← Book details Sirrin Keta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 47

Sashe 43

Sirrin Keta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jin shiru yasa ya durqushe a wajen yana yamutsa sumar sa ji yake kamar ya zauce gaba d'aya kansa ya gama kullewa ruwan dukan sa yake amma sam be damu ba sai bayan wani lokaci yayi tunanin tana matuqar son tsirrai..
Da sauri ya tashi ya nufi wajen da tinda suka sauka nan take kallo a matuqar kid'ime sai juye juye da kalle kalle yake kamar wani sabon kamu duka kan sa ma a sama yake..
Yana tafiya da baya da baya yaji yayi tuntu'be da abu da sauri ya waigo ya ganta yashe a wajen kamar babu rai a jikin ta da sauri ya durqusa yana jijjiga ta tareda kiran sunan ta amma shiru sa'bar ta yayi a kafad'a ya wurga ta mota ya shiga ya jata a sukwane kai tsaye gidan su ya nufa ya tsaya a bakin makeken get d'in gidan har ya danna hon sai kuma yayi saurin surar motar zuwa gaba zagayowa yayi ta qofar baya sannan yayi wa ma"aikatan gidan magana ta wayar sadarwa ta gidan yace a bud'e masa qofar baya,

Cikin sauri suka bud'e ta ya kutsa kai ciki sai dai sam ya manta mad'aukar gidan (camera..,) tana aiki,

(Kun san ni bahaushiya ce ziryan shiyasa nafi son na fad'i komai da yare na abun alfahari na🥰🥰 ba sai na had'a da yaren yahudu ba 🤭🤭🤭😝😝😝)

Dai dai hanyar da zata sada shi da sashin sa cikin sauqi ya tsayar da motar da hanzari ya fito ya sure reetaj yayi ciki da ita bayan ya wurgawa d'aya daga cikin ma'aikatan mukullin motar da kyar ya iya bin mukullin ya d'auka dan kuwa ya gama mutuwa a tsaye yalla'bai qarami ne da mace haka?? Kuma a cikin gidan su ?? Shine abunda ya tsaya masa a qwaqwalwa,,

Har sai da ya dangana da uwar d'akin sa sannan ya juye ta a kan gado,

Fige rigar jikin sa yayi ya jefar dan kuwa ta jiqe zama yayi a bakin gadon yana tunanin abunda ya faru da ita har yasa ta suma dan kuwa yasan ba mutuwa tayi ba..

kamar an tsikare shi ya tashi ya koma kusa da ita ya zuba mata ido qiri gashi dai babu alamun numfashi amma sai dai zuciyar ta tana bugawa da matuqar gudu kasancewar shi likita yasa besha wahalar gane kan lamarin ba dan kuwa a d'aukar da yayi mata yaji yanayin bugun zuciyar ta ya tabbatar masa kafin ta kai ga matsayin suma taga wani abunda ya matuqar tsora ta ta kuma take tsoron sa sosai da alama firgici ne yasa ta fita hayyacin ta har ta kai ga suma mamaki da shakku da tunanin wannan abu yake yi dan kuwa ko menene tabbas yana da tasiri a kanta ,,,

Mhamah ce ke tafiya cikin takun ta irin na isa tayo bayan gidan da alama dai tana jin dad'in ruwan da akeyi ne har zata wuce sai kuma ta tsaya wajen get d'in ta qarasa da mamaki su kuwa duk sun gama firgicewa dan abunda suka gani ya matuqara razana su ga wani kuma wannan babu shakka idan suka bari ta sani shikenan anyi gamo..

A tsanake tace naga kamar an bud'e qofar nan ko???

