← Book details Sirrin Keta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 47

Sashe 47

Sirrin Keta Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Har wani salon taku yake canjawa dan kuwa jinsa yake tamkar wani sarki Allah Allah yakeyi yaje wajen reetaj taga yadda ya hasko kamar tauraro a cikin kayan da tayi masa kyautar su ji yake yana matuqar son kayan sosai...
Sauri sauri yake dan kuwa yasan idan ta ganshi dasu zataji matuqar dad'i,

Ya saka qafa kenan a wajen gidan yaji wani abu daga sama yayi masa wanka fesss da kyar ya iya bud'e idon sa saboda garin kalar da aka sheqo masa ja da blue da yalo kaloli da dama,

Kallon shaddar sa kawai ya farayi yaga tayi bud'u bud'u d'aga kai yayi sama dan ganin wanda yayi masa wannan cin mutuncin duk da yasan kwanan zancen baze wuce ita ba,,,

Daga ita sai wasu y'an qananun kaya riga da wando gashin nan nata baja baja tsalle take tana dariya cike da farin ciki tace bhaiyaaa!!!!!!!!!!!

Ina taya ka farin cikin ranar holly a dawo lafiya kace ina gaishe ta,,,

A hankali ya tambayi kansa ranar holly kuma a yau ???
Aa qarya take yi yarinyar nan kawai dan taga na sa sabuwar kaya shine zatayi min wannan tsintsinar rashin algaitar???

Sakowa tayi ta zagayo inda yake a gaban sa ta tsaya ta warara masa ido cike da rainin hankali tace sadow ya dai??? Kana sauri ne kaje ka nuna mata kwalliyar ba ??? Har wani cewa suke kayi kyau,,

Murmushi tayi tana Ta'be baki tace ni banga ma wani kyau a nan ba gara ma ace ba kaya a jikin ka wala'alla kafi ma kyau amma ka wani saka farin abu kamar wani fatalwa kai bakaji ma kunya ba wai???
Sai wani d'od'ana ka suke kai kuma kana wani fasa kai to sai ka fita mu gani sai dai wata kwalliyar amma ba wannan ba kuma idan zaka shekara kana yin kwalliya suna cewa kayi kyau to fa ka sani baza ka ta'ba fita da ita waje ba iya cikin gida zaka yi duk abunda kake so amma ka sani banda bare a cikin shirgin mu kar a kawo mana dai y'ar baqa ace a gidan mu,
Kaje ka canja kaya ka saka wanda ka saba sakawa sannan ka fita nasan dai kayi ne saboda ita to kuwa baza ta ga wannan ba tamun dai da bata son gani itace kuma idan kana ganin zaka iya to mu zuba d'an halak ka fasa,

Daga haka ta juya tana karairaya ta bar wajen,

Mhaaaaamaaaaaaaaaah

Ya qwala mata kira da sauri ta tashi tayo waje suka biyo bayan ta rungume ta yayi ya fashe da kuka ,,,

Itama rungume shi tayi tana shafar kansa tare da hura masa iska a kunnen sa har ta samu ya nutsu
Sannan tace bethaa ?? Fad'a min ya akayi meye ya faru haka???

A shagwa'be yace mhamah ayaana ce kawai ta watsa min kala kuma wai bazan saka sabon kaya ba ni kuma gaskiya idan ba dasu ba bazan fita ba kuma bazan qara ko magana ba kuma kuka zanyi har nan da dare kuma mhamah ina son kayan sosai,,,

Shiru tayi kafin ta kalli rooooh tace ina ne ake samun irin wannan kayan ???

Da yake suna shiga lungu da saqo yasa be sha wahalar gano wajen ba yace zanje in siyo masa,

Yayi kyau kayi sauri sannan a kai d'inki a d'inka kuma cikin lokaci yanzu ka kawo masa ya saka ina so yaje masallaci da su,

Kallon sa tayi tace hakan yayi maka???

Shiru yayi sai ma sakin ta da yayi ya koma wajen abbhai ,

Janshi yayi suka koma ciki,,,

Haka yayi ta mazga musu shagwa'ba iri da kala ya hana kowa sakat....

Wayar sa ce take ta faman ihu mhamah ta miqa hannu ta d'auka......

Miqawa sithara wayar tayi tace kice baya cikin yanayi koma waye,,

Da sauri sithara ta kar'ba dan kuwa tasan kwanan zancen samu tayi ta lalla'ba tabar wajen sannan ta d'aga,

Reetaj tace hello yalla'bai ya na jika shiru???

Sithara tace ai bavie in gaya miki bhaiya
Chapter 47 · 0% Book details