana shan iska ,,,

Kwashewa sukayi da dariya ayaat tace kai bhai Aslam Wallahi mutuncin ka sai du"a"i.
sithara tace kaii ni y'ar bhabha anayi ina shan mama,

A hanzarce islam yace A"uzubillah"
Ke iskancin naki ma har yafi na Aslam d'in ,

Dariya sukeyi sosai.
roooh yace kaji shegiya ke ko kunya ma bakyaji??
Ke bama shayin kike sha ba tsabar kin raina mana hankali ,

Ayaana tace wallahi da gaskiyar ta kowa fa yasha na lokacin sa itama ku barta ta qara ,

Aslam yace ke dama ai indai hauka ne baki da tsara,

Ayaat tace dama dai bhaiya yaji ki ya casa ki,

Ayaana ta ta'be baki tace wani bhaiya can?? 'Dan rainin hankali da jar fuskar sa wannan mugun miskilin ma har wata casa mutum ze iya yi??

Sithara tace kaiiya ai bhaiya ko?? garantin miskili ne yayi ta wani manyance amma idan aka saka gasar rawa har yafi bhai iyawa ,

Roooh yace wallahi kuwa d'aid'ai ne zasu zo kai d'aya da bhai amma koda yaushe shine a sama sai an gama kuma yayi ta wani qasa da ido ,

Aslam yace to yanzu gulma kuke ko munafurci??

Islam yace duk wanda ka za'ba ,

Aslam yace qananun arna kuje gaban sa kuyi mana,

Sithara tace to bazamu iya bane ???

Ayaana tace tambaye shi dai,

Cikin d'aga murya ayaat tace singham!!!!!!!....

Abun mamaki kafin kace me kowa ya d'au matsayar sa wani yana danna waya me hoto kuwa har ya fara d'auke d'auken sa
Me yin kamar yayi bacci yayi me shiga bayan kujera ya 'buya ya 'buya,,

Dariya ayaat ta saki tana cewa kuji fah kunce zaku iya fad'a a gaban sa amma kuma yanzu bama sunan sa na asali aka fad'a ba duk kun firgice matsorata ,

Islam yace yanzu dama yarinyar nan shirga mu kikayi??

Tace to eh mana tinda gashi har ka gani qananun marasa yaji kawai ,

Roooh yace ai kuwa zaki ga yaji yanzu ,

Kafin tayi wani qoqari sunyi mata qawanya sithara tace yanzu dai sai dai in kin qware taki ta fishshe ki ,

Fakar idon su tayi ta zura da gudu ta fita tayi hanyar da zata maida ita cikin gida suka mara mata baya,

Karo tayi da Abhie ta shiga bayan sa ta 'buya su kuwa duk suka tirje a gaban sa ,

Dariya yayi yace mazaje wai yau me kuka sha ne naga kamar bakwa cikin hayyaci ,

Roooh yace ka dai gan mu nan ni nan ciyawar rabbana na zuqa ingaya maka gaskiya shiyasa ka ganni a make,

Aslam yace ni dama kullum ai a shaye nake ni meye ma bana sha insha shayi insha coffee insha madara insha ruwa insha... Kai ni in gaya maka tsohon d'an shaye shaye ne nan da kake gani na ko d'azu sai da nasha rake ,

Sithara tace ni kuma kawai wata y'ar guntuwa roooh bhai ya d'an zuqa ya rage min kaga yanzu ma ganin ka nake sama a qasa fuskar ka rabi ta haana rabi ta Abhie na,,,

Dariya abhie yayi sosai kafin yace to Allah ya shiryaku y'an gwafar na gwafara,

Reetaj dariya harda hawaye ita babu abunda yafi bata dariya irin na me shan mama da kuma wanda ya fito yaji hammatar sa tana shan iska..
Lallai ta gazgata fad'ar yalla'bai da yace idan suka had'u basu da dama ,

Haka rayuwar take tafiya lokaci yana qara wuce wa,

Sai da ta gaji da laptop d'in sannan ta bawa ameed ya mayar ,

Tana zaune tana wasu y'an aikace aikace muhsin yazo ameed ya shigo ya yace madam. Wannan ma"aikacin da kika sa aka dawo dashi nan yazo yana so ya ganki ,,

Shiru tayi kafin tace ya yanayin aikin nasa yanayi cikin aminci kuwa??

Ameeed yace e madam gaskiya baza"ace a'a ba dan kuwa tinda aka kawo shi nan banji wani laifi da yayi ba,

Tace to da yuwuwar ya gyara halin sa kenan??

Ameed yace banida tabbas madam dan a yanzu kafin ka shedi mutum sai ka fara tabbatar da abunda yake aikatawa bansan abunda yake qudire a zuciyar sa ba madam,

Ta jinjina kai tace shikenan jeka zanyi tunani a kansa idan da yuwuwar ganin sa to?

Fita yayi ya sanar masa abunda madam tace muhsin yaji takaici sosai a ransa yake ayyana kud'i da iko ma sunyi a rayuwa yanzu gashi wata y'ar qaramar cikar yarinya tana raina masa hankali dan yaji mutanen da suka santa sukan ce yarinya ce amma har wani sai tayi nazari ma zata bashi amsar shiga,

Jin bata kirashi ba shiru shiru yasa yace wa ameed ya koma ya qara tambayar ta,

Komawar yayi ya gaya mata,

Dafe goshi tayi tace ahh ameed yanzu na riga na tashi tafiya bazan tsaya sauraran sa ba kawai yaje ya gyara mu'amalar sa da mutane shine idan kuma ya matsu da gani na ya fad'a maka meke tafe dashi sai ka tura min,

Ameed yace to madam ,

Fita yayi ya fad'awa muhsin abunda reetaj ta fad'a a karo na biyu rai a 'bace ya bar wajen ya juya baya ita kuma ta fito tayi tafiyar ta,,,,,,,

A kwana a tashi babu wuya da ikon Allah gashi har yalla'bai ya dawo saboda rigimar da ya sakawa papu tinda ya kira reetaj yaji tana kuka shikenan ya tashi zaune tsaye,

Shida ita baza ka banbance wanda yafi farin ciki ba kwanan sa biyu ya koma kan aikin sa itama reetaj bata fasa zuwa ba,
Chapter 40 · 0% Book details