Qasa sukayi da kai su duka,

Taku biyu tayi sannan tace naga alamar hakan ne ko kuwa zaku ce a'a ne,,

Shugaban su ne ya d'ago ya kalle ta yayi saurin maida kai qasa yana mamakin irin matar nan me kamar aljana qofar da aka bud'e an kuma mayar an rufe ta ruff kamar yadda take daa' amma har ta gane an bud'e ta lallai y'ar baiwa ce haihuwar sa"a ,

Katse shi tayi ta hanyar kiran sunan sa a tsawa ce,

Pandhe?!!!!!!

Da sauri cikin yaren su yace na'am ranki ya dad'e ,

Na zata ba sai na tambaya waye ya bud'e qofar ba kuma da izinin wa aka bud'e ta ,

Cikin kame kame yace..

Kafin yayi magana tace ka tabbatar abunda zaka fad'a min gaskiya ce idan ya kasan ce sa'banin haka???

Da sauri

Yace yalla'bai qarami ne yace a bud'e ta yau tanan ya shigo gida,

Tsamm ta tsaya tana nazari kafin ta juya tabar wajen kai tsaye sashin sa ta nufa...

Tunanin abunda zeyi mata ta farfad'o yake yi kamar daga sama yaji ana qwanqwasa qofar d'akin tare da kiran sunan sa..

Bethaaa..

A hankali da kuma firgici ya furta mhamah?????

Wayyo ubangiji na shikenan tawa ta qare tayaya zan hana mhamah shigowa ina zan 'boye reetha har mhamah baza ta ganta ba???

Qara kiran sa take tana qwanqwasawa,

Shi kuwa duk ya gama tsora ta da kyar yayi ta maza yace mhamah ina zuwa babu riga ne a jikina ,

Oh dan babu riga a jikin ka shine baza ka bud'e min ba na gaji da jiran ka fa'

'Daukar wata rigar yayi ya saka qirjin sa duk a waje lafkeken bargo yaja ya lullu'be ta.. danne duk tsoron sa yayi ya bud'e ta zuba masa ido tana nazar tar sa qasa yayi da kai dan kuwa idan ya bari qwayar idon sa ta shiga cikin tata shikenan komai ya watse ,

Bethaa
Kace babu riga a jikin ka baza ka bud'e qofa ba to yanzu meye marabar ta da babu???

Murmushi yayi a shagwa'be yace mhamaah???

Kai rufe min baki anan meyesa ka bud'e qofar baya ??

Sosa kai ya shiga yi yana qara sadda kan sa qasa yace mhamah to ai na jiqe ne shiyasa kuma naga nan tafi kusa da sashi na,

Runtse ido yayi da qarfi..
a cikin ransa yana me furta Astagfirullah yauce rana ta farko da na ta'ba sambad'awa mhamah ta qarya bana fatan wata ranar tazo wadda hakan zata qara faruwa,

Ohh da kasan na hana ka shiga ruwan sama shine ka biyo ta baya ko??? Kaga ai bazan ganka ba.. to gashi Allah ya kawo ni,

Kama kunnen sa tayi ta murd'e a hankali tana cewa zaka kuma ???

Kanne ido yayi yana cewa Wayyo wayyo bhabhai mhamah ta zata kashe ni dan allah kiyi haquri bazan kuma ba..

Sai kace wani wanda ta kusan cire kunnen🙄,

Sakin sa tayi tace to idan ka kuma kuwa allah ne kad'ai ze cece ka ba bhabhai ba,

To mhamah na yarda,

Qoqarin shiga ciki take tana cewa yauwa dama ina son muyi magana maza zo ka zauna ,

Da sauri yace mhamah dan allah bani lokaci in nutsu kafin zan zo ma har inda kike mhamah yanzu sanyi nake ji,

Bata son takura masa dan haka ta haqura ta fice,

Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa nagode maka Allah,

Komawa yayi wajen reetaj yaga har lokacin bata farfad'o ba shafa kai yayi yana tambayar kansa to yanzu ya zanyi kenan kawai bari in watsa mata ruwa,

Ruwan ya d'ebo ya zuba a hannun sa ya watsa mata amma shiru guntsa yayi a baki ya fesa mata cikin sa"a kuwa taja dogon numfashi,

Zumbur ta tashi tana qwalla ihu ,

Ke kiyi shiru kar mhamah taji manaaa!!!

Tsagaitawa tayi sai kuma ta fashe da kuka tana cewa itace fa itace tazo ta hau jiki na ka gani ka gani wallahi itace bana son ta bana sonta na tsane ta kace ta qyale ni wayyo ammah taaa!!!

saurin hayewa kan gadon yayi yana cewa dan allah kiyi shiru nan fa a gidan mu kike ko so kike mhamah taji ne,

Shiru tayi tana zuba masa ido tace yanzu yalla'bai gidan ku ka kawo ni kuma kace bazan yi kuka ba???

Wannan ce fa ta hau min jiki na,

Cikin sassanyar murya da sigar lumana yace ki nutsu to ki fad'a min wace ce?

Tsutsa mana kawai dan naje wajen bishiya shine ta fad'o min a jiki na ka kalla ka gani fa ta fad'a tana nuna masa hannun ta tareda fashewa da wani sabon kukan,,,

Zubawa hannun ido yayi ga shatin hanyar tsutsar nan yayi jajir ya tashi yayi rututu da alama ma ta dad'e tana tafiya a jikin ta bata sani ba shauki ya d'ebe ta,

Y'ar dariya yayi yace to wannan kuma shine abun kuka harda suma??? Y'ar qaramar hallitar nan do allah ki min shiru mana,

Naqi ta fad'a tana noqe kafad'a gami da 'bere baki tace ni bazan dena kukan ba ka maidani gidan mu mana sai inyi kuka na a can nasan babu me rarrashi na amma ka kawo ni nan kuma ka hani inyi kuka na?? Kukan ma baza a bar mutum yayi a nutse ba ni dai ka maidani gida ,

Saurin janyo ta yayi jikin sa
ya sanya bakin sa kan nata yana sumbatar ta domin hana kukan nata fitowa zazzaro ido tayi a matuqar firgice..
A hankali ta sauke ajiyar zuciya sai kuma tayi laqwas,,,

Qwanqwasawa tayi sau d'aya kawai ta antayo tana cewa shadoww ???? Kazo inji bhai yana neman.... ,,,

Kasa qarasa maganar tayi dan kuwa abunda ta gani yayi matuqar razana ta dan da nan jikin ta ya hau 'bari idanun ta suka qara girma la'b'ban ta na kakkarwa tana girgiza kai da kyar maganar ta fito..

Laa' ayaan laa' ha"ha" ayaaan!!!! A"A ayaan a"a ha'ha fa ayaan....

Fashewa tayi da kuka me tsananin gaske duk jikin ta ya hau mazari,.

A tsananin firgice reetaj ta qwace tana zazzaro ido zuciyar ta na bugun ganguna..

tashi yayi ya nufi wajen ta fuska a had'e yake tambayar ta lafiya ???

A dake tace dama ashe kai d'an iska ne ban sani ba ashe dama haka kake ?? Har mata kake kawo mana cikin gida dama???
Ashe wannan karuwar ka ce dama shiyasa da ta kad'e ni kace ta gudu ko??? ashe dama kai ba mutumin kirki bane kai d'an iska ne ???

Murmushi yayi yace ohh da baki sani ba kenan ? To ai yanzu kinga zahiri ni d'an iska ne me kawo mata cikin gida yanzu wane mataki zaki d'auka?? idan kuma iskancin kike so yanzu zaki ga yadda akeyi,

Ai kuwa sai na fad'awa mhamah yanzun nan kuwa duk sai kun gane kuren ku zaka gane ne mara kunya kawai me mugun hali,,,

Maza jeki idan baki fad'a ba to baki cika ba ,

Ta qara fashewa da kuka ti fice da gudu,
Chapter 43 · 0% Book details